Samarin Bannah (Hausa novel complete Book)

Harira ta katseta da fa'din ai yayine tako ta ina
Saudat Tace ai shegen yarone yasan kan Komai daya dace dashi.
Haka kowa Yata fa'dar albarkacin bakinsa akan RAMADAN
SAILUBAH tayi shuru kawai tana jinsu
Ashe har qawayan Momyn nashi sunyaba da shi

Shiko yana fitowa daga gidan nasu idan shi ya sauka akan Jamila
Wato Jamila wata 'Yar unguwarsu CE tana MASEEFAR son RAMADAN
Tarigada tasan duk wani motsinsa dan haka kanya fitoh daga gida take kafawa ta tsare akan wani dakali da yake fuskanta gidan nasu. Tun baya ganewa har ya ganota suka fara gaisawa
Yafara sakar mata da kalamai. Shikenan fah ya hargitsa mata tunaninta
Kowa yasan soyayya suke

Ya sakar mata Murmushi cikin sanyin murya Yace Jamis tauraruwata yau baxa abari naxo bane
[5:35PM, 09/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Tace hmm nakasa hakurin hakanne shiyasa kuma......
Bata izza xan canta bah ummi 'yar uwar shi 'yar qanwar momynsa taxo shigewa cikin gidan nasu
da sauri Tace Ya RAMADAN tun safe naketa nemanka
Ya xuba mata ido dan ya da'de da sanin yarinyar ta fa'da tarkwan soyayyarsa Amma Sam yaqi yarda ta bayyana masa
Yace ayya lafiya dai ko
Hawaye ya xubo mata Tace har yaushe xaka gane ina sanka
Asan mace da kame darajarta abin kunyane tacema namiji tana sanshi. Amma ni nafurta hakan dan baxan iya jurewa ba

Aqallah ina da 'yan mata sunka 'dari idan na iyasce
Duk acikinsu ba wacce nafara furta kalmar so agareta. Kinga ko idan kinfara furtawa baxanji Komai ba
Ki shiga ciki xan tunani akanki. RAMADAN Yafa'di hakan cikin rashin kulawa
Tace Amma........
Waccan mah budurwa tace ina santa. Ya katseta da fa'din hakan
Ummi talalli Jamila da tayi kicin kicin da fuska suka gallama juna harara sai tashige gidan kawai batare da Tace Komai bah

Jamila Tace wacece ita. Yace wani abune. Tace aa kawai dai naji na tsaneta ne
Yace toh kiji kina santa dan 'yar Uwa tace
Yana fa'din yabarta nan tsaye

Duk 'yan unguwar kallansa suke cikin sha'awar tsaftarsa. Sam baxaka ta6a ganin RAMADAN FAWAS KHAMIS cikin qaxanta ba


Direct gidansu KHAMIS yayi yana xama FAWAS na xuwa
Momyn KHAMIS Tace nidai ina sha'awarku 'yan uku na
FAWAS yayi Murmushi Yace mungode momynmu

Haka suka fito sukayi wajan wankin motar da wannan yarinyar tabayar amata
KHAMIS Yace ta'ina xamu fara.....
Kan suyi magana idan FAWAS ya sauka cikin motar inda ya hango kamar Passport 'dinta
Yace ashe baxamu sha wahala ba
Nan ya bu'de yaga akwai address 'dinta
Cikin murna RAMADAN Yace Allah ya tenake muyi sauri ina da fitta da Auntyna.
FAWAS Yace Aunty LUUVAH (dake haka suke kiranta da shi)
KHAMIS Yace Kasan 'daxo sanda ta maimaita karatunta da xamu dawo gida har Aunty XEE na tayata
Dama ai bakinsu 'daya. cewar FAWAS
Yace inaso nayi Aure cikin lokaci qanqani dan Aunty LUUVAH Wlhi
RAMADAN yayi Murmushi Yace ya kamata kam
Suka shige mitar sai Gidansu yarinyar
Bayan sunyi parking KHAMIS Yace kaduba yanda tayimin datti da mota
RAMADAN Yace toh miye
FAWAS Yace Bakomai tunda so ya kusan toka.
Suka fitoh Suna Tambayar megadi dan Allah miye sunan me motar da suka kawo mata
Yace Ameera
FAWAS Yace dan Allah koxa kamata magana
Yace badamuwa
Nan ya kirata
Tafi toh da rangwa'da kamar yanda KHAMIS ya basu labari
Tace sannunku FAWAS ne kawai ya amsa
Tana cema kallan RAMADAN
Shiko ya 'daure fuska Yace anwuni lafiya. Da sauri Tace lafiya lau
Yace Xan iya samun key na motar can
tace mexai hana bayan takuce
Nan tamiqa mishi
Yayi gun motar da kunnata sannan ya juyata FAWAS ya shiga motar
RAMADAN ya xuge gilashin motar ya kalli KHAMIS Yace muna jiranka a waje pls karka 'dau dogwan lokaci dan Kasan bana ha'da uxirin Auntyna dana kowa
Yana fa'din hakan yafitta da motar

