NIDA ZUCIYATA complete book (Hausa novel)

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 1n2*

Rabab, "je ki dauko kayan haihuwa suna can sama d'akinta, kiyi sauri don Allah Rabab.

Yanda yake maga sai naji yabani tausayi, na juya na tafi in waigo, sai naga Aunty ta sa hannun ta d'aya tana goge mashi ko gumi ne oho, da rawar jiki ya kama hannunta yana sunbata.

Cikin wata kalar murya naji yana cewa.

"Sannu zuciyata sannu. "

"ka daina kuka kaga kasa har jikina yayi sanyi. "
Aunty ke cewa haka.

Ni kuma na tabe baki nayi gaba. A zuciyata nace, naga Romeo and Juliet, wanda har makarantu in za'ayi misalin 'yan soyayya a darasin English Lectures su ake fada. Na haye da gudu na dauko rio da flask din shayi babba cike da ruwa.

A zuciyata nace. "kilan shi ya cika shi, ina saukowa na iske har sunkai bakin k'ofa yana rike da ita, nabi bayansu bakina a zumbure dan haushi. a zuciyata nace kabar mace tayi tafiya da K'afart ka wani k'ank'ame ta.

Ai sai ga yaya Altab, na doka mani tsawa wai inyi sauri in bude mashi mota, da saurina na bude mota , ina kallo ya kamata suka shiga, nikuma na mik'a mashi flask d'in.

Na zagaya na ajiye rio d'in a gaban mota sannan na zauna mazaunin driver,

Yaya mai fad'an gudu sai gashi yau shike cewa inyi sauri.

Asibitin Dr Hakeem, muka nufa _(Hakeem Specialist Hospital_) dama can Aunty ke awo, nan da nan aka kirashi a waya. Ya iso ina kallon Aunty aka turata d'akin haihuwa, nida yaya a ka bar mu a tsaye.

Na samu damar buga waya, na kira Umma na gaya mata muna abibitin Dr Hakeem, tace to intayin addu'a zatayi waya da gwaggo Hauwa ko zata tsaya wajenta, nace to.

Tun k'arfe 9:30 na safe zuwa 10:00 muke asibitin nan, amma har 12:00 tayi amma shiru,

Na matsa kusa da yaya da yake ta share gumi a fuskarsa, nace mashi zanje in dauko Ilham, daga makaranta amma G.R.A. zan kaita yace "to.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***
Ina shigowa asibiti na samu Yaya da jariri, a rungume cikin farin shawul, da kayan sanyi a jikinsa,

Na isa da sauri, tareda tambayar mamaki.

"Yaya ta haihu?"

Da sauri yak'araso wajena yana d'an murmushi.

"ta haifi d'aya, saura d'aya "

"Namiji ne ko mace? "

"Namiji ne kin ganshi"

Ya miko mani shi yace
"kai wa gwaggo Hauwa shi, kizo mu jira ikon Allah. "

Na amsa da to, na wuce na kaiwa gwaggo Hauwa shi, na koma inda Yaya yake tsaye. Nace

"Yaya ka zauna dan Allah "

Ya zaro idanuwan shi gaba d'aya.

"In Zauna? "

Na tabbata Ikram ba'a zaune take ba, ina zan iya zama? Ai bazan iya tab'a zama ba ita tana a tsaye. In zata kwana, nima zan kwana a haka kedai kije ki zauna ke zama ya gano ni zama bai ganni ba

"Rabab, kin san kuwa yadda yayarki ke cikin zuciyata?"

Na girgiza kaina na wuce wajen gwaggo Hauwa na zauna saboda naga alamar in na tsaya kusa dashi to sai fad'a masa bak'ar magana. tunda ni bana son hirar soyayya

Can baifi zaman minti goma ba aka ce ina Altab yake? "

Yace "gashi "

Wata sister ta miko mashi wani jaririn.

Na taso da sauri nace

"Yaya mace ko namiji? "

Yace "0ho. Sister Mace ce ko namiji? "

Tace "mace ce wannan. "

Murna kuwa kamar ya Saki jaririn ya damko bandir d'in kudi 'yan dubu d'aya ya bata

Duk wanda zai wuce sai ya zari kud'i ya bashi saboda murna, can sai ga Aunty an turota za a kaita d'akin hutawa, yayi sauri ya isa gadon da take ya dafa kanta tare da cemata.

"Sannu zuciyata "

Nikuwa nadan dafa gadon da take, ta zuro hannu ta kama hannuna.

Hawaye zuka zubo a kuma tunta na rike hannun sosai tare da ce mata.

"Sannu Aunty "
Ta amsa da. "yawwa"

Muka isa d'akin hutawa, ika kwantar da ita daga gani ba wasa kasan Aunty tasha wahala.

Ni haushi yasa nafita daga d'akin, yanda Yaya ya kankame gadon tamkar ya had'iyeta sai mutane ke nuna shi.nafito waje naci gaba da buga waya, duk wanda nasan yanada hakki a gaya mashi na gaya mashi. Indai da lambar shi a wayata.

Ina nan tsaye ya fito da sauri

"ke jeki wajenta, bani key din mota "

Yana ta sauri kamar zai ruga bakin shi kuwa yakasa rufuwa. Na mik'a mashi da sauri, ya kar'ba

Nikuma na koma ciki na zauna gefen gado kusa da kafafuwan ta na dafa k'afar ta.

"Sannu Aunty "
Tace "yawwa kema sannunki na gode. Allah ya yi maki albarka
Nace "Amiin Aunty "

Duk na fada mata masu gaishe ta, nace "Abba ma gashi nan zuwa "

"Tayi murmushi, da gani na k'arfin haline. Tace

"ina Abban Yasmeen ya tafi? "

"wallahi ban sani ba yace dai nabashi key din mota na bashi k'ilan kayan tea, d'in ze d'auko mun manta dasu mai makon yace naje na dauko "

Tayi murmushi "yanzu haka in don Abban Yasmeen ne ya Manta dake "

Nima nayi murmushin "zai iya Mantawa.kina ganin yadda yake miki nifa kunya ta kore ni da haushi sai mutane keta kallon ku

"Burge su muke "
"Kaji Aunty "

Rabab ki sassauta wa zuciyar ki tsanar aure. "

Na kawar da fuskata "Aunty, kiyi hakuri, wallahi na daina tsanar Yaya tunda kika gaya mini jiya, ni dai ya daina kama ki cikin mutane kada ace maku yan iska "

"Rabab kenan...........
[5/1, 10:14 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*page 3n4*

"Rabab kenan, to zan fad'a mashi. "

K'iri k'iri Yaya yak'i tafiya gida, har k'arfe 12:00 na dare, daga gani daga ita har shi suna buk'atar futawa, ni kaina ina son na huta.

Da k'yar ya yadda can wajen 1:00 na dare, har ya juya zai tafi. ya dawo ya sunbaci goshin ta, sai ta rik'o hannun shi. Yayi saurin juyowa.

"Twin's din fah? "

Yadawo ya sunbaci ko wannen su, sannan ya k'ara sunkuya wa ya sunbaceta.

"Dan Allah ka zauna ka huta. gobe zamu tafi gida. "

"ki daina had'ani da Allah, kin san dai bani iyawa."

"Altab."

Ya juyo da sauri cikin wani yanayi na tashin hankali, ko nidai naji gabana ya fad'i saboda ban tab'a jin ta fad'i sunan shi a gaban shi haka ba.

"Lafiya? " ya tambaya.

"Lafiya k'alau don Allah ka yafe mani koda na sab'a maka a bisa kuskure ko sane "

"A kullun kalamin amsarki d'aya, na yafe maki kuma ke bakya laifi, ni ko kurkuren ma da wuya ayishi,


sai da safe ko? "

Ta amsa "Allah ya kaimu "

Ya lakaci hancin ta.
"Har kin tayar mani da hankali yaushe rabon da ki kira sunana, nima saina rama Ikram "

Sukayi dariya, nima har suka bani dariya basu tab'a abunda nayi dariya ba sai wannan.

Har ya juya ina dariya. yadaga hannu kamar ze dakeni

"shine kike mana dariya ko "

"Yafada yana dariya.

"Ga amana nan
"yaya ban Karb'a ba"
"keeee 'yar k'anwale "
"Allah yaya zan dai kula dasu kamin kazo "
"yayi dariya yayi gaba"

Ni kuma na janyo kujera na zauna gaban ta, wajen k'afafunta. Na dinga matsa mata su har tayi bacci. Ita kuwa gwaggo Hauwa dama tuni tayi bacci itada twins d'in a dayan gadon.

A inda nake zaune na kifa kaina, nima sai bacci. Can cikin bacci naji tana salati. Nayi sauri na tashi na rik'ta

"Aunty lafiya? "
"lafiya kalau k'anwata farkawa kawai nayi "
"Ko zaki sha shayi Aunty? "
"Eh to bani insha "

Na had'a mata tare da mik'a mata tasha abinka da asibiti har dare muka dinga hirar mu.

Na tashi na dauko yaran, ta karbe su ta rungume su tareda fito da na fulanin ta gaba daya kowa ya kama daya yana sha

"Aunty sun kawo ko? "
Tace "nima yanzun naji sunkawo shine na basu su sha"

Suka sha daidai yanda suka samu, sannan na karbe su na mayar dasu gurin gwaggo Hauwa,

Nadawo na zauna tace inje in kwanta. Nace mata nan ma ya ishe ni Aunty.

Tace "Rabab, nayi addu'a a lokacin da nike nak'uda, Allah yabaki miji na gari, na kuma roki Allah ya cire maki tsanar aure a zuciyar ki.

Da tsanar mijina bana son inga kuna zaune haka tunani kala kala nikeyi don Allah ki sassauta bashida amfani Rabab, gashi yanzu 'yan biyu na haifa ina buk'atar taimakom ki. Ki ki zauna mani na shekara daya har sud'an yi wayau "

"Aunty makaranta fa? "
"Basai ki dinga zuwa daga nan ba "
"Aunty kwanta ki huta dan Allah "
"Zan zauna idan har Abban mu ya amince "

Naci gaba da matsa mata k'afafu har k'arfe 4:00 na asuba nima na kife kaina sai bacci.

Jin anata salati kanmu, yasa na tashi a firgice, Yaya da jama'a akan mu na tashi na ja da baya saboda Dr yazo. Atake haushin sa ya saukar mani daga zuwan shi zai tara mana jama'a

Kamar ance in kalli gadon, sai naga Aunty kwance cikin wani mugun jini cike da gadon ta.

Na Saki wata mahaukaciyar kara. Na gigice. Wata mata ta rik'eni gam.

Ihu nake, cewa nake, sake ni in ganta na kubce na tafi da sauri. Ban isa gadon ba.

"Sai naji dr yace "
"Allah yayi mata cikawa"

Kamar inyi tunanin mema naji ana cewa? "

Sai kawai naji yaya ya saka k'ara ya sulale a k'asa mutane suka yo kansa amma ko motsi bayayi

Ni kuma nayi sauri nje na kama gadon ta ina cewa

"Dan Allah Aunty ki tashi
Kar kibar Yaya ya mutu
"Dan Allah ki tashi

Nan aka samu mutane suka kamani inata kiran sunan Aunty. gwaggo goye da d'a d'aya d'aya a kafadar ta tana ta kuka

A nan dr ya karbi wayana ya kira.

Ban fahimce ma me ake cewa ba sai dai naji yana cewa.

Mahaifinta, to yawwa daga asibitin da ta haihu ne Mum kwantar da ita lafiya amma yanzu Allah yayi mata rasuwa."

Iyakar nan naji nasa k'arar ihu, na na fizge na ruga aguje, do kyar aka kamomi ina ina jin daga nan ban sake sanin Inda nike ba.

Sai dai naji ana cewa
"Sannu Allah sarki, ta farko "

Nayi saurin tashi zaune "ina Aunty, ina Yaya, ina suke?ku fada mani.

Na Mike zan tashi tsaye aka rikeni gam can daga saman kaina naji anacewa

"Sannu. Tsaya kada ki tashi ki fadi yayan ki yana nan Aunty kuma tana can a falo kwance

Na mike "ku sakeni in gano Aunty

Sai alokacin ansa hannu an d'agoni. hawaye ne masu gudu da sauri ke fira daga idanuwan ta. Bata iya magana ba sai girgiza min kai.nakara fadawa jikin ta jikin ta muka rungune juna gam sai alokacin naji bakin ta yara magana

"Ikram ta tafi "
Nayi saurin dagowa nace "dan Allah umma karkice min Aunty ta rasu "
"Rabab duk musul mi dolene yayi imani da k'adda kiyi hak'uri wanda yafimu sonta ya karbi abarsa .babu abunda take bukata illa muyi mata addu'...... Bata karasa ba kuka mai tsanani yarufeta "

Nadubi Umma nace "Umma da gaske ne Aunty ta rasu.... Nan na k'ara sulalewa ak'asa....


Farkowar da nyi nan naga suma su Aunty K'adra sun iso daga kaduna, na tashi na isa inda take tsaye tana kuka na fada mata.

Muka rungume juna muka dinga kuka,wasu dangin Ummu suka taso suke rik'e mu aka dauko jariran aka bai wa Aunty K'adra.

Za a iya samun mimtuna kamar talatin da zuwan Aunty k'adra, sanna tace intaso inraka ta gurin Yaya Altab, haka muka tafi munkai mu goma, muka shiga wajen Yaya Altab,

Amma mutane ke saman kanshi ana tofa masa addu'oi, da alama bai san abinda sukeyi ba.

Wannan dalilin yasa dole muka koma cikin, ni kuma sai naji hankalina ya k'ara tashi

_"ki d'auki Altab shine na farko a duniya mai k'aunar yayar ki ban da iyayen mu, idan yanzu na rasa Altab, ki d'auka na rasa zuciyata kwata kwata_ _kada mafarkinki ya karanto maki ranar da d'ayan mu zai rasa d'aya wato ranar dani zan rasa Altab, koshi ya rasani_ _wallahi sai kin tausaya duk wanda aka bari a doron duniya, tausayi irin mai bin jinin jiki_ _ina so ki fara addu'a daga yau Allah yasa ki dace da miji kamar Altab_

Maganar da Aunty Ikram kenan tayi min a daren da zata haihu. na kara kudundume kai na cikin hijab a saman gado amma na k'ara sakin kuka. Ina tunanin magan ganun da mukayi da ita


Lallai na yarda da maganar Aunty, yau ga Yaya Altab, a doron duniya ya zama abin tausayi.

"Rabab da zakiyi min wata alfarma da nayi alfahari dake a matsayin na dace da k'anwa mai k'aunata. "

"Tame Aunty? Ke bakya gajiya, kiyi bacci ki tuna a gadon asibiti kike. Kina buk'atar hutu."

"Ai dama magar hutu zanyi maki, amma wanda in an kwanta ba a tashi, sai dai yaya zakiyi da yaran nan da Altab. ?"

"Aunty kiyi bacci kawai, in Mum koma gida mayi maganar "


"Gida? Aini ai ni gidan da zan tafi ba a dawowa balle har a tattauna da d'an uwa, Altab zai shiga wani hali gashi ba mai kula dashi."


"Aunty dan Allah dan kin haihu sai yaya ya shiga wani hali. Da da kike haihuwa fa ya taba shiga wani hali ?"

"Rabab kina bani tausayi. Duk ranar da kika rasani nida mijina duk da kinada iyaye. ban taba ganin k'anwar da take tsanar mijin 'yayar ta saboda yana nuna mata soyayya.

"Aunty Allah zan tafi gida inbar ki. na fada maki na daina tsanar mijinki. "

"K'ilan ko? "

Na girgiza kaina,

To ko Aunty so take a ranar ta fadamin mutuwa zatayi, ni kuma na kasa fahimtar ta, ire iren wainnan tunanin suka damu zuciyata.......
[5/1, 10:14 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 5n6*

A zuciyata nace, dole Aunty ta tausaya mijinta, saboda tasan ba macen da zai samu kamar ta, ya dinga mak'ale mata kamar dank'on jikin littafin kama b'era.wani lokacin, idan Allah ya sa nakai idanuwana kansu, ko tayi masa rakiya ya mak'alk'ale ta, yana sunbatar ta koya rungemeta gam,

Zan iya cewa yamma tayi. a lkcin ne aka kaita gidan ta na gaskiya,

Ina kwance nan abinda kad'ai ya tashe ni daga inda nike kwance, sallah danayi har sau biyu.

Sai naji anata surutun. Yaya Altab, baya gane kowa, gabana naji ya fad'i, na tashi zaune, amma sai naji inason zuwa in duba shi.

Na mik'e na sunkuya na d'auki furar da aka Kawo mani insha, wacce nayiwa kurb'a d'aya na ajiyeta saboda tsananin zazzabi da nike ji amma na kasa fad'awa kowa.

Ina shiga d'akin da Yaya Altab yake, naji wasu sababbabin hawaye sun cika idanuwa na yana kwance kudundume kamar wani k'aramin yaro.

Na isa nasa hannuna daya na dafa goshin shi, nima haka naga Aunty ikram nayi masa idan yana bacci, ko idan bashida lafiya, yayi wani saurin Bud'e idanuwan shi.

"Yaya tashi ka sha fura, kada yunwa ta shige ka.

Ya mayar da idanuwan shi ya lumshe, hawayen da ke zuba idanuwan shi suka k'ara sauri.

Na k'ara shafa gashin kanshi kamar yadda naga Aunty nayi masa. Ya bude idanuwan shi

"ki daina, kina tuno min da abunda ya wuce, wanda yake tashin hankali a gareni. "

"Yaya kayi hakuri nima nasan dole ka dinga tuna Aunty,

"kasha furar dan Allah "

"bari in kira a tashe ka daga kwance,sai kasha."

"Allah ban iya sha, salati kawai nike yi daga kwancen nan, saboda jiran tawa mutuwar. Saboda tunanina rana d'aya zamu mutu nida Ikram."

"Yaya bazaka mutu ba, in sha Allah sai kaga girman yaranku."

"ni kad'ai Rabab.?"

"Ga ni! Ai ni bazan tab'a yin aure ba, in ma yakama dole sai naga girman 'yan biyun nan. "

Ya kalleni, kallon da yake mani, da yayi mani wannan kallon sai kaji yace mani shasha sha, amma yau sai naga ya girgiza kanshi daga kwancen.

Watau sakar ya ta mishi magana, muna haka sai ga su Yaya furk'an sun iso daga Abuja. Nayi sauri na isa wajen shi na fad'a jikinshi na saka kuka ya dago ni. Idanuwan shi cike da hawaye

"yaya Altab din? "
"da sauki sai dai ya ki cin komai ga fura nan ku bashi. "

Yaya, ya karb'a ni kuma na wuce cikin gida..


A tak'aice kwanaki ukun nan Yaya Altab kwance ya yisu haka nan dai ake kawo shi k'ofar gida a kwantar dashi. Saboda jama'a na son yi mashi gaisuwa. Da k'yar yake magana.

Ni kuwa zazzabi ya takura min.haya niyar gidan mutuwa ya hanani ingaya ko Umma, sai dai in karb'i panadol Extra, wajen Aunty fa'k'a in sha, haka kuma Ilham, baby n Aunty ta farko duk da yarinya ce dole ka tausaya mata. Duk inda na nufa tana biye dani in kuwa bani na bata Abinci ba to kuwa bazata ciba,

Haka wajen kwanan mu d'aya da ita da 'yan biyu, kuma na hana a bawa kowa ya shayar dasu kuma Abba ya goyi bayana, asibiti kawai aka kaisu aka rubuto masu madarar da xa a dinga basu da sauran magun guna .
Harma na cewa Abba in angama zaman makoki, abawa Umma na mijin, ni in rik'e macen, yace makaranta fa nace masa zan samu 'yar reno.

Shikuwa Yaya Altab ba bakin magana....

K'ara ma mahaifiyar shi taso a bata d'aya. Nan aka taru a kace a'a ita da take fama da ciwon sugar, yaushe za a had'a ta da reno. Haka suka hakura,

Sai da akayi kwana bakwai ana zaman makoki, sanna kowa yayi sallama ya tafi nashi gidan, haka yan k'ofar gida maza suma suka tafi, sai dai gidan gaisuwa ba za a rabashi da jama'a jifa jifa ba,


Ni da yaran Aunty kuwa, muna nan gida ni naci gaba da kai Ilham makaran ta do motar Abba ko ta Umma,

Jarirai kuwa Sun sha suna, 'yar macen sunan ta Arwa, namijin kuwa sunan shi Anwar,

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Yau zan iya kiran ta juma'a, itace ranar da Aunty ta cika sati biyu da rasuwa, haka mukan ga Yaya yazo gaishe da su Abba duk d'an kwana biyu, amma yau kwanan shi hudu bai zoba,

Bayan na d'auko ilham daga makaran naje na samu Abba nace zan shirya yara zan kaisu gidan baban su yawon juma'a, daga nan zamu wuce gidan ka kanninsu. Abba yace adawo lafiya

Na shirya su tsaf na d'auki mai aikin Umma muka tafi da ita.

Gidan Yaya Altab, muka nufa, mai gadin gidan ya dinga murna daya ganmu. Shi ya d'auki Anwar, bayan nayi parking din mota. Ya dinga gaishe ni da Far'arshi,

K'ofar falon k'asa a bude take muna turawa tareda sallamar mu.

Yaya Altab na gani kwance a doguwar kujera, yayi irin kwanciyar na ta wayyo ni Allah na, rubda ciki yayi hannun sa d'aya a k'asa yake, tamkar wanda yake fama da wata matsanan ciyar rashin lafiya cikin tashin hankali mukayi inda yake kwance.

Ya d'ago inda yake kwance ya kalle mu, yayi yun k'urin tashi amma ya kasa nayi saurin isa na rik'eshi, mai gadi ne ya fara magana,

"Wallahi Aunty tunda yallabai ya dawo gidan nan ko ina bai fita ba. Baya cin komai, ko nazo na matsa mashi. Sai dai yacemin dan Allah in k'yaleshi. Aunty kin ga wannan kukan shine abincin shi, kayan nan kuwa na jikin shi Sun yi kwana hudu a jikin shi.

nima Nawa hawayen suka dinga tsiyaya haka itama Ilham tahau kuka Tana kira Daddy _Daddy, na cewa mai gadi ya bawa mai aikin Umma Anwar, ya kama yaya yaje yayi wanka.

Bai yi mana gardama ba. da yake mai gadin yaro ne, saboda haka tsab ya iya kama shi, nikuma na shiga toilet na hada masa rowan wankan a bokiti, haka ya shiga nikuma na tafi, nace da maigadi ya tsaya idan ya gama ya rikoshi.

Na nufi sama, na samo mashi T. Shet, da wando iya gwaiwa wanda duk aljihuna ne ajikin shi haka dai naji suna kiran sunan shi (Three quarter) na sauko na bawa maigadi, nace in ya fito ya bashi ya saka.

D'akin k'asa na kai yaran, d'akin da yake da sunan d'akin Aunty na k'asa.

Ni kuma nayi kitchen nayi gaggawar kunna gas, na sa mashi d'an ruwan shayi saboda yunwar da take nad'e a cikin sa. Yadan fara gasa cikin shi da d'an ruwan d'umi.

Bayan ya samu ya zauna ne na kawo mashi kofin shayi, na mika mashi. Amma hawayen furkar shi Sun hana yasha. Na matsa na zauna gefen shi na karbi kofin shayin na dinga bashi yana kurb'a. Idan ya d'aga hannu almar ya isa sai ince sai ya shanye sa gaba d'aya, haka ya hakura ya dinga sha yana kuka, nima kuka har ya gama na kama shi na kwantar dashi.

Na nufi kitchen na d'ora abin ci tuwon shinkafa miyar kub'e wa d'anya, itama nasan Yaya na sonta balle idan an saka ayayo, take na fita na baiwa mai gadi kud'in kub'ewar da ayayo da d'an guntun cefane.

Ina girki ina gyaran gidan. Saboda da alama gidan baya ganin shara haka kuma ina had'a kayan wanki, wanda kayan yaya ne dana Aunty, da wasu na Ilham da aka tara tun kafin rasuwar Aunty.

K'arfe biyu saura agogon k'asa ya nuna.

Yaya ya shigo, yazo ya tsaya yaba kallon mu. na d'an sannan nace

"Sannu Yaya "
Ya amsa da "Yawwa "
In d'aga kaina naga yana ibadar nace

"Yaya Anwar ka bashi abinci Kai ma "
Banyi minti uku da mik'a mashi ba sai naji yana magana

"Me yasa? Me yasa Ikram kika tafi kika barni alhalin kin san muna buk'a tarki nida yarana?

Ya saka kuka mai k'arfi, na ajiye Arwa, na iso na karbi Anwar daga hannun shi.

Yayi saurin durku shewa k'asa da gwaiwowin shi biyu ya dinga doka hanna yenshi k'asa yana kiran

"Why? "
"Why? "

Nayi saurin ajiye Anwar a saman kujera nayi saurin rik'e hannuwan.

"ki k'yaleni Rabab mutuwa tafi rayuwata "

"kada kayi sab'o sannan kada ka zamo mai rashin godiyar Allah, Aunty ikram mace ce idan Allah yaso yanzun sai ya had'aka da wadda tafi Aunty komai da iya komai. "

Ya dinga girgiza kai alamun a'a

"kada kace haka Yaya, Allah fa akace, amma yanzu ka dubi wainnan yaran waya isa yace ba naka bane, ya d'aukar maka d'aya yabaka biyu baki d'aya."

Na amince da magar ki Rabab, amma ina ganin samun mace kamar Ikram da wahar gaske acikin mata, Ikram tana zaune dani da zuciya d'aya, Ikram babu ruwanta da inyi arziki ko talauci, ita ni take so. ba komai nawa ba bazan taba iya lissafa maki halayyar yar'uwar kiba.

Ya saki wani irin jiniyar kuka mai shiga rai tamkar wani k'aramin yaro nasa hannu d'aya na d'ago fuskar shi ina share mashi hawayen.

"idan kace zaka dinga kukan mutuwa har ka mutu bazaka daina ba, Aunty a halin yanzu addu'ar ka kawai take nema, sai kuma ka rik'e mata amanar 'ya 'yanta ka basu tarbiya ta gari.

Yakama hannaye na duka biyun ya rik'e

"Na gode Rabab dan Allah ki yafemin abubuwan da nake maki baya, ba ina nufin na tsane ki ba. Ina son inga kema kin zama yarinya tagari kamar 'yar uwarki. Ashe kina da hankali gane kine banyi ba wallahi Rabab, ina son inga na daina kukan nan, amma na kasa, bani ke yin shiba shi ke zuwa kawai "

Ya rage sautin muryar shi ta koma ta ban tausayi....

"Rabab dan Allah ku dawo nan gidan keda yara, k'ilan ganinku ya rage mani wani bala'in da nike ji a cikin zuciyata da gangar jikina. Kinga gashi yanzu daga zuwan ku har na iya zama harda tafiya.....

*NOTE*: *my friends ina jiran comment d'inku akan magar da Altab, yayi wa Rabab* *miye ra'ayinku akan maganar kun amice Rabab ta dawo gidan* *???*
[5/1, 10:17 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ


*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*NOTE:* _My Friends naji dadin comment d'inku kuma hakan ya nuna min kuna tare dani nima ina tare daku, ina gdya da soyyar ku gareni..._
_Sannan ina gdya da sak'on nan ku gareni, taku mai k'aunar ku Precious girl_


*Page 7n8*

Nasa hannu na d'ago fuskar shi da ke sunkuye, hawayen fuskata suka k'ara tsiyayo wa.Atake na tuna yanda Yaya Altab, ke taku acikin gidan shi. Namiji cikakke amma kalli yanda ya koma. Yayi bak'i ya rame cikin sati biyu kacal. Nace

"Yaya kaje ka tambayi Abba da kanka, ko ka tura Abban ku. K'ilan Abba ya yadda. Amma kasan idan nayiwa Abba magana ba yadda zai yiba. Balle yasan ba shiri muke da Kai ba abaya. amma zan yi mashi. Kaima kayi mashi sannan kasa Abban ku yayi mashi.

Idan ya k'i nidai shawara ta had'a kayan ka ka koma gidan ku kawai, ko kasamu dattawa biyu ka dauke su aiki ka dauko Ilham ka dawo da ita gaban ka, kabar 'yan biyun wurina, ta haka zaka samu sauk'i. Amma ka k'aro wani mai gadi tsoho, sai ka koyawa wa d'ayan mota ya dinga Kai Ilham makaranta da d'auko ta. Nikuma nayi alk'awalin rik'e maka su Arwa da Anwar amana.

Sannan duk juma'a zan dinga kawo su dan su saba da y'ar uwarsu, kuma kaima ka dinga kaita gida tana ganin su.

"Rabab, Ilham na buk'atar tarbiyya irin ta uwa. Saboda ta fara girma. "

"To ya kake so? Aunty dai ta tafi tafiya ta har abada, Aunty bazata tab'a dawowa ba."

Na d'aure fuska tare da sakin hannu wanshi na mik'e tsaye.

"Zanji haushi yanzun, zan Tsane ku a yanzun Kai da duk wadda zaka auro a wannan lokacin, zan kuma ce kaci amanar Aunty. Satin ta biyu kayi maganar aure. "

"Rabab wazan auro no kuwa yanzu? Da kinji yanda na tsani aure a zuciyata da bakin Man wannan magar ba. "

"Too me kake nufi da Ilham tana buk'atar uwa.?"

"Wallahi abinda nike nufi, ki dawo ki kula da ita, ko ta zauna wurin Umma. "

Na jiyo nayi murmushi cikin kuka....

"har kasa naji dadi na zata zakaci amanar Aunty. "

"Allah ya kiyaye ni da aure.... "

"Ni ban hanaka aure ba kadai bari ta shekara biyu ko? "

"kima daina maganar. "

"Na daina Yaya."

"Yaya dan Allah ka dinga cin abinci, ga ruwan shayi can da zuba maka a flask, da ka tashi da safe ka had'a ka sha, mu zamu tafi. Sai kuma juma'a in Allah ya kaimu."

"Zan zo gobe ki gaishe mani dasu Abba da Umma..

Ya biyo mu a hankali saboda har yau tafiyar shi ba k'arfi sosai yayi mana rakiya har muka tashi mota, shida mai gadi suka dinga d'aga mana hannu.....

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Muna isa gida Ilham ta ruga wajen Umma tana ta bata labari....

Bayan Ilham ta tafi d'akin Umma tana cin abinci...

Na Kalli Umma duk da ba wani goyon bayan duk wani shiri in dai nawa ne take yiba. Amma ganin wannan ba nawa bane yasa na fara yimata magana

"Umma, Allah Yaya yana neman taimako. Kin ga kuwa yanda muka iske shi? Wallahi idan kika ganshi sai kinyi masa kuka. "

"Lallai yau nasan anyi mutuwa, wai Rabab yau keda bakin ki kike fad'ar tausayin Altab, mutu Men da kamar kuga hanjin juna. "

"Umma dan Allah ki ture wannan. Yanzun ma ba wani jinshi nike a jikina ba, wallahi tausaya mashi kawai nike. "

Na kwashe labarin duk yanda na sameshi na gayawa Umma ita ma har hawaye sai da tayi. Ta girgiza kai.

"Allah Rabab, shiyasa har gobe ina tsoron yi maki aure, saboda halayyar ki, to kinga iron yanda ake son mace ta zama gurin mijin ta, ko bayan ranta zata samu yabo da k'auna a wajen Mijin ta, ai Ikram ban tab'a haihuwar 'ya kamar taba. Hankali, hakuri, tunani, sanin ya kamata.

