SA MAZA GUDU part 2 (Hausa novel)

SA MAZA GUDU
Littafi na biyu(2)
Complete book 2
Typing Suleiman zidane kd.
Whatsapp 09064179602
................
A tare suka waigo baya suka duba,sai suka ashe
Lasurat ce mahaifiyar Malika.Ta tunkaro su
fuskarta cike da alamun damuwa.Koda ganinta sai
sarki ya mike tsaye ya taryeta yana mai rike
hannayenta a lokacin da ta kurawa hannun
Malika idanu.Sarki yace kwantar da hankali yake
Ummul Malika,kiyi sani cewa raunin da Malika taji
Karami ne kuma da wuri zata warke.Koda jin
wannan batu,sai murmushi ya kubucewa Lasurat
tayi doguwar ajiyar numfashi tace,to nagode da
abinda ya tsaya iya haka amma yaya akayi ta
sami wannan raunin alhalin nasan cewa duk inda
zata je kana bata tsaro mai kyau na dakaru?Sarki
Sharkuf ya numfasa yace,ni kaina nayi mamaki
yadda al'amarin ya faru,amma hakan bazata sake
faruwa ba.Yanzu ki tafi da ita izuwa turakarki ki
lallabata ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali
domin akwai alamun cewa tana cikin damuwa.
Batare da wata gardama ba Lasurat ta kama
hannun Gimbiya Malika tajata suka nausa izuwa
can cikin gidan sarautar.Shi kuwa Sarki Sharkuf sai
ya bita da kallo cikin alamun tsananin damuwa
gami da tunani mai zurfi.Na take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa saboda
tausayin da ya kama shi.Ba komai ne ya sanya
masa wannan tausayi ba face a binciken da yayi a
hallarar tsafinsa ya gano cewa bayan mutuwarsa
sai wannan 'ya da uwa sun rabu sakamakon wata
kaddara wacce basu isa su guje mata ba.Tunda
farkon Yammaci Gimbiya Malika ta caba ado tayi
shirin tafiya izuwa wannan Gida na Yarima
Lahaman.Bayan ta hama shiri tsaf,sai hankalinta
ya DUGUNZUMA bisa dalilai biyu,dalili na farko
shine bata san yaya taza sulale ta fice daga gidan
sarautar ba tare da wani ya ganta ba.Dalili na
biyu kuma bata san ko nawa Yarima Lahaman zai
siyar mata da wannan bawan nasa ba Wanda taji
ta kamu da tsananin sonsa farat daya.Duk da
tasan cewa komai tsadar bawan zata iya
sayensa,amma tayaya zata iya fitar da kudade
masu yawa daga gidan sarautar batare da sarki
ya gane dukkan shirinta ba?Idan tace kogon ta na
dukiya zataje ta debo kudin tafiyar mai tsawon
gaske ce,ba zai yiyu ba.Bisa wannan dalili ne yasa
Gimbiya Malika ta kama zarya a cikin babban falo
na turakarta ta kasa zaune ko tsaye.Kuma
Hankalinta ya DUGUNZUMA,taji kamar ta fashe
da kuka saboda bata da wani buri da kuma 'doki
wanda yafi taje ta gana da wancan bakon bawa
ko don ma ta sake ganin fuskarsa,Zuciyarta ta
huta da tsananin begensa da tunaninsa.Malika na
cikin wannan hali ne Shugabar kuyanginta wata
mace yar kimanin shekara arba'in da daya mai
suna Lasmira ta shigo cikin falon tare da wadansu
kuyanci guda uku,domin su gabatar da irin
aiyukan da suka sabayi kullum.Koda Lasmira taga
gimbiya a tsaye tana kaii kawo cikin alamun
damuwa,sai ta sallami wadannan kuyangi guda
uku dake tare da ita,suka juya da baya suka fice
daga cikin falon.Lasmira ta karasa gaban Malika ta
dubeta tace,Ya shugabata menene ya dameki
haka harzaki kasa zama ko tsayuwa?Koda jin
wannan tambayar,sai Malika ta koma kan kujera
ta zauna tayi shiru kamar baza tace komai
ba,tana mai kurawa Lasmira idanu.Daga can sai
tayi gyaran murya ta dubi Lasmira cikin nutsuwa
tace,yake Lasmira kiyi sani cewa na yarda dake
kuma nasan zaki iya rufe sirrina tunda tun ina
yarinya karama kike aiki a karkashin
Mahaifiya,kuma ban taba jinta tayi korafi akankin
yi mata wani laifi ba,bisa wannan dalili yanzu zan
sanar dake abinda ke damuna akan amana kuma
ina son ki bani shawarar abinda zanyi na sami
mafita.Nan take Gimbiya Malika ta zaiyanawa
Lasmira duk bukatunta.Koda jin wannan bayanin
nata,saiLasmirata kyalkyale ta dariya.Al'amarin
daya bawa Malika haushi da mamaki kenan
tace,mene kuma abin dariya a cikin wannan
Al'amarin?Lasmira tace,ai gani nayi ga magani a
gonar yaro amma bai sanshi ba,ai warware
wannan matsala taki abu nemai sauki tamkar cire
silin gashi daga cikin tandun mai.Abinda nake so
dake kawai shine kibi duk irin umarnin dana
baki,in kikayi haka dake da duk adadin kudin da
kike bukata zaku isa kofar gidan Yarima na can
bayan gari a asirrance kuma zaki dawo a asirrance
batare da kowa ya sani ba.Ko jin wannan batu,sai
farincik ya lullube Malika ta dubi Lasmira cikin
zumudi tace,Fadi duk irin abida kike so
nayi.Lasmira tayi murmushi tace,yanzu dai da
farko ina son ki bani Dinare dubu goma kacal
wanda zanje na aiwatar da wadansu ayyuka a
cikin gidan nan dasu,zan dawo nan da kafin cikar
rabin sa"a.Batare da gardamar komai ba kuwa sai
Malika ta shiga cikin kuryar turakarta ta debo
dinare dubu goma a cikin jakar kudi ta mikawa
Lasmira.Lasmira na karbar wannan kudi sai ta
boyesu acikin rigarta sannan ta juya ta fice daga
cikin turarkar.Lasmira bata zame ko ina ba sai can
kofar dakin shugaban dakarun dake tsaron gidan
sarautar,wani barden jarumi wanda ake kira da
suna Mahutur bin Kauzif.Da isarta sai ta
kwankwasa kofar dakin sau biyu kacal,faruwar
hakan ke da wuya sai Muhutur yayi magana daga
ciki yace,to Lasmira shugabar yan cuwacuwar
gidan nan yau kuma dame aka zo mini don nasan
cewa unguwa bata jewar banza.Lasmira tace ai sai
ka fito waje kaji abinda nazo dashi.Muhutur yace
ai zaifi kyau ki shigo daga ciki komai zaifi
sirri.Idan kuma matarka tazo ta ganmu fa sai ta
zata amanarta zanci kuma ka sani cewa kawata ce
ko?Haka ne to bari na kimtsa gani nan fitowa.Jin
kadan saiga Muhutur ya fito yana goge bakinsa ga
dukkan alamun abinci ya gama ci.Maimakon
Lasmira ta bude baki tace wani abu,sai ta dauko
kudin Dinare dubu uku ta mika masa.Cikin
kaduwa da Mamaki Muhutur ya karbi kudin yana
mai jinjina su akan tafin hannunsa,sannan yayi
waige waige da dube dube yai sauri ya Soka kudin a
cikin aljihun wandonsa ya dubeta
yace,wannan kuma fa na menene?shin wani abu
za'a siyowa Gimbiya a boye?Lasmira tace a'a itace
da kanta take son ta fita daga cikin gidan sarautar
nan tare da dukiya mai yawa saboda taje ta siyo
wani bawa a can gidan Yarima dake bayan
gari,kuma komai ana sin ayi shine a asirrance ba
tare da sarki ya sani ba.