KHAMIS ya kalli Ameera Yace da fatan nasameki lafiya
Tace lafiya lau
Naji da'din yanda kabani mamakin Ashe kai 'din na da banne
Yace toh fa'damin
Ta'dan Sosa qeya Tace kai ya kamata ka fara fa'da
Yayi Murmushi Yace toh ina sanki sosai
Tayi cikin gidansu da gudu tana cewa nima ina sanka......
KHAMIS yayi dariya ya ficce daga gidan

Daga yanayinsa sukasan yaci nasara
Hakan suka dawo unguwarsu RAMADAN
Dai-dai lokacin SAILUBAH tafi toh daga gidansu ita da XEE da Amarya da wata qawarsu Jidda

Ba qaramin bala'in kyau sukayi bah
Cikin shigarsu ta net dogayan riguna red color tayi musu kyau Sosai

Musamman SAILUBAH RAMADAN Yace toh sunfitoh mah wai gun walima xan kaisu
FAWAS Yace Aunty LUUVAH da Aunty XEE Yace eh
Nan suka qaraso Tace yauwa kunxo a dai-dai qannanmu
Saudat Tace toh gamunan muma.
SAILUBAH Tace toh
Suka shiga motar
XEE Tace harda kune arakiyar
SAILUBAH Tace eh mana Kinsan inba wani dalili ba ba'abinda yake raba kawunansu
Tace umm kumafa
Nan suka kaisu Shamsi hold
Sunyi parking sunfito kenan wani saurayi ya parka tashi motar da fitowa ya nufi SAILUBAH aqallah xaikai shekara talatin da 'daya Yace dan Allah kijini ka'dan dan tun daga layinmu nake binki
Ta 'daure fuska Tace inajinka.......
Kan yayi magana RAMADAN ya fitoh yaxo garesu Yace sannu
Cikin kulawa mutumin Yace yauwa Qanina da ganinka kai qanintane
RAMADAN ya gya'da kai Yace hakane
Mutumin yayi Murmushi Yace dan Allah ka bu'de min hanya dan nalura Auntyn taka xata ban wahala
Yace kome yasa
Yace ina Santa ne ina qaunarta daxa ta ban ha'din kai Wlhi xanji da ita fiye da tunaninta
Bu'dar bakin RAMADAN sai cewa yayi tab ai ammata miji.......
SAILUBAH da XEE da KHAMIS FAWAS suka saki baki da mamaki
Cikin wani yanayi mutumin ya kalleta Yace ayya kiyi hakuri dan Allah bansan sani bane
RAMADAN yasan baxata iya cewa Komai ba awannan lokacin
Dan haka Yace la karka damu ai akwaita da yima irinku afuwa
Mutumin ya shiga motarsa ya tafi
SAILUBAH ta kalli RAMADAN Cikin bala'in 6acin rai
Sami sami yayi cikin motarsu yajata dan yasan ya bari tayi furucin bakinta bamai kyau bane xai fito gareshi

By Hajju
[20/03, 17:09] 80k: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯**Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 16 to 20