Haka shima Altab, d'in ya iya tafiyar da rayuwar ta, suka zauna lafiya, kiga fa har aka gama zaman makoki a kwance yake, shiba mutun ba shi ba gawa ba. Kin ga kuwa dad'in zama ya kawo haka. "

"Umma, ni kibar maganar aure. Kin San ni idan da abinda na tsana a duniya, bai wuce aure ba. Ko ince maza gaba d'aya kuma duk Yaya Altab ya janyo masu.

Mugu ne nan da kike ganinshi. Ba irin gallazawar da bai yiwa Aunty ba. Hakuri kawai take dashi. "

"Wace irin gallazawa yake yimata Rabab? Mudai bamu taba ji ko gani ba."

"Umma kenan, nifa ke zaune gidan su, tun ina yarinya ta. "

"Shin nace wace irin gallazawa? "

"Umma duk inda Aunty ta sa k'afa Yaya sai ya bita, baya barin ta sakewa.gashi k'ato da shi amma sai ki ganshi kwance saman cinyar ta. "

"Too ke kuma tsaye kike masu, ko lek'en su kike? "

"Haba Umma in lek'e su? Allah ya kiyaye nida ko ganin Yaya bana son yi balle har in dinga lek'en su, idan anyi akasi dai... "

"yanzu dai ki tashi kije kiyi sallar isha'i, wannan zancen naki ya isheni haka nan. To meye na tausayin shi kuma yanzu tunda wacce yake gallazawa ta mutu ya huta. "

"Ya huta? _Innalillahi_,Allah Umma idan Yaya yazo nan sai kinyi mashi kuka. "

"Tashi kije kiyi sallah mace. "

"Ai dama nasan Umma ke ba saurarar matsalata kike ba. "

"E, wanda yake saurarar taki yana masallaci, yanzu zai dawo sai kije ku k'arata can.."

Na tashi ina zunbura baki, nayi gaba, ban da surataina da nike tayi akan yadda Umma ke yi Mani, ni tamkar ba ita ta haife niba, sam bata yaba mani, akan komai sai kushe ni..

Bayan duk na kammala komai ne, cin abinci, sallah, basu Arwa da Anwar, abin cinsu na ajiye su bayan sunyi bacci, na tafi falon Abba, na zauna na bashi labarin duk yanda muka samu Yaya.

Ya girgiza kanshi alamun tausayi.

"To yanzu Abba ba wani taimakon da za ayi mashi.?"

"Yanzu Rabab, ya kike ganin za ayi? Ai kin San ni dake bata b'aci. "

"Abba ya koma gidan su sai abashi 'yar sa daya, asamu masu kulawa dasu dattawa. "

"To me yasa baki yi masa wannan maganar ba? Ai yanzu zai fi d'aukar maganar ki... "

"Saboda me Abba.? "

"Saboda yasan kina kulawa da 'ya'yan shi. "

"Nayi mashi. Amma amma shi sai yace wai ni ya kamata inje in zauna sai a sama mani masu taya no aiki. "

"To ya kika ce mashi.?"

"Cewa nayi yazo ya tambaye ka ko ya turo Abban shi ya tambaye ka. "

"Lallai gaskiya, ni ba zan amince ba kuwa. "

"Allah sarki Abba saboda me.?"

"Saboda nasan ba k'ya jituwa keda shi, Auntyn ki ma na nan ya aka k'are, balle ku k'adai kullun fad'a kamar ba Mijin yayar ki ba. "

"Allah Abba yanzun ba zan yi mashi ba, dama can shiya jani na tsane shi. "

"Da yayi maki me.? "

"Da yake gallazawa Aunty. "

"Altab din.?
"kana mamaki ne Abba.? "

"gaskiya yanda na d'auki Altab mutumen kirki. "

"Kama daina bashida mutunci kwata_kwata."

"Subhallah, har ina kwadayin nema masa 'yar abokina.?"

"Ai Abba babu mai iya zama da Yaya Altab, a matsayin matar shi sai Aunty. "
"me ye halayyar shi.?"

"Mhn, idan na fara fad'a maka sai kayi mamaki. "

"Gaskiya, ai har na fara mamakin tun a yanzu. Amma bani labari Auta inji, har kinsa ma naji bazan bashi jikokina ba. "

"Wayyo, Abba ai yanzu ya zama abun tausayi. Yana buk'atar taimako. "

"To ina jinki. "

"Mhn Abba, ka dai tambayi Umma, ai na fara bata labari tace intashi in taba waje. "

"Gaki a gabana wace Umma can.? "

Umma ce tayi sallama ta shiga da farantin kayan abinci a hannun ta.

"Abba kaci abinci idan Umma ta fita zan dawo in baka labarin.. "

"To shikenan Auta ina jiranki zanyi saurin sallamar Umman ku tun da ma ba kiran ta nayi ba. "

Nidai bance komai ba kada Umma ta dake ni. Na tashi na fecewa ta.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Tun karfe 5:30 na safe nike tashi. Dama tun a gidan Aunty na saba da hakan. Saboda gudun makarantar yara, saboda nasan makaran tar su akwai tsanani. Na kammala masu, mun fita za mu tafi....

Sai naga su Yaya Altab, sun tsaya a mota, k'anen shi Tarik' shiya turosu. Shida Abban su. Dama Abban su ya iya sammako, idan zai shiga unguwa, kodan yana tsoho.

Nayi saurin tsayawa da mota, na sauko da yaran duka muka zuk'unnan muka gaishe da Baba nida Ilham. Ya dafa Kai na yace mani.

"Allah yayi maki albar ka kinji.

Nace "Amiin."

Na waiga na gaishe da Yaya Altab, sannan Ilham itama ta gaishe shi. Tarik' kuwa ta d'auke shi tamkar abokin wasan ta sukayi wasar su sannan muka wuce da kular ta a hannu.

Banyi mama kin ganin su ba, saboda nasan maganar data kawosu baya wuce maganar da mukayi nida Yaya, na tafi ina addu'ar Allah yasa Abba ya amince.

Daga b'an garen Abba kuwa, Abba yayi manyan bak'i, tunda safe haka 7:30am,da kad'an ta wuce suka shiga ciki bayan Sun gaisa Tarik' ya fita ya jirasu waje, Altab shima ya gaishe da Abba ya tashi zai fita...

Baba Alhaji yace zauna ayi a gaban ka.
Alhaji dama d'anka ne ya same ni yau da safe da wata muhimmiyar magana, amma ni ba sak'on shi ya kawu niba, nawa sak'on na zo dashi. Shi sak'on shi inzo in tambayeka kabashi yarinyar nan k'anwar matar shi ta zauna da yaran shi, da shi asamo masu masu aiki a had'a su saboda dalilin ta saba da yaran kuma yaran zasu Manta da mutuwar uwar su da wuri. Saboda yanda take son su da kulawa dasu tun 'yar uwar ta na raye, har yau bata canza ba, shima ya rage zaman kad'ai ci, na amince da maganar d'anka. Amma ni nawa sak'on yasha ban ban dana d'anka

Ni da naso nawa sak'on, sai an kwashe 'yan watanni sannan inzo infade shi tare da neman alfarma, amma tunda shi ya fara fad'ar nashi sak'on ni ma ga Nawa, adai yi hak'uri kada aga mun taru munyi rashin hankali daga rasuwa sati biyu kacal.

Alhaji a gaskiya ni ban amince da zaman yarinyar ka gidan d'ana ba wata magana ba, magana kuwa itace, ina neman wani irin a hannun ka, saboda munji dad'in wanda ya wuce...

Ina nufin a had'a yarinyar nan Aure da d'anka, sai taji dad'in rik'e 'ya 'yanta da hujja, amma ya ka gani, shi kanshi banyi shawara da shiba, gaban kaina kawai nayi. Kuma na dad'e da tunanin a zuciyata.

Tun ranar da akayi mutuwar, sai dai nayi hak'uri sai mun d'an warke da ciwon mutuwar tukunna.

Yayi shiru, Altab kuwa daga gani kasan hankalin shi ya tashi matuk'a.....
_To fah, friends kunji shin kun tashi aurar da 'yar ku Rabab ga Altab???_

_ku kasan ce tare da alk'alamin Precious girl_✍
[5/1, 10:17 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

_Wannan page d'in naku ne 'yan k'ungiyar IWA, da duk wani masoyin NIDA ZUYATA, kuyi yanda kuke son yi dashi_๐Ÿ’œ

*Pege 9n10*

"To Alhaji, kasan dai Kai mai iya aurar da 'yayana ne ko ina raye ko bayan na mutu, to balle Kai da kanka kazo nema, bama wani kazo nema wa ba."

Ya d'an yi shiru, Wallahi Alhaji ba abinda zaka zo nema wajena in hanaka, amma ina shakkun had'a auran nan, saboda d'iyar nan taka da kake ganinta nan ba abinda to tsana sai abu biyu, Wato aure da d'ana Altab, gashi nan a gaban ka ban San abinda ya had'a suba, tun tana 'yar matashiya, ba abinda zaka fad'i kaga b'acin ranta kamar kace mata aure, sai kuwa kace Altab."

_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,_ me yayi zafi haka Altab.? Inji Baba Alhaji.

"wallahi Baba bansan abinda nayi mata ta tsane ni."

"K'arya kake mutumen banza, da akwai dalili."

"A'a Alhaji babu wani dalili mai k'arfi, jiya tazo nan Tana son gaya mani dalilin, sai ga Umman su ta shigo, amma tace wai gallazawa 'Yar uwarta yake, yana cutar da ita shiya ta tsane shi."

Tsanar shi cema tasa ta tsani aure, da ma namiji baki d'aya, saboda wannan ak'idar tata kowa ma ma yasan ta ta rashin son aure, tun bata fi 'Yar shekara sha d'aya ba, amma tace duk shi Altab d'in ne yasa tak'i aure.

Abinda Umman su ke gaya mani kenan jiya, amma naga tsanar da sauki tunda har ta iya zuwa ta rok'ar masa alfarma, da tausaya mashi.

Jiya da ta gaya mini, nace bazan yarda taje can gidan ba, saboda Altab, ya tsanar mani ita, cewa tayi itace ta tsaneshi, bashi ba, ba kaga yanda hankalin ta ya tashi ba sosai to nidai yanzu matsala ta d'aya, Yaya za a tunkare ta da maganar aure, kuma auran ma na wanda tafi tsana a duniya.?

"To kai Altab, tsakanin ka da Allah miya had'a ka da ita.?

"Wallahi baba ba komai, ni rashin wayon tane, da rashin hankali ke had'ani da ita, Idan nayi mata fad'a sai tafi baya ma."

"To kai Altab ya kake ganin wannan al'amarin naku.? Kasan dai Rabab nika d'ai na iya da ita duk duniyar nan, sai kuwa 'Yar uwarta da ta rasu.

"Abba ni gaskiya ina tsoron auren Rabab, saboda nasan ba jituwa tsakanin mu, duk da daren da yayar ta zata rasu na hanata kwanciya nace taje ta jiyo mani wai miye mahad'ina da k'anwar ta.

Dalilin na yin hakan kuwa, abinda muke da k'anwar ta na damunta, sai dai ta kasa yi mani bayani, har ina tunani ta fara zargin koda wani b'oyayyen abu a tsakanin mu amma ta kasa magana.

Allah ya taimake mu gaba d'aya ita ta gamsu da bayanin 'yar uwarta, nikuma nafita daga zargin matata, ta rasu a zuciyarta ba wani Abu da take tunani damu. "

"To me tacewa 'Yar uwar tata.? Inji baba Alhaji.

"Irin dai hirar su ce ta mata, kyau asamu wata wacce jinin su ya had'u, zata gaya mata sosai, abinda kawai na lura, Rabab batasan miye aure ba.

Saboda a kanshi take magana, nidai da taimaka mani aka yi taje ta zauna har indawo daidai sai insamu wata can in Aura

Wallahi tsoron Rabab Nike. "

Sukayi dariya su Abba

"shasha sha, kana namiji zaka dinga tsoron macce. "

"E Alhaji da gaskiyar shi auta ta abin tsoro ce wallahi, idan dai akan maganar aure ce, ni kuma yanzu kun saka ni zullumi.

Amma yanzun Altab, shine abinji, idan dai har ya amince wa zuciyarshi yana sonta da aure, zai iya zama da ita ya karyota ta dawo mutun, ta fahince shi ta faminci aure, to abune mai sauki tunda tausayin shi yafara shiga zuciyar ta,shi dama so ai rukunin shi tausayi, aciki sai dai kuma komai ayishi cikin hikima da dubara. "

"Ana magana kayi shiru.? "

"To Baba ni ba abinda zance, sai abinda kuka yanke amma ni ina tsoron Rabab. "

"Cewa akayi zaka iya ko A'a.? Amsar da muke son ji ke nan, ai mu ba mahaukata bane da zamu kama d'aura maku aure a yau ko gobe, ko sati mai zuwa, dole sai anbar ku kun fahimci juna ko?

"A'a Alhaji shi dai zai zama da ita idan ba so ko jituwa ai bazai iya tafiyar da ita ba, kasan mace idan namiji ya iya tafiyar da ita nan da nan zata so shi har ta zauna dashi. Altab, yaya ka gani.?


"Abba Rabab, batada kyau, ko jiya dana mata maganar Ilham tana son kulawa irin ta uwa, gashi ta rasa uwa.

Kaga yanda tayi mani har razana nayi, wai tayi tunanin aure zance zanyi, da sai ta kashe matar saboda anci amanar 'Yar uwarta, nace mata a'a kulawar ta kota Umma nike nufi.

Sai tace mani kar inji komai, ita bazayi aure ba har aboda, zata zauna ta rike mani yarana har lokacin da zasu girma, ko Abba yayi mata alkawalin bazai yi mata aure ba.

Sukayi murmushi jin yadda sukayi, "sai naji banji dadi ba, sai nayi saurin cewa.

"Amma ni ina son Rabab, balle yanzu naga ta sauko, kuma dama can ina son k'anwata, ita ce dae ke tsanata."


"To Allah dai ya zaba maku abunda yafi zama alk'airi gareku..... Inji Baba."

"Ai alherin ne na wannan, sabida yarinyar nan nada k'ok'ari ko akan 'yayan nan gaskiya nima na shaida."

"Hakane Alhaji yanzu fah a gidan nan bata bari kowa ta tab'a mata 'ya'ya sai ita."


"To yanzu ku tafi tunda dai ya amince, nima zansan yadda zan shawo kanka zanyi magana da bbar Auntyn su zamu san yadda zamu b'ollowa lamarin, sannan kuma.

"Kai Altab, kasan komai game da Rabab, zata dinga zuwa gidan ka duk juma'a tana Kai maka 'yayanka ka gansu, koda wasa kada ka nuna mata wata alk'a tsakaninku sai ta yaya da k'anwa.

"Ni kuwa Alhaji kallon sauk'i nike wa yarinyar nan ga hankali.......inji Baba Alhaji."

"E to idan a haka zaka ganta tanada hankali, da sauk'in ma, abunda ke damunta rashin wayau kawai, sai wanda ya santa zai iya zama da ita. "

A haka dai suka ci gaba da tattaunawar su har sukayi sallama.

Ina isowa k'ifar gida, su kuma sun fito, nayi saurin parking, na fito da hanzari na, nayi masu sallama, sannan na koma mota na d'auko 'yata Ilham,

Alhaji Baba yace "Allah ya tayaki rik'o."

Nayi saurin cewa "Amiin Baba, amma fa bazan aura maka ita ba, naga sai kamfe kake tun jiya."

Yayi dariya, Ga shi kuwa kin makaro, ita tace ba wanda take so sai tshoho. "

"Kai baba ita batayin so balle taso tsoho, kadai ajiye mata chocolate d'in zata dinga zuwa kar b'a."

Akayi dariya sannan suka shige mota, yanda naga yaya a d'inke naga alamun ba nasara.

Amma banida damar in tambaye shi, saboda Alhaji baba, da Abba ne kawai zan iya tambaya, suka wuce da motor su nima na shiga da tawa cikin gida.

D'akin Abba na nufa, na tsugunna na gaishe shi, sannan nace.


"Abba ka barni.?"
Ya girgiza Kai, na mik'e da sauri in mashi yanda na saba yi.

Yayi murmushi, "wai meyasa kike son zuwa gidan Altab, a yanzu, alhali a baya 'yar uwar ki na gidan da k'yar kike zuwa.? "

"Abba wallahi in ba kowa kusa Yaya zai iya mutuwa. "

"In ya mutu ba shikenan kin huta ba, ko kin Manta lokacin da kika ce mani dama ya mutu da kin huta saboda ya matsan tawa rayuwar ki.?"

"Allah yanzu idan ya mutu sai mun tausaya 'ya 'yan shi ba uwa ba uba, kuma Abba yanzu ai nasan mutuwa, na d'and'ani d'acinta. Bana son kowa nawa ya k'ara mutuwa Allah Abba. "

"To kince zaki fad'a mani abunda yasa kika tsane shi a baya. "

"Allah Abba zan fad'a maka, sai idan ka bar ni zuwa tukunna."

"Ba barki Rabab amma zamu yi wata magana nida Aunty ki, sai inkin amince, kuma saboda 'ya 'yanki badon Altab ba, tunda ya tsanar mani autata, nima naji ya fita raina. "

"Wayyo Abba a baya kenan, Allah yanzu ya daina, tunda akayi mutuwar nan Kai tun ma saura kwana d'aya ta mutu, ta fahimtar dani kad'an, don dai ma ni na rik'e na saka mugun tsanar shi a zuciyata. "


"To kinji fa, kada ma yaje ya kashe ki cikin dare. "


"Wayyo Abba mutumen da yake yini kwance kamar ruwa, Abba baka ga yanda ya rame yayi baki."?

"Na gani, nidai bancin nasan auta ta munyi alkawalin bazan mata aure ba, sanna k'ari da wani saurayi ne ba yayanki Altab ba, da sai ince kilan suriki zan yi. "

"Meye Suriki Abba,?
"Wanna zaki Aura.

"Wayyo ai dai kasani banida saurayi, kuma haramun ne ma k'anwa ta auri mijin yayar ta ko Abba.? "

"Kwarai kuwa, a hadisinki ko.?
"Meye hadisi na.?"
"Shin dai ba aure a tsakaninki da Altab ko a hadisin ki.? "

"E ai kasan Abba ba aure a tsakanin mu, ni bama zan iya auren shi ba."

"Saboda me.? "

"Saboda Azzalumi ne, macuci, nida in auri Yaya Altab k'ara a dinga yankan naman jiki na ana zubar wa har in mutu. "

_"Sabhallahi_ yanzu kika gama ce mani kin daina tsanar shi. "

"To tashi ki tafi, amm gaskiya idan irin tsanar baya zaki nuna mashi zan hanaki zuwa. "

"Wayyo Abba ina tausayin shi kuma inajin wani abu wanda ban san minene ba, kuma wancen zamanin ya wuce Abba."

"Na mik'e na shiga gida ina murna, saboda abba yace zamuje gidan Yaya Altab ranar jumu'a dad'i kawai nike ji saboda yaya zai d'an warware."

*ONE WEEK'S LETTERS.........*_๐Ÿ•‹Jumu'at kareem 2 u, my lovely friends and family_๐Ÿ•‹๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[5/1, 10:18 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*U are always in my heart*๐Ÿ’œ
*Ameena Abba*
*Ummy Abdoul*
*Ummun meenal*
*Momyn Afrah*
*hafsee*
*Ummu Abideen*
*Beebah muh'd*
*Haleemah Abdullah H. @.S*
*E. T. C*

*Page 11n12*

"Yau juma'a shirye shirye muke yi nida mai aikin Umma zamu tafi gidan yaya Altab, Abba ne da kanshi ya kaimu a Mortar shi, Niku wa murna nikeyi tamkar zan tafi Abuja, saboda can kad'ai nake wa murnar zuwa, gidan Aunty kuwa sai dole nike zuwan shi, sannan ya fa'da min zasu zo shida Aunty. "

Yaya na kwance a k'asa, saman kafet. Muka shiga ya yunk'ura zai tashi zaune, sai kawai amai ya b'alle, nayi saurin rugawa wajen shi, na ajiye su Anwar saman kujera, sannan na isa na dafa kafa d'ar Shi.

"Sannu Yaya."

"Bai iya amsawa ba, Abba ya shigo, shima yayi tsaye yana kallon shi. "

Ilham kuwa sai kuka takeyi, atake Abba ya buga waya, sai dai naji yana kwatancen gidan, da yake layin fitacce ne, tunda akwai fitaccen mutanen kirki a wajen ,kuma d'an uwan Abban mune.

Dr na isowa, sannan amai ya lafa, inata aikin kwashewa, na kira mai gadi nace ya d'auke kafet d'in ya kaishi wanki,.... Yabini da to.

Na kawo kud'in mashin na bashi, sannan na k'arasa gyaran wajen na kawo mashi abu ya kurkure bakinshi ciki, na feshe falon da turaren k'amshi na d'aki, _(Room freshner_). Bayan Dr ya d'au lokaci yanata auna shi, tare da yi mashi tambayoyi.

A k'arshe dai ya rubuta mashi gwaje gwaje, na jini da sauran gwaje gwajen su na likito ci. Sannan ya jaddada ya dinga cin abinci ya kuma rage damuwa.

Ya rubuta mashi magun guna harda allurai, anan take yayi mashi wata allurar, sannan ya tafi tare da cewa.... A bashi wani abu yaci saboda allurar na da k'arfi.

Abba ya iso ya zauna, sannan ya fara magana...

"Wanda duk ya yadda da k'addara mai kyau ko marar k'yau. To Allah yana tare da shi. Altab, kada kasa damuwa a ranka, damuwar ka da rashin ta duk baza mu iya maka maganinta. Tunda bazamu iya dawo maka da matar ka ba, hak'urin da zakayi shine yake nuna wa Allah ka amince da yanda yayi maku kuma ka gode.

Saboda haka sai Allah ya dube ka yayi maka canji ko musaya mafi alk'airi, amma zaunar da damuwar da zakayi a ranka kamar kana nuna jayayya ne wajen Allah.

Idan har da k'arin maganar jiya, zamu iya janyewa ba dole fah, dama dan Kai za ayi da 'ya'yan ku ku samu natsuwa ba cuta ba cutar wa amma zan samu Alhaji sai........

"A'a Abba wallahi ba ita bace, tambayi Rabab shekan jiya yafi haka ma yanda suka sameni, Abba tun daga ranar da Ikram batada lafiya nike ciwo nima har yau."

"To ni zanje na d'auko Auntyn ku."

Ya Mike makayi sallama tare da rakiyar shi har wajen mota.


Yaya ya koma falon sama ya zauna...nima nazo na zauna rai na a b'ace.

"Yaya Rabab.? "
"Abba ne da k'yar ya barni."

Ya taso ya tsugunna a gabana tare da kama hannaye na duk biyu.

"Rabab ni nasan zaman ki bazai yiyu ba.... Yayi shiru.

"Me yasa kike son zama tare da ni.?"

"Saboda bakada lafiya kuma kad'ai ci ya maka yawa....na rage murya tare da sakin kuka...

"Ni! Ni!! Bana son ka mutu kaima."

"Me yasa Rabab.? "

Na k'ara kuka mai k'arfi, shima hawayen idonshi suka gangaro a kumatun shi.

"Rabab idan kina son zama dani to kije ki tambayi Abba yabani ke, bayar wa ta har abada. "

"Kai Yaya ka tab'a ganin inda akayi k'yautar mutun babba kamata.?"

Na fad'a cikin kuka, ya tashi ya zauna kusa dani, ya janyo kaina ya kwantar a cinyar shi. Ya sun kuya ya sunbaci kuma tuna. Sai naji gabana ya fad'i nazaro ida nuwana duk biyun.

"Ana yin k'yautar mutun mana, ya yarki ma k'yauta aka bani ita muka dinga zama mutawa ce kawai ta raba mu. "

Ga bana ya k'ara fad'uwa. amma na kasa sanin dalilin yin hakan.. Na d'ago da kaina

"Kana ga Abba zai yadda.?"

"Zai yadda mana. amma idan anbi sharud 'd'an musulun ci."

"Miye sharud' d'an musulun ci.?"

"Abba duk zai maki bayani idan kinje ki tambaye shi, sai ki gaya mashi yanda mukayi dake."

"Allah idan ya hana ba zan zauna anan ba.tafiya ta zanyi Abuja har sai hutun mu ya k'are, saboda bazan iya ganinka cikin wannan halin ba Kai kad'ai."

Ya tallabo kuma Tuna duk biyu muka had'a ido da shi, gabana naji ya k'ara fad'uwa.

Nayi saurin sun Kuyar da kaina, wai atake sai naji kunyar shi ta sauko mani... Ko meyasa haka.?

Ni nasan dai banajin kunyar Yaya, sai dai haushin Sa.
Ya k'ara d'ago kai na.

"Miyasa bakison had'a ido dani yanzun.?"

"Nima ban sani ba Yaya, kawai ji nayi ina jin kunyar ka."

Yaya murmushi cikin hawaye.

"Rabab ko yaushe zaki girma? Gaskiya zan baki shawara ki daure ki dinga karatun littafan turanci ki dinga yawan kallo, ta haka zaki yi wayau."

"Bani da wayau Yaya.?"

"A'a kina da shi, ki k'ara nike son cewa."

"Har nayi mamaki, ace duk girmana bani da wayau."

"Zan siyo maki littafai ko kinji haushi, kada ki ajiye haka kallo ma ko kinji haushi kada ki daina."

'Amma bana aure ba ko? Yaya nifa duk abinda ya shafi maganar aure bana son shi kwata -kwata."

"To meye aure Rabab?"

"oho, ni sunan shi kawai naji ana fad'a."

Yayi murmushi, "idan kina da k'awar da tayi aure ki tambaye ta meye aure? "

"Ba jiya na ganshi a TV ba, sai dukanta yake ya hanata abinci, ita kuma d'ayar da tsohon ciki amma ya lik'e mata, sai binta yake duk Inda ta nufa, k'ila ma maye ne so yake ya cinye mata d'an cikin ta."

Yayi dariya....Lallai Rabab halayyar ki sai Abban ki.

Ya mik'e tsaye ,na mik'e nima.

"Ka zauna in kawo maka abinci, ka ga kada ciwon ka ya taso."

Na tafi da sauri na d'auko mashi farantin da na jera mashi abinci.

Ina cikin zuba mashi abinci, mai gadi ya shigo wai Oga, yayi bak'i daga Office d'in su zun zo su duba shi. Yace su shigo.


Sai gashi Sun shigo Sun Kai su goma maza da mata,. Na durk'u sa na gaishe su, sannan na wuce na d'auko masu Juice da ruwa, na kawo masu. Nace bari naje na d'auko masu abinci... Suka ce inbar shi sun k'oshi.

Yana cikin sha, sai amai ya taso masa, cewa yake amai, amai, na ruga aguje na d'auko wani k'aton tsumman towel, na linke shi nace yayi ciki.


Ya dinga yin aman har ya kai ga bani tausayi, na iso na kama shi ina cewa.

"Sannu Yaya."
Ina kuka, har na samu ya k'arasa, na d'auko ruwa na bashi ya kurkure baki.

Na cire d'an kwalin kaina na goge mashi zufar goshin shi da ta tsatstsafo da bakin shi. Na dafa goshin shi.

"Sannu Yaya."
Sai kawai naji wani daga cikin su yace.

"Da ma matan ka biyu ne.?"

"Yace a'a k'anwar mata ta ce data rasu. "

"Anyi maku aure da ita.?"


"A'a"
Yanda yake bada amsar ya d'an nuna rud'ewa.

"Amma ita za a Aura maka?..Da alama tana da kula, zaka ji dad'in zama da ita. "


Na harare shi zanyi magana Yaya ya rik'e hannu na ya girgiza Kai, alamar inyi shiru.

Haushi yasa na kwashe kayan aman da Yaya yayi na tafiya ta d'aki. Ina ta fad'a nidai bansan tafiyar suba saboda haushin da suka bani, sai dai naji Yaya na kirana...

Da sauri na tashi.. Amma sai da na lek'a falon naga ba kowa, sannan na isa wajen shi.

"Yaya wannan bashida hankali, da ka banni in gaya masa magana.

"Ki manta da maganar shi... Kinji kukan Arwa Naji, jeki gani ko lafiya .


Na tafi da sauri harda guduna Na nufi falon k'asa.... Sai ga Aunty Shukrah, babbar yayar mu...

Falon k'asa ta tafi dani, ni kad'ai tace in zauna. Na zauna ni abin ma har ya fara bani tsoro. sai da ta nisa sannan ta kira suna na.

"Rabab ki natsu ki saurare ni sosai, kin san ni a hidimomin ki na shirme bana wasa dake, kuma bana tsayawa in saurare su."

Saboda haka magana zanyi dake, ina son ki fito fili kiyi mani duk tambayar da take zuciyar ki, nima ki bani duk amsar tambayar da zan yi maki. "

Tayi shiru "Aunty wani abu akace nayi."

A'a ki saurare ni dai.....

"Ke keson zama tare da Altab.?"

"E Aunty."

"Miyasa kike son zama dashi.?"

"Saboda ina tausaya mashi."

"Da akayi me.?'

"Da Aunty ta rasu."

"Aunty me cece d'inshi.?"

"Matar shi. "

"Shi fa.?"

"Mijin ta."

"Rabab ba a zama mace da namiji a gida d'aya sai idan an d'aura aure, sun zama miji da mata."

Na zaro ida nuwa na, "Aunty ban gane ba.?"

"Musulun ci ya haramta zama tsakanin namiji da mace, face da aure tsakanin su."

"Aunty wallahi Yaya Altab abin a tausaya mashi ne, tambayi Abba."

"Na sani, idan har kina son taimaka wa yayan ki Altab, sai dai idan ki aure shi."

"Na mik'e tsaye, "Aunty......

"Zauna Rabab aure a wurin 'ya mace dole ne."

"Aunty Yaya Altab mutumen da na tsana a duniya za ayi mani abin da na tsana dashi, wai aure."

"Kina iya fad'a me yasa kika tsane shi baya ,yan zu kuma kike tausaya mashi.?"

Na kwashe komai da na gaya wa Aunty Ilham kafin ta rasu, na gaya wa Aunty, da wasu ma da nike jin kunyar gayawa Auntyn, shine naga yana yi mata fyad'e tana kuka. Shekarun da suka wuce..... Aunty tayi shiru...

"Ya akayi kika san fyad'e alhalin ba kya son maganar aure?"

"A makaranta na tambayi k'awata, shine shine take fad'a Mani, fyad'e ne yayi mata har ta nuna mani irin yanda akeyi a wayar ta kinji dalilina na tsanar shi."

"Lokacin kina 'Yar shekara nawa ta nuna miki?"

"Ina jami'ar nan."

"Ganin fyad'en kuwa tun kina 'Yar yaushe.?"

"Tun banfi shekara sha biyu ba, naje gidan ta hutu, na hau sama in kai mata Ilham, tana kuka na iske shi. "

"Sun ganki.?"

"A a koma wa nayi, nima na dinga kuka yanda naji Aunty na kuka ita ma."

_"Innalillahi._ kin tab'a gaya wa wani.?"

"A'a sai wannan k'awar tawa, itama bance mata yayata ce ba, cewa nayi wani gida naje na iske haka."

"Rabab abinda Altab yake yiwa Auntyn ki shine so da k'aunar da kikaji ana fad'a, hanata sakewa da kika ce yanayi, itace kulawa duk macen duniya na son ayi mata haka.

Rabab, Altab yana da halayya na gari, Altab mutumen kirki ne ya rike mana 'yar uwar da amana. Ni nan da kike ganina nafi Ikram jin dad'i, wallahi tafi ni samun kuwa a wajen mijin ta, idan kika auri Altab zakiji dad'in rayuwa. "

"Aunty Altab? Na fad'a ina kuka.