Koda Lasmira tazo nan a zancenta,sai hankalin
Badakare Muhutur ya DUGUNZUMA ainun ya rasa
abinda ke masa dadi domin yasan cewa hadarin
dake cikin wannan aikiyana da yawa saboda ko
yaya aka sami akasi ya rasa aikinsa kenan .Don
haka sai ya murtuke fuskarsa kuma ya murza
gashin bakinsa yace,kai ungo kudinki bazan yi
wannan aiki ba,hadarin dake cikinsa yafi abinda
kika bani.Koda jin haka,sai Lasmira ta sake saka
hannunta cikin aljihunta ta dauko wani damin
kudin Dinare dubu uku ta wurga masa tace,ga
wadansu dinare dubu ukun kaga ke nan inka
hada dana farko sun zama dinare dubu shida
daidai albashinka na shekara biyu kenan,shin ka
amince yanzu zakayi wannan aiki?Koda jin
wannan tambaya,sai jikin Muhutur ya kama
kyarma ya rasa hukuncin da zai yankewa
kansa,saida yayi duru duru yayi gaba yayi baya
sannan ya juyo ya fuskanci Lasmira yace,to ina
kudin dakarun dake aiki a yau?kinsan cewa suma
sai na raba musu wani abun sannan zasu ki duba
duk abinda za'a wuce dashi.Koda jin haka sai
Lasmira ta zura hannu cikin aljihun rigarta ta
dauko wani kullin kudi na dinare dubu ta mikawa
Muhutur tace,wannan dinare dubu ne nasan ya
isa ka raba musu,wane lokaci za'a fito da Gimbiya
da dukiyarta?Muhutur yayi shiru yana tunani
sannan yace,ai yau talata ce kuma duk ranar
talata da yammaci ne sakalaiya Sarki ke kwanciya
domin ya huta ba zai sake fitowa waje ba sai
gobe da safe don haka a daidai wannan lokaci
za'a fito da Gimbiya.Lasmira tayi murmushin farin
ciki ta juya da baya da gudu taje ta sanar da
Gimbiya Malika duk abinda ya faru tsakaninta da
shugaban dakaru Muhutur.Sannan sai ta dauko
wani shudin magani a cikin wata yar karamar
kwalba ta mikawa Malika tace,ungo wannan kisha
makurwa biyu kacal,batare da gardamar komai
ba ko tsoron wani abu sai kawai Malika ta karbi
ruwan maganin ta cire murfin kwalbar tasa a
bakinta tasha makurwa biyun kamar yadda aka
umarce ta.Bayan kamar dakika ashirin da faruwar
hakan sai Malika ta fara jin jiri,ta kama tangadi
daga tsaya sannan ta tafi luu.. zata fadi,amma sai
Lasmira ta tafa hannunta sau uku,saiga wadansu
hadiman gidan su Gimbiya Malikan guda uku karti
sun shigo,dayansu dauke da wata doguwar
akwatin katako.Da zuwansu sai suka ajiye akwatin
suka bude shi saiga matattun beraye,kyankyasai
da sauran kananan kwari masu addabar mutane
a gidan.Kawai sai suka daga abinda ke dauke da
wadannan kwari daga cikin akwatin sai ga katon
fiki a kasan akwatin aka saka gimbiya Malika a ciki
sannan suka dauko katakon dake dauke da
matattun kwarin suka dora a saman Gimbiya
Malika ya zauna darama.Komai kallon
kurilla,mutum bai isa ya iya ganewa cewa akwai
wani abu a kasan akwatin,saidai ayi tunanin cewa
akwatin cike take da wadannan kwari babu komai
a kasanta.Bayan an rufe Malika a cikin wannan
akwati sai kuma wannan hadimai uku suka shiga
can cikin kuryar turakar gimbiya suka rinka fito sa
irin akwatunan har guda arba'in,ashe kowacce a
kasanta lu'u lu'u aka zuba dunkim a samanta
kuma aka zuba matattun kwarin.Akwatuna guda
arba'in da daya aka loda su a kan keken shanu
aka tunkari kofar fita daga cikin gidan
sarautar.Saida aka wuce ta cikin kofofi tara,kuma
duk kofar da akazo ko tsayar da keken shanun
ba'ayi,da an hango su daga nesa sai a bude
musu kofa tun kafin ma su iso.Saida kawai su
wuce.Haka dai direban keken shanun ya cigaba
da wucewa har ya iso kofar karshe,har masu
gadin sun janyo kofar sun bude masa zai fita
kenan,sai sukaji an daka mus tsawa,a firgice
direban keken shanun tare da dukkan masu
gadin kofar kimanin su dari suka waiga suka duba
inda sautun tsawar ya fito saboda sun dauki
murya.Ba muryar wani bace face ta sarki Sharkuf
yana tahowa daga cikin gidan sarautar bangaren
da turakarsa take.Sarki Sharkuf ya kara so garesu
fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri,ya dubi
direban keken shanun ya sake daka masa tsawa a
karo na biyu yace,ya kai Zarhus yau kuma wace
irin sharace za'a fitar da ita da wannan yammaci
sakaliya haka?Koda jin wannan tambaya,sai jikin
Zarhus ya kama tsuma ya sauko daga kan keken
shanun ya zube a kasa gaba Sarki tamkar zai
masa sujjada,sannan ya bude baki cikin rawar