SAILUBAH tayi kwafah. Wlhi xan gyarama yaran nan xama. Cewarta
XEE tayi dariya Tace baxaki iya masa Komai bah aikun saba hakan
Haka suka shiga da jera kayansu drink da sauransu
Baifi minti biyar ba saiga Su Amarya Saudat
Nan aka fara gabatar da walima kamar yanda kuka sani. Anayin walima irin wannanne dan Jan hankalin Amaryar tabi mijinta
Toh Madallah Gaskiya nasihar da Jan kunne ta ratsa xuciyar duk Wanda yake gun
Haka akaci akasha aka Washe
Surajo saurayin XEE shi yadawo dasu SAILUBAH gida


Tana kwance baje baje agado lokacin ana kiran sallar isha'i dama tana period shiyasa batayi yun qurin yiba
Tunani take meya hana Alhaji Jamilu kiranta ko dama irin mayaudaran nan ne
Ta danna wayanta tana neman numbarsa.
Duk daba kiransa xatayi ba. Amma me sai tanemi numbar sama ko qasa ta rasa
Shuru tayi tana tunanin ya akayi haka itadai bata gogeba toh waya goge mata
Ai kamar an muntsineta tatashi. Ba shakka wannan aikin RAMADAN ne
Kut Amma fah yaran nan ya rainani
Baqin ciki ya cika xuciyarta
Ta'dau kusan awa 'daya tana saqa da warwara tasan bayan ya goge har blocking yayi
Tashiga tunanin sosao dan tanasan tasan hanyar da xatabi da Qanin nata

In zagine ba irin xagin da bata masa akan samarin nata ba. Ba irin jan kunnan da bata masa ba akansu ba
Tabbas tasan indai xataci gaba da bayyana samarinta afili kuma ya gansu ba shakka Saidai ta tsofe agida batayi Aure ba

Ta 'daga wayan nata takirashi
Kaxo ina San ganinka yanxu
Abin da Tace kenan ta kashe wayan
Canko sai gashi ya shiga 'dakin nata da xama ahannun kujera. Amma Sam baiyi gigin kallanta bah
Yace Auntyna gani......
Tashi tayi taxo taxauna agabansa kamar me neman gafara ananne suka ha'da ido
Cikin sanyin murya Tace me yake damunka ne RAMADAN
Yayi shuru
Ya kakeso nayi da rayuwata. Duk wani saurayi daka ganni dashi saika koreshi hankalinka yake kwantawa.
Na xageka naci mutuncinka akan haka Amma kamar tunxira xuciyarka nake
Me nene dalilinka nayimin hakan
Ya shagw6e fuska cikin wani yanayi Yace hmm matsalar 'daya CE Auntyna shine duk wa'yanda suke xuwa gareki basa dacewa dake...........
Cikin maseefa ta katseshi da fa'din.... Ya isa Ya isa haka. Nagaji dajin wannan kalmomin naka. Kullun abu 'daya kake fa'damin. danka rainamin hankali
Toh bari kaji narantse maka da Allah tatsaya anan. Karka kuskura ka qureni
Ganin da tayi Sam maseefar tata bata shigesa ba shiyasata fashewa da kuka
Anan ya rikice ya durqusa gabanta yahau lallashinta ya saka hankicif 'dinsa yana goge mata hawayan nata
Cikin kamilalliyar murya Yace yi shuru Auntyna indai nine baxan qara yi miki haka
Dan Allah kiyi hakuri Wlhi nadena kukanki maseefa ne agareni
Ta tsaya da kukan. Ta kallesa yayi kalar damuwa Tace ka'dau alqawarin Gaskiya wannan karan
Ya 'daga mata gira da cewa eh
Ta'dan daki qirjinsa. Kai yanxu baka tausayina kaga yanda Abbana yasani gaba in fidda miji Amma kake korarmin Su
Yace nadena
Shuru sukayi ahaka
Can Yatashi Yabu'de furiji ya 'dauko madara da xubawa akofi ya bata
Sha Auntyna xai temaka miki wajan saki nisha'di yanxu
Ta kar6a da 'Yar harararsa Tace kaci abinci
Xama yayi suna fuskantar juna Yace eh. Kana ya fara danna wayarsa
Tsakaninka da Allah
Ya kalleta ka'dan da jifanta da wani kallo sanda taji gabanta ya fa'di. Yace Wlhi naci
Shuru tayi mai
Yasan dame ya bita dashi dan duk macan da yayima wannan kallan rasa nutsuwarta take. Yayi Murmushi yatashi. toh sai Allah ya kaimu safiya my Aunty.
Har yakai 'kofa tace xa'aje gidan she'dan kenan yau
Yayi Murmushi yana gyara takalminsa dan ya gane club take nufi gidan rawa...
Yace bakin hanani xuwa bah
Tace shine dai abinda har yanxu banyi nasarai hanaka bah
Ya kalleta da Murmushi ya futa daga 'dakin
Sam SAILUBAH bata san idan sunfara hira da Qanin nata surabu.
Ta yarda tana samun nisha'di Sosai agareshi kodako fa'da sukayi