"E Altab autar Abba. Ni kaina mahaifin ki ina so ki aure shi, idan kuwa ba haka ba, to bazaki k'ara komawa gidan shi ba.

Saboda addininmu ya haramta irin zaman da kike son yi da Altab.

"Abba Kai fa kayimin alk'awalin bazaka min aure ba har abada, kuma in auren zaka yimani, tunda ka karya alk'awalin da kayi mani, sai ka samo mani ba Yaya ba, Abba yaya ya cuci Aunty sosai.ya gallaza mata. "

"Auta abubuwan da kika fad'a duk ina jinki daga d'aki shima Altab d'in yana jinki dukkan abunda kika fad'a shi ne aure.

Amma tunda baki son auren Altab, uwata ki tafi da ita Abuja, kada ta dawo sai ta kawomin mijin aure.

Kai kuma Altab kayi hak'uri ka zauna da 'ya'yanka gasu tsohuwa nan, duk ta koya masu komai, har Allah ya baka matar aure. Kada kuma ki k'ara cewa kina tausayin shi,idan kina son zama da shi, aure shi ka'dai xaku yi ku zauna har abada a tare ba mai zargin ku, ba mai ce mana bamuda hankali.

"Abba dan Allah abar min su Anwar da Arwa in tafi dasu. "

"A'a ki bar shi da 'yayan shi, tunda bamu isa dake ba, baki yarda damu kuma ba, kina ganin zab'in da muka yi maki bai miki ba amma ki sani aure fah dole ne a gare ki ko kin shirya ko baki shiryawa, kije ki kawo mani mijin da kike so ke.

"Abba dan Allah kada kayi min aure bana son shi kwata kwata."

Na tashi na isa wajen abba.....

"Abba ka tuna Kai da bakin ka ka yimin alk'awari."

"Rabab na gama magana, daga gobe yau bana son ganin ki a gidan nan."

Ya k'wallawa Yaya kira....

"Kai ma ka k'arbi yayan ka, gaba d'aya."

"Abba kayi hakuri kada kayi fushi da yawa kasan Rabab batada wayau Kai da bakin ka ka fad'a, zan cen a tursasa mata dole, abi a hankali da ita.

"Altab, Rabab ba yarinyar da za a tsaya yiwa haka bace ba, sam wannan yarinyar bazata tab'a tsayar da hankalin ta ta gane komai ba, k'wa k'wal War kifi aka yi mata.

Hukuncina idan tana son zama dani ta auri wanda nace, in kuwa bata so, tabi 'Yar 'uwar ta, wata ukku na basu ta kawu miji, can tayi mata aure ni ba ruwana da auran ta......
[5/1, 10:19 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 13n14*

"Abba, kada kayi mani haka dan Allah, wallahi Yaya Altab mugu ne na gaya maka."

"A haka nake son ki aure shi idan ya cuce ki Allah sai ya saka maki."

"Abba, ni nayi hak'uri kabata wanda take so."

"Altab, wa Rabab take so?.. Ai in dai namiji ne ba ruwanta dashi, balle har tafahim ci so, idan kun yanke hukunci keda 'Yar uwarki, sai ki sanar dani nan da wata biyu ayi bikin su."

Ya wuce warshi kawai.

Na durk'u she nasa kuka mai tsanani.

"Aunty ki taimaka mani dan Allah, wallahi bani son aure, don Allah Aunty."

"Naji zan rok'ar maki shi, amma yanzun je ki kwaso kayan ki."

"Aunty shi kid'ai fa za a bari, wallahi bashida lafiya."

Aunty tayi murmushi mai fitar da sauti.

"Ke Rabab abin naki na kasa gane shi, tashi mu tafi kinji."

Nayi wajen Yaya Altab da saurina.

"Yaya ka rok'ar mani Abba."

"Ba ruwana Rabab Abba ya riga yayi fushi baya sauraro na, ki k'yale ni, nagode da taimakon da kika mani a baya. Allah yasaka maki da alheri."

Ya fice yayi tafiyar shi... Nan na durkushe na dinga kuka, Aunty ma tashi tayi tafiyar ta.

Na gama had'a kayana tsab, yara kuwa nata bina suna kuka, itama Aunty sai da ta koka, Yaya kuwa tunda muka shigo muka same shi falo ban k'ara ganin shi ba har na gama.

Na fito rungume da su Arwa Ilham itama kuka kamar na mutuwa, muka iso k'ofar falo, ko sallama ban iya jin zan yiwa yaya ba amma sai naga ya taso yazo wajen mu.

Aunty tace mashi "Mun kammala zamu tafi, bai iya yin magana ba, sai dai ya mik'o hannuwan shi wai in bashi su Arwa, na zaro idanuwa na tare da juyawa alamun bani bayar wa.

Aunty tasa hannu to karb'e su tare da cewa..

"Ki bashi yaran shi mizakiyi da zuri'ar shi tunda shi ba k'ya son shi, ai mai son ka yaso 'ya'yan ka, haka mai son 'ya'yan ka yaso ka.

"Aunty dan Allah ki bar mani su."

Ta harare ni ta mik'a mashi yaran shi.

Na sa sabon ihu ina bin yaya amma ko waiwayo ni bai yiba ya haye sama dasu.

A daren nidai banyi bacci ba saboda sabo dasu Arwa, haka na dinga tunanin yanzu haka Yaya na can idon shi biyu k'ilan ma kuka Yake yi.

Har na d'auki waya in kirashi sai na tunano Abba, wai in auri yaya, haushin shi ya saukar mani a zuciyata nan take na lumshe idanuwa na na kuma yi addu'a..

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***
*GARIN ABUJA...*

Na samu sati d'aya kenan a garin Abuja amma ni kaina na rasa abinda ya hanani walwala a rayuwata, ba kamar da ba idan nazo gidan kowa sai yasan ina nan.

Kwance nike ina tunani da zuciyata.

Yanzu aure suke son yi mani.?

Na gyara kwanciya ta... Haba jama'a yama za ayi in auri Yaya Altab, Abba ko mantawa yayi mijin yaya tane."

"A'a ya ma za ayi ya Manta. Shiya ya fad'a da bakin shi, to wai irin zaman da nayi mashi yanzun shi ake so inci gaba. Amma a d'aura aure.?

"To ai idan irin shine ai ba wata matsala ki yarda mana ki taimaka mashi kawai keda 'ya'yan ki.

"Allah ko.?"

"E mana.?"

"Amma d'aurawa kawai za ayi kada ki yadda ayi wani taron buki."

"Saboda me.?"

"Saboda kowa zai san kinyi aure, in kuwa d'aurawa akayi ba wani shagali, ba wanda zai ce kina da aure duk ranar da kika gaji da zama ko yaran ki suka girma sai kawai kiyi tafiyar ki gida ko inshi yayan zai yi aure.

"Haka za ayi kije ki samu aunty kuyi maganar."

"A'a Abba ya kamata ki gaya wa."


"A'a Abba bazai saurareki kiba gara dai Aunty, ko ki raba kanki da wannan k'uncin zama."

"Haka za ayi kuwa.. Ke dai na gode k'awar."

"Wacece k'awata.?"

"Zuciyata."

"Ni da zuciyata nike shawara, hakan kuma da ta gaya mani yayi mani daidai, dama ni banida wata k'awar da ta wuce zuciyata, balle ta gaya mani shawarar banza."

"K'arfe 11:00 na safiyar litinin muka wayi gari bayan yan aiki Sun gama gyara 'yan makaran ta Sun tafi. Da gama gyaran gidan nikuma na koma d'akina nida zuciyata muna hirar komawata katsina..

Inata murna yanda Yaya zai ji idan na koma gidan shi da zama.. Na k'agara Aunty ta shigo Sa shenta daga sashen mijin ta Kanal, domin in gaya mata shawarar da muka yanke *NIDA ZUCIYATA*.

Ina son to gayawa Abba.. Can sai naji ta shigo sashen ta na gane hakan ne ta gaisuwar da naji masu aikinta nayi. Nima nayi zunbur na fita falon ban ma jira ta shigo ba gudu nike kada ta wuce wata hidimar.

Ina fita ta maido hankalin ta akaina, irin kallon tambaya shi tayi mani, saboda tasan inba da wani abu ba, babu abunda zai fito dani waje..

"Aunty dama....."

Dama mi?"

"Maganar da abba yiyi min."

"Sai akayi mi.?

"E daman...

"Daman mi ki fito kiyi magana ko nabar mki d'akin."

"Ki fad'awa Abba na amince zan aure Yaya amma.... "

"Amma mi.?"

"Dan Allah Aunty bani son taron buki."

"To yayi bara na kira Abba."

Ta d'auki wayar ta ta kira abba tayi masa bayani banji mi yace mata ba saidai naji tana cewa...

"To Abba sai munzo "

"To Rabab ji ki ki shirya yanzu zamu d'auki hanyar komawa katsina abba yace za ya kira kowa a had'u nan gida.... Cewar Aunty.

Murna nikeyi zanga Yaya wadda hadda Aunty saida ta fahimta..

"Kin ganki Rabab Allah ya shirye ki."

"Amiin Aunty."

Ya tashi na shiga d'akina da guru....


*KATSINA*

"Tsit kake ji a felon, babu abinda ke kid'awa sai iskan fankokin da ke ciki kowa yayi shiru. "

Baba Alhaji shine ya fara magana...

"Alhaji kayi shiru alhalin da maganar ka zamuyi amfani, yanda kace haka shi za ayi...

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!....*muna yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan zaman dan farin ciki za ayi shi kuma hakan da Allah ya nufa shine yafi zama alheri...

"Mama na "ita da bakin ta tace ta amince a d'aura."

"E Abba da bakin ta."

"Shike nan magana ta k'are, ayi yanda ta buk'ata Idan Allah ya daidai tasu can su cigaba da auren su haka ake so, idan basu daidai ta ba, bama fata, sai a raba auren nasu, tunda dama makaran ta takeyi a yanzu ,badon komai na yanke wannan hukuncin ba, sai saboda yin haka zai kawo wa kowa kwanciyar hankali balle su da yaran kuma. Tunda shima yana son zaman nata nasan shima don 'ya'yan shi badan so da k'auna ba kun san mai d'a wawa ne,. Ganin 'ya'yan shi Sun karkata wajenta yasa shima ya karkata ga son ta zo ta zauna.

Saboda haka Kai Alhaji, kai kasan yanda 'yarka take, sai ka taya shi tafiyar da ita kilan a dace, saboda ba wanda ta cancanci ta aura kamar shi, sun saba da juna sosai, a haka cikin fad'an nasu da tsanar juna sai gaji sun daidai ta kansu.

" Kilan ta hakan ya canja mata rayuwa har auren ya d'ore, saboda haka ina wakilin shi za a yanka sadaki. ta?...Ragowar kayan bidi'a sai nan gaba Sun daidaita, watau lefe, da sauran 'yan abinda Al'adarmu keyi. "

A take aka Sa sadaki dubu hamsin, Alhaji baba ya zaro ya Dada yace raguwar taron d'aurin auren naku ne, nidai daga nan sai dai inbi da adduar zaman lafiya, da daidaituwa da zuri'a d'ayyaba.

Bancin ma shaidu na jama'a, da mun d'aura shi yanzun, amma d'aurawa masallacin ma yana da amfani saboda kore kokwanto na jama'a.

A haka akayi addu'a a ka watse kowa yayi gidan shi ,haka su Aunty suka shigo da matar yaya furk'an da Aunty fa'ik'a da Aunty shukrah suna ta hirar yanda akayi.

Ni kuwa ina kwance tamkar barci nake, Yaya furk'an sai cewa yake, ina sane nake wani sakar cin don Abba na goya mani baya.

Aunty Fa'ik'a da Aunty k'adra suke goya mani baya
Amma har Yaya Tarik' da yaya Fu'ad duk bakin su d'aya da yaya Furk'an.

Ni kuwa banma fahimci sakar cin da nike yi ba, ni dai nayi imani iya gaskiya ta nake fad'a, Abba ya sani, itama Umma ma tasan bana k'arya.

K'arfe 10:00 na safe, a masallacin jumu'a na nan wajen unguwar mu a nan akayi addu'ar Aunty Ikram, sannan aka d'aura auren *ALTAB DA RABAB*........_Kuyi hak'uri da wannan wallahi bana jin dad'i nd ur prayers plz_๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™
[5/1, 10:20 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*AlHAMDULILAH...*
_Ina gdya da nuna k'aunar ku gareni, kun nuna min soyayya ngde da addu'oin ku gareni kuma nasamu sauk'i cikin yar dar ubangiji, ana mugun tare irin totally d'innan_๐Ÿ˜

*Page 15n16*

Murna duk ta cika ni da aka dawo ana murna, ana cin goro da dabino, ni kuwa na gama had'a kayana guri d'aya, jira nike Abba yace, to fito akaiki, saboda daman shi ke kaini gidan, da rarrashin sa..

Amma har yamma shiru, Abba na falon sa, sai ma bak'i yake tayi, ana ta Kai lemo, da d'an abinci, da wasu 'yan lashe lashe, mutanen unguwar mu kuwa dan gulma sai shigo suke suna Allah yasa alheri..

Yamma nayi wajen k'arfe 5:00pm, sai ga yaya Altab ya shigo yasha manyan kaya kuwa, _white color shadda_,tasha aiki. Abinka ga farin mutun tayi masa k'yan gaske.

Nayi saurin tararshi yanda na saba,

"Kai Yaya kayi kyau."

Sannan na gaishe shi, shi kuma sai sunkuyar da Kai yake tamkar mai jin kunyata, nikam naci gaba da tambayar shi...

"Yaya unguwa zakaje ne? naga k'afar ka na ciwo, Yaya Kai ka tuk'o motar.?

Kamin ya bani amsa sai ga wasu abokansa sun shigo su biyu,

Ganin na k'ara tambayar shi yace "Abokin sa ne ya tok'o motar, zuwa sukayi sadakar arba'in d'in Aunty, nace to, sannan na tafi, saboda har sun nufi falon Abba.

Suna fitowa, Abba ya fito shima, yace inzo mu tafi, yaran gidan mu suka d'auki akwatuna na suka sa motar Abba, daga ni sai Abba muna tafe yana yimani fad'a kamar dai yanda ya saba, idan zai kaini gidan Aunty.

Sai da ya rakani har cikin falo, su Yaya Altab suka shigo suma, sannan naji yana yiwa Yaya fad'a shi ma.....

"Rabab ba kamar Ikram ceba, wayau, da hankali, da natsuwa, duk ba iri d'aya bane dana Rabab. Shirme, da sakarci, shine na ita wannan, saboda haka kayi hak'uri da ita, ka kuma koyi hanyoyin tafiyar da ita, ku daidai ta, in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki, saboda ba wayau.

Ni da Kai munfi kowa sanin haka, yawan cin mutane gani suke kamar ta san komai, wallahi da gaske take bata san komai ba, duk abinda yafito daga bakinta shine har cikin zuciyar ta.

Kai kanka yanzu ya isa ka fahimci haka, yanzun haka da gaske ba ta san aure ba, balle so, sai ka kiyaye, Allah daidata ku ya taimaka ya raya zuri'a.

Abokanshi suka ce "Amiin"

"Auta Altab shine babba a gidan nan duk inda zakije koda yarane, a tambaye shi kamar gobe za a tafi, kada a tafi kawai sai an dawo za a fad'a.

Kada a d'auko mayafi a ce za a tafi sai ya amince da tafiyar, haka komai kuke buk'ata ko yara shi zaki gaya mawa bani ba, tunda kin zab'i zama k'ark'a shinsa.

Kuma komai kikaga ya faru tsakaninki dashi, kiyi shiru kada ki gayawa kowa, in ma yazama dole ki fad'a to ki fad'a mani ni kad'ai, bana so inji wani yaji wani abu ya faru a nan gidan.

Rabab kina da biyayya, ni na sani, kina da tausayi da kula nina san da wannan kada ki canja halayyarki ta haka nan ,saboda yaran Ikram da baban su suna buk'atar kulawar ki da tausaya warki, mijin ki kuma na buk'atar biyayyar ki.

Komai ya k'are a gidan nan ki gaya mashi kada kice zaki tafi kawai ki siyo koda kuwa baya nan, sai dai idan kin sanar dashi ta waya, ya amince da fitar taki... Wallahi na samu akasin yanda nike so, zaki dawo gida.

Banda yawo, a dinga zama a gida sai Inda ya zama dole, in an kusa komawa makaran ta a Tuna mashi tun saura sati d'aya, kada gari ya waye a d'auki mayafi. Kai tsaye kice kin tafi makaranta.

Allah yabaku zaman lafiya yasa albarka ga zamanku.

Abokan Yaya suka ce "Amiin."

Sannan Abba ya ce ya tafi.

Nayi sauri na bi bayan shi, ina yi mashi rakiya, har bakin mota, sanna mukayi sallama yaja mota ya tafi....

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

K'arfe 5:00, na yammacin yau tayi daidai da watana d'aya kenan a gidan yaya ,Yaya yayi kyau yayi k'iba shida 'ya'yan shi..

Na fito d'akin mu na shigo falo,naga Yaya bayanan, na haye sama sai na same shi zaune saman gadon shi, da hoton, Aunty Ikram, na isa na d'auke hoton na ajiye shi a gefe d'aya.

"Yaya Allah ka rage wannan tunanin, wanda ya riga ya mtu har abada bazai dawo ba."

Na sassauta murya..

"Yaya ina bata maka rai ne ko bana kulawa da Kai ko yaranka.?"

Yayi ajiyar zuciya, sanna ya juyo rik'e hannuwa duk biyun.

"Rabab idan nace ba kya kula damu nida yara, nayiwa Allah butulci, sai Allah ya kamani, kina da matsala ne Raban."

"Yaya ta me.?
Na fad'a cikin sauri.

"Da har yau baki san aure ba."

"Yaya miye aure kuma Ba gashi an d'aura mana ba.?"

Yayi murmushi,

"Wai in tambaye ki.?"

"E Yaya."

"Ba kya zuwa islamiya ne.?"

"Ina zuwa mana."

" A islamiya ba a yi maku wa'azi a kan aure.?"

"Ana yi amma idan anfara fita nike, Yaya nifa ko so naji ance nagama yiwa wanda yace magana, balle yayi zancen aure har abada bana k'ara gaisawa dashi.

"Ba kwa hira da k'awayen kine akan aure.?"

"Nifa duk wanda yasan ni ya san dokata ce ma, ba a hirar aure a gabana shiyasa bana kallo banajin wak'e wak'en zamani."

Nifa bana komai na zamani, gudun kada a mani aure ko soyayya.

"Ya kike ji in ance maki.?"

"Ji nake tamkar zuciya ta balle sai in tsani mutun kawai."

"Yanzu tashi kije k'asa."

"Saboda mi Yaya? Kar fa kaci gaba da tunani kar ciwon kanka ya dawo."

"Ba zanyi ba.. Ke dai je k'asa kawai. "

"Ya.... "

Ya d'aga mani hannu.

"Kiyi hak'uri, je k'asa kawai."

Na mik'e tsaye na wuce, amma sai naji raina ya baci matuk'a, na isa d'akin mu na fad'a gado sai kuka. Ni kuma na rasa mi yasani kuka, nasan dai banji dad'in korar da Yaya yayi min ba.

Na tashi na zuba kayana na fara had'a su cikin akwatina ina kuka na cika akwati d'aya, ina shirya d'ayan sai ga Yaya ya shigo..

"Rabab me ya faru haka.?"

Yazo ya tari gabana na goce naci gaba da d'ebo kayana a durowa ya isa ya kama hannuwa na masu kaya.

"Yaya ka sakeni, kaga ina ganin mutun cinka, tunda ka koreni k'ara intafi banida wani amfani wajen ka."

Ya rik'o ni ta baya, nayi nayi in k'wace na kasa, ya zauna saman gado dani ina kuka. Kaina ba d'ankwali ya dinga shafa gashing kaina.

Ya sunbaci wuyana, "Rabab ya za ayi in koreki daga gidan nan koda kuwa na haukace? Ya kike so in kadan ce idan kika tafi kika barni nida yara, kin san wahalar da na shiga wanccen tafiyar da kikayi ki kalle ni a yanzu daga ni har yaran hankalin mu ya kwanta, kiyi hak'uri na samu kaina a wani yanayin canjin rayuwa ne a lokacin .

"Nifa ba tunanin Aunty ya bani haushi ba, Kora ta da kayi. "

"To kiyi hak'uri bazan k'ara ba shike nan ko.?"

Ya d'ago ni ya janyo fuskata ta kalle shi ya sa yatsun hannayen shi ya goge mani hawaye na.

"Ayi hak'uri autar Abba, so kike abba ya zane ni ko na batawa autar shi rai.?

Nayi murmushin kunya.

"Shike nan ko.?

Na d'aga kaina."

"To tashi ki tuk'a mu, mu d'auko yara islamiya."

"Ba Abba ya hana ba.?

"Yau ni nace."

Nayi murmushi na tashi nayi gaba.

"Rabab ina hijabin?"

"Ai mota ce ko Yaya."

"E mota ce amma a d'auko hijan dai yafi koh?"

"To Yaya. "

Ya d'auki hajabi muka tafi..... Wata d'aya sai yau naga waje...

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Odar mota mukaji ,nida su Arwa da Anwar muka ruga aguje duk da bayan su Nike ina kiran _ga daddy, ga daddy, oyoyo oyoyo_

Su kuma suna hudu.

Muna fita wajen gidan yana Bud'ewa fito wa, ya isa wajen su da sauri ya d'auke su kamar yanda ya saba sanna nima na shigo na shige tsakiyar su. Ya had'e mu gaba d'aya ya sunbaci kowa a goshi.

Sannan na k'arbi su Arwa na bar mashi Ilham, muka shiga gida, kayan cikin mota kuwa maigadi ke kwashewa ya Kai ciki har sama muka rakashi sannan muka fito.

Domin ya canja kayan shi, dama haka muke idan yadawo Office,

Yana fitowa daga d'akin shi ya nufi dining table cin abincin sa, nida su Anwar muka je taya shi hirar cin abinci,hakan yasa na kwallawa mai aiki kira nace ta d'auke su domin ya samu yace abinci....

Suna kuka yana yi masu dariya har aka tafi dasu.

"Rabab yaran nan na sonki, da uban yaran."

Nayi murmushi.

"Kai kuwa sabo, mu kwana tare mu tashi tare tun suna jarirai."

"Yaushe zaki daina kwana d'akin su.?

"In koma ina kuwa in kwana.?

"Sama. "

Na zaro ido.

"Haba Yaya lafiyar ka kalau kuwa, dan dad'i sai inje Inyi gadinka."

"To ai suma dan dad'i kike gadin su, lafiyar su kalau suma. "

"Ai su yarane. "

"Nima daga yau na zama yaro, azo adinga tayani kwana."

Nayi dariya.....

"Yanzu aka ganni saman ka na kwana ace me.?"

"Ace kina gadin Mijin ki."

Na zaro idanuwana....

"Miji Yaya.?"

"E Rabab."

Ya rage murya...

"Lokaci yayi Rabab da zaki gane ina da hakk'i a wajen ki."

"Hakk'i Yaya... Me na d'aukar maka.?"

"Hakk'in Aure mana."

"Shin Yaya wai meye a cikiin aure har ake son shi.?"

"Kina so ki sani, ki gani."

"E Yaya."

"sai kinyi min alk'awarin zaki tsaya ki gani, bazaki tashi ba."

"A ina zan gani.?"

"Ki zo yau samana, zan kunna maki kaset d'in da yake magana akan aure,"

"Nayi maka alk'awali, amma idan naji abin haushi ai zanyi magana ko.?"

"E, amma irin abin haushin da zakiji tambaya zakiyi, sai a fahimtar dake."

Ya janyo kujerar sa ta abinci ya matso kusa dani ya kama hannaye na duk biyu, yasasu a kuma tunshi ya lumshe, harda sakin numfashi.

"Yaya, ciwon kan ne, ko k'irji.?"

Ya girgiza Kai....

"Meye kuma Yaya.?"

Ya bude idanuwan shi, yayi murmushi.

"Matso kiji abinda ke damuna."

Na k'ara mtsawa ya sako kanshi ta wuyana yana sunsuna ta yasa bakin shi ya sunbaci wuyana sannan yace.

"Ke ce, ke damuna a zuciyata."

"Na d'ago kaina da sauri.........
[5/1, 10:20 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 17n18*

"Da na yi maka me?..ina ta burin nan da sati d'aya in tafi gida."

Yayi saurin bude idanuwan shi.

"Lafiya zaki tafi.?"

"Ganin nayi su Arwa sun d'an girma."

"Amma ke da bakin ki kikace shekaru uku zakiyi sannan ki tafi, idan ansa su Arwa makaranta."

"Ai gani nayi Sun d'an girma yanzu fa shekarun su d'aya fa da rabi."

"Me akayi maki ne."

"Yaya k'ara na koma gida nima gaban iyayena."

"Me zakiyi masu tunda ke matar aure ce.?"

"Yaya auren wasa fane."

"Yanzu Rabab Ashe zaki iya rabuwa dani da yarana.? "

"Ba haka bane gani nyi kamar zan takura. "

"Meye na takura acikin Aure?.... Kin Manta kema an d'aura maki aure tare dani, gashi kuma muna zaman mu lafiya."

Da dare bayan an gama hira yara sun kwanta, kizo sama kamar yadda mukayi d'azu kina jina.?"

Na d'aga kaina alamar to.

"Kiyi hak'uri kici gaba da zama dani. Idan kika tafi rayuwata zata k'ara dagulewa."

Ya Sun baci kumatu na, ya mayar da kanshi ya kwantar a k'irjina, na mayar da idanuwana na lumshe ida jin shi yana mayar da nunfashi.

Nayi saurin bud'e idanuna, na d'ago kanshi muka had'a ido, sai mukayi murmushi, gaba d'aya kunya ta kamani, na d'aga hannuwan shi na tashi zan nufi d'aki.

Ya rik'o hannuna d'aya, ya taho zai iske ni inda nike tsaye, nayi saurin kwace hannuna na nufi d'akin mu, na fad'a saman gadon da nike kwana duk da d'akin ba kowa.

Duk yaran suna wajen tsoguwa mai aiki, ni kaina na rasa me ke damuna, me kuma zanyi tunani, na mirgina na kalli fanka na kad'awar bada iska.

Shin ko wannan da Yaya yake yawan yimani wasu lokutta, shine ne auren, yana yawan jana a jikin shi,?

Na tab'e.

"Amma kuma ina jin dad'in hakan... Kada kiyadda kunya ta shiga tsakanin ku."

"Allah ko.?"

"K'warai ki tsaya kada kiji kunyar sa."

Nace, "Haka ya kamata."

Nida zuciyata muke ta hira.

Na tashi da k'yar kamar mai ciwon jiki, na fita wajen gida, na dinga zagayen gidan nan a hankali kamar lokacin da Aunty keda ciki, da nike taya ta zagayen gidan.

Kamar an ce d'aga kanki sama, ta tagar yaya, sai na hango shi tsaye ya kama k'arafan taga, jikin shi ko riga babu, da alama shima tunani yake, na d'aga mashi hannu, amma da alama bai ganni ba.

Hankali na ya tashi saboda idan tunanin shi yayi zurfi zai iya tayar mashi da ciwon shi. Nayi saurin dawowa ciki, sama na nufa da saurina har saida na shiga amma Yaya bai jini ba, harda sallamata kuwa.

Na isa na kira sunan shi Yaya, amma baiko motsa ba na dafe kafad'ar shi, tareda kiran sunan shi,
Yayi wata irin firgita harni sai da na tsorata.

"Yaya lafiya?"....Na fad'a cikin dariya Yaya ashe tsoro gareka.?

Yayi murmushi, "Wallahi ji nayi tamkar muryar Auntyn ki."

"Kenan tunani kake yi ko yaya.?"

"Ai tunani ya zama dole."

"Dole Yaya.?"

"K'warai, zuciyata ce ta kamu da son wanda bai san so ba, ita kanta zuciyar bata tab'a zaton taso wata macen bayan Auntyn kiba."

Sai naji banji dad'i ba ashe har yaya ya fara son wata ba niba.... Na b'ata rai na juya zan tafi..

"Kada ki tafi don Allah ki tsaya ki bani shawara..

"Sha warar me kuma Yaya.?"

"Rabab jeki kawai, duk, zan gaya maki anjima da dare."

"Ni bana son ka dinga tunani."

"Ya kike ji in kinga ina cikin damuwa.?"

"Hankalina ke tashi nima matuk'a."

"Hakan yana d'aya daga cikin alamomin so."

Na zaro idanuwana duk biyun, ya lumshe nasa idanun, ya bud'e tare da yin murmushi. Na zunbura baki nikuma nayi gaba abina.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Gaba d'aya muna falon k'asa, har su tsohuwa muna ta kallon kaset d'in su Ali nuhu wai shi _(Rumfar shehu_) su tsohuwa sai dariya akeyi nikuma Arwa na hannuna ina ta jijjigata har tayi bacci.

Anwar, tuni yayi bacci yana kan cinyar baban shi duk wani mitsina sai ya bini da kallo.

Da na maida idanuwana wajen Yaya, sai inga no kawai yake kallo.wanan Dalilin yasa na nufi d'akin mu, domin in kwantar dasu Arwa, bayan na kwantar dasu, nasamu minti talatin a d'akin inata game d'in wayata, sai naji kira, ina dubawa Yaya ya gani, na d'orata a kunnena.

"Yaya lafiya.?"

"Ba lafiya."

"Me.? "

"Ba lafiya."

Na tashi da sauri na nufi falo.

Yaya na kishingid'e saman kujerar dana barshi, da wayar shi a hannu sa..

Naci gaba da magana...

"Meya sameka.?"

"Falon ne yayi mani duhu."

"To me za ayi mashi yayi haske.?"

"Idan kika dawo kika zauna cikinshi zai yi haske."

Nayi murmushj, "Allah Yaya wani lokaci kaima kamar auta."

"Ya auta yake.?"

"Ban sani ba don ka dinga tsokana ta."

Na kashe wayata na samu kujera na zauna.

Bayan kowa ya kwanta sai nida ke kashe wutaccen falon k'asa, sai Yaya ya tafi ya kashe, yakuma rufe mana gida, daman mun saba haka,wani lokaci duk sai sun kwanta zan d'an yimana d'an wani abinci mu zauna muci..

Yau ma Pepe chicken nayi mana, Yaya na son shi, na d'auka mukayi sama,bayan mun gama ci, ya kunna mani kaset d'in da yake magana akan aure.

Hausa sukeyi amma na kasa gane me suke cewa kwata kwata tamkar bana zuwa islamiyya a rayuwata.

Ya kalleni "Dawo nan in rik'e ki, kada ki gudu."

"Allah Yaya nace maka bazan tafi ba."

"Taso dai."

Na tashi na koma kujerar da yake zaune nayi kwanciya ta ma.

"Me kika k'aru da abinda kikaji.?"

"Yaya Allah kuwa basuda kunya. "

"Rabab wannan shine aure, shi akeyi cikin aure ba wai zama da dafa abinci ba."

Can yana magana a kunnena, sai naji ya d'auke ni cak, ya d'ora saman gado,

Gabana naji ya fad'i, na yunk'ura zan tashi yaya ya danne ni gam a saman cinyar shi ya kama sunbatar wuyana, yana shafa gashin kaina.

"Yau ne ranar da yakamata kisan aure kema."

"Yaya wannan shi iskanci ne yake fad'a."

"Ba iskanci bane, shine aure, shi nake son yau nima muyi dake."

"Yaya.?"

"K'warai kuwa, kin manta muma an d'aura mana aure.