murya yace,Ya shugabana sharace ta matattun
kwari kuma tayi yawa ne shi yasa kafin mu gama
kwasheta lokacin ya kure mana.Koda jin wannan
batu,sai Sarki Sharkuf ya sake bata rai yace,ban
yarda ba a bude akwatunan gaba dayansu na
gani.Dajin haka sai dakaru suka rugo izuwa kan
keken shanun suka kama bude akwatunan sarki
Sharkuf yazo kan akwatin farko wacce a
karkashinta ne Gimbiya Malika ke kwance tana
fama sharar barci kamar gawa.Koda sarki Sharkuf
yaga matattun beraye da kunamai da kyankyasai
har sun fara doyi sai yayi sauri ya toshe
hancinsa.Har ya yunkura zai duna cikin ta biyu sai
ya dawo da baya ya daga kwagirinsa da nufin ya
lumata cikin akwatin farko domin ya jiyo karshen
zurfinta,kawai sai yaji an kwala masa kira,yana
waigawa baya yaga ashe shugaban tsaro na gidan
ne ya tawo da gudu yana sassarfa da tuntube
kamar wanda zai fadi yana cewa,ka gafarceni ya
shugabana nayi kusjure da baka riskeni ba anan
bakin kofa.Koda jin wannan batu,sai sarki Sharkuf
ya basa luma kwagirinsa a cikin akwatin ya juyo
ya fuskanci Badakare Muhutur yana mai kyalkyala
dariya yace haba yakai Muhuru ai bazaka tabayin
laifi ba a wajena saboda yau shekara arba'in da
biyar kenan kana aikinka na tabbatar da tsaro,ba'a
taba kama da laifi ba,wata almundahana ko rashin
gaskiya ba.Shin ka caje wadannan akwatunan guda
arba'in da daya na shara ka tabbatar cewa sharace
zalla a ciki ba'a boye wani abu ba?Muhutur ya
gyada kai yace,na caje su gaba daya ya
shugabana,babu wani abu a ciki sabanin wanda ka
gani.Koda jin haka sai Sarki Sharkuf ya saki
ransa,hankalinsa ya kwanta,ya kyalkyale da dariya
sannan ya dafa kafadar Muhutur yace,na yarda dakai
dari bisa dari nasan cewa ba zaka taba cin amana
taba,kuma bazaka taba yarda ayi wani abu ba wanda
zai cutar dani koya cutar da wani nawa.Koda gama
fadin haka sai Sarki Sharkuf ya dubi Zarhus yace ko
kayan laifi ka dauko a yaudai ka sha.Zarhus ya
risina yayi godiya sannan ya sake hawa kan keken
shanun ya saki linzami ya fice daga cikin gidan
sarautar.Sarki Sharkuf ya bishi da kallo kawai a
lokacin da Muhutur yaji idanunsa sun ciko da kwalla
kamar ya fashe da kuka,saboda yasan cewa tabbas
yasha cin amanar sarki ana shigowa gidan da
abubuwan da basu dace ba ko kuma a fitar da
wasu.
Tafiyar rabin sa'a kacal direba Zarhus yayi ya iso
kofar gidan yarima Lahaman dake bayan gari.Da
isowarsa sai shugaban masu gadin gidan ya
dubeshi ya daka masa tsawa yace,kai kuma wane
irin wawa ne da zaka kawo shara nan gidan?Waye
ya baka umarnin yin hakan?To kayi sauri ka bace
daga nan tun kafin Yarima ya fito ya ganka yasa
takobi ya sareka.Maimakon Zarhus yace wani abu
sai kawai ya sauko daga kan keken shanun ya bude
wannan akwatin ta farko.Yana budewa saiga Gimbiya
Malika kwance a ciki tamkar gawa bayan ya dauke
matattun kwarin dake samanta.Cikin kaduwa da
mutukar firgici masu gadin gidan sukayi kamar su
ruga izuwa cikin gidan amma sai suka fasa
sakamakon ganin Malika zaune a cikin akwatin
tamkar gawa ta faso kabari.Ashe dama can kuyanga
Lasmira ta auna iya tsawon lokacin da Malika zatayi
barcin kuma ta farka adaidai lokacin da Zarhus ya
iso kofar gidan Yarima Lahaman.Shiyasa tace da ita
tasha wannan maganin barcin makurwa biyu.Koda
Malika ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin keken
shanu,ga akwatuna arba'in a bayanta kuma gata a
kofar gidan Yarima Lahaman,sai farin ciki ya
lullubeta ta sako kasa daga kan keken shanun
sannan ta dubi shugaban masu gadin ta daka masa
tsawa tace zakaje ka gayawa ubangidan naka cewa
gani na iso ko aa?Kodajin haka sai badakaren ya
juya da sauri ya fada cikin gidan.
Acan cikin gidan kuwa sarki Hilairu tare da ragowar
jama'arsa bayi mutum dari na zaune sunyi jugum
jugum suna tunanin halin da suka tsinci kansu ta
rayuwar kunci,damuwa dakuma wahala.A yau dinma
tun safe da aka basu abinci ba'a sake basu
ba.Gashi har rana ta fadi magariba ta doso
kal.Dukkanninsu jikinsu yayi sanyi lagwab tamkar
jikakkun tsumokara musamman matan cikinsu
wadanda dole ne mutum ya kamu da tausayinsu
Idan ya kallesu saboda su masu rauni ne basu da
juriya irinta maza.
Kwatsam sai ga....

Suleiman zidane kd .