Haka ko akayi kusan sha'dayan dare sun gama xagaye 'yan matansu
RAMADAN FAWAS KHAMIS sukayi club
Kamar yanda suka saba
'Yan matan mu musulmai sunfi yawa agun Wa'iyaxubillah
Yarane xaka gansu qanana dagasu sai rigar mama da 'dan qaramin siket Suna 'dirkar rawa agun

Duk masu xuwa gun sunsan Su KHAMIS farin sani
Xasu xone sukaraci kallansu susha drink kala kala Su rungumi mata da 'dan tsotse tsotse Amma har yanxu dai basu xama mazunatan ba

(Toh Allah ya karesu ko agaba. HAYATUDDEEN Yace hmm da wiya in har xasuci gaba da xuwa irin gura rannan Aunty Rahamat)

Toh yau abin yaxo musu wani iri
Inda wata she'daniyar yarinya bata wucce 13 years ba ta'dane cinyar RAMADAN hakama sauran suka 'dad'dane cinyoyin Su KHAMIS
RAMADAN ya xubama breast 'dinta ido ta qara ban qarosu. ya lumshe ido tare dakai hannunshi Kansu yanasan wasa dasu.....
Tace honey na da'de ina sanka dama......
Warin giyan da tasha ya bugi hancinsa tuni ya han ka'deta tafa'da qasa. Wasu suka bita da kallo wani yaxo ya jata yana murna xai biya buqatarsa
RAMADAN ya lumshe ido cikin maseefar sha'awar mace
Yace innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un

Nan ya maida kallansa gasu FAWAS. Inaaaa... sunyi nisa Sosai baxasuji kira cikin Sauqi ba
Dan haka yajanye matan daga garesu ya tasasu agaba suka fitta daga gun.
lokacin kusan qarfe 2:30am

Shika'dai ne me hankalin cikinsu dan bai shiga da yawa ba
FAWAS ya kalli KHAMIS Yace naso hutawa yau Amma 'dan iskannan ya kwafsa mana.
KHAMIS yayi shuru yana tuno saura ka'dan ya fa'da mummunan yanayi Allah ya temakeshi
Yace hmm sa6an Allah da da'di yake
FAWAS Yace Wlhi kuwa dan yau Allah ne ya ku6utar damu kai gaskiya nagaji ina sha'awar mace
KHAMIS yayi dariya Yace kayi Aure kawai awucce gun
Yace kasan Dadyna ba barina xaiyiba. Cewa xaiyi ban kai ba kai kasani
RAMADAN najinsu yayi shuru shidai burinsa. yaje gida yayi jinyar kansa

KHAMIS suka fara saukewa
Sannan RAMADAN yayi parking a kofar gidansu ya kalli FAWAS Yace toh sai da safe ya fita daga motan FAWAS yajata

Kamar yanda yasaba buga gidan yayi ahankali megadin nasu ya bu'de mishi kofa. RAMADAN ya bashi dubu biyu yayi part 'dinsa cikin san'da

SAILUBAH tayi Murmushi dan duk lokacin da RAMADAN ya dawo daga club idanta biyu tana kan sallaya
Cikin baqin ciki ta kira wayansa
RAMADAN na Ganin kiranta yajah tsaki da fa'din ita wannan wai me yake hanata bacci ne dan Allah Kullun sai taji dawowata .
Ya dai 'dauki wayar Tace ya maka kyau. kadawo ko
Yace Allah banje ba fah Auntyna
Tajah tsaki ta kashe wayan
RAMADAN yabi wayan da kallo......By Hajju 07038260028
[20/03, 17:09] 80k: [4:32PM, 10/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯**Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 21 to 25