Nayi saurin rufe fuskata da hannayena Yaya naji ya kai mani sunbata ga bayana daidai wajen da yake bude.

Jin yana zuge zip, d'in bayana, yana bin bayan da sunbata yasa nayi saurin tureshi jikina na rawa.......
[5/1, 10:20 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

_Wannan page d'in nakine Meena Abba kiyi yanda kike so dashi..._๐Ÿ˜๐Ÿ˜


*Page 19n20*

Na mik'e nayi k'asa da gudu, ban tsaya ko ina ba sai d'akin Aunty, inda kayana suke a wardrof d'inta.

Na jingina jikin wardrobe d'in na dinga mai da numfashi, Kai na kuwa sai juyawa yakeyi.

Cikin kukana nake fad'a....

"Bana son aure!"

Na fad'a da k'arfina, na bude wardrobe d'in, na janyo rigar bacci na, ina k'arasa zuge zip d'in rigata, na wurgar da ita gefe, na cire sket d'in atamfar na Jafar dashi ma.

Sai kawai naya Yaya ya shigo, da Sauri na shige cikin marfin wardrobe ina cewa.

"Kaya zan saka dan Allah Yaya ka fita."

Ji nayi ya mayar da k'ofar ya rufe.

Nayi saurin sakin ihu, ina bude idanuwa, sai naga Yaya a tsaye, nayi sauri na fito daga cikin wardrobe d'in da rigar bacci a hannuna, amma na kasa guduwa, sai kawai na tsugunna na matse jikina gam.

Ya rungumo ni a jikin sa, sai ji nayi yafa magana...

"Kar kiji tsorona Rabab, ni mijin kine na sunna. Rabab nayi hak'urin ki gane yanda aure yake da kanki, amma na fahimci haka zamuyi ta zama dake."

"Dan Allah Yaya kada kayi mani fyad'e."

Na fad'a ina kuka.

Sai naji ya d'auke ni cak! Nasa ihu yayi saurin ajiye ni saman gado naga ya nufi k'ofar fita,

Wani dad'i ya saukar mani a zuciya, nayi saurin jan bargo sannan na lullube jikina.

Duhu naga ya garwaye d'akin, tare da alamu na kulle d'akin da makulli.

"Yaya! Yaya!!,
Wallahi na tuba.

"Dan Allah ka tai maka mani, kada kaci mutun cin rayuwata Yaya."

Jin ya runguma ni a jikin sa yasa na k'ara sakin ihu, ji nayi yayi saurin had'a bakin sa da nawa.

Nayi nayi in kwace, amma na kasa, sai ma ji nayi ya balle rigar na fulani na, ihu na k'ara Saki yanda naji yana matsar su yana lumshe ida nuwan sa, ihu nake amma bakina a toshe,

Amma Yaya bai saurare niba ,nikuma bansan lokacin da nahau dokan shi ba da dukkan hannuwana.

Wannan ma ya k'ara masa azamar kwantar dani, yasa hanna yenshi ya danne hannaye na, jin ya saki bakina yasa na ci gaba da ihu mai k'arfi, amma sai kawai naji yana karan to wata addu'a, ni kuwa addu'ar shi bata hanani ihu naba.

Yana fad'ar _"Bismillah Allahumma jannib nash shaid'an, wa jannib minash shaid'ani ma razak' na ..._ tayi daidai da wani k'wak'waran ihu dana saki, daga shi kuwa bakina ya mutu, tamkar na zama bebiya, sai dai hawaye wani na korar wani.

Za a d'auki mintuna sittin, sannan naji wani ihu na tashi, ni kaina na firgita, tunanin wake ihun, sai da nasamu 'Yar natsuwa sannan na gane Yaya ne.

Sai gani ni kuka, yaya kuka riris, ni d'in nasan ko kukan me nakeyi to shifa.

Mun d'auki yan mintuna sannan naji Yaya ya rik'o ni nayi kokuwar kwace jikina amma na kasa, yana kuka ya dinga shafar gashin kaina amma bai iya yin magana ba.

Tun ina iya kokuwar kwace kaina, har na hak'ura, ji nayi ya janyo bargo ya lullube mu dashi ya dinga sunbatar gashin kaina da na fulani na.

Bai iya yin wata magana ba sai dai naji yace.

"Sannu.... Sannu."

Haka d'akin nan yayi shiru, sautin kukan mu kawai kake ji, ba wanda ya iya cewa komai.

Nidai a haka ban sake sanin kaina ba,

Sai dai naji ana rik'eni ana salati....

"Rabab dan Allah ki tashi yayan kine bana son na rasaki."

"kiyi hak'uri, wallahi ban yi maki haka don mugunta ba ko wulak'an ci, nayi haka ne domin ta haka zaki hak'ura ki zauna auren ki."

"Rabab ina sonki, bazan tab'a iya rabuwa dake ba, ni kaina ban san lokacin da sonki ya shiga zuciya ta ba, idan har manyan mu suka san zaune muke kawai wallahi raba auren nan zasuyi.

Nikuma na riga na kamu da ciwon sonki a zuciyata Rabab bana barci, ke kad'ai nike tunani a raina.

Ya sunbaci goshina.

Da k'yar yasamu yakai kan fridge ya d'auko ruwa ya yayyafa mani.

Na Saki wani kuka mai k'arfi sai a lokacin nasan Inda nike.

"Kiyi hak'uri nima ba a son raina nayi maki haka hakan da nayi itace babbar mafita a gareni, gudun nike kada in rasa ku ku duk ku biyun ba Aunty ki babu ke.

Nidai babu abunda nike yi sai kuka raina kamar zai fita.


Ya mayar dani ya kwantar a kafa d'arshi ya zame ya kwanta ya rungume ni gam. Sai bacci...


Kafin safe zazzabi ya sauko mani ,ina kallon shi wajen asuba ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya d'auro alwala.

Bayan ya kammala sallar shi yazo Kai na yana cewa.

"Rabab. "

Na d'ago nayi mashi wani mugun kallon harara, ga ida nuwa cike da hawaye,

Ya shafa gashin kaina...

"Tashi muje In taimaka maki kiyi wanka, amma irin wanda kike yi idan kin gama period shi zakiyi banban cin su kawai niyya.

Yayi shiru zuwa wani lokaci..

'Dan Allah kada kisa tsanata a zuciyar ki don girman Allah."

Ya d'ago ni nayi alamar ya sakeni, ya daka wani wata irin tsawa, nayi Sauri zan tashi amma na kasa.

"Kibi a hankali tsaya in kamaki yayi saurin zagayo wa ya kamani ya d'aura mani towel ya d'auke ni cak sai toilet.

Bayan ya fito dani bai ajiye ni ko ina ba sai kan sallaya ya d'auko dogowar riga da hijab ya sakamin.

Da zaune nayi sallah, ina cikin lazumi naji motsin shi.
Nayi saurin kifa kaina a cinyata tareda da sakin kuka mai k'arfi.

Motsin shigar Sa toilet naji, ina d'agowa naga ya yaye bed sheets d'in ya shimfida wani.

Ina nan zaune har yagama wanke wa, ya fito ya fita waje ya shanya,

Banji motsin shigowar saba sai dai naji an d'auke ni cak babu inda ya direni sai tsakiyar gado.

Ya fice baifi minti biyu ba yadawo, tare da Tea da soyayyan kwai da magani a hannun Sa kuka kawai nikeyi.

Bai ce mani komai ba, sai dai ya tayar dani a jikin shi, a hankali ya dinga bani Tea din har nayi fam, sannan ya d'auko wasu magunguna ya bani nasha, ya maidoni na kwanta shima ya kwanta kusa dani ya maido Kai na a kirjin Sa.

"MY DEAR."

Naji wani yar, bai tab'a kirana haka ba.

"Allah yayi maki albarka.

Wannan kalmar tun jiya nike jinta a bakin sa,

"Na rasa kalmar da zanyi amfani da ita wurin gode maki hak'ik'a kin shayar dani zuma mai dad'i, Am really proud of you,"

"Rabab kiyi hak'uri da halina na kasan ce ina son matata da yawa kuma ko wane lokaci ida son naji d'umin ta."

Muyi zaman mu na jin dad'i please.


"I love you Rabab, with all my heart"

Kai nidai ban san Inda wa'innan maganganun suka tsaya ba, bacci yayi awon gaba dani.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Ina bud'e ido najini nad'an ji sauk'i,

Na kalleshi yanata faman shirin fita office.

"Ni zanje office in dawo yanzun, me zan siyo maki."

"Zanje d'aukar izinin jinya."

Ban san sanda na harare shiba yayi murmushi ya k'ara gaba,

Bayan ya fita sai naji ko in d'auki wuk'a in caka mashi, amma sai Aunty ta fad'o mani a raina.

_"Ki daina tsanar mijina, mijina na sonki, shiyasa yake yi maki fad'a..._

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Durkushe nake a gaban Abba inata zubda hawaye, Abba ya girgiza Kai tare da kwantawa, irin ta manya.

"Yaushe yayi maki fyad'en? "

"Jiya da daddare."

"Dama tunda kike zaune a gidan bai taba yimaki ba sai jiya.?"

"E Abba."

"Lallai Altab ya kyauta, ki kyaleni dashi, zan Sa yan sanda su kamo mani shi su dinga dukanshi har sai ya mutu, gawar shi ma bana son gani. "

"A'a Abba kada a kashe shi, 'ya 'yan shi zasu zama marayu, ba uwa ba uba... Ayi mani mani tsakani da shi kawai, kuma abi mani hakk'ina, sannan a warware auran da aka d'aura mani, saboda dashi yayi amfani jiya yayi mani haka.....
_To fah friends ku tayini fitar wa Rabab hakk'in ta ku sanyo wa Central tayu..._๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ
[5/1, 10:23 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

_Alhamdulillah..._
_'yan uwana masoya na masu k'aunata ina godiya da addu'oin ku gareni nagode Allah yabar zumunci..._


*Page 21n22*

"Bangane ba.?"

"Sai ya dinga cewa wai shi mijina ne an d'aura mana aure, na gaya masa auren wasa ne yak'i dainawa."

"Yan zun ki koma gida..."

"Abba ni na gama zama gidan shi har abada, yara ne dama nike tausaya mawa, kuma sun girma."

"To ai yanzu idan baki koma can ba, ya za ayi in nakai k'ara a yadda, tunda bak'ya cikin gidan, kuma kada ki kuskura ki fad'awa kowa wannan maganar kin jiko."

Na d'aga kaina alamar to.

"Bari in kirashi in maku tsakani ba ruwan shi dake, ni kuma yanzu zanje in shigar da k'ara kotu, a d'aure shi tunda bakya son a dake shi."

Sallamar da mukaji ita ta tsayar da maganar Abbana wadda tuni na gane muryar Yaya ce, gabana kuwa ya dinga fad'uwa. Ya shigo kai a sunkuye ya zauna k'asa gaban Abba,sannan ya gaishe shi,

"Ni bani amsa gaisuwar kuma ka kyauta, yanzu dama zan je neman ka in d'auke ka in kaika kotu. Kai haka akeyi shekara d'aya da wajen rabi tana tayi maka bautar 'ya'yanka, sai yanzu da rana tsakiya ka k'irk'iro mani sakar ci kawai.

To yanzu ka tashi ka koma gida, itama yanzun zan kawota, amma nayi maku tsakani ba ruwanka da ita, ka jirani zanzo da 'yan sanda a tafi dakai, komai ya dace suyi maka. Kai ko kisa ne ma ba ruwana."

"Abba nace banda kashewa 'ya'yan Aunty zasu zama marayu."

"Ba gani ba. gaki duk ma kula dasu."

"Abba ba kamar baban su ba."

"To naji tashi muje in kaiki gida."

"Abba ka bari mu tafi tare. In yaso Kai ka iso daga baya."

"Abba na fasa ni bani shiga motar shi Abba azzaluni ne."

"Shike nan tashi kaje, aci gaba da hak'uri, komai zai wuce nan gaba kad'an."

Ina kallon shi harda godiya, ya tashi ya tafi, na bishi da harara, har ya fita.

Muna tafiya Abba na magana cikin natsuwa irin ta manya.

"Ba ruwanki da shi, ba ayiwa babba rashin kunya, nasan ba halayyar kibace, kiyi zamanki wajen yaranki kamin na gama yanke hukumci."

"Abba amma gida zan dawo ko.?"

"E amma dole sai an warware auranku, in ba haka ba nan zaki ci gaba da zama."

"Abba zama ni bani k'ara zama gidan shi."

"To shikenan, sai abinda hukunci ya bada."

Ina shiga, Yaya yayi tsaye a jikin motar shi, yayi sauri ya tare ni.

"Ba zazzab'i ajikin ki ko.?"

Ya kawo hannu zai tab'a ni, na goce na harare shi, na wuce.

Ya biyo ni abaya, na nufi d'akin yara. Ya bini har can, ba kowa a d'akin na zauna kan gado fuskata a d'aure, gata a kunbure tasha kuka har ta gaji, ya iso ya tsugunna a gabana.

Yayi alamar kamo hannuna, na jaye hannuna, yayi murmushi wanda yake nuna alamar nadama.

"Rabab."

"Ni kada kace mani komai dan Allah, tunda dama dan ka cuce ni ka yarda na zauna gidan ka, Allah na gani domin in taimakawa rayuwar ka da 'ya'yan ka na zauna."

"Tsakanina dake Rabab ba cutar wa, sai dai k'auna da soyayya mai tsanani, ni kaina ban san lokacin da tashiga zuciya taba."

Ya taso ya zauna kusa dani, nayi saurin hayewa gado sosai.

_"Innalillahi..._Rabab guduna zaki dinga yi...Nifa mijin Ki ne."

"Allah ya sauwak'e."

Ya matso, na sauka da sauri, ina sauka wani irin ciwo ya dirar mani.

Nayi saurin durkushe wa tare da cewa.

"Wayyo Allah na."

Yayi wani irin sauri ya iso wajena ya kamani.

"Sai kin dinga bi a hankali..taso in kamaki kije ki kwanta ko abinci ma baki ciba."

"Bana so ni ka barni ni nan... Mugu Kawai.

Na k'ara sakin kuka.


"Ba zai yiyu inbarki cikin yara kiyi jinya ba gashi kuka yaki tsaya wa a fuskarki so kike suma su gane kin san fa sirri na da dad'i. "

"K'arama su gane ubansu macuci ne tun yanzu."

"Rabab."

Yayi tsaki ya tashi ya fita daga d'akin.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Kwana uku kenan, amma zan iya cewa gaba muke da yaya, kullun zai shigo d'akin yara, yayi tsaye baya yimani magana sai dai zanji yana tambayar naci abinci, nayi wanka.

Idan dare yayi kuma ina kallon shi zai shigo ya tsugunna ya sunbaci kuma tuna,ko ya zauna gefena ya d'age ni ya rungume ni, har ya dinga sakin wani numfashi.

Wani ikon Allah yau banji shigowar shi ba, bacci yayi nauyi da yawa, sai dai farkawa nayi naji bayana rungume gam a kirjin Yaya na gane hakan ne ta sautin tashin numfashin sa.

Nayi niyar zamewa in tafi, amma sai nayi tunanin rigima kawai zamuyi cikin dare, saboda bazai yadda in koma k'asa ba, nadai yankewa zuciyata shawara da safe zanyi tafiya ta Abuja, saboda ko naje wajen Abba wayo zai yi mani ya dawo dani, haka na hak'ura na kwanta badan raina naso ba, shikuwa yaya bacci yayi dad'i har da nasari, kenan bacci yayi dad'i.

Daya motsa sai inji ya k'ara rungume ni gam, tareda sunbatar wuyana ta baya, a haka har akayi sallar asuba, ido na biyu ya kammala sallar asuba.

Ya zo yayi tsaye yana kallona, ni kuma ina Kallon shi ta lunshe war idanuna sai da ya zauna sosai sannan yad'an shafa kafad'ata zuwa cinyar hannuna ya sunkuya ya sunbace ta.

Sannan naji yace....

"Rabab.!

"Rabab.!

"Tashi kiyi sallah."

Nayi mik'a, sannan na tashi a firgice ya rik'eni.

"Ki bi a hankali ko."

"Me yasa ka kawo ni nan ba dai wani.....

Ya rufe bakina da hannun sa.

"Bana iya bacci tsawon kwanakin da kika gujeni, hankali na ya tashi matuk'a ganin kina fushi dani, bana son fushin nan shiyasa na yanke shawarar d'auko ki.

Ta yiyu idan naji d'umin jikin ki a jikina zan iya bacci.

Na kalleshi kallon bak'in ciki, na tab'e fuskata tare da sakin tsakinnan na cikin zuciya sannan na sauka daga gadon shi.

Ban tsaya sallah ba nayi k'asa abina yana tsaye shi kuma yana kallona.

*** *** *** *** ***

Sai da muka iso Abuja, sannan na kunna wayata, shima dan inga k'arfe nawa. Karfe 4:00 na yamma, kiran Yaya naga ya shigo, banda message's da dama na gani a wayata,

Nayi saurin kashe waya, sannan na tari mota sai unguwar su Aunty ban iya gidan taba sai k'arfe 5:30 na yamma.

Tun daga get na maigadi ya shiga da gudu, sai gasu duk sun fito.

Aunty ta kalleni irin kallon tambaya...

"Daga ina kike.?"

"Daga gida."

"Wa kika fad'awa.?"

"Ba kowa."

"Wai ke miyasa bakijin magana, kinbi duk kin tayar da hankalin mutane.

To mijin ki na can ya fad'i in kin kashe shi ai kin huta.shigo muje ciki in gaya wa Abba ko hankalin shi ya kwanta, so kike ki kashe su ki huta, idan bakya son uban naki mu muna son shi, sun kirani yakai sau ashirin kin zo yan zunnan shirin tafiya nike gobe.

Har muka shiga ciki tana yimani fad'a, nasamu kujera na zauna na dinga kukana, ita kuwa sai fad'a take tayi tak'i tayi shiru.

Ina jin tana cewa Abba gatanan ta iso yanzun.

"To Abba zanyi insha Allah."

Ta kashe wayar..

Sai naji tana cewa.

Ilham ina daddyn ku, nasan bashida lafiya bashi kice masa nice. gatanan ta iso yanzu, amma ba abinda ta gayamin, amma Abba yayi mani bayani, kayi hak'uri yarin tace da rashin wayo, to Allah yabaka lafiya to bazan yi mata komai ba ai Kai da Abba ku kuka d'aure mata gindin wannan sakarcin, ni bata yi mani shi nan to sai ka kira... Allah ya tashe mu lafiya. Amiin.

Ta waigo ta kalleni....

"Ki tashi kije kiyi wanka kici abinci, ai da gaskiyar Altab d'in da yake ce maki shasha sha, wannan wawanci haka ni wallahi ban Tab'a jin hauka irin taki ba."

Anya kuwa kwakwalwar ki nada lafiya.?

Sai na kaiki asibitin masu hankali an auna min ke, gaskiya shirmen ki ya wuce hankali.

Nidai naja akwatina na bar ta nan tana fad'a...

K'arfe 8:00 na dare,bayan na kammala sallar isha Aunty ta shigo, ina zaune saman abin sallar ma ban tashi ba, tace inna kammala in sameta d'akin ta, na amsa da to.

Ina shiga ta mik'a mani wayar ta.

"Ki bude wayar ki in kin tashi, daga nan yanzu ki k'arba ana magana."

Na k'arba na dora a kunnena.

"Rabab."

Ban iya amsawa ba.

"Kina so nima in barmaki duniyar irin na Aunty ki ko, kin tayar mani da hankali, gani nan yanzu haka bana iya ko tashi tsaye, don Allah kiyi mani magana ko zuciyata tayi mani sanyi."

"Ina wuni.?"

Ya saukar da ajiyar zuciya mai k'arfi.

"Na gode, ki bud'e wayar ki zan kira da anjima, ki daure dan Allah."

"To."

"Sai na Kira."

Na kashe wayar na mik'awa Aunty.

"ki zauna sosai ki baza kunnuwan ki ki saurareni. Rabab lokaci yayi daya kamata ki fahimci komai na rayuwa.amma Allah yayi maki kwakwalwar yara, har yau kwakwal warki tana aikin 'yan sheraka sha biyu, wata 'yar shekara sha biyun tafiki sanin yakama.

Ni na gaji da b'oye b'oyen da ake yi maki yau zan fito fili in sanar dake komai.....
[5/1, 10:23 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 23n24*

"Rabab Altab shine mijin ki na har abada, shi muka zab'a maki ya zamo mijin auren ki, saboda halayyar shi na kirki da sanin yakamata, Altab ba azzalumi bane, kuma Altab ba fyad'e yayi maki ba, ban ma san Inda kika samu wannan kalmar ba."

Kada ki k'ara amfani da ita a bakin ki, abinda Altab yayi miki yayi bisa ka'ida ta addinin musulun ci, wannan kuma shine aure da kikaji ana fad'a, shi nike yi nan,

Ikram ma Allah yajikan ta, itama shi tayi, kowace mace a duniya shi takeyi.shin in tambayeki me Allah ya rage Altab dashi ne.?

Yaro ne dai ba kyace mashi tsoho ba, shekarun sa na haihuwa in sunyi yawa su Kai arba'in, saboda yana d'an shekara ashirin da shidda ya auri Auntyn ki. Kije ki zauna ki karanta Altab a zuciyar ki, me Allah ya rage shi dashi.

Wallahi a mazan nan na zamani, samun kamar Altab sai an tona Altab yana da son k'yautatawa iyalinsa, yanada kulawa wadda ita kike cewa mugunta, wallahi dukkanin mu Ikram tafi mu more aure.

Kiyi hak'uri kije ki cigaba da yiwa Altab biyayya, zakiji dad'insa a nan gaba sosai ma, kuma wannan da kike gani a hankali ake sabo dashi, sai kin daure.

Altab ga kyau ga hankali, ga kud'i daidai na kulawa da iyalinshi da 'yan uwa da iyaye, ga kulawa, gashi da ganin yanda yakeyi yau kad'ai ma kin San ya kamu da sonki.

So shine duk wani motsin da zakayi mijin ka tamkar ya had'iye ka, idan bakida lafiya kuwa, kusan tare zakuyi jinya ga son ya matso kusa dake, bai ki kullun yana rungume dake ba.

Babu zancen raba aure har abada, kuna tare da Altab sai dai idan mutuwa ta rabaku, kuma komai yayi miki bakiji dad'in saba, shi zaki gaya wa ba Abba ba,

Rabab kina da ladabi, ga kunya, kina da sanin yakamata, kinga abinda kike wa Altab na kulawa to ki k'ara da yawa.

Abincin shi ya zamo na musamman, zannuwan gado ma haka, kullun ki gyara gida da jikin ki dana mijin ki. In zai fita ayi rakiya, shagwab'a tana karasa miji ya k'aunace ka, ki yawai ta kallon kasusuwan da zaki ga yanda ake kulawa da miji, da akwai littattafan da zan baki duk ki karanta, ki tallafi mijin ki, ki nuna masa kulawa kema zai kula dake.

Altab a yanzu yanda na lura, ko ince yanda ya fad'a bazai iya rabuwa dake ba."

"Aunty an tab'a yin aure ba biki ba Kai amarya, kuma da kayan Aunty zan yita rayuwa.?

"Rabab ke kikace ba k'yason buki, in kina so yanzu ma sai ayi miki, amma sai dai ayi shi anan Abuja, saboda 'yan katsina Sun san tuni kinada aure, har na shekara d'aya da watanni."

Kiyi hak'uri wasannin soyayya duk Altab zai koya miki, haka sukayi da Auntyn ki har ta koya.

"Aunty yanzu babu haramci ga auren mu tunda aunty yaya tace.?"

"Babu haramci a yanzu tunda ta rasu, da dai tanada rai shine haramun, amma yanzu musulunci ya halatta hakan."

"Aunty yanzu ba aci amanar Aunty ba.?"

"Ba wata amanar ta da kukaci, kin Manta da kissar 'ya'yan manzon Allah (S. A. W.), da sayyidina Usman (R. A.) ya auri Zainab ta rasu ya k'ara auren Ummussalma ita ma ta rasu, har manzon Allah (S. A. W.) yace da yanada wasu 'ya'yan daya dinga aura mishi, kin ga kuwa da haramun ne da manzon Allah (S. A. W.) ya hana.

Yanzu bazaki koma ba sai nan da sati biyu, anyi maki kayan d'aki, an cire na matayu, kuma anyi yinin biki, sai akai amarya katsina zanyi magana da Abba.

Zanyi dashi Altab d'in nasan zasu yadda, sai dai ki dinga d'aga wayar shi tare da amsa mai kyau, nasan k'ilan yazo, in yazo ki saurare shi, Rabab nayi maki murna kwarai da gaske. Yanda bakida wayau da ba Altab bane ban san yanda za ayi zaman auren ba. Idan zaki tunano Altab, ki lumshe idanuwan ki, kifara karanto fuskar shi, idanuwa, yanda yake magana, kalarshi, murmushin shi, idan kina haka zakiji kema kina son shi. So shine zakiji idan mutun ya fita kiji kin kagara ya dawo, wani lokacin ma tamkar kada ya fita.ke sona da yawa sosai.


A hankali zaki fahimce su sosai, nan gaba ma sai kin sanyawa Abba albarka da duk wanda yasa baki a silar auren ku.

Aunty ta dinga karanto mani, dad'i da ma'anonin aure, da kuma wahalar shi tunda ibada ce mai kaiwa aljanna, da kuma yanda zan zauna lafiya da 'ya'yan shi.

Muna cikin magana kiran wayar Altab ya shigo. Aunty tace in tashi inje in amsa wayarshi, in tabbatar nayi mashi sannu da jiki.

Wai ana cewa ba'a ganni ba ya fad'i ya suma, da k'yar aka same shi.

Nan na tashi na nufi d'akin da nike sauka, kenan d'akin yaran ta duk da basunan suna makaranta.

Na d'auka tare da cewa...

"Hello."

"Ko kinyi bacci.?"

"A'a."

"Me kike kallo.?"

"Ina wajen aunty ne.? "

"Ta gaya maki ni Mijin kine a yanzu.?"

"E. "

"Kin amince da hakan har zuciyar ki.?"

"Ni.?"

"Ke me Rabab ya kike son inyi kina son nima in mutu ki huta.?"

"Ka san dai bana son maganar mutuwa ko."

"Rufe idanuwanki k'anwata, ki kwanta a rigingine zan fad'a maki wani sak'o."

"Nayi yanda kace."

"I really miss you, na daina jin d'umin matata, na kasa komai saboda ba kya kusa dani kina tunanin zan iya ci gaba da rayuwa bada ke ba ki dawo gobe ki rungume ni a jikin ki ko na samu saukin ciwon rashin ki."

Na saukar da numdashi saboda ni ban ma san amsar da zan bashi ba.

"Yaya ka daina kaga ina jin kunyar ka."

"Ki cire kunyar nan bana sonta, ki koyi zama dani."

"Yaya."

"Na'am dan Allah ki dawo gobe, ko in turo a d'auke ki, ni ban iyawa da cikin daren nan zan taho, nayi kokari tun d'azun amma na kasa."

"Ai Aunty tace bazan dawo ba sai...."

"What.?"

"Meya faru, me nayi mata nadai nufin ta a rabani dake ba kar kisafa kafin safiya sai gawata."

"Yaya kana son mutuwa Kai dai dan kasan bana son ka mutu."

"Saboda mi baki son in mutu, bancin ba k'ya sona."

"Nifa ban san shiba."

"Shi wa.?"

"Shi wanda ka fad'a."

Yayi murmushi.

"Zan shayar dake shi, har sai kin k'oshi, tunda Allah ya jarebeni da sonki fiye da rayuwata yanzu miyasa Aunty tace haka.?"

"Ka kirata zata gaya maka."

"Bani minti goma. Wash!"

"Yaya kasan dai bani son in ganka bakada lafiya ko."

"Me kike ji.?"

"Hankalina ke tashi matuk'a."

"Irin wannan kulawar taki ita ta jani ga sonki tunda dad'ewa, na gode ki jirani kada kiyi bacci."

"Me kuma zanyi maka, nima fa banida cikakkiyar lafiya."

"Na sani.. Harda shi yasa hankalina ya tashi, saboda ina son jinyar matata a kwance saman k'irjina."

"Yaya."

"Kiyi hakuri ina yimaki ne don ki saba kema ki dinga yi mani nan gaba, tsaya in kira Aunty. "

A yanda nake kwance ban ko motsa ba na mayar da idanuwana na lumshe..

"Me yasa ake son yimani aure alhalin ansan bana son shi.?"

"Saboda shine rahamar 'ya mace."

"To yanzu ya ya zanyi da yaya Altab a matsayin mijin aurena.?"

"Ki so shi kawai, kiyi hak'uri da kalar rayuwar shi tun yana baki haushi har ki daina ji."

"Yan zu kina ga zan iya zama da wanda na tsana a baya."

"A baya kika ce ba a yanzu ba."

Wayata ita ta tsaida ni shawarar da nike da aminiyata, zuciyata kenan."

Na d'ora waya a kunnena...

"Nifa fa bazan iya jure sati biyu ba k'ya nan ba, kin san ko yara ma basa yarda. "

"Ka gayawa Aunty haka.?"

"Na gaya mata sai tace wai........
[5/1, 10:25 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 25n26*

"Na gaya mata, sai tace, wai yin hakan yanada fa'Ida tsakanin mu."

"Yaya"

"Na'am k'anwata ina sane kina jin haushina, bazan baki hakuri ba sai na ganki a idanuwa na."

Nan ya dinga surutun da jinsa kawai nake, wasu bazan tab'a iya mayar masa da amsa ba.

Yau kwanana ukku a Abuja, amma kullun muka zauna da Aunty hirarta kwatanta mani rayuwar aure.

Haka Aunty fa'ik'a data zo daga kaduna, ita ma haka ta yimani tata nasihar da koyarwa.

Wata k'awar kuwa, kausar ita gidanta ta tafi dani ta dinga fad'a mini abubuwan da Aunty batama fad'a mani suba, a ranar ta kaini wani salon na gyara gashina.

A salon d'in tasa akayi mani wani abu, wanda naji suna cemasa dilka, suka koya mani kwalliya ta siya mani ket d'in kwalliyar gaba d'aya.

Bata maidani gida ba, sai dare, harda yi mani d'inkin gaggawa, tace in sa shi gobe tunda safe inyi irin wannan kwalliyar da aka koyamin.

Ina shiga gidan Aunty, Aunty da 'ya'yan ta suka dinga yabawa wai nayi kyau duk na nuna masu abubuwan da ta siyamin hadda su, English Wears, aka yaba kaya na shige d'aki, nayi wanka na saka kayan baccina.

Na haye gado na duba sak'on da Yaya ya turomin.

_"Ina kika shige, kika ajiye mijinki shi kida'a ki kirani idan kin natsu bey._"

Ban san lokacin da na mayar da idanuwana na rufe ba, sai gashi ina karanto waye Altab nida zuciyata.

*** *** *** *** ***

Altab khidir haifaffen cikin garin Agadez ne ,mahaifin shi cikakken wayayyen d'an kasuwa ne, gashi kuma yayi ilimin zamani gwargwado, bai tab'a aikin gwamnati ba, sai dai zamani yasa yazama hamsha k'in d'an kwangila.

Sai dai 'ya'yan shi duk karutu sukeyi, matar shi d'aya tak, mahaifiyar Altab. ita ma buzuwa ce ta cikin garin nijar, fara ce tas da gashin ta har tsakiyar bayan ta ga kyau ga kirki, 'ya'yan ta uku kacal.