Kwatsam sai ga Yarima Lahaman ya shigo cikin
dakin dakarunsa na take masa baya fuskarsa a
murtuke babu alamar annuri.Kai tsaye Lahaman
ya durfafi inda sarki Hilairu ke zaune ya dube shi
yace,ya kai wannan sarki naga alama cewa kai
mutum ne mai sa'a domin gashi ina shirin na
siyar dakai gobe ga manyan attajiran da zan sami
babbar riba,amma sai gashi 'yar uwata tazo
yanzu domin ta siyeka.To ka sani cewa karkon
kifi
zakayi domin babu wani abu da ya taba shigowa
hannuna kuma ya kubuta.Nayi maka alkawarin ko
ka subuce mini yanzu nan,ba da dadewa ba saika
dawo hannuna,kuma saina siyar dakai ga inda
za'a tafi daku izuwa wani bangaren na duniya
mai nisan gaske inda ko duriyarka ba za'a sake
jiba.Koda gama fadin hakan,sai Yarima Lahaman
ya fice daga cikin dakin tare da dakarunsa masu
take masa baya suka nufi can wajen
gidan.Gimbiya Malika na tsaye kusa da keken
shanunta mai dauke da akwatunan kudi saiga
yarima Lahaman ya fito daga cikin gidan.Koda
yaga Malika a gaban keken shanu mai daukar
akwatunan sharar gidan sarauta saiya bushe da
dariya yace,yanzu yar sarki ce guda a cikin kekn
daukan shara,to yanzu ina kudin da zaki siyi
bawan?Koda jin wannan tambaya,sai Malika ta
turbune fuskarta tace,a ina ka taba ganin anyi
cinikin kifi a ruwa,muje ka nuna min abinda nazo
siya na ganshi a raye cikin koshin lafiya sannan
muyi cinikin ba biya.Koda jin haka,sai Yarima
Lahaman yayi murmushi yace,Tabbas kina da
wayo da dabara ki biyo ni a baya muje kiga
muradinki.Yana gama fadin hakan sai ya juya ya
shige cikin gidan.Kawai sai Malika ta dubi
dakarun
dake kofar gidan tace,ba baku ajiyar keken
shanuna da direbansa,idan na fito na iske wani
abu ya taba lafiyarsu abaka cin rayuwarku.Tana
gama fadin hakan sai tabi bayan Yarima
Lahaman
da sauri har suka iso dakin dasu Sarki Hilairu ke
ciki.Da zuwansu aka bude musu kofa suna shiga
sai Sarki Hilairu da Gimbiya suka hada Idanu take
yaji zuciyarsa ta buga da karfi karo na biyu na
haduwarsu.Ita kuwa Malika ji tayi gaba dayan
tsigar jikinta ta tashi kuma sai kwarjinin Hilairu
da
tsananin kyawun fuskarsa suka dimantata tayi
sauri ta dauke mazansu da matansu.Take taji ta
kamu da tsananin tausayinsu don haka sai ta
dubi yarima Lahaman tace ciniki ya sauya salo
yanzu ba mutum saya kadai nake so ka siyar min
ba,gaba dayan bayin dake cikin dakinnan nake
bukata.Koda jin wannan batu,sai yarima
Lahaman
ya bushe da dariyar keta yace,yaya ke da bakizo
da kudin siyan mutum daya ba ma amma kike
tunanin siyan mutum dari?Malika tace,ai sai ka
bari mu gama cinikin tukunna idan kaga na kasa
biyanka kudinka shine kake da bakin
magana.Lahaman yayi gyaran Murya sannan
yace,shidai wannan saurayi ma'abocin kyawu da
kike son ki fansa sai kin biyani kudi dinare dubu
dari biyar.Su kuwa ragowar yan'uwan nasa ko
wane dayansu sai kin biya dinare dubu hamsin
sannan zaki mallake su.Koda jin wannan batu,sai
Gimbiya Malika ta dubu Yarima Lahaman cikin
alamaun fishi da bakin ciki tace,haba yakai
yarima ai ko ranar kasuwar garin nan ba'a taba
siyar da bawan da darajarsa takai dinari dubu
biyar ba amma kai yanzu gashi kace na siyi
kowane daya akan farashin dubu hamsin.Shidai
wanacan saurayin ma'abocin kyau da kwarjini na
yarda na siye shi a farashin da ka fada,domin
darajarsa ma tafi haka,amma ina neman sassauci
akan ragowar bayin.Koda jin haka sai Yarima
Lahaman ya turbune fuskarsa yace,ai ba neman
kai nake yi ba dasu,idan ba zaki iya siyansu ba a
wannan farashin saidai ki hakura gaba
daya.kuma
inda kina bukatarsu sai ki biya kudinsu yanzu
take
sannan ki kada ki tafi dasu.Malika tayi murmushi
tace,kudi ba matsalata bane yadda zan kashe su
shine matsalata.muje wajen keken shanun na
biyaka kudinka duka,amma lallai kasa a kwance
wadan nan bayi daga cikin sarkoki su biyo mu
izuwa waye.Batare da wata gardamar komai
ba,yarima Lahaman yasa dakarunsa suka kwance
bayin daga cikin sarkoko aka tusa keyarsu izuwa
wajen gidan Sarki Hilairu ne akan gaba ana
ingiza
keyarsa ana kai masa bugu.Da fitowarsu kofar
gidan sai aka jera bayin akan layi sahi sahu
sannan Lahaman ya tsaya a gabansu dakarunsa
kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika
ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin
wannan tambaya sai ya sauko daga keken
shanun
ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama
mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u
birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa
Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata
da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu
kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi
arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka
cika
da tsananin mamaki yadda akayi ta
mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman
tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin
daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar
mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi
wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga
adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare
dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun
biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a
cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna
wannan aiki sannan suka kammala amma duk da
haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da
aka umarce su kuma suka rage kudade da
yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya
karba yana ta farin ciki da walwala sannan an
saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai
Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta
sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da
lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum
guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a
rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar
dayake so yana walwala batare da sun
kareba.Koda Yarima Lahaman...


Zidane kd..


Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido yaga wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya
turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani cewa
babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk
irin tsananin son da yake mata saboda ya
kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin
'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunawa Yarima
Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A
zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi
wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na
sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin
baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a
harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai
tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu
na tara dukiya da baka da kaso daya cikin
gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya
a wannan zamani nice babbar dilar da babu
kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna cikin
shiri kwanan nan zan karbeta na zama na ni ke
sarrafata a duniya,ba don komai ba sai domin
nayi maganin manyan azzalumai irinku.Yanzu dai gani ni kadaice na zo babu wani badakare ko
guda daya daya rakoni don bani tsaro.Idan ka
gadama ka turo min gaba daya dakarun naka su
tare mini hanya kafin na isa cikin gari suce zasu
kwaci wannan dukiya da wadannan bayin dana
siya wajenka.Na rantse da gemun Mahaifinmu dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba.Idan kuma
kana ganin cewa kai ne da kanka zaka tareni to ina jiranka ai KAR TA SAN KAR ce kuma shege ka
fasa.Koda Malika tazo nan a jawabinta sai ta dubi
su sarki Hilairu tace,wuce gaba mu tafi izuwa inda zan ajiye ku.Cikin tsananin farin ciki su sarki Hilairu suka wuce gaba sannan Malika ta hau kan keken shanu Zarhus ya tuka suka bi bayan su
Hilairu.Dama tunda Gimbiya Malika ta fara
bayaninta ga Yarima Lahaman sai jikinsa ya kama
tsuma,idanunsa suka kada sukayi jawur ya kamu
da tsananin bakin ciki kuma ya rinka ji kamar ya zare takobinsa yaje ya afka mata da yaki,amma
sai ya daure ya hakura sa'adda ta fadi kalma mai
zafi da muni a gareshi sai dakarunsa su yunkuro
zasu afka mata,amma sai ya dannesu,saboda
yasan cewa AJALIN su zasu gaiyata kuma shi
kansa bazai iya karesu ba da komai.Har Saida Malika tayi nisa da barin kofar wannan gidan nasa
har ya daina hangosu ita da dukan bayin data
siya a hannunsa,sannan ya takarkare ya kwarar
uban ihu mai tsananin ban tsoro sannan kuma ya
durkushe kasa bisa guiwowinsa ya fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki.Adaidai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tafka
walkiya da tsawo amma saboda tsananin bakin
ciki sai Yarima Lahaman yaki tashi ya shiga cikin
wannan gida nasa.Aikuwa take aka tsuge da
ruwan sama kamar da bakin kwarya,koda ganin
yadda ruwa yake dukan Yarima Lahaman kuma gashi ruwa ne mai karfin gaske dauke da iska,sai
daya daga cikin wannan dakarun nasa ya matsa
daf dashi yace,ya shugabana zaifi kyau ka tashi
daga cikin ruwan nan domin zai iya cutar da lafiyar...Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa
tuni Yarima Lahaman ya shammaceshi cikin bakin ZAFIN NAMA ya zare takobinsa ya share masa makogwaro,kawai sai gani akayi jini yayi feshi
daga cikin wuyan badakaren sannan ya fadi
matacce.A sannanne Yarima Lahaman ya mike
tsaye ya goge jinin dake jikin takobinsa akan
gawar badakaren sannan ya mayar da takobin cikin kufe ya daga kansa sama yayi KURURUWA
mai razanarwa tamkar zaki yayi GUNJI a dawa.Nan take duk wani abu mai rai dake kusa
ya dimauce,hatta ragowar dakarunsa dake tsaye a
wajen da wanda ke cikin gidan saida suka firgice
suka rikirkice suna neman su cika wandonsu da iska,amma sabida tsoro sai suka kasa guduwa
izuwa ko ina.A sannanne Yarima Lahaman yayi
rantsuwa da darajar uwarsa yace,daga yau Malika
baza ta sake yi masa wulakanci ba,kuma komai
dadewa sai ya kasheta da hannayensa ya huce
takaicinta,koda samun nasarar yin hakan na nufin mutuwar duk wani abu mai rai dake cikin kasar
nan.Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya
shige izuwa cikin wannan gida nasa.
Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da suka yi
dan nisa ga barin gidan Yarima Lahaman tare
dasu sarki Hilairu itana bisa keken shanun su kuma suna tafiya a kasa bisa kafafunsu kuma taga
hadari ya gangamo an fara walkiya,sai ta bayar
da umarni aka rugu cikin wani kogon dutse domin
a fake.Ai kuwa suna gama shiga cikin kogon
dutsen nan ruwan saman ya tsuge,nan fa
kowannansu maza da mata ya sami wuri ya zauna,aikuwa aka fara ruwan saman mai dauke
da iska mai sanyi ya addabi kowa.Koda ganin
haka sai Malika tayi amfani da karfin sihirinta na
tsafi ta kunna wutar jin dumi har guda uku.Daya
sai gaba dayan matan suka kewayeta dayar kuma
sai mazan suka kewayeta,ya zamana cewa saura wutar guda daya babu kowa a gabanta,shi kansa Zarhus tuni ya zaro bargo a cikin keken shanunsa
ya kwanta ya lullube jikinsa gaba daya.Nan fa ya
rage saura Gimbiya Malika da sarki Hilairu a tsaye
a can gefe daban daban suna kallon juna,kuma
suna kallon wannan wuta guda daya data rage wacce babu kowa a gabanta,kamar hadin baki sai
duk su biyun suka taho izuwa gaban wutar a
lokaci guda suka zauna suna jin dumin kuma suna
fuskantar juna.Tsawon 'yan dakiku dayansu bece
uffan ba kawunansu na sunkuye suna kallon
kasa.Kawai sai suka dago kai a tare kuma kowannasu ya bude baki da nufin yace wani
abu,koda muryoyinsu suka sarke a lokaci guda sai
suka kyalkyale da dariya saboda mamakin yadda
al'amarin ya kasance haka.A sannane Gimbiya
Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murmushi mai
taushi tace,ya kawai wannan saurayi Ma'abocin kyau da kwarjini waye kai kuma yaya akayi ka
tsinci
kanka a cikin wannan rayuwa ta bauta?Kasani
cewa
a karon farko dana ganka jikina ya bani cewa ka
fito daga babban gida kuma asalinka baka kasance
bawa ba.Koda Malika tazo nan a zancenta sai taga
hawaye a zubowa sarki Hilairu,al'amarin daya
karya
zuciyar kenan taji ta kara kamuwa da tsananin
tausayinsa.Ta dubi Sarki Hilairu cike da tsananin tausayi tace,yakai wannan sarki me yasa kake
zubar
da hawayenka alhalin ka tsira daga hannun dan
uwana kuma kasan cewa bazan taba cutar dakai
ba,kayi sani cewar bana kubutar dakai bane don
cutarwa,na kubuto daku ne domin tsirar daku daga
cikin kangin da dan uwana zai saka ku a ciki.Koda
Sarki Hilairu yaji wannan gada Gimbiya Malika,saiya
girgiza kai ya saka hannu wansa ya share
hawayensa ya dubeta duba na tsanake sannan
yace,yake wannan gimbiya kiyi sani cewa ba ina kuka bane don shiga halin dana kasance a ciki
ba,kuma banajin shakkar komai daga gareki na
tabbata kin kasance mace mai tausayin na kasa
dake.Wannan kuka da kikaga inayi inayinsa ne
kawai don rasa matata danayi sannan kuma ina
mutukar tausaya miki dake da mahaifinki da kuma sauran al"ummar wannan birni gaba daya.Koda
dayazo nan adaidai zancensa sai Gimbiya Malika ta
dago kai a cikin kidima ta dubeshi domin batasan
wane irin tausayi ne Hilairu yake musu ba alhalin
sun kasance basu da wata lalura data
addabesu,babu fari bare wata cuta data kunno kai cikin kasarsu.Don haka cikin azama ta dubeshi
tace,yakai wannan sarki sanar dani dalilin dayasa
kake jin tausayinmu,meya faru haka da har ka
kasance cikin tausaya mana alhalin da
idanuwankan
kaga ni babu rashin ci da sha a cikin birninmu sannan babu wata rashin lafiya uwa uba kasarmu
tana dauke da mayakan da a kaf nahiyar nan ba a
isa a zo aga bayansu ba.Tana zuwa nan a zancenta
sai Hilairu ya tareta dacewa,ko kina da labarin SA MAZA GUDU?Gimbiya Malika tayi shiru tana tunani a cikin ranta ta girgiza kai alamar batada labarinsa.Sarki Hilairu yace,dakina da labarin SA
MAZA GUDU dana sanar dake dalilin dayasa nake tausaya muku,amma idan kin koma cikin gidan
sarauta ki tambayi mahaifinki wanene SA MAZA GUDU,in har ya sanar dake kadan daga cikin
labarinsa ni kuma zan sanar dake dalilin da yasa nake tausayinku nake jin kanku badon komai ba
sai don kyautatawa dakika yimin.Gimbiya Malika takara
zuba masa idanu tana mamakin maganganunsa
gareta tace,yakai wannan sarki ina bukatar ka sanar
dani ko kadan daga ciki kafin naje ga mahaifina na
tambaye shi wanene SA MAZA GUDU,inason kafara
sanar dani ko yaya ne sannan ka sanar dani dalilin
dayasa kake tausaya mana.Kodajin haka sai sarki
Hilairu ya daga kai yace zan sanar dake kadan daga
cikin alakarmu dashi,amma labarinsa sai idan kinje
kin tambayi mahaifinki ya karasa miki sani
akansa.Dajin haka sai takara gyara zama tana mai
sauraronsa shi kuma ya ciga da cewa.............