Kana yayi calli da wayan Yace matsala
Sannan ya shiga wanka yayo alwala yayi Sallah Raka'a goma Sha biyu wannan ya xama jikin RAMADAN dan akwai shi dasan ibada
Sannan ya 'daga hannu sama yanata xuba addu'a
Addu'ar RAMADAN tafarko itace Allah ya bashi masoyiyarsa wacce yake bala'in so kana kowace addu'a take biyowa baya
Sanda ya idar yabi lafiyar gado
Ya lumshe ido yana tuno yarinyar da tahau kan cinyarsa a club.... Nanya sake shiga wannan yanayin daya shiga 'daxo


SAILUBAH ko qa'idar tane ko tana period qarfe 2:00am nayi xata tashi tahau kan sallaya tayita xikirorin Allah da yima Annabi salati wannan RAMADAN ne yayi nasarar cusa mata ra'ayin hakan dasan ibada
Tunanin shi da rana kawai takeyi har abin ya shiga jikinta har cikin dare
Shi dai ya nuna mata ba halittar da Allah bayaso kamar mushe akwance
(Wato mutum yasaki baki yata bacci kamar wani wawa)
Yace tadinga tashi qarfe hu'du sallar Asuba tadinga samun
Ita kuma ganin xata iya tashi qarfe biyu shi yasa take tashi
har ya xaman mata jinin jikinta .

Ta juya ta kwanta tana tunanin wacce hanya xatabi tahana RAMADAN xuwa club
Nan bacci yayi awan gaba da ita tare da mafarkai barkatai duk nashi

Shima RAMADAN wani lamarine ya faru dashi acikin mafarkinsa
Gaskiya ne ya kwanta da sha'awar mace Amma abinda ya burkita kwa kwal warshi shine yanda ya gansa yana saduwa da Auntyn tashi har yana mata sambatu
Kiran sallar Asubahi ne ya farkar dashi
Yafi minti talatin axaune yana tuna mafarkin nashi kana ya tashi yayi wankan Sarki Sannan ya gabatar da sallar


Da misalin qarfe tara lokacin SAILUBAH tagama shiri
Surajo yaxo shida XEE 'daukarsu dan ita takira XEE tagaya mata yau ba mota a hannun RAMADAN dan bata manta tashin motar da taji Cikin dareba tasan FAWAS yayi da ita gidansu

Suka gaisa da Surajo Yace yau gani nixan kaiku
Tace hmm ai ka kyauta. Bara nakira RAMADAN Yace OK
Nan tashiga gidansu direct part 'dinsu Dadyn shi tayi suka gaisa da Momy
Sannan tayi part 'dinsa
Ya gama tsaf yana fesa turare tashogo 'dakin
Ya qura mata yana tuno mafarkinsa
Ta gallamai harara da cewa Lafiya
Yayi murmushi Yace qalau my Aunty dafatan kin tashi lafiya Tace lafiya muje ko
Ya'dan Sosa qeya cikin rashin gaskiya Yace jiya Wlhi.......
Ta katseshi da fa'din na tambayeka
Ya girgixa mata kai
Tace hmm Wanda yayi da kyau ai ya sani. Fatana katemakeni kadena xuwa hankalina na tashi yayinda xuciyata take ciki da ba'inci
Yayi shuru dan xancan nata ya shigesa.....
Ya kama hannunta xan dena pls kici gaba dayimin addu'a
Ta hararesa ai kullun acikin ci gaba dayi maka nake
Ya kaima hannunta kiss da sakin hannun suka fitoh gwaninban sha'awa

Bayan sun shiga motarne cikin tsokana XEE Tace wannan wanka haka RAMADAN
Yace Aunty XEE kenan
Tace yau Asma'u ko Amina suka ganka saisun tsure.
Tayi Murmushi kawai
Surajo Yace kema kin yaba kenan
Tace kasan qannan namu akwai iya wanka Gaskiya na yaba Sosai Yace gashi ni ba gwanin iya wanka ba bare inqara shiga ranki Tace karka damu soyayyarka ta isheni ma haka. Inka qara da wanka xaka cutar dani.
Bana ganin wankan kowa sai naka wan nan ma dan qaninmu ne. Shiyani Yaba masa