Kasuwan ci ne ya kawo su katsina, mahaifinshi ya girma sosai sai dai daka ganshi kasan akwai jin dadi har yanzu.

Na juya tunanin, ya ya Altab yake..?

Altab farine tas kamar mahaifan sa, tamkar larabawa, gashin kansa irin na larabawa ne a kwance yake koda kuwa ya aske sai ka ganshi a kwance.

Altab dogone shi yana da 'yar kiba kad'an, idanuwan shi kuwa tamkar mai jin bacci, bakin shi daidai fuskar shi, idan kuwa yana magana dalla-dalla yake yinta shekarun sa na haihuwa zasu Kai Arba'in.

'Yayan shi uku harda 'yan biyu, Altab mutun ne mai son kulawa, na gane hakan ne ta zaman nan da nake dashi.

Nayi tunanin dole Altab ya kamu da sona, saboda kalar shirme na. Na tuna da ranar da yadawo daga office, riga da Wando ne a jikina, wandon jins ne, rigar kuwa mai dogon hannu ce body hook, dama tubarkalla inada na fulani a k'irjina, rigar ta fito dasu sosai, ga daga gaba Sun had'u sun bada tsakiya.

Dama idan yadawo, duk aikin na nikeyi sai na raka shi sama, sannan indawo k'asa, yawanci kuma yara sun tafi islamiyya, in alhamis da jumu'a ne suna wajen lelensu, har sai ya gama cin abincin shi ya huta sannan suzo.

Ranar sai yace na yanke masa farce, na zauna k'asa na kama yankan farce, duk d'agowar da zanyi sai inga yana kallona. Har na Kai da cewa ya daina kallona. Sai yace wai kaya nane sunyi mai kyau nima sun mini kyau, nace na gode naci gaba.

Dare na yi kowa yayi bacci, nikuma da akwai ni da bin gida naga ko anbar wani abu a kunne, ko kulle k'ofa kamar dai yanda naga Aunty nayi.

Ina fitowa falo, sai na hango fitilar sama a kunne, kuma rigar bacci ce ajikina sai kawai na haye abina dama kuma ya saba ganin hakan.

Wani lokaci yace in dinga rufe jikina saboda aljannu, ashe shine babban aljani, ina shiga d'akin sa na same shi yanata juyi yana wani irin nishi.

Hankalina a tashe na isa na kama shi da tambayar meya same shi?

Sai yace k'irjin shi ke ciwo wai dama yakan yi, a cikin tashin hankali na tambaye shi wane magani yake sha.?

Sai cewa yayi wai ya k'are, amma idan na kwanta saman k'irjin na matse shi zai samu bacci, haka na kashe fitilar d'akin nayi yanda yace bai daina wannan juyi ba sai ma ya k'aru.

Ganin ya matse ni gam har jikin shi ke rawa can naji yayi wani irin ihu, har saida na tsorata, can sai naji yana bacci.

Gudun kada in motsa ya tashi haka na hak'ura mak'ale a jikin shi, nima bansan lokacin da bacci ya d'auke niba, sai da asuba duk muka tashi.

Ko ajikina, ni tambayar shi ma nayi yaji sauk'i.?


Ya amsa mani da eh.

Sai yanzu duk nakejin kunyar shirmen danayi, nayi murmushi na juya na rungume filo, a take na tuno ranar da zan gudo Abuja.

Irin yanda ya dinga lallashina, tausayin shi ya kama ni, nan take na bai wa kaina laifi, saboda ni na janyo Yaya a jikina har yayi sabo da sona ya shiga zuciyar shi.

Nan take bacci yayi gaba dani sai safiya....

*** *** *** *** ***

Tunda wuri na shirya Jikina, Aunty ta sakani aiki a kitchen nayi mata danbun dama, da shinkafa da pepe chicken, na kammala wajen 11:00 na shaga d'aki na k'ara gyara jikina da fuskata, ganin na saka sababbin kaya..

Atamfa ce ajikina tayi mani dab-dab a jikina tayi mani kyau matuk'a abinka ga farar fata, na k'ara taje gashin kaina, na d'aure shi na sake shi a bayana, na d'auki janbaki na saka a bakina. Sai naji kiran Aunty a falo nayi saurin fitowa na nufo felon.

Nayi tsaye cak a daidai lokacin da idanuwana suka hango farin kyakkyawan mutun a tsaye.

Babbar riga ce a jikin shi farar shadda, sai kuma bak'ar hula, a saman kanshi, ganin nida shi an rasa mai matsawa, Aunty tazo ta wuce ciki, ta barmu a falon.

Ina kallon shi ya taho wajena, amma na kasa koda matsawa, har ya iso inda nike ya tsaya yana kallo na, no kuma na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannu na.

Ya matso dab dani, nayi sauri zan tafi. Ina jinshi yayi saurin rik'o hannuna, ni kuwa nayi alamar tafiya, a hankali ya matso inda nake.

Ina ji ya sunbaci bayan hannuna, nayi saurin mayar da idanuwana na lumshe, kamin inyi wani tunani ya rungumo ni ta bayana..

Naji yace.

_"Innalillah Fatabara kallahumma ahsanul khalik'in tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan sura...._"

Tare da saukar da ajiyar zuciya sai da ya Kai mani sunbata a kunne na sannan naji yace.

"Kiyi mani hak'uri Rabab bazan k'ara yi maki abunda ba kya so ba."

Na kwace jikina alamun zan tafi, yayi saurin juyoni na kalle shi yasa hannuwan shi ya rallabo fuskata.

"Kinyi mani hak'uri k'anwata.?"

Na d'aga mashi Kai alamar "Eh."

Yasa hannu ya tallabo hab'ata, ya d'ago fuskata sama.

"In shanye janbakin ki in shafa maki wani.?"

Kafin na bashi amsa sai naji ya fara kissing d'in bakina yana saukar da wani irin numfashi kamar wani mayun waci..

Nayi sauri na k'wace kaina, na shige ciki...

Ina jinshi yana kirana amma na kasa dawowa,

Ina shiga d'aki na zauna saman gado naji kamar numfashina na neman tafiya na mayar da idanuwana na lumshe.

"Yaya Altab"

Na fad'a a fili...

Nayi saurin bude idanuwana jin wayata na k'ara. Ganin Aunty ce ke kirana nayi saurin d'orawa a kunnena...
[5/1, 10:26 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_


*_kada ka la'anci duk wanda ka gani a cikin tarkon shed'an, rok'ar masa gafara da shiriya a gun Allah, domin kai ma baka wuce shiga cikin tarkon ba..._*
*_Nasiha ce:_*๐Ÿ‘Œ


*Page 27n28*

"Kina ina.?"

"Ina d'aki Aunty."

"Ya kika barshi a falo shi kad'ai.?"

"Aunty kunya nikeji."

"To fito ki Kai mashi wani abu yaci ko, tun k'arfe biyar na asuba ya baro katsina a hanya yayi sallar asuba."

"To Aunty kema ki fito dan Allah."

"Naji ganinan fitowa."

Na tashi na saka hijab a jikina. sannan na fita.

Yana zaune, ya kwanta bayan shi jikin kujera ya lunshe idanuwan shi.

Jin motsin shigowar mu yasa ya bude idanuwan shi, daga kwancen nan yabimu da kallo tamkar marar lafiya.

Na isa wurin shi na ajiye babban Faranti a gaban shi, sanna na tsugunnan na fara zuba mashi, shinfaka da miya, sannan nazuba mashi fruits salad a cup, sannan nace..

"Yaya kaci abinci."

"Bana iya cin abinci k'anwata."

"Saboda me.?"

"Saboda kin rikita mani lissafi kwata kwata, sai dai kibani kamar yanda kike bani idan banida lafiya, k'ilan in iya ci."

"Yaya nan fa gidan mutane ne."

"Ki barshi kawai na k'oshi, k'ilan anjima anci."

Na ajiye filet d'in abinci, na mike raina a b'ace.. Yayi saurin rik'o hannuna.

"A yi hak'uri zanci kada ayi fushi dani, in fita da mota idanuwana su kasa gani."

"Yau zaka tafi ne.?"

"Haka nike so in ya samu, saboda na baro 'yan aiki a gida."

Na sa hannu na sab'ale hannunsa daga nawa. Sannan nace

"A sauka lafiya."

Nayi gaba zan tafi, yayi saurin tarar gabana.

"Bana son inga kina fushi dani, na hak'ura da tafiyar sai gobe. Amma ki sani da anyi la'sar zamu fita."

"Ina zamuje ne.?"

"Yawo."

"Kai Yaya nifa kunya nikeji."

"A baya ne yakamata kiji kunya, amma a lokacin sam baki damu ba wani abun in kinyi shima nike jin kunya, yanzu kuwa ai kowa yasan ke matata ce, ke kanki yanzun kin amince dani mijinki ne."

"Waya gaya maka.?"

"K'awarki."

"Wacece k'awar.?"

"Zuciyarki, na lura zuciyarki kawai kika yadda da ita, ita kad'ai kike shawara da ita."

"Gidan mutane ne fa."

Ya ja hancina, ya koma ya zauna.

"Bazan iya binka ba. Allah kunya nake ji."

"To shikenan."

Ya zauna ya cigaba da cin abincin shi, ni kuma na tafi d'aki na zauna, amma sai naji duk banida wata natsuwa. Ina cikin wannan tunanin sai ga Aunty ta shigo.

"Rabab ya kika barshi shi d'aya, daga yau idan an kaiwa miji abinci zama ake har sai ya gama ci."

"Aunty..."

"Aunty me.?"
Ki tashi ki tafi kawai.

"Aunty ni gaskiya.... "

"Ke gaskiyar me taso muje in bai gama ba, Ki Kai mashi kayan abincin sashen bak'i, in kuma ya gama ki raka shi can.

"Aunty."

Ta zauna ta dafa kafad'ata.

"Rabab kiyi hakuri, ki daure nasan sabon al'amari ne ya sameki, ki sani muna 'yan uwanki duk sabo yake a wajen mu, ki d'auke shi a matsayin k'addara kawai, kije ki zauna ki fahimci mijinki. Altab bashida matsala ko d'aya a rayuwa, sai dai ta ajizancin d'an adam na yau da gobe."

Hawaye suka tsiyayo daga kumatuna. Aunty ta jiyo da fuskata da hannayen ta, tasa hannu ta goge mani.

"Sam zuciyarki ta daina karanta maki za aci amanar 'yar'uwar ki, musulunci ya amince da haka, kuma na karantar dake hakan a baya."

Ta kama hannuwana ta tashe ni tsaye, tare da Sa gefen hijab d'inta ta share mani hawayen fuskata.

"Ki sani Allah kike bautawa bani ba, ba shi ba.

Sai da ka kawo ni har bakin k'ofar d'akin, sannan ita kuma ta koma.

Takun tafiyata yasa ya d'ago daga kwanciyar da yayi saman kujera, haka ya janye k'afar shi d'aya daya mik'ar da ita tamkar mai wani gaggarumin ciwo.

Yayi murmushi, hakan yasa nima na lunshe idanuwana, na Bud'e tareda d'an murmusawa ta.

"Yaya ashe ba abinci kake ciba.?"

"Taya zan iya cin abinci ba kya kusa dani."

Ya rage sautin muryar shi.

"Rabab keda 'yar'uwar ki kun koyar dani wani abu mai wahalar dainawa."

"Me kenan.?"

"Ikram idan ta kawo min abinci zama take kusa dani, sai ta tabbatar na k'oshi take tashi.

Haka dana rasata, k'anwarta Rabab ita ma bani abinci takeyi a bakina, har sai ta tabbatar na k'oshi.

"Yaya.... Na fad'a cikin sautin shagwab'a.

"K'arya nayi Rabab.?"

"Ni bance ba..amma ai lokacin bakada lafiya ne."

"Ko lafiya k'alau ana bani."

"Ai.... ai..... Lokacin bana son inga kana cikin damuwa."

"Yanzu kuma kina son ganina cikinta, ta ma kashe ni ki huta ko.?"

Nan take na d'aure fuskata, alamar naji haushi.

"Sorry, kada kiyi fushi dani, wallahi ba kiji yanda gabana ya wani daku ba ganin kin had'e fuskarki ba."

Nayi murmushi.... "To kada ka k'ara."

"Dan Allah Yaya kaci abincinka, kaga bakada cikakkiyar lafiya."

"Rabab jiran matata nikai tabani a baki."

Na jinjina Kai tareda kad'a idanuwana ina murmushi, sannan nace...


"A taimakawa wannan matar saboda tana jin kunyar gidan mutane."

"Dan Allah kiyi shawara da aminiyar ki ta amince mu fita yawo."

"Ai ka rabani da ita... Kace yanzu kai ne aminina."

"To ni nace kizo mu fita yawo."

"A'a sai anyi bikinka da dani."

Yayi dariya...

"Rabab kina burgeni sosai, ki kan k'ara shiga raina, duk bayan sakan d'aya."

"Ni ka daina."


"Rabab dole nefa in nuna maki abunda ke cikin zuciyata."

"Yaya amma ba irin na Aunty ba ko.?"

"Tabd'i, lallai ai ya ninka na Aunty sau d'ari ma."

"Kai Yaya."

"Rabab sai dai kiyi hak'uri, a hankali zaki saba, da yardar Allah."


"Ni...? "

"Ke.....ya kwaikwayi muryata mukayi dariya."

Da k'yar na samu yaci abinci, haka ma dana rakashi madaukin shi sai da ya nemi in tayashi zama na k'iya, da k'yar na tsaya yayi mani wasu 'yan tambayoyi game da lefen da zai yi mani.

Wani in naga dama in bashi amsa, wani kuma inyi shiru a haka dai har na samu na gudo falo, inda shima ya biyo ni.

Falo muke amma kad'an kid'an muke kallon juna muyi murmushi, hakan yasa nayi sallama dashi na tafi d'akin baccina.

*** *** *** *** ***

K'arfe 12:30 na dare, naji wayata tayi k'ara, nayi sauri na d'auka, saboda kada ta tashi 'yan d'akin, ko tsayawa dubawa banyi ba saboda zuciyata tabani Yaya ne.

"HMN!... Haka kawai nace dana d'orata a kunnena."

"Na kasa bacci Rabab, kin riga kin shagwab'ar dani, kullun dare sai kin zo kin sani bacci kamar k'aramin yaro amma kin janyeni daga rayuwarki, kinyi mani adalci.?"

"Sorry, a lokacin baya ban saka a zuciya da wani suna na daban ba, bacin sunan yayana, mijin yayata, wacce ta rasu ta barka, tausayinka da son inga kana cikin walwala shi kad'ai ne acikin zuciyata."

Ya d'anyi shiru sannan yace.

"To yanzu fah.?"

"Ai yanzun sunanka, da zaman danayi da Kai a baya ya canza salo."

"Wane salo ya canza.?"

"Mhn!"

"Ban yarda da irin wannan maganar ba, ki fito ki sanar dani sirrinki da aminiyar ki."

"Yaya."

"My lovely sister, tell me please."

"Ni ma! Ni ma... "

"Ke ma me.?"

Yayi murmushi cikin waya.

"Tell me please."

"Yaya zan fad'a maka amma ba yau ba."

"Bashi."

"Na yadda."

"I love you Rabab."

"Yaya."

"Nasan ba kyaso, amma ki d'auki hakan a tarihinki na baya, saboda yanzun kin shigo fagenshi."

Nayi murmushi sannan nace..

"Yaya ka kwanta kayi bacci."

"Rabab ki tuna idan na kasa bacci irin haka, me kike yimani inyi bacci.?"

"Ka mayar da wannan tarihi."

"What?.. Karma kisa yanzun in buga muku gida da an bud'e ince matata."

Nayi dariya har saida na mirgina nayi rigingine.

"Kina ganin wasa nake yi ko.?"

"A'a ban isa fad'ar haka ba. Allah huci zuciyar ka saura kwana Nawa akawo maka amaryar ka.? "

"Ya sa wata irin dariya sannan yace.....
[5/1, 10:26 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)


*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Wannan page d'in nakune 'yan group d'in NIDA ZUCIYATA, da duk wani masoyin shi, ina godiya da soyayyar ku da addu'oin ku gareni, Allah yabar zumuncin k'auna..._*๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜


*Page 29n30*

"Rabab gobe zamu tafi gida, wallh na matsu naji d'umin matata".

Nayi shiru, "Ban gane ba?"

Ni gaskiya ban yarda ba ka Tab'a ganin inda akayi aure ba biki.?

"Kwarai ko, Rabab biki bidi'a ne, d'aurin aure shine aure, kuma an d'aura mana tun kusan shekara biyu da suka wuce."

"Ni dai.... Na fad'a cikin shagwab'a.

"Don Allah kada kiyi kuka na sanki, yanzun kina iya yimin kuka ganin bana kusa."

"To ba kai bane."

"Zolayar ki nake, za ayi buki, har aje fati, zaki gayyaci k'awayen ki ko?"

"E Aunty tace fa za ayi, amma a nan Abuja za ayi daga nan sai mu dawo nan katsina."

"An gama gimbiya, sai kuma me"

"Amma zaka zo ko?"

"Ai ni da so nayi na zauna nan hai sai ranar tafiya. "

"Kai sai fa nan da wata ukku."

Ya saka wata dariya da har saida na firgita.

"Yaya lafiya, Kai dawa?"

*"NIDA ZUCIYATA*."

"Kai ma ashe kana shawara da ita.?"

"Bana shawara da ita, kece zuciyar tawa, kina ganin mutun zai rayu ba zuciya a jikinshi."

"Sosai ma."

"Rabab ni bana iya yin wata ukku ba tare da keba, ki ma canza shawara".

"Yaya ai.... "

"Rabab, idan zolaya ta kike ki daina kawai, kada ki Sa cikin daren nan in had'a maki katsina ta waya".

"Allah yaya ba zolaya, ka tab'a ganin aure ba shiri?"

"Shirin me zakiyi wanda sati d'aya bai ishe kiba?"

"Yaya Allah..... "

"kinga sai da safe! Kada ki sa in mutu kafin safe".

Na kurawa wa waya idanuwana tare da tambayar, me Yaya ke nufi da aure cikin sati d'aya, kamar ba auren 'yar mutun ba, to kuma meye na fushi haka."

Take naji raina bai min dad'i ba, saboda ganin Yaya yayi fushi dani.

Take na daddanna waya na kira shi amma harta gama ringing bai d'auka ba, sai da nayi kira ukku amma yak'i d'auka.

Sai na yanke shawarar bara na kira Abba.

Abba cikin muryar bacci ya amsa waya.

"Yaya auta?.

"Abba ba Yaya bane ba?"

Na sa mashi kuka.

"Dakata! Dakata!! daina kukan tukunna gaya mani yaya akayi.?"

"Wai don nace mashi sai nan da wata ukku za ayi hidimar buki, saboda shirye shirye, sai yayi fushi."

"Me yace maki?"

"Cewa yayi wai nan da sati d'aya ya isa."

"To sai kika ce me.?"

"To shine nace mashi, da akwai shirye Shirye da yawa shine ya kashe waya, na kira shi sau ukku yaki d'auka."

"Rabab, ki k'yaleni da shi, sai naci mutuncin shi, ke ni idan har ya nemi takura ki ma zance an fasa auren kwata kwata. "

"Abba ba haka nake nufi ba."

"Na sani, ni kedai na fara gajiya da halayyar shi."

Nasa kuka, "To ya isa Ki k'yale ni dashi kinji ko, insha Allah zan kira shi yanzun zanji meye."

Za'a samu mintina sha biyar zuwa ashirin, sai naji kiran waya, a take naga sunan Yaya, har naki d'auka sai dai na d'auka.

"Rabab meyasa kike son had'ani da Abba, idan munyi abu tsakanin mu.?"

"To bakai bane kayi fushi."

"To sorry, sai da safe mayi maganar."

"Bacin ma... Sai nasa kuka."

"Rabab kiyi hak'uri na amince da yanda kike so, shi ke nan ko."

"To bacin kayi fushi."

"Na huce, kuma bazan k'ara yin fushi dake ba har abada, wannan ma na matsu ne in ganki cikin gidan ki, ko na samu natsuwa, wallahi na rud'e na zauce, na sukurkuce, sosai saboda bani da wanda ke kulawa dani.

Tunda kika taho, kuka, kwanciya, sune abokan rayuwata, sai yau d'innan nasan naji farin ciki a raina, saboda inada yak'inin na sameki ba kamar abaya ba, da nake ganin tahowarki na iya zama sanadiyyar rabuwata dake.

Yayi shiru, sai da safe kada in hanaki bacci, saboda ni nasan bazan tab'a iya yinshi ba, tun daga yau har nan da wata ukku, da kike buk'ata.

Ya kashe wayar..

Take naji tausayin shi ya dirar mani a zuciya, na mayar da waya na d'ora a k'irjina tare da saukar da ajiyar zuciya na mayar da idanuwana na lumshe.

Ba kalar tunanin da banyi ba, hira kuwa nida zuciyata ba wacce banyi ba, wata ta bani amsa, wata kuwa banida amsa, a haka har aka kira sallar asuba.

K'arfe 8:00 na safe Aunty ta shigo ta sameni akan abin sallah, tunda nayi sallah ina nan ban tashi ba, na gaisheta ta amsa, sannan tace inzo muje kitchen mu had'a wa Yaya breakfast.

Muna kitchen naji tafara magana...

"Rabab meyasa kike son tayar da hankalin mijinki dana mahaifinki, kin san Allah akan irin haka zaki iya sa su kamu da wata cuta, ko kuwa bugawar zuciya.

Rabab dan kinga suna sonki, sun damu da duk wani motsinki, kinyi kuskure tun farko, ke kika koyar da Altab ya soki, yazo ya kamu da ciwon sonki, duk wanda ya rasa mata kamar Ikram, yasamu wacce tafita komai sai ta ja ra'ayin shi, to balle ke zama kikayi dashi gida d'aya, kika koyar dashi sonki da k'aunarki cikin k'ank'anin lokaci ya kuma koya.

Rabab ina gaya maki gaskiya, ko a da Altab bai iya barin Ikram tayi tafiyar kwana ukku, sai dai idan tare da shi.

Yayi k'ok'arin gaske kwana biyu ,shi ma kuma sai ya baki tausayi, saboda yanda yake komawa kamar wani maraya, idan yakita a waya kuwa tamkar yana gadon asibiti, ta ya za ayi kunyi zaman tsayin shekaru kusan biyu tare, cikin shekarun harda auren ku, yanzu farat kice zakiyi wata ukku ba kya tare dashi, Allah zaki kashe mijin ki, rana d'aya za a aiko maki yayi bindiga ya fashe.

Nayi 'yar dariyar murmushi, tare da cewa...

"Kai Aunty."

"Allah ba k'arya nake maki ba, kinga da Ikram, ta rasu kowa tunaninsa buyu, ya za ayi, lokaci d'aya, taimakon da Allah ya kawo mashi na gaggawa shine ke da Allah yasa mashi tausayinshi cikin gaggawa kika je kika zauna dashi, yau da gobe har ya saki ya hak'ura, yanzu kuma yana tunanin ya kamaki sai ki dawo da hannun agogo baya, k'anwata kiyi hakuri kije ki zauna da mijin ki lafiya.

"Alk'awari d'aya dana yi maki shine, nan da sati d'aya kawai zaki bamu ya ishemu shiryawa, a had'a maki komai, d'unkuna kike ji za a iya yin su cikin kwana biyu kacal.

Ta d'an yi shiru..

"Kawai ki hana bayin Allah bacci, mijinki da babanki tun asuba Abba ya kirani yake gaya mani, shi kuwa yanzun nasan sai ikon Allah k'ilan ki same shi ba lafiya, duk da na d'an kirashi a waya na kwantar masa da hankali kad'an.

Dan Allah idan kika kai mashi abinci, kada ki yarda ku k'ara yin maganar nan, koya maki ita kice yayi hak'uri, ke bakiyi zaton abun ya tasar mashi da hankalinshi har haka ba, in kuwa so kike ya cika dam ya fashe, to bisimillah.

Muka Sa dariya...

"Gashi yau zai tafi kije kisa shi yayi had'ari a hanya "

Nan take gabana ya fad'i, a haka dai Aunty ta dinga yi mani nasiha, wani lokacin inji kamar inyi ihu, wani lokacin in yi dariya.....
[5/1, 10:28 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Wannan page d'in naku ne Ummu Abideen & Maryam Mommy Afrah, Allah ya raya mana my cute son, Abideen n my daughter Afrah akan sunnah_*


*Page 31n32*

K'arfe 9:00, daidai muka kammala, Aunty tace inje inyi wanka in shirya jikina, siket da riga ne na Las's ruwan Ash, da ratsin pink, na saka a jikina, d'unkin yabi jikina ta ko ina, saboda tellor d'in bashida wasa.

Ni kaina nasan idan nayi kwalliya tana yimin kyau, saboda yanda d'unkin ke kwanciya a jikina sosai, ban tsaya d'aura d'an kwali ba, sai dai na saki kalabar dake kaina, amma guda hud'u kacal tayo gaba, ragowar nasa abin d'aure kai na d'aure su, na sakesu baya.

Masha Allah nikai na nasan nayi kyau, sai da na tsaya gaban madubi na juya na koma juyawa, sannan na juya na k'urawa madubin idanuwana.

Masha Allah da su, na marmara su na lumshe su na rufe, sannan na bud'a bakina a hankali daya sha pink d'in jambaki mai d'an duhu, dark pink, sannan na sunkuya, wai ina koyon irin gaisuwar da zanyi mashi.

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
_To fah su Rabab ko an fara tsunduma wa, a kogin lov, wannan gayu haka, hadda su koyon irin gaisuwar da za'ayi mashi..._๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜


Na d'auki mayafi na d'ora saman kaina, sannan na feshe jikina da turaren Oud touch, na saka takalma a k'afata pink haka shima mayafin pink, ne.

Na isa kitchen na d'auko kayan breakfast d'insa na nufi sashen shi, na k'wank'wasa k'ofa, da k'yar naji ance shigo, na bud'e tare da yin sallama, sannan na d'auki farantin na ajiye k'asa, saboda in samu damar bud'e k'ofar.

Yana kwance a k'asa saman kafet a jikin doguwar kujera, pillow d'in da aka tanadar wa kujerar domin k'ara mata kyau shine pillown da tare kansa, ganina yasa yayi d'an yunk'urin tashi.

Nayi saurin isowa na ajiye farantin dake hannuna, na iso na kama shi da sauri.

"Ina zaka haka?"

"In taso, in d'aukar maki kayan."

Na zauna gefen kujera, ya matso sosai ya kwanta saman cinyata.

Na dawo da kallona gareshi, ya mayar da idanuwan shi ya lumshe, harda saukar da ajiyar zuciya mai tsayin gaske, na d'ora hannuna d'aya saman goshin kanshi na shafa tare da cewa.

"Ina kwana Yaya?"

"Lafiya kalau k'anwata, ya mutanen gidan suka kwana.?"

"Lafiya k'alau."

"Rabab kiyi Hank'uri jiya na bata maki rai, nayi hak'uri Rabab kiyi yanda kika ga yayi maki dad'i."

"Ni ya kamata na baka hak'uri, wallahi ban fahimce kaba."

Nayi shiru, ya d'ago kanshi ya kalleni daga kwancen nan da yake, take yaja wani numfashi mai tsayi, sannan yasa hannun shi d'aya ya shafi gefen fuskata."

"Rabab kiyi hak'uri dani dan Allah, wallahi ina cikin rud'ani ina son naji d'umin matata."

Ya d'an yi shiru tareda lumshe idanuwan shi biyu, ya mayar da numfashi, sannan ya fara magana a hankali.

"Na shiga rud'ani, na rasa mi kemun dad'i a duniya, duniyar nan ta fita daga raina, Rabab ina ma ace ana rok'on Allah ya d'auki ranka, ya amsa maka kamar yanda yake amsa mana idan mun rok'e shi buk'atun mu, dana kwana rok'in shi ya d'auki...... "

Na sa hannu na rufe bakinshi, bai bud'e idanuwanshi ba, yasa hannu ya kama hannuna ya shafi gefen fuskarshi dashi.

"Rabab rayuwata ta dagule, ke kad'ai naga kin rage mani wacce zaki dawo dani mutun, amma ke kuma guduna kike, me yasa, me nayi maki, meye halayyata marar kyau.?"

Na kanyi tur! Da kaina idan naga hankalinki ya tashi a kaina, ke nake ganin kamar kin cike mani gurbin Ikram, amma sai naga har yanzu ra'ayin mu bai zo d'aya ba.

Yayi shiru tare da saukar da numfashi mai k'arfi.

Yaja hannuna d'aya ya kai a k'irjin shi.

"Ji nake tamkar k'irjina zai b'are biyu."

Nasa hannuna d'aya na shafi goshinshi, na sunkuya na sunbaci goshinshi, ya mayar da numfashin shi da k'arfin gaske, sannan naga yayi saurin bud'e idanuwanshi.

Nasan hakan ya samo asali da d'igar hawayen da suka fito daga k'wayar idaniyata, yasa hannu ya dangwalo ruwan hawayen daya d'iga a fuskar shi, yayi k'ok'ari ya tashi zaune.

"Me! Me!! Me ya faru na dame ki ko.?"

Na girgiza kaina..

"Ni dai ka daina yin maganganu irin wad'annan bana son ka mutu."

Yayi murmushi mai fitar da sauti.

"Rabab na daina, in sha Allah bazaki k'ara samuna da irin wad'annan maganganun ba tunda har suna b'ata maki rai."

Ya numfasa sannan yace "Yunwa nake ji sosai."

Na d'ago nayi mashi irin hararar shagwab'a, yayi murmushi.

"Ke kika saman sonki cikin k'ank'anin lokaci ya shiga zuciyata, rana d'aya sai kice sai na hakura dake, ai mai yi maka wannan zazzafan hukuncin sai Allah.

Shi kad'ai ne zai d'auke maka naka, kana son shi ka hak'ura dole, amma kin san Allah ba zan iya rabuwa dake ba, sai dai nima in Allah ya d'auki kayan shi."

Nayi alamun zanyi kuka. Yasa dariya.

"To sorry my lovely wife, kin amince yanzu zaki iya zama dani a matsayin mijinki ko.?

Nasa hannuna d'aya na d'an ture shi, har sai da ya d'anyi k'ara.

Yasa hannuwan shi duk biyu ya tallabi kumatuna, tare da saka manyan 'yan yatsun shi biyu ya goge mani hawayen dake tsatstsafowa daga idanuwana, sannan ya had'a goshin mu waje d'aya.

"Zan yi maki kuka, nima yunwa nake ji."

Nasa hannuna na d'an naushi cikin shi kad'an.

Yace "Wayyo."

Ya janyoni ya rungume a jikinshi, sannan ya had'e da fad'ar.

"I miss you so much."

Ya d'ago ni ya sunbaci goshina, na samu na tashi na d'auko farantin abincin da na shigo dashi, na d'ora saman kujera, sannan na bud'e kololin dake rufe, farfesun Anta ne amma ya d'an dagwalgwale, kenan ya dahu sosai.

Sai soyayyan arish tareda kwai, a saman farantin kuma bread ne, sai kofin Tea da spoon d'insa ga 'yar wuk'a a gefe d'aya, tare da kwangwanayen kayan had'in shayin.

Na bud'e d'ayan kular, d'umamen tuwon shinkafa ne da miyar shuwaka tasha gasash shen kifi, saboda ita Aunty abinda mai gidanta yafi so kenan a rayuwarshi.

Saboda haka kowa yazo gidanta, sai yaci d'umamen tuwo da duk miyar da ka samu.

Na had'a mashi Tea sannan na d'auko bread yanka d'aya zan mik'a mashi.