SA MAZA GUDU
Littafi na biyu(2)
Part D
Dajin haka sai ta kara gyara zama tana mai
sauraronsa shi kuma ya ci gaba da cewa:
SA MAZA GUDU guguwa ce wadda batada abin
tarewa a duk sa'ilin data nufo kasa ko
nahiya,bata tsawaita,sannan masiface babba a
cikin rayuwar duk wani mai rai dake doron
duniya,ba'a fatansa ba'a kuma marmarin
ganinsa.Duhu ne shi mai mamaye duk wani
haske,masiface shi mai tattare da dukkanin
masifa yake wannan Gimbiya,ki sani cewa
wannan runduna ta SA MAZA GUDU bata da kula kan duk abinda ta sako shi a gaba,tana da ta'adi
ga duk wanda ta fuskanta bata barinsa sai taga
ta bata cikin kasarsa da jini,tayi masa ado da naman sassan bil'adama.Ina son ki sani cewa
wannan sadauki da ake kira SA MAZA GUDU dan uwa ne a gareni wanda muka fito ciki daya,kuma
a duniya bashi da wanda yake so sama dani don
haka yabar ni akan mulkin kasar mu ya fita duniya.Zan cigaba da baki labarinsa a lokacin da
kika samu saninsa daga mahaifinki.Sannan kuma
ya cigaba da sanar da ita yadda Yarima Lahaman
ya kashe masa matarsa a daren farkon amarcinsu
bayan yayi mata fyade,wacce ta kasance tana
tsananin kama da ita.Da yadda Yarima Lahaman
tare da dakarunsa suka yita kashe mutane a
birninsa suka kwashe dukiyoyinsu suka kone
gidajensu kuma suka maishe dasu bayinsu.Koda
Sarki Hilairu ya gama baiwa Gimbiya Malika
wannan labari sai taji ta kamu da tsananin
tausayinsa dana jama'ar sa fiye da koyaushe
kuma taji sonsa ya karu ninki baninkin a cikin
ranta don haka bata san sa'adda hawaye ya zubo
mata ba,ta dubi Sarki Hilairu ta kwashe nata
labarin ta zaiyana masa har duk irin kiyayyar
dake tsakaninta da dan'uwanta Yarima
Lahaman,da irin GWAGWARMAYAR data sha a
rayuwa domin ta kare kanta daga sharrin Lahaman da kuma kokarin kawo rugujewar
dukkan mugun nufinsa a nahiyar gaba daya.Daga
karshe sai ta dube shi tace,yakai wannan sarki
mai daraja kayi sani cewa ban siyeka ba a
matsayin bawa na,na saye kune domin kubutar
daku daga sharrin dan uwana Yarima Lahaman
saboda nasan cewa sai ya tarwatsaku ya siyar
daku ga mutanen daza su rarrabaku izuwa sassan
duniya yanda har abada da yawanku bazasu sake
ganin juna ba.Nayi muku alkawari indai ina raye
kuma ina da koshin lafiya saina taimaka muku
kun fita daga wannan nahiyar lafiya kun koma
izuwa kasarku ta haihuwa kun sake gina birninku
kunci gana da rayuwarku kamar yadda kuka saba.Duk abinda kuke bukata na kudi zan taimaka
muku dashi,kuyi sani cewa yau saura kwana uku
kacal nayi shiri na bar kasar nan saboda haka
kuma saiku zauna cikin shiri domin tare zamu bar
kasar nan.Lokacin da Malika tazo nan a jawabinta
sai farin ciki ya lullube sarki Hilairu da dukkan
jama'arsa.Suka kama yi mata godiya da jinjina
suna shewa daga can sai sarki Hilairu ya dubeta
cikin alamun damuwa da fargaba yace,yake wannan yar Sarki mai adalci yanzu bakya tunanin
cewa wannan dan uwa naki bazai shirya tuggun
da zai raba mu dake ba ba,bare har kin sami
damar taimakonmu?Koda jin wannan tambaya sai
Gimbiya Malika tayi murmushi sannan tace,idan
har kaga wani tsautsayi ya sameku to tabbas
nima ya sameni,idan har kayi imani cewa ni mai
kaunace a gareku ba mai cutarwa ba to tabbas
zaku tsira da mutuncinku,rayuwarku daafiyarku.Abinda nake bukata daku kawai shine
kuyi duk irin umarnin dana baku,kada ku kuskura
kuyi wani abu daban bisa yin kanku face bisa izinina da umarnina.Koda Gimbiya Malika tazo
daidai nan a zancenta sai suka ji an dauke ruwan
saman dake ta tafkawa yayi dif tamkar ba ayiba
har wasu daga cikin jama'ar sarki Hilairu sun
yunkura zasu fita daga cikin kogon dutsen sai
Malika ta daka musu tsawa tace,ku koma ku
zauna ashe bana gaya muku cewa kada kuyi
komai ba sai bisa umarnina.Koda jin haka sai
kowa ya koma inda yake ya zauna suka shiga
taitayinsu,Malika ta mike tsaye tsam ta fito waje
daga cikin kogon dutsen,tana fitowa saita tsaya
cak ta kasa kunnuwanta sosai tana sauraran duk
wani sauti dake cikin dajin kuma ta dubi gabas da
yamma,kudu da arewa kawai sai taji a jikinta
cewar akwai sauyin yanayi a cikin dajin wanda
bata gamsu dashi ba,don haka sai kawai tayi nuni
da hannunta izuwa kofar wannan kogon dutsen
wanda su sarki Hilairu ke ciki.Nan take wata irin
yanar tsafi mai kauri ta lullube kofar yadda babu
wani abi da zai iya ratsawa ta cikinta.Faruwar
hakan ke da wuya kuwa sai taji takun sawaye da
yawa a saman kan duwatsu ana gudu alamar
cewa akwai mutane da yawa kewaye da wannan
kogon dutse,kwatsam saitaji hucin kibiya ta taho
da gudu zata soketa a kirji,cikin ZAFIN NAMA tasa
hannunta ta cafe kibiyar kuma ta cillata izuwa
saitin inda aka harbota kawai sai tajiyo ihun
kato,saiga wanda kibiyar ta caka ya sallamo daga
can saman dutsen dake gabanta ya fado kasa tim
a gabanta ya zama gawa alokacin da jini ke
kulbulowa daga cikin kirjinsa sakamon kibiyar
data cake masa da hannunta tayi masa KAIKAYI KOMA KAN MASHEKIYA.Faruwar hakan keda wuya
saiga dakarun sumame a cikin shigar bakaken tufafi kuma sun rufe fuskokinsu su da yawa suka
baiyana akan duwatsun a saman Malika kuma dukkaninsu sun dana kibiya akan bakansu sun
saitota.Ba tare da wata alama ta fargaba ba ko
tsoro sai Gimbiya Malika ta gyara tsayuwarta tana
kallonsu kawai.Nan take shugaban dakarun
sumamen ya daga hannunsa sama yama mai
bayar da umarnin a sakar mata harbi,aikuwa sai
gaba dayan dakarun sumamen suka harbowa
Malika kibiyoyin,nanfa suka ga abin Al'ajabi saboda duk kibiyar data durfafeta take take
ruburbushewa tazama gari.Koda ganin abinda ya
faru sai shugaban dakarun ya zare takobinsa take
sauran yaran nasa sukayi koyi dashi suka dako
tsalle kasa suna masu dira bisa kafafunsu suka rutsa ta da makamansu alhalin ko tsinke babu a hannunta da sunan makami wanda zata kare kanta.Lokaci guda suka afka mata gaba dayansu da nufin suyi mata rubdugu su daddatsa sassan jikinta.Cikin wani bakin zafin nama Malika tayi wani irin katantanwa a kasa ta buge kafafun dakarun sumamen dake gabanta duk suka zube kasa.Kuma ta taso sama kamar an harbota tayi fanka da kafafunta akan fuskokin dakarun sumamen dake samanta ta tarwatsa su da karfin tsiya kuma tayi wuf ta cafe takobin daya daga cikinsu.Kafin ta duro kasa ta hausu da SARA DA SUKA,nanfa wurin ya hargitse aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI yazama cewa duk inda Malika tasa gabanta saidai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe gona.Nanfa ihun mazaje ya cika dodon kunne jini ya rinka feshi da fantsama,karafkiyar karafa ta cika dodon kunne yazama cewa yawan dakarun sumamen yazama na banza amma saboda suna da bakin naci da kuma taurin rai sai gashi indai ba kawunansu Malika ta sara ba bata samun nasara.Aka cigaba da gumurzu sannan kuma sai suka rinka rugowa da gudu izuwa kofar wannan kogon dutse domin su shiga ciki su hallaka su sarki Hilairu,amma duk wanda ya sari wannan yana mai kauri wacce ta lullube kofar kogon sai yaji kamar dutse ya sara domin kuwa tarwatsin wutane ke tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma takobin nasu ke dakushewa.Saida aka shafe sama da sa'a hudu ana yin wannan masiffafen yakin tsakanin Gimbiya Malika da wadannan dakarun sumamen yazama cewa ita bata karar dasu ba,su kuma sun kasa koda lakutar jikinta kuma sun kasa shiga cikin wannan kogon dutsen.Koda shugaban dakarun ya lura da cewa Gimbiya Malika tayi musu mummunar barna don ta kashe masa yara sama da guda dubu daya,sai yayi sauri ya zaro wani karamin kaho ya busa,take gaba dayan dakarun nasa suka dira akan saman duwatsu sukabar Malika a tsaye ita kadai jini na diga a jikin takobinta,kawai sai shugaban dakarun ya diro kasa kusa da ita suka fara kallon kallo.Shidai wannan shugaban dakarun sumamen ya kasance narkeken kato mai kira irinta mutanen farko domin tsayinsa ya ninka na gimbiya Malika sau biyu kuma ya kasance kakkaura mai fadin kirji gami da lafta kaftan hannaye.Koda ya tsaya a gaban Malika sai ta zama yar kankanuwa tamkar an ajiye dan tsako a gaban shirwa,duk dacewar Malika ta yarda da kanta tasan cewa ita jaruma ce ta kwarai saida ta dan razana ta dan ja da baya.Nan take shugaban dakarun ya kama rigarsa da hannu ya tsarge ta daga sama har kasa,yayi wurgi da ita saiga damatsan sa da kwanjinsa sun baiyana kai kace duwatsu aka cuccura aka lika masa ajikin nasa ga kuma tarin jijiyoyi sun tashi sunyi burdin burdin kai da gani kasan cewa dole ne a sami gagarumin karfi a tare dashi.Kawai sai ya zare wadansu tagwayen adduna daga jikin guibin cinyoyinsa dama da hagu.Addunan sun kasance masu fadi da tsananin kaifi.Shugaban dakarun ya gyara tsayuwa yana mai bude hannayensa alamar cewa a shirye yake a fara kafsawa.Koda ganin haka sai itama Malika tayi wuf ta suri wata takobi dake kasa wato ta hada gud biyu hannunta ta gyara tsayuwarta tana mai fuskantarsa.Bayan sunyi kallon kallo na tsawo dakiku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna a tare suka kacame da azababben yaki.