D'ago kan da zanyi sai naga ya bud'e baki, nasa 'yar dariya tare da harararshi, ya lumshe idanuwanshi ya bud'e alamar magana.

"Kai d'innan Aunty Ikram ta shagwab'a ka."

"Ke kuma sai ki d'ora a inda ta tsaya, ba kuma dan ta gajiya ba, kema ina fatan bazaki tab'a gajiya ba."

"Ni dai gajiya zanyi."

"Ai kuwa da ranar a d'aki zan kulle kaina har sai kin ce kin huta zaki cigaba."

"Ba shikenan na huta ba, sai dai in zura maka abinci ta taga."

"Ai bazan ciba, jera maki abinki zan tayi ta k'ofa."

Nayi dariya, na gutsiri bread d'in, na had'a da dangwaleliyar miyar Anta, na nufo bakin shi, yayi saurin bud'ewa, harda kama hannuna da hannuwanshi duk biyu tamkar wani yaro k'arami.

Naja kunnen shi d'aya da hannu d'aya, Yasa k'ara harda kiran Aunty....

Nayi murmushi a inda na koma wajen aminiyata, na tambayeta.

"Yanzun kalar rayuwan nan zanci gaba.?"

"Ki gode Allah ai kin more, dama ni nasamu."

"Wannan rayuwar fa ita na tsana a rayuwata."

"A lokacin da take ba taki ba, yanzu kuwa ta zama taki."

"Yaushe kike ganin zan saba.?"

Ina a haka naji yaja hancina, nayi murmushi.

"Nace maki nine abokin shawarar ki, ki saki wannan tsokar."

Nayi murmushi, naci gaba da bashi abincinshi, haka muka dinga yi har na tabbatar wa kaina ya k'oshi, amma hakan baisa ya banni na tafi ba, sai lokacin da yayi shirin tafiya katsina.....
[5/1, 10:28 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IAW*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Wannan page d'in goro ne, da duk wani masoyin NIDA ZUCIYATA, Allah yasa mu amfana da darasin da ke ciki..._*


*Page 33n34*

*_One week letters..._*

Yau ne ranar da za a kaini wai gidan mijina, kamar yadda ake yiwa ko wacce mace a duniya, daga Abuja zuwa katsina, hidima kuwa ansha ta, fati kala biyu akayi, da akwai wanda ma a silver bed akayi shi.

Ango kuwa dashi aketa hidima, kwata kwata ya tare a Abuja sai yau da asuba ya koma katsina, wai acewar sa, yafi son yana tsaye a k'ofar gidan shi yaga amaryar sa an kawo mashi ita.

Ni kuma duk wani abu da ake yiwa k'awayena, sai da aka yimani, lefe, d'unkuna, k'unshi, gyaran jiki, gyaran gashi, gyran fuska, (make up) da sauran su.

K'arfe 6:00, na yamma motocin amarya suka iso katsina, madadin in ga sunyi (Lay_out) gidan Aunty Ikram, sai naga an nufi hanyar bayan liyafa Palace Hotel, ni da ke cikin katsina ban tab'a sanin da gidaje wajen ba har da yawa haka ba.

Zuciyata tabani k'ilan wata aka biya a ajiye ta gidanta cikin k'awayen Aunty shukrah, gida kam mai kyan gaske, amma sai naga motoci a k'ofar gidan, a zuciyata nace gidan yawa ma take.

Ganin anata parking da motoci, yasa nace lallai wannan k'awar ta Aunty, Aunty naji da ita, d'ago kan da zanyi, sai naga wasu sun fito daga cikin gidan a daidai lokacin da ake bud'e get d'in gidan.

Na bud'e idanuwana sosai, wad'anda dama kaina ne kawai lullub'e da mayafi, amma su suna kallon ko ina, wa suke neman su gane mani.

Yaya Altab ne rik'e da gwangwanin Moltina a hannunshi, yayi wani irin mugun kyau, tamkar ba shi ba, babbar riga ce tasha aiki a jikimta, farar shaddace mai haske sosai, hular saman kanshi ma fara hakama takalman shi.

Bakin shi kuwa a bud'e yake tamkar mai tallar macline, nayi murmushi a zuciyata shi nake wa dariya, kamin in k'arasa tunanina, sai naga motar da nake ciki tana shiga cikin get d'in nan.

"Ki sauka da bisimillah."

Naji an rad'a mani a kunnena.

"K'afar dama zaki fara sauke wa."

Shima naji an fad'a, banki ba dai nayi yanda akace mani, ganin ana tafiya dani na amince azuciyata nan ne gidan da za a kawo ni.

Yanzu Yaya Altab gida ya canza, nasan banida wata amsa, kamin inyi wani tunani sai naji ance.

"K'afar dama ki shiga da bisimillah, tare da karanta Ayatul_k'ursiyyo, saboda itace maganin ko wane bala'i da masifa."

_"Innalillahi, Wa'inna ilaihi raji'un..._shine naji jama'ar da suka rufa mani bayana na fad'a, wa'inda duk 'yan'uwana ne da abokan arziki.

Ba wani abu suke ma wannan kalma ba, illa kyau da had'uwar da gidan yayi, ga kayan alatu yasha, ban iya tsayawa kallo ba, sai dai aka wuce dani d'aki.

K'amshi ke tashi cikin gidan, amma k'amshin dake tashi cikin d'akin yasha bamban dana waje, aka zaunar dani saman gado, sannan naji ana cewa ayi addu'a Allah yakawo Rabab d'akin auren ta lafiya.

A ka bud'e fili da addu'a, sai naji ana cewa, ga malama Sumayya nan zatayi wa'azi akan zaman auratayya, da abinda ya kamata mace ta ta rik'e a d'akin mijin ta, saboda shine dad'in duniyarta da lahirar ta.

Tace lokaci ya k'ure, saboda ta dad'e tana jiran isowar mu, anan naji ta fara kamar haka.

Aure dai ya k'unshi, Amana, gaskiya, b'oye sirrin Mijin ki, kiyaye hakk'insa, fita da izinin sa, hak'uri yayin da b'acin rai ya gifta, kulawa da gidanshi da dukiyar shi da duk wanda yake k'ark'ashin shi, dafa mashi abinci, da tsaftace ko'ina na gida, da kuma jiki.

Da farko ina so in fara dake amarya, saboda kece uwar gobe, sannan ke zaki k'ara jan ragamar al'umma tun daga yau, kenan mijinki da duk wani bak'on shi ko naki, da 'yan uwan shi, da mak'o tanki gaba kad'an 'ya'yan ku su biyo layi.

Kada kiji ko ki gani ana tayin diramomin fina_finan duniya, Larabawa, Hausa, India, America, ki d'auka duk raha ne abinda suke nunawa, kenan bazai yiyu ba ko baki yi.

A'a ana yi, kuma yana yiyuwa, kuma kullun suma darasi ne suke koyarwa da wa'azantar wa ta hanyar zamani, tare da masu rubuta maku kuna karanta wa.

_Kada ki karanta littafi ki wuce kawai, ke yayi maki da'di, ko soyayyar tayi maki ta ciki, amma ke ba wani darasin da kika d'auka a Kai..._
_Ba wai sukan rubuta abubuwa domin rashin kunya ba, a'a suna rubuta ingantacciyar rayuwar da ko wacce Mace zataji ina ma ace ita ce..._
_To ita ce, amma idan ta kwantar da hankakin ta ta koya a gidan auren ta, amma fa sai idan mace ta amince azuciyar ta cewar, zaman aure ta zo, shine tasan aikinta tun wayewar gari har zuwa lokacin kwanciyar baccin ta..._

Ki d'auka cewa da gari ya waye zaki fara tsabtace gidanki, kenan bayan sallar asuba, bayan tsabtace gida sai tsabtace jikinki.

Sai kuwa abinda zai zamo abinda mai gidanki zai ci yaji dad'i a zuciyar shi, sannan kisan lafazin da zai rinka fitowa daga bakinki, a koda yaushe ya zamo mai faranta mashi rai da son ya zauna hira dake.

Ki zamo tamkar mage a wajen mijinki, kenan kullun kina manne a jikin shi, wannan had'a jikin yana kawo shak'uwa da k'ara son juna, da sasanci, da sassauci acikin al'amurran zaman takewarku ta aure,

Matsalar da muke yawan samu mu mata shine, wasun mu basu amince da abunda suka jeyi a gidan mijin su ba, basu amince cewar bautar Allah suka je yiba, su jajirce su zage damtsi.

Su abinda suka d'auka, dolene mijin su yabasu dukkanin abubuwan da suke buk'ata na yau da kullun, amma basuda lokacin da zasu zauna suyi tunanin yau me zani yiwa mijina na ba_zata.

Kenan ki burge shi yaji dad'i har a zuciyar shi, yasa maki albarka, kuma ko wane ana son na farko ga girki, yau bari inyi masa ba zata da abinda yafi so yaci, ko in ga in zai ci.

Na biyu kwalliya, yau tafi ta jiya kyau da burgewa, a'a kyakkyawan zuwa d'akin yau yafi na jiya rud'a mijinki, a'a wacce kalar oyoyo zanyi yau.

A'a wacce kalar rakiya zanyi masa yau, addu'ar dawowa tayau ya zan tsara ta gobe wane dad'ad'an kalamai zan furta masa ya fita cikin farin ciki.

K'yakk'ya wan abunda kika aikata mashi irin k'yakk'yawan sakamakon zaman lafiyar da zaki samu gidan mijin ki, zai zamo kullun shima mi zai yi maki ki yaba, ya kuma burgeki, kada ki damu koda kina yi ba a yabawa, wasu mazan haka suke, amma idan har yaji dad'i a ransa ke zaki gane,

_Ku sani mata, farin cikinku d'akin auran ku, k'yakk'ya war rayuwarku kwanciyar hankalin ku..._

Amarya daga yau zaki samu kanki a bak'on al'amari, ko in ce bak'in al'amurra.

Ki sani haka nayi, haka maman ku tayi haka duk wata mace tayi, shi kuwa wa'innan bak'in al'amurran ba komai ne kesa su zama jikin mata ba, face hak'uri,da gaskiya, da girmama mijin ki, watarana zakiga tamkar ba kya ma komai a gidan mijinki, saboda Sun zame maki jiki, banda sauran fushi, banda kwashe duk abinda kikayi da miji ki gaya wa kowa.

Koma miye amfison ki gaya mashi, in na gyarawa ne ya gyra, in na bayanine yayi maki shi a natse, har ki zamo kin samu natsuwa da abinda yake fad'a.

Gaskiya mu mata munada wata matsala wacce ke mugun damuwar maza, haka wannan matsala duk itace ke kawo duk wata tab'arb'are wa ta aure, wanda har sai kaga ana zaman aure tamkar ana zaman mugunta, saboda wannan matsalar da ta kasa magan tuwa a cikin al'ummarmu ta duniya.

Ita wannan matsalar kashi hamsin na maza, arba'in na fama da ita a wajen matayen su.

Bincike ya nuna mani cewa, da mata zasu gyara, su yarda ibada suka zo yi ta musamman da an samu zaman takewa mai kyau ga al'umma ma, ba miji da mata ba kawai.

Saboda idan mace nada kwanciyar hankali a wajen mijin ta, hankali da natsuwa da tunani mai kyau, kun ga duk wanda yazo wajenta yanayin zai samu na tsatsan rayuwa mai kyau.

Haka miji zai fita cikin farin ciki da natsuwa a gidan shi, wannan zai hana mashi zafin zuciya a wajen neman abincin shi, amma sau dayawa maza da fushin matansu suke hucewa a kan wani a waje.

Kuyi hak'uri 'yan uwana, kada kuji komai a ce Mata! Mata!! Mata!!! Mu mata mune jagorar duniya gaba d'aya, haka Allah ya wakilta mu.

Malamai, sarakuna, hafizai, da shuwagaban nin k'asashe, duk a wajen mata suke komai in sun tashi daga kujerun mulkin su, ko wa'azin su, ko koyarwar su, haka iyayen su ma matane.

Haka idan gida suka nufa wajen iyaye mata, idan sun tashi daga makarantun su, ko tallace tallace, ko wasannin su, duniya duk mata ke goya duk wani d'an adam da bayansu.

Su d'auki cikinku, su haifo shi ta jikinsu, su bashi mama ta jikinsu, barcinsa, haka kuma in mace ta gama rainon farko, mace matarsa zata ci gaba da na biyu har k'arshen rayuwar sa.

Na san suma maza suna da nasu matsalolin, amma sau dayawa matsalar maza ta kan samo asali ne daga mace, uwa, ko mata, ko budurwa, amma ku sani maza, don Allah kusa hak'uri ga rayuwar ku, saboda ku kuma ku Allah yafi bai wa juriya da sanin yakamata da shugaban ci, rud'anin ku zai iya tab'a al'ummar duk da ke k'ark'ashin ku.

Masu aiki, 'ya'ya, iyaye, da sauran mabiyan ku, wannan nasiha nada tarin yawa, sai dai a tak'aita ayi hak'uri haka nan, sai wani lokaci, kuyi hak'uri na baku abubuwa a k'udundume ,ina jin d'an nauyi ne da kunya.

Wad'an nan abubuwan da na fad'a sune abinda yafi dacewa mu rikeso su zama takobin mu, mu mata da mazan ma, daga nan akayi addu'a aka tashi saboda dare yayi.

An tashi a haka, ana ta godiya da sa albarka, saboda dare yayi, duk suka kama hanyar gida jensu.

Aunty da wasu k'awayen ta suka tashi suka k'ara gyara gidan.

Nima akace in tashi in k'ara shiga wanka, haka na k'ara shiga wanka aka k'ara gyareni da kyau, Aunty ce ta d'auko mani wani kwali ta bani, tace idan zaki kwanta ki sakata, rigar bacci ce.

Nayi dariya tare da zare idanuwana.

Aunty tayi murmushi tace.

"Rabab kenan, zauna in karanta maki ki gane, daga yanzun nan zaman da kikayi da Altab a baya ba irin sa bane ba a yanzun, shi kanshi ma bazai amince da irin wancan zaman ba.

To don haka kema ki gyara, Nasiha koyarwa duk munyi maki, don girman Allah ban da kiran Abba ki gaya mashi matsala, k'arama ki kirani ki gaya mani ta waya, ke har zuwa ma sai inyi kina jina.?
[5/1, 10:28 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Masoyana, masu kirana da masu turomin tex ta private, ina godiya Allah yabar zumunci, sanna ina baku hak'uri akan k'orafin ku na in k'ara bud'e maku wani group, bank'i taku ba, amma gskya banida ra'ayin bud'e group har 2, saboda wasu dalilai, amma insha Allah zan k'ara tunani akan k'orafin ku..._*


*Page 35n36*

Na d'aga Kai na alamar eh.

"To Aunty, yaushe kuma zanbar gidan Yaya Altab, in koma gidan Abba.?"

Tayi dariya.

"Rabab kenan, ai kinzo nan har abada, kamar yadda kike zuwa gidajen mu, kema sai dai azo gidan ki, tsakanin ki da Abba da Umman mu sai dai kije gaishe su, shima fa sai kin gayawa Altab yace kije."

Na zaro idanuwana,

"Aunty yanzu da akwai lokacin da zai ce kar inje.?"

"K'warai kuwa".


"Lallai kice da rigima".

"Ke bana son shirmen ki wanda kika saba".

Da haka suka turareni da hayak'in turaren wuta, da kwalliya mai k'yan gaske, da wani material duk yaji stone ajikin shi sai walk'iya yake.

Fari ne k'al, jikin shi, amma stone d'in jikin shi red ne, sannan sai walk'iyar Ash a jikin shi, mayafina da takalmina duk farare ne, haka kayan cikin jikina duk farare ne.

Daga nan suka yi mani sallama, da sunan sai sun zo yimani bankwanan komawa Abuja, na biyo su har falo ina cewa Aunty abar mani ko mutun d'aya ne.

Bata kai ga bani amsa ba, muka same shi, shida k'awayen shi a zazzaune, ganin su yasa nayi saurin rik'e Aunty,

Ta k'walk'wale hannun ta, tayi gaba nikuma nayi baya nasa kukan hawaye.

Ina jin hayani ya da tashin motocin su, na koma saman gado na zauna sai hawaye keta gudu a kumatu na.

Za a samu kamar minti 20, da wucewar su haka, sai naji sallamar Yaya shida wasu, acikin zuciyata na amsa, suka shigo suka zauna akan kujerar bakin gado, shi kuwa Yaya ya d'an zagayo Inda nike zaune ya zauna.

Wannan rana ita naji k'awayena na yawan kiranta a rayuwar su, idan har za ayi maganar aure ,ita ce wai suke son gani, duk da ni ba cika tsayawa nayi inyi hira irin haka ba.

Wasa irin na abokan miji suka dinga yi mani, kamar su Amarya ta Ango, Amarya kin sha k'amshi, nidai kaina a sun kuye baya ga 'yan gidan mu babu wanda nike tunawa.

Anan sukayi 'yan nasiho hi sannan suka rufe da addu'a, sannan Yaya ya rakasu suka ja motocin su suka wuce.

Ina jinshi yana kulle k'ofar get, ni kuma ina nan zaune na rafka tagumi hannu bibiyu, babu abunda nike tunani sai aunty Ikram, nayi tunanin yanda take son mijin ta, a yanzu idan zata dawo yaya Zara ji.

Sam banji shigowar sa ba, sai dai naji an d'auke duk hannuwa na biyu daga tagumin da nayi.

"Yau shine ranar ki ta farin ciki, bai kamata ace ki cikata da tunani ba."

Yau nikuma ita ce rana ta ukku a farin ciki, ranar da aka kawo min yayar ki da sunan matar aure na, rana ta biyu ranar da aka kawo ki bayan ta rasu, yau kuma an k'ara kawoki a matsayin amarya mafificiyar wancen lokacin.

Yasa hannu ya goge hawayen dake fitowa daga idanuwana, ko wace 'ya mace ta duniya idan aka rabata da iyayen ta dan tayi kuka ba laifi bane, amma fitar hawayen ki a gabana zai iya haifar mani da wani tashin hankali.

Ya mik'e ya cire babbar rigar jikinshi, ya nemi waje ya ratayeta sannan ya sunkuyo.

"Amarya an sha kyau."

Na d'an harare shi alamar haushi.

"Shi ne daidai danayi a yau d'innan, raba mutun da iyayen shi ai k'aton aiki ne."

Ya wuce ya shiga toilet, yana fitowa yace mani in shiga in yi alwala zamu yi sallah, banyi gardama ba na mik'e yana kallona na shiga toilet.

Bayan nafito mukayi sallah raka'a biyu, mun samu tsayin mintuna saboda addu'oin da ya dinga yi hadda wacce ya dafa kaina, muna kammalawa ya tashi ya fita, ba a jima ba ya shigo da ledar sa a hannu.

A take na tuna wata k'awata da naji tana bada labarin ledar nan.

Sai da ya cire rigar shi ta sama sannan ya zauna, daga shi sai dogon wando da singlet, ya zauna.

"Zo kisha fura, ita kawai na siyo mana ta Habib, saboda nasan baza mu iya cin abinci ba, sai nama gashi nan kizo muci."


"Ina yara, me yasa ka kawo ni nan su ka barsu can.?

Yayi murmushi.

Ba can na barsu ba suna gidan Abba, nima sai da nayi nayi abani suka k'iya, nan kuma gidan kine, wancen kuma gidan Ikram ne, idan muna cikin shi har abada bazamu manta da rasuwar taba, duk da yanzun ma bazamu iya mantawa ba, amma canja wajen yakan iya sa mu rage.

Ya d'ebo naman ya nufo bakina, nayi alamun kaucewa, ya matso sosai naji ya had'ani da jikin sa.

"Na tuba ki bud'e bakin ki."

Na kudun dume cikin mayafi na.

Cikin hikima ya zare mayafin jikina sai naji yace.

"Ni nasan nazo duniya cikin sa'a, in Allah ya yadda lahira ta ma haka zaka zamo."

Ya sunbaci doron bayana, nayi saurin cewa

"Yaya".

"To kici idan har ba kya so."

Na bud'e bakina, madadin ya saka mani nama, sai naji ya saka mani halshen shi, nayi saurin d'auke kaina, amma ya rik'e kaina gam.

Ban hana ba, gudun kada in shiga zunubi, kamar yadda malama tace, sai da yagaji dan kansa ya sakeni, ya koma ya kwanta a k'irjina yana numfashi a hankali.

Ya d'ago ya kalleni hawaye ne a fuskata.

Yayi murmushin da ke d'auke da kunya, ya sunkuyar da kai tare da d'an shafa kanshi.

"Kiyi hak'uri Rabab, haka nike, ni mutun ne da nike son matata fiye da komai a duniya, kuma bani iya b'oye kalar son da nake mata.

Rabab nasan ke macece wadda kika tsani aure, kiyi hak'uri zaki so aure.

Ya d'an yi shiru, ya kama kame kame da alama ya rasa bakin magana, nasa hannu na d'ago kanshi, ya kalle ni yayi murmushi, na daure dak'yar na mayar masa.

Ya kama hannuwa na duk biyun ya sunbace su.

"Na gode Rabab, in sha Allah zaki same ni mai kulawa da rayuwar ki da ta 'ya'yan ki."

Ya koma ya kwanta a cinyata, tare da rungume kuguna gaba d'aya, ni kuma na sunkuyo na sunbaci gashin kansa ya Saki nunfashi a hankali tare da cewa.

"Tai makeni ki had'a muna ruwan wanka."

Amsar ta iya leb'e ta tsaya, ta mik'e a tsorace, dan taga takorar Yaya na son yin yawa gareta, wani sashe na zuciyarta ya gargad'e ta da kul, ya kike k'orafi aikin mijin ki, kina sakaci da ladarki Aljannar ki kuma.

A hanzar ce na tashi naje na had'a mana ruwan wanka.

Yace in shiga in fara yi, wani dad'i naji arai na saboda bana son yaga shirina.

Bayan na fito shima ya shiga, na tsaya gaban mirrow ina feshe jikina da turarukkan da Aunty ta bani sannan na d'auko kayan bacci na saka.

Jin saukar ruwa a fuskata ya firgitar dani, a tsorace na bud'e idanuwana, Yaya ne na gani dab dani da d'an figaggen towel d'aure a cikin sa, ya mik'o mani wani k'arami wanda ya lafa a kansa yace.

"Ki idar da ladarki tunda kin kasa taya Mijin ki wanka. "

K'warai ya bata kunya, ta kasa ma d'aga kai ta kallesa ya sake matsota jikin shi yasa hannun sa tareda d'ago hab'ar ta yace.

"Ba zan samu taimakon ki ba kenan."

Ya janyo hannun ta ahankali ya d'ora a k'irjin sa, d'ayan hannun ya kashe wutar d'akin, don yana ganin hasken nan ke hanata tayashi saboda kunya.


Ya sauke ajiyar zuciya, yana shafar bayan ta a hankali, ya rasa inda zai sakata saboda so, ji yake kamar za'a k'wace masa ita.

Ya lalubo bakina yana wasa da halshenata cikin salon gwanance wa, yasa hannun sa ta baya tare da zuge zip d'in rigar ta cikin hikima.

Ita kanta Rabab dakewa kawai tayi, amma tsikar jikin ta sai wani yar take yi, bata mai da masa martani ba, kamar yadda bata hana shi ba, yayi nasarar rabata da rigar jikin ta.

Take ya fara kissing d'ina ta kowane gefe, ya kasa controlling d'in kansa, magana yake yi cikin husky voice d'in da shi kansa yana tantamar tashi ce ko a rota yayi.?"

"Ina sonki Rabab, Yau zan tabbatar miki da hakan, _I really love you, you are my happiness..._ina matuk'ar sonki kece farinci kina,dafa k'irjina yayi sannan yace.

"Kinji bugun zuciyata tare da k'aunar ki yadda suke fita."

"Rabab kanta a rikice take da yanayin yayan nata, amma wasan yayan nata ya tsumata, ya k'ara matseta a k'irjinsa, tabbas ji yake yi kamar ya mai dasu halitta d'aya, ya kasa jurewa wasan.

Cak ya d'agata sai kan gado, salon wasan ya canja......
[5/1, 10:29 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ


*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Wannan shafin nakune, k'awayen arziki..._*

*_Ameena Abba_*
_Marubuciyar {Afrah_}

*_Ummun Meenal_*
_Marubuciyar {In ba duniya_}

*_Ummu Abideen_*
_Marubuciyar {Lainat_}


*_Da sauran k'awayena 'yan IWA ban manta daku ba kuna ❤ d'ina_*


*Page 37n38*

Altab sam baya cikin hayyacin sa, tun Rabab na daurewa har hak'urin ta ya kasa, ta fashe da kuka tana cewa

"Dan Allah Yaya kayi hak'uri kar kamin komai, wallahi da zafi, sannan ta k'ara fashe wa da kuka."


Hakan ya k'ara rud'ar da Altab, tare da k'arin jin wata daddad'iyar sha'awarta, wadda ya dad'e yana b'oyewa a zuciyarsa, yau ne zai k'ara bayyana mata ita.


Nan ya fara kissing d'in lips d'inta yana shafar jikin ta, yana Tsotsar na fulanin ta, yana wasa da su, ita kuwa nunfa shin ta sai k'ok'arin d'aukewa yake, wani sabon kuka ta k'ara a zamai mai ban tausai.Sam baya jin kukan ta, yariga ya yabar k'asar ya lula dad'i world, sai sakin sabbatu yakeyi.Sai dai kawai taji ya d'ora bakin sa a kunnen ta yana karanto mata wata addu'a.Tayi daidai da wata k'ara mai ratsa zuciya da ta saki, tare da saukar da ajiyar zuciya mai zafi, ta langwab'e masa gwanin tausayi, babu abunda idanuwanta ke yi sai zubarda k'walla masu zafi, bai saurara mata ba sai kusan asuba, sai da ya tabbatar ya maida ita cikakkiyar mace.Sai a lokacin ya dawo hayyacin sa, ko motsi batayi sai hawaye wasu na korar wasu, ya rungumeta yana kukan tausaya mata, shi kansa yasan ya bata wuya, amma hakan ya samo asaline da azababben son da yake mata.Ya tashi ya shiga toilet, ya had'a ruwan zafi, sannan yazo ya d'agata sai bathroom, wata 'yar k'ara ta saki, sosai ya gasa mata jikinta, sai ajiyar zuciya takeyi a hankali, tana lumshe ido.Bai fitar da ita ba, sai da yaga tana neman yi masa bacci, sannan ya nad'ota a towel, kamar jaririya sai kan gado, gefe ya koma yana shafar ta, har bacci ya d'auketa.Kallon ta yakeyi kallon so, kallon k'auna, kallon sha'awa, kallon yabawa da girmamawa, komai Nata burge shi yakeyi, sai saka mata albarka yakeyi.Shima nan bacci yayi gaba dashi.


Sai asuba ya tashi, yayi k'ok'arin tashe ta tare da taimaka mata ya kaita toilet suka d'auro alwala, sukayi sallah.


Ya d'auketa cak, suka koma gado, tasa hannun ta d'aya ta rufe fuskar ta, matsananciyar kunyar sa ta darfafo mata, ta sauke k'wayar idonta, don baza ta iya jure wannan kallon ba da yake yi mata.


Ya d'ade ya kwarara mata addu'oi sannan yaja bargo ya rungumeta sosai a jikin sa, yana furta mata kalaman sa.


"Rabab yau kin shayar dani zumar da ko wanne d'an adam yake buk'ata wajen matar sa, ya shiga fad'a mata kalamai masu dad'i da wuyar mantawa."


"Rabab kin san yadda nake jin safiyar nan, tamkar ina cikin gajimare saboda nisha d'i, i really love you my wife, ya janyo ta ta kwanta a cikin sa, suna kallon juna. "My happiness, bana gajiya da ke, ko in k'ara kad'an?"


Wani kuka ta k'ara fashewa dashi."Wife, Sorry, wasa nake maki kinji, ayi min afuwa, yau na tab'a autar Abba nasan yau sai nayi tsallen k'wad'o."


Duk wani motsin shi sai ya rad'a mata kalmar yana sonta, a haka har wani baccin ya kwasheta.


Kallon to yakeyi, kallon tausayi sai ajiyar zuciya takeyi, shi kam anurin fuskar shi ya canja, wannan dare yana cike da tarihi.


Ya d'auko wayar sa ya shiga Reminder tare da Ticking date, na ranar da yasamu mallakar Rabab, ya rubuta a (Diary) d'insa, har ya rad'awa ranar suna da (Unforgettable day ).


Kwance take riras, ga dukkan alamu baccin yayi mata dad'i, sai numfashi take saukewa a hankali.


Ya dube Agogon, dake manne a bangon d'akin k'arfe 11am, a hankali ya taso a hankali ya zauna gefen gadon, ya k'urawa k'afafun ta ido.

Farare tas dasu, kamar bata taka k'asa, ya dad'e zaune, sai ya d'aga hannunsa nufin sa ya tashe ta, sai kuma ya fasa.

Ya yanke shawarar kawai ya tashe ta, tana bud'e idon ta sai hawaye ta rufe fuskar ta"Rabab tsorona kike na zama dodo ne.?"


Ta girgiza kai alamar a'a.

Yayi murmushi tare da nunata da d'an yatsa yace.


"Har yanzu ban kawar da wannan kunyar ba.?"

Ta rufe kanta maganar shi mai girma ce, tana matuk'ar jin nauyinta, ya tallabo ta tare da bata kiss a gefen fuska, ya d'auketa suka k'arayin wani wankan, ya kawo ta falo, suyi breakfast.

Shi ya had'a mata ruwan Tea, yana bata tana sha kad'an kad'an, motsi d'aya zai mata sannu.

A zuciyar shi yake tunanin an halicce shi da sonta ne kawai, duk wani motsin ta idon sa na kanta, da yanada iko numfashi ma zai yi mata.........

*_Plz kuyi hak'uri da wannan yau ina busy ne..._*

*_Take har kullun_*
*_Precious girl ✍_*
[5/1, 10:29 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*Page 39n40*

Rayuwa mai dad'i, rayuwar da ko wacce mace take burin samu gurin mijinta, rayuwar farinciki, soyayya, k'auna, tsantsar kulawa, tausayawa, itace Altab yake nunawa Rabab.


Rabab kuwa yanzu an d'an shigo gari, tana tausayawa mijin ta kuma tana son shi, kuma duk wani hak'i da mace ya kamata ta bawa mijinta Rabab tana k'ok'arin taga ta bashi, a kullun k'ok'arin ta taga farin ciki a fuskar shi.


Tayi imani da k'addarar da Allah ya rubuto mata, kuma tana rok'on Allah ya bata ikon yi masa biyayya ta k'ark'a shin sa ta samu aljanna, shi yasa a kullun fatanta wa'inda ma suke tare dashi suga murmushin shi ya k'aru fiye da, da.


Kamar kullun dai dai Rabab tayi wankan ta ta feshe jikin ta da turarukka, tayi simple makeup, d'inta tayi k'yan ta sosai.


Motsin shigowar Altab, taji.


Altab ne ya shigo tare da kulolin abinci a hannun sa, nayi sauri na k'arba, daman tun ranar da aka kawoni Unman su ce ke kawo mana abinci.


Na isa gurin dining table, na ajiye, shi kuma ya shiga toilet yayi wanka.


Bayan ya shirya ya fito, sai k'amshi yake, kamar wata amarya, muna cin Abinci sai wani kallo yake yimin, har yakai na fara jin kunya.