Zidane


Wohoho idan jarumta ta hadu da jarumta kuma
gwaninta tayi karo da takwaranta tofa dan kallo
ya shigo tashin hankali bare wata halitta mai rai
data ra'bi kusa da inda ake gumurzun.Koda
Malika da shugaban dakarun suka fara kawai
junansu sara da suka cikin zafin nama,juriya da
bajinta sai nan da nan suka tashi hankalin
bishiyoyin da dukkan duwatsun dake wajen domin
kakkaryewa da farfashewa suka
kamayi,sakamakon masifar kaifin addunan
shugaban dakarun da kuma nauyin saransu.Nan
fa tarwatsin wuta da hayaki ya cika wajen ya
addabi sauran dakarun sumamen dake sama bisa
duwatsu suna kallon wannan bakin artabu.Nanfa
Malika ta gane cewa ta gamu da gamonta domin
bata taba jin mutum mai nauyin sara da iya yaki
ba kamar wannan shugaban dakarun face
mahaifinta sarki Sharkuf.Duk sa'adda ya kawo
mata sara ta kare da takubban hannayenta biyu
saita durkushe kasa bisa guiwarta guda ko duka
biyun ma saboda nauyin saransa.Badan ma tana
da mutukar zafin nama ba gami da juriya da naci
da tuni ya zargeta gida biyu.Duk da haka wani
lokacin yana samin nasarar gabza mata naushi ko
bugu da hannu da kafa ta kife kasa amma sai tayi
wuf ta mike tsaye su cigaba da fafatawa.Lokacin
da Malika ta fahimci cewa idan fa suka cigaba da
gumurzu a wannan yanayi zai sami nasarar
galabaitar da ita,idan kuwa ta galabaita take zai
hallakata,nan take ranta ya baci ta tuna cewa
wadannan dakarun sumame Yarima Lahaman ne
ya turosu domin su hallakata kuma su hallaka su
sarki Hilairu,idan kuwa hakan ta faru karshen
adalci da zamam lafiya yazo karshe a nahiyar
gaba daya tunda dai shi ma Sarki Sharkuf girma
ya kama shi,a kodayaushe ajali zai iya riskarsa ya
zama cewa babu wanda zai iya takawa Lahaman
birki.Koda gama aiyana hakan a cikin ranta sai
zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata kone nan
taje taji wani irin gagarumin karfi ya shigeta don
haka sai ta faki numfashin shugaban dakarun ta
daka tsalle sama a lokacin da ya kawo mata wani
mummuna suka da adda tagoce a saman ta
gabza masa wasa naushi a fuska da dukkan
karfinta.Take hakorinsa guda daya daga cikin
bakinsa yayi fitar burgo gami da feshin jini saboda
karfin naushin sai gashi ya ya fadi kasa dukda
girman nasa.A lokacin dayaji jiri ya kwashe
shi,kafin ya mike tsaye tuni Malika ta dako tsalle
sama ta dira akan kirjinsa kuma ta soka masa
takobi guda a cikin bakinsa.Aikuwa sai takobin ta
bullo ta keyarsa ta cake cikin kasa jini na
bulbulowa.Koda sauran dakarun sumamen suka
ga abinda ya faru ga shugabansu sai suka firgice
suka tarwatse izuwa cikin jejin da gudu domin su
tsira da rayukansu.Ita kuwa Malika sai ta bingire
kasa daga kan gawar shugaban dakarun ta kama
haki har tana furzar da gudan jini daga cikin
bakin nata saboda tasabar lugudan naushin da
tasha,saida ta huta sosai sannan ta iya mikewa
tsaye taje tayi nuni da hannunta izuwa ga
wannan yana data lullube kofar kogon
dutsen.Take yanar ta bace bat Malika ta kunna
kai cikin kogon dutsen tana tafe tana layi da
tangadi kamar zata fadi kasa ga jini na yoyo a
hancinta.Koda su sarki Hilairu hangota taho
garesu a cikin wannan hali sai suka firgice,Sarki
Hilairu bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur
ya rugu gareta,kafin ya isa wajenta ta langabe
zata fadi kasa,amma sai yayi sauri ya cafota ta
sume akan kirjinsa.Nan da ya dauketa a dimauce
yazi ya kwantar da ita suka shiga kokarin ceto
rayuwarta saboda tuni a wannan lokacin
numfashinta ya dauke kuma ba komai ne ya
haddasa hakan ba face mugun naushin da
wannan shugaban dakaru ya jera mata akan
kirjinta ba,in badon ma ta kasanace BASADAUKIYA
ba da tuniya ya karya kasusuwan kirjinta,duk da
haka jini ne ya kume mata daga cikin kirjin nata
shi yasa tashiga wannan mugun hali.Sa'ae da
akayi daga cikin matan dake wajen akwai
likita.Koda likitar tayi nazarin jikin Malika ta gane
cewa tasha naushi da bugu a kirjinta sai nan take
tasa akaje aka tsinko mata wadansu ganyaye a
cikin daji da yan dabaru aka hada murhu aka
dora tukunya aka dafa ganyayen sannan bayan
ruwan maganin ya dan huce sai aka durawa
Malika a baki.Faruwar hakan ke da wuya sai ta
farfado ta kama aman bakin gudan jini,saida ta
amayar da jini mai yawa sannan ta dawo cikin
haiyacinta,a sannane ta iya bude idanunta tayi
arba da sarki Hilairu a zaune daf da ita idanunsa
na kallonta suna zubar da hawaye saboda
tausayin Halin da yaga ta shiga,suma sauran
jama'ar tasa duk sun zageta sunyi jugum jugum
kamar ana zaman makoki.Malika ta dubi sarki
Hilairu cikin matukar karfin hali tayi masa dan
guntun murmushi kuma ta budi baki da nufin yi
masa magana amma saita kasa.Koda ganin haka
sai wannan likitar ta dubi zarhus tace,dole ne ka
hanzarta mayar da gimbiya can gidan sarauta
domin likitanta ya kara taimaka mata saboda ni
anan banida magungunan da ya kamata acigaba
da bata.Koda jin haka sai Zarhus ya mike tsaye
da sauri yaje ya janyo keken shanunsa mai dauke
da akwatuna guda Arba'in da daya yazo gaban
gimbiya Malika ya dubi sarki Hilairu yace,kusa
Gimbiya a daya daga cikin wadannan
akwatunan.Batare da wata fargabar komai ba
kuwa suka kinkimeta suka sanyata a ciki tamkar
sun sanya gawa domin ko motsin kirki batayi.Nan
take tsoho Zarhus ya zira hannunsa a cikin aljihu
ya dauko yar karamar kwalbar nan mai dauke da
maganin barci wacce kuyanga Lasmira ta bata
tasha,ya bude kwalbar ya diga wa gimbiya digo
hudu na maganin a cikin bakinta ta hadiye.Take
barci ya dauketa,koda ganin haka sai ya dauko
mushen kwarin nan ya kifa akanta sannan ya
dubi su Sarki Hilairu yace,ku cigaba da zama a
cikin wannan kogon dutse kada dayanku ya
kuskura ya fita waje nan da kamar sa'a uku gimbiya
zata turo dakarunta su dauke ku izuwa inda zasu
tsira.Koda gama fadin haka sai tsoho Zarhus ya
zaburi keken shanunsa da gudu ya fice daga cikin
kogon dutsen ya nufi hanyar dazata mayar dashi
cikin birnin Madinatul Zauwara.Su kuwa su Sarki
Hilairu sai hankalinsu ya DUGUNZUMA ainun saboda
suna ganin cewa koda yaushe Yarima Lahaman da
dakarunsa zasu iya zuwa wajen su kawo mus hari
su kashe su ko su kame su.
MEYE A CIKIN LABARIN JARUMI SA MAZA GUDU?
WANE IRIN MASIFA ZAIZO TA ITA?
SHIN SARKI SHARKUF ZAIBAR GIMBIYA MALIKA TAYI
WANNAN TAFIYAR?
SHIN YARIMA LAHAMAN YANA SAKE KAWOWA SU
SARKI HILAIRU HARI?
INA LABARIN SAURAN DAKARUN SUMAMEN
DASUKA GUDU?
SHIN INA SUKA TAFI?
Mu hadu a cikin littafi SA MAZA GUDU littafi na uku
dan jin wadannan kayatacce lbr..

Naku Suleiman zidanekd.
Whatsapp 09064179602

Post a Comment

Previous Post Next Post