Bayan mun kammala Altab ya d'auke cak, bai direni ko ina ba sai...Bedroom ya direni saman bed yana mani chakulkuli sai dariya mukeyi, wani mayen kallon Altab ya mata Wanda Rabab, da taga irin wannan kallon tasan me yake nufi,Altab yace "wife yanzun ba kya jin kunyata ko.?murmushinta me kyau ta saki "ka godewa Allah ma Da Allah ya kare maka ni iya haka, kuma ma ai watarana ina jin kunyarka, kasan na saba da kai shi yasa bana boye ma komai, kai wacce kunyace da kai?


"Ai ban kaika ba ko
kafarka ban kamaba."To naji fada min ni wacce rashin kunyar nayi miki ?cewar Altab.


kallonsa tayi tare da yin wani fari tana juya idanunta masu rikita Altab, see u kana danne yar mitsilar yarinya a bed kana sabbatun ka, ranan ma ina jinkafa kyaleka nayi dan kawai naji zafi ne amma wacce kyauta ce baka min ba, fad'a masa ta farayi ohhh Baby, my life ahhh na baki garin katsina, ke da Abuja ma, impact Nigeria duk zan siya miki, darling duk nakine sai abinda kika ce.


Dariya Altab, keyi sosai karyar da Rabab ta sambad'o masa yasan yayi sabbatu amma bai k'irgo da cities ba.


"kiji Tsoron Allah wife yaushe nace haka.?


"Oh to ai lokacin ka bar k'asar nan ka Lula dad'i world, amma wai
kana zancen wai a kiraka me kunya.


Wanne tabo ne ban sani ba a jikinka? Zaka dinga min pretending, ka fito min a Mutum sak ba wani kwane kwane."To naji amma ban yarda ba in kin isa zo a karayi aji idan zanyi sabbatu wannan lokacin, ai na daina sambatu.


"Ni kuma nace dole sai kayi,musu ne ya kaure tsakaninsu shi yana a karayi bazai Sambatu ba yayiwa Rabab wayo bata gane ba tace duk da ba dadi nake ji ba azaba nake sha a kara yi yau sai an kure Wanda baida gaskia, kasan kuwa irin sambatun da kakemin har kuka kayi a last da kayi,to yau kace baza kayi ba.


"Habawa malam dole sai kayi Sambatu, yarinya ai waccen dan ban shirya bane amma wannan ba wani sambatu.A haka ya rinjayi Rabab ta yarda ita dole sai ta kure karya,da suka fara ma jajurcewa tayi iya fasaharta ta nunawa Altab wai duk dan yayi sabbatu ta kureshi, sabbatu Altab Ke mata sosai tana ta Kara jajircewa,ai kuwa Altab bai San kadan ba sai wajen asuba ya kyaleta, baya gajia da Rabab Sam.


Rabab, kam yau sai murna takeyi tana na kureka Allah sai sabbatu kakeyi wooooo,ai dama na fada ma."Altab murmushi yayi to naji kin kureni ai zan rama, kema zakiyi fin nawa watarana.


"Suna samun natsuwa rungume take jikin Altab yana wasa da dukiyar fulaninta.


Tace Yaya Kasan me.?

"Sai kin fada cewar Altab.


Hmm "Allah kaga na yau da kayi min baka ji ba kamar dadi dadi kuma zafi zafi, sai naji kamar kwakwalwata zata buga.


Dariya ta bawa Altab sosai, ba'a yin 1mnt, bata bashi daria ba shi yasa yake matukar kaunarta, tana burgeshi ko yaushe nishadi take sashi, shi yasa ko ko ina baya iya zuwa sai tunanin matarsa, shi kadai zakaga yana murmushi.


"To next idan munyi dadin zaki ji gaba daya na fada miki, tab ai kuwa zaka jini wurin Abba, kai na yau ma fa jurewa kawai nayi.


Yawwa ni kuwa Yaya yaushe 'ya'yana zasu dawo, Allah kuwa nayi missing d'in su.?


Dariya Altab yayi sannan yace "haba wa ai sai mun gama cin amarcin mu, ko Umma fa irin wayon nan nyi mata nace ta bani su, tace a'a sai an kwana biyu, bata san nima nafison ta rik'e su can ba.


Dariya Rabab tayi tana cewa "Allah kuwa sai na fad'awa Umma.


Murmushi Altab yayi yana bubbuga mazaunanta kamar jaririya yace lazy kinji maza muyi bacci.


Haka suka kasance cikin jin dadi da kwanciyar hankali har Rabab ta shafe 2 Week's, gidan Altab.


Safiya na wayewa bayan sunyi break fast, kuma kama shirye shirye dan yace mata zasu je suyi ziyara.

Bayan nayi wanka naje na d'auki wani material mai k'aramar kwalliya, material d'in fari ne da adon flower, kalar sararin Sana niya (sky blue), tasa yayi mata kyau sosai ta d'auko farin gyale da farin takalmi ta sa.


Shima ya shirya cikin wata shadda, babbar riga da wando, itama mai kalar sararin samaniya, yasa husa zanna bukar, da farin takalmi da agogo, dama agogon sa kullun na (silver) ne.


Ya fita, kafin ya shigo, na gyara gadon, na kwashe kayan da muka cire na nad'e na gyara komai tsaf, ya shigo yace "Ai da kin bari na gyara miki d'akin."


Tace "kai zaka gyara d'akin da muke kwana.?


To daga yanzu na hutar dakai daman can dan bana jin dad'i ne kakeyi.


Yayi dariya yace " Amarya your wish is my command."

Tayi dariya ya sunbaceni suka fita.


Muna fita suka wuce can gidan su yaya, muna shiga gidan su Ilham dasu Twin's suka zo da gudu suka rungume, ga Aunty! ga aunty!!.


Sai murna suke yi, muka wuce can cikin gida wurin Umman su.


Muna shiga Umma sai murna take, na gaishe ta cikin ladabi da biyayya, itama ta amsa, tana tambaya ta su Umman mu nace "suna nan lafiya.


Altab kuwa yace "ai rabon ta dasu tun ranar da aka kawota, yanzu ma daga gida muke."


Umma tace "to waya tambaye ka.?


Kunya ta kama ni na rasa inda zan saka kai na.


Umma tace "kaga yanzu kasa taji kunya ko.


Yace "don na fad'i gaskiya, to bari in yi k'arya, gata nan ki tambayeta da kanki.


Umma tace "fice mani daga d'aki!! Yace "ayi hak'uri.


Can sai ga baba Alhaji ya shigo, na duk'a na gaishe shi, irin gaisuwar ban girma, ya amsa ya kuma yaba da hankali na, a ransa yace "Lallai dole d'ansa ya rud'e a kan wannan zuk'ek'iyar yarinyar, yayi farin ciki, yace lallai zan k'ara samun kyawawan jikoki, sai yayi kiran Umma.


Bayan sun fita, yazo ya rik'e hannuwa na yana wasa dasu, sai ga Umma ta dawo, data gansu sai kawai ta juya, nan da nan Rabab taja jikin ta saboda kunya.


Altab ne yace "Umma kin dawo.?


Bata bashi amsa ba ta koma ta zauna sannan tace " Tashi kaje Alhaji yana son ganin ka.


Yace "amma Umma da mun gama magana dashi gida zamu koma.


Umma tayi dariya tace "naji marar kunya kai kayi sabuwar amarya ko.?


Yayi dariya ya wuce yana susar k'eya.........
[5/1, 10:30 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*_Masoyana! Masoyana!! Masoyana!!!, Wallahi banida kalmomin da zanyi amfani dasu wurin gode maku hak'ik'a kun nuna min so da k'auna, ina godiya ga masu kirana da masu turomin tex, suna yimin gaisuwa hak'ik'a kun nunamin ana tare, ngde ngde ngde._*


*_Masoyana 'yan group d'in NIDA ZUCIYATA, da 'yan INTERLLIGENT WRITTER'S PANS, ina k'aunar ku tamkar yanda kuke k'aunata, masoyana da bazar ku nake dancing, thanks so very much for the love and support._*


*_Friend Asmeey Baffa, ina taya ki murnar kammala book d'in ki Ma'aikaciyar gwamnati, Allah yk'ara basira da zak'in hannu, thanks for the love_*


*Page 41n42*


Bayan sun gama magana da Abba, ya fito ya nufi d'akin Umma, ransa kamar a b'ace, amma baya son Umma tagane hakan.


Bayan ya shigo ne yake cewa Umma zaizo zuwa gobe ya d'auki su Ilham da su Twin's.


Abun ya bawa Rabab mama ki yanda lokaci kad'an ya canza, sai dai tasan koma minene zata sani.Sunyi sallama dasu Umma, su Ilham da twin's sai kuka sukeyi, da kyar Umma tayi masu wayau tace ita zata kaisu da kanta.


Da zasu tafi baba Alhaji yayi mata alheri mai yawa, kun san dai kyautar manya, Umma ma abin nata sai wanda ya gani, daga nan suka wuce suka shiga motor.


Suna tayi cikin motor, amma babu wanda yacewa kowa ko tak ba, sai tuk'i yake yi ga alamu dai kamar tunani yake yi.

Da k'yar ta samu ta bud'e bakin ta tana cewa "Yaya lafiya naga lokaci kad'an duk yanayin ya canza.?"


Anjima kad'an kafin ya bata amsa "Rabab Abba ne yayi min wata magana wai gobe gobe yana son in tafi Abuja, akwai wani taro da zan Wakil ce shi, wallh lokacin da yayi min wannan maganar sai da gabana ya fad'i."


Dariya Rabab tayi duk da itama bataji dad'i ba amma bata son yagane hakan.


"To meye ne, ni wallahi na zata ma wani babban abune."


"Haba Rabab duka duka fah yanzu iyakar mu 2 Week's da tarewa, wallahi daidai da minti d'aya bana son nayi ba tare dake ba.


Daidai lokacin Sun iso gida, mai gadi yazo ya bud'e masu get, suka wuce ciki.


Bayan sun shigo cikin d'aki, bai ce mata komai ba ita ma tayi shirun ta, ya tashi ya shiga toilet yayi wanka, ita ma tashiga tayi wankan ta, bayan Sun kwanta zasuyi bacci yake cemata.


"Wife naga kema kinyi shiru ko na b'ata maki raine.?"


"A'a babu komai, Kai ne kawai naga kana cikin b'acin rai."


Yayi murmushi sannan yace "Ai dolene na shiga cikin wani yanayi zanyi missing d'in matata, zanyi kwana biyu ko ukku ban ganta ba."


"Har kwana ukku zakayi, to kawai muje tare sai ka ajiye ni gidan Aunty idan zaka koma sai mu koma tare ko.?"


"Haba wife, kin san dai Aunty bazata yadda ba, kuma nima gaskiya bazan yadda ba, amma gaskiya da an k'are taron nan ko awa d'aya bazan k'ara ba zan juyo gida.


Nan dai suka k'ara more amarcin su, suka kwanta sukayi baccin su.


*** *** *** *** ***

Washe gari suna gama breakfast, suka kama shirye shiryen tafiyar sa, amma ya lura da ita yau batada wata walwala.


"Wife, miye ne wai ko in fasa tafiyar nan wai.?"

"Duk lokacin da nike tare da kai nakan manta da kowa da komai a duniya sai ni da kai, yanzu ni bansan yadda zanyi ba idan ka tafi, dan nidai a wurina rayuwa idan ba tare da kai ba shirme ce, sai hawaye suka fara zuba wasu na korar wasu, ga kuma muryar ta na rawa.

"Altab yayi saurin rungume ta yana fad'in "Rabab don Allah kiyi hak'uri, kamar yau ne idan Allah ya yaso, kuma idan kina kuka bazan iya daurewa ba, yasa hannu yana share mani hawayen.


Cikin kuka nike cewa " Yaya, I want to be with you, please don't leave me, I can't live without you, I want to go with you, I love you." Ina Altab shima sai ya fara kuka Yana cewa.


"Dan Allah kiyi shiru idan kina kuka, bazan iya tafiya ba, ya jawoni jikinsa yace "Oh! sweet heart, kiyi shiru, nan danan wasa ya canza salo, ya tallabo fuskata da tafin hannun sa, yana kallona cike da hawaye, haka shima nasa, yasa halshen sa yafara lasar hawayena yana tsosar kwarin idona.


Ya fara wata sheshshe ka, Altab da yaji daidai bakin ta sai tsaya ya dubeta yace "Rabab". Ta bud'e idon ta ta kalle shi cikin ido, tayi wani luum da idonta, kuma ta bud'e labb'an ta, Altab yace "Oh my god". Tuni ya had'e bakinta na nasa ya fara tsotsa, itama tana mayar masa abinda yake yi mata.


Can ya sake mak'aleta, yana shafar sauran sassan jikin ta, ya Saki bakin ta, ya nemi wuyanta daga nan yakai zuwa k'irjin ta, sai nunfashinta yake k'ok'arin d'aukewa, tace "Yaya a falo fah muke". Yace " ai k'ofar a kulle take babu wanda zai ganmu. Tace "Uhum!!".


Yaci gaba da abinda yakeyi, a hankali ya b'alle mab'allin dake gaban rigarta, tayi wani d'an kuka, wanda yasa yasake mantawa da kansa, can sai sukayi phone d'insa ta fara ringing, yayi sauri ya saketa yasan Abban shine ke kiran shi, yayi sauri yaje dan yayi yyi picking Call d'in.


Tayi sauri ta mayar da mab'allan rigarta da d'an kwalinta, yayi shiru na d'an wani lokaci, itama haka, suna ta mayar da numfashi a hankali.


Nan ta fara kuka tana cewa "nidai na baka amanar kanka, dan Allah ka kula da kanta nasan halin da kake ciki, bana son ka daina sona ko kuma a raba muna son".


"Kema kinsan bazai yiyuwa ba, ki daina shakka dan Allah, cikin zuciyata banida wacce nike so sai ke".


Nan suka ci gaba da hirar su suna kuma Romancing each other, sai wajen k'arfe 12pm, sukayi sallama, yace "Abba yace ya wuce daga nan zai turo driver ya kawo su Ilham, nan ya k'ara kissing d'inta sukayi sallama.


Kwanci tashi yau kwanan Altab biyu kenan, amma babu ranar da baza suyi waya ba, gashi kuma yau ta tashi da wata irin kasala bata jin dad'i.


Gaba d'aya gidan ya hautsine saboda shirye shiryen y'an makaranta, duk da a kwai mai aikin da take taimakamin, duk da kasalar da nake ji bai hanani taimaka mata ba gurin gyaran su, nan muka shiryasu tsaf driver yazo ya d'auke su, nan nace mashi idan ya d'auko su ya ajiye su gidan su Umma.

Nan nacewa mai aiki koda ta kammala abinci karta tasheni zanyi bacci, yau banajin dad'i tace min "To."


mai ai ki kuma ta shiga kitchen ta na aiki.


Ni kuma na koma d'aki na kwanta sai bacci nikeyi har kusan 4pm, ban falka ba.


K'arar waya ya tasheni, nan d'auka cikin kasala duk da baccin da nayi amma zazzab'in yak'i sakina.


"Hello".

"Wife nayi missing d'inki ,wallahi tun safe muka shiga meeting sai yanzu muka gama, kuma yau yau zan kamo hanyar dawowa dan gaskiya bazan iya Jira har sai gobe ba."


"Allah ya kawoka lafiya."


"Amiin, wife ya naji muryar ki kamar ba daidai ba.?"


"Wallahi Yaya tun safe banajin dad'in jikina komai naci bana jin dad'in sa."


"OMG ai dolene ma na dawo yau dan nayi jinyar matata."


Tayi murmushi tace "Karfa ka tayar da hankalin ka ba wani abu bane zazzab'i ne kawai kuma zanji sauk'i."


Yayi ajiyar zuciya yace "ga Abba nan yana kirana bara mu gama waya sai muyi waya ko.?"


Tace " OK I wish you the best of luck, Take good care of yourself. "


Yace "I will and you too bye."


Nan na tashi a hankali nashiga toilet nayi wanka na d'auro alwala, bayan na gama sallah naje falo, na d'an ci abinci kad'an sannan na dawo d'aki na k'ara wata kwamciya, sai gurin 6pm, Yaya ya kirani.


Nace "Ran Mai gida ya dad'e".


Yace "Mai gida ko mai gira."

Tace "Ya haka?".

"Lafiya amma ina wani gari kema kina wani garin, ina zancen mai gida?". Nayi dariya. Yace "Ya jikin naki". Nace "Ai naji sauk'i.

"Ko dai new baby, zan samu ne.?"


Nayi dariya nace " haba wa wane irin New baby ai su Twin's sun isheni.?"

Yayi murmushi yace "Ashe in k'ara himma, da na dawo mu samu baby koh?".


"Hmm, dagaji magar tayi mata nauyi da yawa."


Yace "ki k'ara himma, don naga alamar raggwancin daga wurin kine."


Nace "Kai yaya ba kunya gaba d'aya, nidai na fad'a maka zazzab'i ne kawai yake damuna.Yayi murmushi yace "Wallahi Rabab duk randa mukayi waya bana iya bacci, na dinga tunanin ki da kuma yadda muryar ki take da surarki, gashi banida yadda zanyi in ganki, ballan tana na biya buk'ata ta sai dai nayi ta mafalkin ki."


Nayi dariya...


Yace "Wife". Ta amsa a hankali. Yace "Wayyo dan Allah ki bari don wannan ai is a bedroom voices, idan kika ci gaba bazan iya daurewa ba.


Tace "Yaya ni banyi komai ba. "Kai bakajin yanda kake magana.?" Yace "ya nikeyi?". Tace "kaima da ita irin husky voices d'innan. Yace "Allah da gaske?. Tace "Allah da gaske nike. Yace "Bada niya nayi ba, ke kika Sa ni."


"Wife kin san me?.

"A'a sai ka fad'a".

"Gani fa nan inata sharar hanya, da naso kawai ki ganni muna k'are magana da Abba na fad'a mashi na kammala komai, shima ya k'ara bani k'warin gwaiwa na dawo".


"Haba dan Allah da gaske kake ko zolayata kake? ".


"Allah da gaske nake d'azun da mukayi waya ba na fad'amaki zan dawo ba?".


"Allah kuwa na d'auka wasa kake min, amma bara na tashi na gyara".


"OK, I missed you."
Nace "Me too."


Na tashi nayi k'ok'arin gyara ko ina, nashiga toilet na k'ara wanka nayi simple makeup d'ita na d'auko wata doguwar riga na saka na feshe jikina da turarukka.


Wasa wasa ina nan zaune har dare ya tsala, amma banga kiran Yaya ba kuma nayita kiran wayan shi switch off, sai nayi tunanin k'ilan ya tsaya wani gurine ya kwana, amma idan har ya tsaya wani guri ai ko aron waya zai iyayi ya kirani amma shiru ko d'aya, nan wani zazzab'i ya k'ara rufeta, tunani takeyi da 'yan sak'e sak'e har bacci ya kwashe ta.


Safiya na wayewa, tunda ta farka gabanta ke fad'uwa sallah kawai tayi ta d'auki waya ta kira shi amma har yanzu wayar shi a kulle take.


Hankalin ya tashi matuk'a ta rasa yanda zatayi wata zuciya tace mata taje gidan su taji, amma dai tace bara ta kira wayan Umma taji ko sunyi waya dashi.


Tayi wa Umma kira yakai biyu, sai ga na uku ta d'auka.


"Hello Umma".

"Rabab jiramu gamu nan zuwa".

Take gabanta ya k'ara fad'uwa dajin muryar Umma da alamu kuka takeyi.


Cikin tashin hankali nace "Umma dan Allah mike faruwa?".


Bata bani amsa ba kawai ta tsinke waya.


Nan danan naji hawaye suna sulalo min k'asa nike sama nike oho.


Sai dai naji motsin shigowar su Umma ita da wasu, ina kan gado ko motsi na kasa, Umma tazo kai na ta rik'eni itama tanata kuka.


Cikin kuka take magana tana cewa "Rabab kiyi hak'uri duk musulmi sai yayi imani da k'addara kuma sai Allah ya jarebe shi Rabab kiyi hak'uri da jarabawar da Allah yake jarabtar ki da ita ki sani yafi kowa sonki.

Nan na k'ara fashewa da kuka ina cewa.


"Dan Allah Umma ki fad'amin mike faruwa dan Allah ina yaya yake ki fad'amin Umm....

Bata iyar da magana ba wani kuka ya k'ara kucce mata.


Duk wanda yake falon, nan sai da yayi kuka saboda tausayin ta.


Cikin kuka Umma ke cewa


"Rabab kiyi hak'uri Altab ya samu mum munan jarabawa a kan hanyar shi ta dawo yayi had'ari ya..........


Wata irin k'ara na Saki nan na sulale na fad'i k'asa sume.........
[5/3, 8:21 AM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_


*ALLAHUMMA BALLIG AYYAMANA ILA RAMADAN, WAR'ZUK'UNA BIMAFIHI MINAL KHAIRAT*๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿคฒ๐Ÿป

*Ya Allah kaja kwanakkin mu izuwa watan Ramadan, kuma ka azurtamu da alkhai ran dake cikin watan ameen*๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป*Page 43n44*

Hankalin su Umma yayi matuk'ar tashi ganin Rabab a kwance ko motsi batayi, haka suka tallabeta a rud'e basu tsaya ko ina ba sai asibitin Dr Hakeem, daidai lokacin da suka iso daidai lokacin da su baba Alhaji suka iso cikin motar ambulance, sun d'auko Altab.


Gaba d'ayan su cikin asibitin aka shige dasu, inda akayi da Rabab sashen mata, Altab shima aka wuce dashi sashen maza, su kansu likitocin sai da suka tausaya masu ganin halin da Altab yake ciki, gashinan cikin jini kwance ko motsi bayayi, taimakon gaggawa Dr Hakeem shida sauran likitoci suka basu nan danan.


A b'angaten Altab kuwa an shiga da shi d'akin da ba'a barin kowa ya shiga yagan shi, Dr Hakeem yayi saurin kiran wasu abokan shi likitoci, take suka iso cikin gaggawa, Oxygen sukayi k'ok'arin saka mashi cikin gaggawa, nunfashin sa sai Seasing yake yi, da k'yar suka samu sukayi aune aunen da zasuyu, duk da sai sun dannan k'irjin shi da sauri nunfashin sa yake fita, bayan sun gama aune shine suka yi mashi allurar bacci, gaba d'ayan su suka fito suka shiga d'akin da zasu fidda results d'in matsalar daya samu.


A b'an garen Rabab kuwa likitoci ne mata kanta da Nurses Nurses, bayan sunyi mata allurori ne suka saka mata drip, Umma ce kuka da ita babu abunda takeyi sai kuka, dan ita ta riga ta fidda rai da Altab, likiton nan sukayi ta bata hak'uri suna kwantar mata da hankali suka ce ta kwantar da hankalin ta, suma ce tayi nan da d'an wani lokaci zata farka, nan suma suka fita office d'insu domin fidda results d'in awon da suka yi mata.


Umma zaune take sai sharar kuka take, can sai taga hannun Rabab d'aya ya fara motsi, da sauri Umma taje ta zauna kan gadon, daidai lokacin da tafara bud'e idanuwanta da sukayi jajir sai k'walla suke fitar wa, Umma cikin kuka take cewa.


"Dan Allah Rabab ki daina wannan kukan, babu abunda kuka zai haifar maki sai matsala, nasan irin rad'ad'in da kikeji, amma idan kika tuna kullu nafsun za'ik'atul mau..........
Da sauri ta rufewa Umma baki, cikin kuka mai tsuma zuciya take cewa.


"Dan Allah Umma kar kicemun Yaya ya mutu, wallahi Umma Yaya bazai mutu ya barni ba, na rasa Aunty na wacce bayan Abban mu tafi kowa sona, kuma Umma yanzu zan rasa yaya bayan na saba dashi, Umma dan Allah ki fad'amin me na aikata ne Allah yake jarabtata da wa'innan k'addarorin Why! Why!!, nan ta k'ara sakin wani irin kuka da har Umma sai data taya ta, dan Allah ki kaini wurin yaya na ganshi, wallhi zuciyata bugawa zatayi, nan ta fara k'ok'arin cire drip d'in da aka saka mata, da k'arfi ta zare allurar hannunta, nan take jini ya biyo baya sai jini yake zuba a hannunta, hankalin Umma ya tashi sai k'ok'arin hanata take amma sai da ta mik'e tsaye, babu abunda take ji sai jiri ke d'ibar ta, nan ta fad'i kwance a k'asa."


Da gudu Umma taje ta kira Nurses, da sauri suka iso nan suga ganta tanata k'ok'arin tashi amma jiri take gani ta tana fad'uwa, da sauri suka iso kanta inda Nurses d'in ta rike ta gam tare da taimakon Umma, Rabab ta koma kamar wata mahaukacciya, nan take Nurse d'in tayi mata allurar bacci, kafin allurar tafara aiki nan ta dinga sabbatu tana cewa.


"Dan Allah ku kaini naga Yaya, nasan yanason ya ganni, dan Allah Umma ki kaini wurin ya......... Nan bacci ya d'auketa."


A b'angaren su baba Alhaji da abban su Rabab, tsaye suke kowa yayi shiru sai safa da marwa suke kamar masu aikin hajji, Abba ne ya fara cewa baba Alhaji.


"Dan Allah Alhaji kad'an zauna ka san fa halin da kake ciki, kai ma fa ba isassar lafiya gareka ba."


Nan baba Alhaji ya fashe da kuka kamar wani k'aramin yaro yana cewa.


"Ai bazan tab'a zama iya zamaba sai naji halin da Altab yake ciki, wallahi tunda nike da Altab dadai da rana d'aya bai tab'a yimin musu ba, yaron da yaffison farin cikina bisa da nas.........."


K'arar bud'e k'ofa ne ya tsaida shi daidai lokacin Dr Hakeem ya fito, Abba ne yayi saurin tareshi yana tambayar shi.


"Dan Allah Dr ka fad'a muna idan Altab ya mutu mu sani, tunda mu dai ba k'anan yara bane."


Dr Hakeem yace "Su biyo shi zuwa office d'in shi."


Shigar su kenan ko zaunawa basuyi ba sai dr, ta shigo cikin ladabi ta mik'awa Dr Hakeem results d'in da ta samu game da test d'in da tayiwa Rabab, nan ta fita ta barsu.


Office d'in yayi shiro babu abunda kakeji sai motsin fankoki dake kad'awa Dr kuwa sai kallon takaddat yake.


Abba ne ya fara magana "Dan Allah Dr ka sanar damu mike faruwa, kai musulmi ne muma haka, kuma munyi imani da k'addara mai kyau ko marar kyau."


Dr Hakeem ne yafara magana "Alhaji tsakanina daku babu wani b'oyo, tun ban kawo haka ba kuke tare dani, kuma Altab shima d'anane, result na farko shine na Rabab, ga dukkan binciken da muka yimata ya nuna mana tana d'auke da ciki, kuma cikin k'arami ne dan haka tana buk'atar kulawa sosai, kuma ayi k'ok'ari aga damuwar da take ciki ta samu sauk'in ta, saboda damuwar zata iya haifar mata matsala, hatta abunda ke cikinta."


"Result na biyu kuma shine na Altab, sakamakon had'arin daya samu kansa ya bugu sosai da har yad'an tab'a brain d'in shi, ko wane d'an adam yanada wasu ruwa cikin brain d'in shi wa'inda ruwan nan suna cikin wata tsoka Allah ya b'oye su, ita kuma tsokar tana tarene da wata jijiya wacce tun cikin kan mutun take har zuwa k'afafun sa, to da zarar ruwannan aka samu matsala suka zube to mutun bazai k'ara wani aiki ba, idan kuma ruwan suka d'an hude zasu dinga d'iga daga lokacin wani sashe daga jikin ka zai daina aiki, zai dinga sabbatu, zaiji kamar ana saka mashi iska a kanshi, idan ba'ayi saurin ganewa ba dasun gama zuba shikenan ka zama na kasash she, kuma hakan yana faruwa ne daga had'ari ko kanka ya bugi k'asa sosai, amma shi anyi sa'a basu zube ba illa dai sun fara d'an d'iga, shiyasa mukayi mashi allurar bacci munfison koda zai falka anriga anyi mashi aikin, dan kada wata matsala ta b'ullo duk da ba fata muke ba."


Kowa yayi shiru, baba Alhaji ko motsi bayayi kamar wanda bashida rai, Abba ne yafara magana.


"A matsayin mu na musulmai wa'inda sukayi imani da k'addara, to komai ya same mu farin ciki ko akasin hakan babu abunda zamuce sai ALHAMDULILLAH, ita kuma Rabab Allah ya sauke ta lafiya, kuma ya bata lafiya, dan bamuda wani taimako da zamu bata wanda ya wuce addu'a da lallashi, dan bazamu iya hana abunda Allah ya k'addara ba."


Shi kuma Altab a yanzu dai aikin gama ya gama, kuma hakan bazai nuna kamar Allah yaba son shi ba, ko wane d'an adam tun kafin yazo duniya da k'addarar da Allah ya rubuto mashi, a yanzu dai Dr miye mafita kuma miye abunyi?.


"Too mafita dai d'aya ce, dole aiki za'ayi masa, kuma sai mun nemo wani dr daya fimu k'warewa akan matsalar, nan Nigeria yake amma a India yayi karatu, yayi karatun sane dangane da duk abunda ya shafi kwakwalwa, kuna duk Nigeria su ukku kawai ne, ya kuma iya aiki sosai dalilin hakan ne yasa suka rik'e shi can yana masu aiki, idan kun amince kuma zaku saka hannu, zan kirashi yau, insha Allah zuwa gobe zai shigo jirgi yazo Nigeria, saboda yana matuk'ar kishin k'asar shi."


"Too Dr idan akayi aikin ana dacewa.?".......cewar Abba.


"Eh to, amma kasan komai sai yadda Allah ya tsaro, mu likitoci iyakar mu muyi aiki, bada sauk'i da waraka kuma yana wurin ubangiji, za'a iya samun nasara ko akasin hakan, a gaskiya dai wasu ana samun nasara, wasu kuma ayita hala har ku koma ga Allah."


Cikin nasarori guda ukku, da za'a samu saboda komai Allah ya k'addara to daidai ne ga bawansa, dolene d'aya zai kasan ce ansamu.


"Abu na farko shine, zai iya rasa rayuwar shi kwata kwata, na biyu kuma, zai iya samun sauk'i ya warke kamar ba shiba, sai na ukkun, zai iya manta kowa ya manta komai ya manta rayuwar da yayi gaba d'aga, ma'ana yayi loosing memory d'in shi."


Wannan karon ba baba Alhaji ba har Abba sai ya ya zubar da hawaye, cikin murya irin ta tausayi yake cewa Dr.


"Yan zu mun amince duk abubda za'ayi masa ayi, fatan mu dai Allah yasa ayi cikin nasara."


"Dr yace "Amiin..... Amma akwai wata shawara da zan batu, kuje makaranta da masallatai da duk wani wurin da jama'a ke taruwa, ku kai masu sadaka, domin neman addu'a asamu nasara, kuma daga yau bacci bai gane kuba, ku tashi cikin dare ku kai kukan ku wurin ubangiji."


"In sha Allah Dr haka za'ayi, kuma muna godiya da irin taimakon daka bamu."


"Haba Alhaji wace irin godiya, ai anriga da anzama d'ai."

*** *** *** *** ***

Kwanan su Alhaji biyu a asibitin, sannan Dr d'in ya iso Nigeria, wanda suke kiran shi da Dr Manduler, an gama duk wani shiri da za'ayi, shiga dashi kawai za'ayi, kuma duk shawarar da Dr Hakeem ya basu sun aikata, sun sa anyi saukar alk'ur'ani ba iyaka da neman addu'oi wurin jama'a.


Dr Hakeem ya basu umurnin su shigo su ganshi, kafin su shiga aikin da shi, nan suka iske Dr Manduler yana aiske duk wani gashin kan shi kwata kwata.


Baba Alhaji ne yake tambayar shi "Dr miye amfanin yin hakan ne.?"


Dr yayi murmushi yace "Ai duk wanda za'ayi wannan aikin sai anyi mashi haka, idan kuma mace ce zamu iya aske daga wurin da zamu yanka, kai idan takama ma zamu iya aske gashin gaba d'aya."


"Too Dr yanzu bazamu iya d'auko matar shi ta zo ta ganshi tayi masa addu'a kafin a shiga ba."


"What.... Kasan me kake fad'a kuwa, ai a halin da take ciki yanzu bamu son wata damuwa ta k'aru, bayan wacce take ciki yanzu, babu abunda yake nema yanzu wurin ta da wurin ku illa addu'a."


A b'angaren Rabab kuwa, ta farka amma banda kuka babu abunda takeyi, kuka shine abincin ta duk ta rame, kamar ba ita ba ta zama Abun tausayi, idan ka shekara kana mata magana ko uffan bazata ceba kuka shine amsar ta.


A b'angaren su Dr kuwa duk wani abu da za'ayi anyi, nan suka sako kayan su na aiki wurin su shidda, shima suka cire mashi kayan shi suka saka mashi rigar aiki, saman wani gado suka turo shi, nan suka shige dashi cikin d'akin aiki suka rufe.


Su Abba da baba Alhaji suna nan tsaye har aka wuce dashi babu abunda sukeyi sai addu'a da zubawa sarautar Allah ido...............
[5/7, 10:50 AM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*﷽*

ุงู„ู„َّู‡ُู…َّ ุตَู„ِّ ุนَู„َู‰ ู…ُุญَู…َّุฏٍ، ูˆَุนَู„َู‰ ุขู„ِ ู…ُุญَู…َّุฏٍ، ูƒَู…َุง ุตَู„َّูŠْุชَ ุนَู„َู‰ ุฅِุจْุฑَุงู‡ِูŠู…َ ูˆَุนَู„َู‰ ุขู„ِ ุฅِุจْุฑَุงู‡ِูŠู…َ، ุฅِู†َّูƒَ ุญَู…ِูŠุฏٌ ู…َุฌِูŠุฏٌ،

ุงู„ู„َّู‡ُู…َّ ุจَุงุฑِูƒْ ุนَู„َู‰ ู…ُุญَู…َّุฏٍ، ูˆَุนَู„َู‰ ุขู„ِ ู…ُุญَู…َّุฏٍ، ูƒَู…َุง ุจَุงุฑَูƒْุชَ ุนَู„َู‰ ุฅِุจْุฑَุงู‡ِูŠู…َ،
ูˆَุนَู„َู‰ ุขู„ِ ุฅِุจْุฑَุงู‡ِูŠู…َ، ุฅِู†َّูƒَ ุญَู…ِูŠุฏٌ ู…َุฌِูŠุฏٌ

*Page 45n46*

Tun safe da suka shiga sai yamma suka fito aikin, inda suka bar su baba Alhaji nan suka fito suka same su, fitowar su keda wuya su baba Alhaji da Abba suka tashi tsatstsaye baku nan su cike da tambayoyi.


Dr Hakeem ne yayi masu iso da su biyoshi zuwa office d'in shi, da zuwan su bayan sun zauna, Dr Hakeem ya dube su cike da murna yayi murmushi yace..


"ALHAMDULILLAH...Godiya ta tabbata ga Allah, ga dukkan alamu muna saran aiki anyi shi cikin sa'a, kudai ci gaba da addu'a kuma yanzu insha nan da zuwa gobe zai falka."


Su baba Alhaji da Abba cike da murna, fuska cike da annuri, cikin murmushi yake cewa.


"Dr, muna godiya Allah yabar zumunci..."

"Amiin Amiin Alhaji, ai babu komai yiwa kaine."


Nan suka tashi, suka fito domin ganin lokacin sallar magrib ya gaba to...


Bayan sun fito daga sallar magrib, ne suka nufi wurin da aka kwantar da Rabab, nan suka isko Ummu na bata d'an ruwan Tea tana sha a kad'an kad'an, bayan sunyi sallama sun gaisa ne, nan suka shiga fad'awa Umma duk abunda ya faru, murna Umma tayi jitake kamar ta rungume Alhajin ta, nan suka shiga kwantar wa da Rabab hankali cewa ta kwantar da hankalinta Altab yana nan raye be mutu ba, da sauri ta saki cup d'in Tea ta rungume Abba ta na kukan dad'i, nan take cewa Abba dan Allah akaita wurin shi ta ganshi, nan suka fad'a mata komai da dr yace, sai zuwa gobe zai falka...


Daren ranar dukansu baccin dad'i sukayi, Rabab kuwa ta k'agu taga safiya ta waye taga yayan ta.


Bayan wayewar safiya, sai 8am, suka iso wurin dr, bayan sun gaisane nan dr yake cemasu ai tun 6am, ya falka, kuma tunda ya falka babu abunda yake kira sai Rabab, yanzu ma shirin da nake naje na sameku muzo da ita, kasan duk abunda marar lafiya yake so, anaso ayi gaggawar bashi, balle ma shi d'an lele, na sukayi dariya gaba d'ayan su cike da raha, baba Alhaji yace mai ai duk gaba d'ayan mu mukazo, mun baro su wajene.


Nan dr yace "To su taso suje."

Bayan sun fito waje, nan suka gaisa dasu umma da Rabab, nan suke mashi bayanin itace matarshi, nan yake cewa ai kuwa kamar ya santa lokacin da aka kawo ikram haihuwa nan, Abba ne yake ce mashi ai k'anwar tace bayan rasuwarta aka had'a su aure, nan dr yayi murna kuma yaji dad'in hakan.


Gaba d'ayan su suka nufi d'akin da Altab yake, yana zaune akan gado babu abunda yake sai faman kuka, yana ganin mu da sauri yayi k'ok'arin tashi, dr ne yayi saurin rike shi saboda akwai drip a hannun shi, murmushi yake cike da kukan dad'i dayaga su Abba da umma da Rabab.
Rabab kuwa ta riga ta manta tare su wa suka shigo da saurinta ta isa wurin shi ta rungume shi suna ta kukan dad'in su.

Ganin hakan yasa suka fito gaba d'aya suka barsu su kad'ai, nima nan na tattara alk'alumma na, na rufo masu k'ofa nace "Asha love lafiya.."


Suna fitowa nan suka nufi office d'in dr, nan yake ce masu sun k'ara yi mashi wani scanning, sun gano yanzu babu matsalar komai, dan haka zamu sallame shi ku koma gida dan sai yafi masu kwanciyar hankali, zan rubuta maku maganun nukan da za a dinga bashi nan suka k'ara yiwa dr godiya tare da tarin alherai suka bashi suka yi sallama.......

*** *** *** *** ***

*TWO WEEK'S LETTER......*

ALHMDULILLAH...Altab ya warke yaji sauk'i sosai, bayan an sallami Altab daga asibiti abubuwa na alkhairai da dama Sun faru,, Altab yana samun cikakkiyar kulawa wurin Rabab komai ita tale yi mashi daidai da wanka bata bari yayi da kansa, yayi k'ibar sa yayi b'ulb'ul abunsa, ya murmure kamar bashi ba, har ya fara fita, Rabab kuwa ita ma tayi b'ulb'ul tayi k'iba farinta ya k'aru sai wani haske take abun ka da Mai ciki,, cikin tama ya fara girma babu ranar da baya magana da babyn sa.


Yau ce ranar da gaba d'aya family d'in su daba baban shi da nata duk su zo k'ara duba shi, nan suka zo masu da abubuwan alherai masu yawa, sukayi zumunci sosai duk da anyi kewar juna sosai, nan sukayi sallama zasu wuce, umma ce ta k'ara yiwa Rabab hud'uba, kuma ta bata wasu maganun nuka, Abba ma sai da ya tambaye ta akwai wata matsala tace babu komai, nan sukayi addu'a suka fito zasu wuce, har k'ofar gete muka rakasu, nan suka bar su Ilham, sukayi sallama suka wuce, bamu wuce ba har sai da motar su ta tashi ta wuce, sannan muka dawo cikin gida nan suka wuce cikin daki ya d'auketa cak sai kan bedroom, nan yafara kissing d'inta ta ko ina daman an dad'e ba a had'uwa, nan yakai hannun shi ga na fulanin ta, take ya k'ara rud'ewa jinsu yayi Sun Kara ciccikowa, gaba d'ayan su suka lula sama ta bakwai, daman dukan su sunyi missing d'in junan su, nan ma na k'ara rufo masu k'ofa nace "Aci amarci lafiya.."


*** *** *** *** ***

Gabad'aya gidan ya hautsine saboda shirya 'yan makaranta, duk da masu aiki na taimaka mata, amma ya zama dole infita saboda su Anwar da Arwa, in bani na shirya su ba, basa tsayawa.


Ni kaina wata ranar suna gudu ina sa masu kaya, in ba Allah ya taimake ni Yaya ya sauko ba, duk da bancika so ya sauko ba saboda baya barinsu su sake.


Ko ya sauko zaunar dashi nake in ce ya zama d'an kallo, sai yaga mun kusan makara sannan.


Yau ma haka akayi yana falo, a zaune da jaridar shi mai suna leadership, a hannun sa, yana rabi dubawa, rabi kallon mu.


Anwar ne ya fito a guje daga shi sai d'an k'amin wando pant, na biyo shi da gudu, tare da kayan makarantar shi, a hannuna ina ta kiran shi, falo ya nufa kanshi tsaye yanda ya saba, yayi tsalle a wannan kujerar, ya koma waccen, sam bai fahimci baban shi na falon ba, har sai da ya isa, d'ago kai kawai yayi ya kalle shi, sai yayi saurin sunkuyar da kai tare da tsayawa cak!....Ya d'ago ya kalleni fuskar nan tashi a d'aure.


"Saka mashi kayan, maza ka tafi ka saka shoe's d'in ka, idan an saka maka kayan, kana jina."


Ya d'ago kai tare da nufo inda nike, inata nishin gajiya, nima sai da na d'an ja kunnen sa sannan na saka masa kayan, na ce masa.

"Ka d'auko shoe's d'in na saka maka."

Ya ruga a guje, sai ga su sunfito tareda Arwa.


Na tsugunna duk na saka masu socks and shoes, sannan nace su tafi motor zan kawo masu lunch box d'in su, ba gardama suka wuce cikin dubara na yunk'ura na tashi banji isowar yaya ba, sai dai naji ya ruk'o hannuna, sai dai ya girgiza kai bayan na juyo sannan ya fara magana.


"Rabab dan Allah ki dinga hutawa."

"Jira in kammala dasu in dawo."

Ya rik'e ni sosai....

"No wife, ki tuna fa bake kad'ai bace ba yanzun, cikinki ya fara tsufa, ki d'an dinga samun hutuwa."


"Yaya karka damu, ina iya komai."

Ya b'ata fuska sosai..

"A'a k'anwata, kiyi hak'uri bana son in ganki cikin irin wannan yanayin, kina wahala.
Ya sunkuyar da kansa.


"Bana son gardama, haka mukayi da Auntyn ki, sai gashi daga baya dole aka nemi hutun da bashida wani amfani."

Jin muryarshi tayi k'asa yasa na hannayena da d'ago fuskarshi.


"Yaya ba abinda dai same ni da yardar Allah."


Hawaye naga sun gangaro ga kumatun sa, cikin yanayin tashin hankali na rik'e fuskarshi da hannayena duk biyun, tare da cewa.

"Yaya..."


"Rabab bana son in rasaki kema, wallhi na rasaki mutuwa nima zanyi...."
[5/7, 4:58 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_


*Nine things will give you benefits everyday:*
*1/ ุชุฑูŠุฏ ุงู„ุณุนุงุฏู‡ = ุตู„ ุงู„ุตู„ุงุฉ ููŠ ูˆู‚ุชู‡ุง.
1. *If you seek happiness: Offer salat on time.*

2/ ุชุฑูŠุฏ ู†ูˆุฑ ุงู„ูˆุฌู‡ = ุจู‚ูŠุงู… ุงู„ู„ูŠู„.
2. *If you want light on your face:*
*Rise up for tahajjud in the night.*

3/ ุชุฑูŠุฏ ุงู„ุทู…ุฆู†ูŠู†ุฉ = ุนู„ูŠูƒ ุจุชุฑุชูŠู„ ุงู„ู‚ุฑุขู†.
3. *If you want tranquility and peace: Recite the Qur'an slowly and carefully.*

4/ ุชุฑูŠุฏ ุงู„ุตุญู‡ = ุนู„ูŠูƒ ุจุงู„ุตูŠุงู….
4. *If you seek health: Fast*

5/ ุชุฑูŠุฏ ุงู„ูุฑุฌ = ู„ุงุฒู… ุงู„ุฅุณุชุบูุงุฑ.
5. *If you seek inner joy: Keep on with repentance.*

6/ ุชุฑูŠุฏ ุฒูˆุงู„ ุงู„ู‡ู… = ู„ุงุฒู…
ุงู„ุฏุนุงุก.
6. *If you want to be free from sorrow: Keep on praying.*

7/ ุชุฑูŠุฏ ุฒูˆุงู„ ุงู„ุดุฏู‡ = ู‚ู„ ู„ุงุญูˆู„ ูˆู„ุง ู‚ูˆุฉ ุฅู„ุง ุจุงู„ู„ู‡
7. *If you want violence to disappear, say: La hawla wa lรข quwwata illa billah.*

8/ ุชุฑูŠุฏ ุงู„ุจุฑูƒู‡ = ุตู„ ุนู„ู‰ ุงู„ู†ุจูŠ ูˆุงู„ู‡ ุงู„ุทูŠุจูŠู† ุงู„ุทุงู‡ุฑูŠู†.
8. *If you seek abundance:*
*Recite praises and greetings to the Holy Prophet (saww) and his virtuous family and companions*

9/ ุชุฑูŠุฏ ุญุณู†ุงุช ุจุฏูˆู† ุชุนุจ =
ู„ุงุชุญุชูุธ ุจู‡ุง ุฃุฑุณู„ู‡ุง ู„ูŠู†ุชูุน ุจู‡ุง ูƒู„ ุงู„ุงุญุจู‡
ุณุจุญุงู† ุงู„ู„ู‡
ู…ู† ูƒุงู† ู…ุน ๏บ‚ู„ู„ู‡ ูƒุงู† ๏บ‚ู„ู„ู‡ ู…ุนู‡
ูˆู…ู† ูƒุงู† ูŠุญุจ ๏บ‚ู„ู„ู‡ ูƒุงู† ๏บ‚ู„ู€ู„ู‡ ูŠุญุจู‡
9. *If you wish to do goodness without getting tired: Do not keep this message to yourself. Let your loved ones benefit from this too*.

*Allah (SWT) is with those who are with Him and consider His commandments*

*Allah (SWT) loves those who love Him.*

ู‡ู„ ุชุนู„ِู… :
ุนู†ุฏ ู‚ุฑุขุกุฉ ุขูŠุฉ ุงู„ูƒุฑุณูŠ ุจุนุฏ ูƒู„ ุตู„ุขุฉ
ูŠbbุตุจุญ ุจูŠู†ูƒ ูˆุจูŠู† ุงู„ุฌู†ู‡ ุงู„ู…ูˆุช ูู‚ุท
ุชุฐูƒูŠุฑ :ู„ุง ุชูƒุชู… ุนู„ู…ุงً ุฎูŠุฑุงً ุชุฌุฒู‰ ุจู‡

*Do you know?*
*If you recite the Ayat al Kursiyy after prayers, only Death will remain between you and the paradise*

*Page 47n48*

"Me yakawo maka wannan tunanin har haka.?"

Ya sakeni ya tafi ya zauna, na tafi zan isa wajen shi, naji Ilham ra fito, tare da tambayata su Anwar, na amsa mata suna mota.

Tare da bata umurnin ta d'auko kulolin abincin su da lunch box d'in su Anwar da Arwa, sai da na rakata har k'ofa, kamar yanda na saba, sannan na dawo ciki.

Hankalina a tashe na isa wajen Yaya, da sauri cikin yanayi na firgita ya rungume ni gam, na samu na d'ago shi daga jikina, sannan na tallabi kuma tunsa.

"Yaya.... Na fad'a cikin siffa ta tashin hankali."

Cikin k'ank'anin lokaci duk ya firgice yayi sauri ya kama kumatuna ya tsotsi bakina, na d'ago shi.

"Yaya ka kwantar da hankalin ka."

"Rabab dole hankalina ya tashi matuk'a, idan har na tuna da kalar rayuwuwar da nayi da 'yar'uwar ki, cikin k'ank'anin ta tafi ta barni, Allah ya kawo mani canjin wacce ta fita.

Ki tuna wajen haihuwa ta tafi ta barni, kema kuma kinzo irin yanayin da ta tafi ta barni.

Rabab kina sona da yarana, wannan ne ya sani mugun sonki, haka tun farko son 'yar'uwarki da kike shi ya dawo kaina, kinga albarkacin ta nike ci, Yaya zan so ki tafi barni ni kad'ai.

"Yaya ce maka akayi mutuwa zanyi, waya gaya maka, kawai shed'an yake saka maka haka ka kwantar da hankalin ka insha Allah lafiya kalau zan haihu, komai ya zama tarihi, kuma kasa a zuciyar ka haihuwa goma zanyi da kai, insha Allah ba zan mutu ba, tunda mata da yawa basu mutu ba.

Ita ma Aunty sanadiyyarta ta rasu, saboda Allah ya k'addara ina da 'Ya'ya tare da kai, kuma ta hanya Mai kyau yake so mu haife su, kaga dole ita za a kawar don in shigo in haifa maka 'ya'ya, tare da baka ingan tacciyar kulawar rayuwa."

Ya d'ago fuskata wacce hawaye suka gangaro mata.

Cikin kuka nake cewa.

"Ka sani ban isa in hana mutuwa zuwa ba idan lokacina yayi, amma ka sani ko gida ba zanje wanka ba, na riga ma na kashe wannan maganar tun kafin tazo kunnena, na gaya masu bani iya rabuwa daku, idan na barku ya zakayi kai da yarana."

Amma in na gama wankan sai naje inyo sati ukku."

Na fad'a cikin sigar shagwab'a, sai a lokacin naga yayi murmushi.

"Sati uku, ai ma matsala bane, k'ara da kika fad'amin da wuri in yi mana tanadin tafiya hutun sati uku."

Na harare shi nace.

"Dawa zan tafi.?"

"Dani da zuciyata da hantar jikina."

"Ban gane ba."

"Zaki gane idan ranar tazo."

Nayi murmushi nace, "Lallai akwai aiki."

"Aiki?..... Kad'an kika ambata, cewa zaki da akwai gumurzu."

Nasa dariya...."Kai d'innan.'

"Kima sani nafi haka, mantani kikayi, don a lokacin baya, ba kya son ganina, amma haka nayi wa 'yar'uwarki, satinta biyu aka koro mu.

Nan hajiyar mu tazo tana tayi mani fad'a, na hana yarinya zaman gidan su a kula da ita, nidai nayi shiru, a zuciyata kuwa cewa nake, kulawa ta wuce ni, waya sakar mata ciwo, ni! Don haka ni yakama ta inyi jinyar kayata."

"Ai ni zan biyo kaba."

"Abu Mai sauki, sai muyi zaman mu, ni kin sa ma tun yanzun zan fara tura yaran gida don ki samu ki huta, kamin mu same can."

"Ban gane ba."

"Su tafi wajen Ammi suyi zaman su, ke kuma ki huta dama su Anwar sai gajiyar dake suke yi, kinji yanda nike ji kamar in yita dukan su."

"yawwa daman ina son magana dakai, game dasu."

Naja kunnen shi d'aya har sai da yayi 'yar k'ara tare da fad'ar.

"Wayyo me nayi.?"

"Me yasa kake takurawa yarana, ka duba fa Anwar ganin ka kawai yayi ya natsu."

"Me kika ce yanzun?... Ya natsu baya Sa kuka ba, ko ya hau kyarma, wannan idan yayi d'ai daga cikin su sai kice na takura su, amma waccen natsuwa yayi, kuma taimaka maki da tarbiyyar su nakeyi, kin gamsu.?"

"E to sai nayi tunani."

Ya wani zabura, ke ban gane ba, me kike nufi?... Nunawa kike yi ma kin fi sonsu dani, wallhi ban yarda ba, gaya mani wa kika fi so, ni ko su.?"

Na yatsine fuska....

"Kai ma kasan ai albarkacin su ka samu shiga."

_Innalillahi wa'inn ilaihi raji'un,_ a she ni aikin banza kawai nike yi.?"

"K'warai kuwa".

"To bari inzo inyi damben samo matar dake sona..."

"Sonka?".

"K'warai kuwa".

Ya mik'e ya fara kaiwa da komowa, wacce zan dinga sunbatar ta, a labban ta, na shafi labbana, wacce zan dinga rungumeta a jikina."

Nayi sauri na mike tsaye na nufi inda yake kaiwa da komowa....

"Yarinya kyakkyawa, wacce zata dinga yi mani wanka, ta bani abinci inci in k'oshi, Innalillah har na kallo irin yanda zan kasance da ita."

"Yaya bana son irin wannan wasan."

Ya juyo da sauri, "Wasa tabd'ijam a wajen ki ko, ni nan babban al'amari ne wajena, nida ba a so, ba dole in shiga duniya neman mai sona ba, tazo in mik'a mata kaina gaba d'aya.

Ku kuma mu bar maku gidan keda 'ya'yan Ki."

"Yaya kaga ka daina, kai baka san wasa ba?"

"Ban San wasan rashin so ba".

"Haba Yaya na, taya ma za'ayi ince bana sonka?"

"Ban amince ba, sai na gani a k'asa".

"To me zanyi maka ka gani?"

"Oho, nidae ba abinda zai hanani k'ara aure."

"Meye haka?"

"Rabab aure shine in kawo ki gidana, mu zauna tare in dinga sunbatar ta ako da yaushe, yanzu kin gane aure ko?"

Na harareshi, nayi tafiyata har had'e k'afa nakeyi, wai harda ce mani inbi a hankali, ko sauraran shi banyi ba.

Ina shiga d'aki, na d'auki wayata na kira Abba, ina cikin cewa "Abba ina kwana"

Ya shigo ya fige wayar daga hannuna ya kashe, kamin yayi magana ankira wayata.

Yaya ya d'aga, na dinga binshi ya bani ya k'iya.

"Abba ina kwana "

"A'a lafiya kalau, wai mafarkin ka tayi shine tace bari ta kira ka, nasan hankalin ta shine na karbi wayar, gudun kada ta tayar maka da hankali."

"Abba... "

Yayi gaba "To zuwa anjima inta dawo daidai zan kiraka ku gaisa......... To Abba a gaida su Umma...... e, sun tafi makaranta....... To sa ji."

Ya kashe waya, ya janyo ni muka fad'a gado.

"Ke tsaya, tsaya mana."

Ni kuwa inata fizge fizge na.


"Kin san Allah in baki tsaya ba, yanzun zanyi tafiyata baki kara ganina sai nayi wata uku."

"Sai me?........ Ai dama ba sona kake yi ba."

'Tabd'i!.. Kece dai ba kya sona.............
[5/12, 4:08 PM] ✨Precious girl✨: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*NIDA ZUCIYATA*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ

*๐Ÿ’œA heart touching story*๐Ÿ’œ

*IWA*
_(Onward together_)

*Written by*
*Precious girl*✍

_In the name of Allah the beneficent the most merciful_

*___________________*
*DUNIYA MAKARANTA*

_Duk yanda kayi sai wani ya zageka, Manta da mutane kayi komai yanda yaka mata_

_Duk abinda zakayi, kayi shi da zuciya d'aya_

_Idan Allah yabaka lafiya, ya baka komai_

_Yafewa wanda ya cuceka ni'imah ce, tuna abin bakin ciki da damuwa, wahala ce, manta alkhaeri burul cine_

_Kafin ka roki Allah abunda bakada shi, ka fara gode masa akan abinda kake dashi, domin shine ya baka_

_Yaaaa, Allah ka dauwa mar da hasken imani cikin zuciyar mu..._๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป
*___________________*


*Page 49n50*

"Waya fad'a maka bana sonka?"

"Rantse da Allah in kina sona?"

"Wallahi ina sonka, kaine baka sona, kawai iyaye ne suka Sa ka aure ni."

"Waya fad'a maki?"

"Rantse da Allah kana sona".

"Na rantse da sarkin daya busa raina ina matuk'ar son matata Rabab fiye da rayuwata, ita ce bata sona".

"in ji wa?".

"Ba wani saboda yara kike zaune dani".

"Wallahi ba haka bane, farko saboda yara da tausayinka, amma daga baya naji sonka ya kamani, shine mafarin da nace maka zan koma gida, a raba auren da aka ce an d'aura".

"Rantse da Allah".

Na sunkuyar da kaina ina murmushin kunya....

"Na rantse da Allah ina son mijina altab, da ban san shi bazan yadda inta suma saboda shi ba, kuma inki tafiya gida".๐Ÿ˜

Ya d'ago kaina nayi saurin fad'awa k'irjin shi na b'oye fuskata ina jin shi ya sunbaci gashin kaina....

"Na sani Rabab"......ya fad'a cikin murya Mai sanyin gaske.

Ni kaina zuciyata ta gamsu da muna son junan mu ba don kowa ba.

Ina yi maki godiya da hakan, ban kuma k'ara yadda ba sai yau, nagode Allah ya rabaki da cikin nan lafiya, Rabab Ki sani Allah wallahi duk maganar da zan fad'a kilan ta sosa miki zuciya, amma kiyi hakuri sai na fad'eta zanji dadi a zuciyata....

"Wallahi son da nake maki yafi na 'yar'uwar ki sau dubu, kar kiji haushina, wallahi ni kaina na tsinci kaina da jin haka har cikin raina da jinina, na sani naso Ikram sosai, amma wanda nike ji a yanzu yafi duk wani tunaninki, ji nake da ke na rasa sai na kashe kaina".

Nayi saurin d'agowa nasa hannuna na rufe bakin Sa, ina girgiza kai....

"Ka daina kada kayi sab'o, Allah yana iya jarraba ka da hakan, yaga ya zakayi, ka sani kuma duk wanda ya kashe kansa ya zama kafiri.

Ni kuwa ba zan taba son haka ba, saboda zaka yimana asarar ka a lahira nida 'yar'uwa ta, saboda kasan in sha Allahu kaine
mijinmu a aljanna, idan ka mutu kafiri kaga haka zamu zauna ba muda kowa.

"Na daina k'anwata, zan raki Allah gafara da gaggawa, kema ki taya ni, tare da tayani addu'ar Allah ya kawo amarya ta lafiya".

"Allah ka daina ko in saka make ihuuuuuuu".

"Kaiiiiiiiiiiiii...... Da naji haushi, ai yin ihun ki tamkar nayi asarar rai ne".

Na daki k'irjin shi nayi dariya, na koma na kwanta, ya wani zabura.

"Wayyo kina danne cikinki, kibi a hankali".


Hahhhhhhha.... "Da cikin dani wa kafi so?"

"Innar cikin, ayimin afuwa".

Na d'ago na ciji labb'ansa, ya sa k'ara tare da k'ara manna ni a jikin sa.

"Wai in tambaye ki?"

Na d'aga kaina daga saman k'irjin shi.

"Don Allah mi yasa kika tsaneni a baya, Rabab bana mantawa har ranar da ikram zata haihu haushina kike ji, me yasa?"

Don Allah ina son ki fad'a mani gaskiya.

"Saboda abinda kake yi mata a lokacin d'aukar shi nake zalunci".

"Kamar me?"

"Kawai babba da kai sai ka haye mata cinyoyi, kuma da akwai ranar da na tab'a iskeku d'akin ta, nayi sallama takai sau hud'u, baku amsa ba, can sai naji sautin kuka, nayi saurin shiga d'akin, sai na iske ku kuna sunnah, amma a sai na d'auke shi fyad'e wannan yasa na k'ara tsanar ka da yawa, har a lokacin ji nake da za'a bani izini nice ajalinka saboda NIDA ZUCIYATA Mun sha ayyana in kashe ka, amma da yake wani lokaci k'awar tawa tafini hankali, sai ta hanani.

Kasan me take cemin?....... Yaya Aunty zata yi da yayanka, Allah ban tab'a tunanin tsanar da Nake maka zata zama sooooo".

"Yaushe kikaji kin fara sona?"

"A ranar da muka tab'a kwana tare, ranar dana sameka bakada lafiya da dare, kana ciwon ciki, wanda da kyar na samu kayi bacci ,a rashin sa'a saman gado na hau na kwantar da kai akan jikina har ka samu kayi bacci, nan take naji zuciyata tana wani irin abu, na k'ura maka idanuwa, sai naji wani sabon al'amari ya shiga zuciyata, shine gari na waye wa nace maka gida zan tafi.

Amma ka san Allah duk a baya ban tab'a tunanin komai ba, ko zargin komai, kuma Allah ban san cewa haka aure yake ba, nidai tabbas na san ana haihuwa, amma a nawa haukan ban ma tab'a tsayawa tunanin ya ake ana samun cikin haihuwar ba, kai nifa duk abinda ya shafi maganar aure ko a zuciyata bana tunano shi saboda tsananin na tsani aure, tsana ta gaskiya ko kalmar so naji an fadi sai naji kamar in mutuuuu".

"Yanzu fah?"

"Kaga Yaya ka daina".

"Gaskiya nayi mamakin ranar da aka kawo ki, meye sirrinnnnnnnn? "๐Ÿ˜


Hahhhhhha..... "A Abuja aka fahimtar dani komai, amma Allah ko lokacin naji ina sonka, ban taba sanin yanda ake aure ba, ni a tunanina yanda muke zaune shine kawai auran".


Yayi 'yar dariya da har saida hasken hak'oran sa ya bayyana..... " Hakan dana tabbatar wa zuciyata yasa ni aikata miki wannan, amma Allah ba don mugunta ba, don nasan idan magana ta fito ba wani abu daya tan's shiga tsakanina dake, har maganar taje gurin su Abba, cewa za'ayi inyi hakuri dake, ni kuma bazan tab'a iya hakura dake ba, shi yasa na daure na cije na aikata maki hakan, saboda haka shi zame mani alkhaeri a rayuwata, gashi kuma".

Na ciji gefen tsokar hannun shi, ya d'au k'ara ya matse ni gammm.


"Ni yanzu d'aya ke tayar mani da hankali, shine ranar da zaki haihu, komai nake idan na tuna da ranar hankalina mugun tashi yake".


"Ka daina tayar da hankalin ka, insha Allah sai nayi 'Ya'ya da yawa dakai, irin na Aunty, ita ma aunty na gaya maka k'addarar dole ce, sai nayi zaman aure da kai ne yaja mata mutuwa.


Wai yanzun na mutu, Yaya zakayi, yanzun fa sai ka samu wata kuyi zaman ku ko?"

Ya d'ago ni ya tashi ya zaune, tare da b'ata fuska.......

"Bana son irin wannan maganar, raina........

"Sorry na daina har abada".

Na fad'a tare da kamo kuma tunshi na yi kissing d'in su.

Yayi murmushi yaja hancina....

"Dama 'yan karin magana sun ce " _d'an koyo yafi gwani..._

Na kad'a idanuwana tare da maganar nan ta nifa gwana ce..

Nace " _Kad'an kenan, sai ma nan gaba zaka ga aiki da sai........._
_Kash ruwan ๐Ÿ–Š sun k'are..._๐Ÿ˜๐Ÿ˜

_Thanks so very much for the love and support, sai kun jini sooner or later..._๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

Post a Comment

Previous Post Next Post