Cikin jin da'din furucinta Yace Naji da'din furucinki....
Nan fah suka fara kalaman luv


RAMADAN ya kalli SAILUBAH cikin muryar can qasa kuma a shagwe6e Yace sun fara damun kunnena fah Aunty
ki duba yanda suke kalamai agabana ina qanin su
Kan tayi magana XEE ta cafke da fa'din ayya Qanina mundena kaji.

Shuru yayi yana fa'din axuciyarsa Aunty XEE ba dai kunne ba

Dai dai nan sukayi faking cikin skull
Kuma atare sukayi department 'dinsu. RAMADAN na murnar yau Allah bai ha'dashi da 'yan matan nashi ba


Lokacin da suka tashi KHAMIS ya gyara faking 'din motarsa. Dan shi sun da'de da futowa

XEE tashiga SAILUBAH ta shiga
RAMADAN xai shiga kenan Yaji an kirashi.
Cak ya tsaya harta qarasu Yace Asma'u ya dai
Ta'dan harareshi har yanxu kaqi ban kalmomin naka
Kuma dan baka damu da niba shine har xaka tafi baka Neman ba
Yace am sorry my baby
Yau xan baki mamaki insha.........
Bai qarasa ba SAILUBAH tafara mai maseefa karka shanyamu kamar Wasu kayan wanki pls. Cewar SAILUBAN
Ya kalli Asma'u Yace sai munyi waya Tace hmm Amma Gaskiya Auntyn nan taka mafa'da ciyace
Yace ke Auntyna cefah
Tace eh ko Auntyn takace saina fa'di gaskiya
Ya 'daure fuska Yace toh ya isa haka sai anjima
Tace dan kawai nayi maganarta shine.........
Eh dan kinyi maganar tane. Ita'din sa'arkice
Tace aiba wani abu nace ba
Ya katseta cikin tsawa da cewa ke nagajima dake kije na baki hutun shekara 'daya

Tace hutu ame
Yace a SOYAYYA
Yana fa'din haka yashige motar
KHAMIS ko ya jata

Asma'u ta dafe kai Tace ban ta6a ganin 'dan iska 'dan rainin wayo irin RAMADAN ba. Ko a ina ya ta6ajin an bada hutu a asoyayya oho 😆
[11:10PM, 10/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Dake SAILUBAH Tace kanta na mata ciwo sai kawai KHAMIS yasha Sha taletale ya fara saukesu ita da RAMADAN
Sannan yakai XEE ya wucce gida

Aranar ne aka 'daura Auran Saudat da mijinta Aminu
Qarfe bakwai RAMADAN yana gaban SAILUBAH yana lallashinta tatashi aje kai Amaryar da ita
Tace dan Allah karabu dani kaina namin ciwo
Yace haba Auntyna bata da qawar da tawucceki pls dan Allah badan niba tashi kije
Sanin halinsa da naci yasata tashi tayi wanka tashirya kicin wasu riga da siket na atamfa sun amsheta matuqa
XEE tayi dariya Tace aigwara da 'dancin naki yasaki tashi dan abinda kikasoyi Sam bai dace ba
Ta feshe jikinta da turare suka fitoh
Lokacin yayi daidai da xuwan angwaye masu 'daukar amarya
Nan samari masu ji da kai suka yimusu cah akai wannan Yace sushiga motarshi wannan Yace tashi
Ahaka dai suka shiga motar wani Abbas yajasu Cikin sauri sanda ya fitta daga layin ya fara tafiya ahankali
Ya kalli XEE Yace qawarki tayimin dan Allah kiban ita
Tayi murmushi Tace indai SAILUBAH ce nabaka ita
Nan yacika da murna yace xan iya samun numbarta Tace eh mexai haka
Ahaka yadinga Jan XEE da xance tana biye mishi duk akan SAILUBAH ne
Tana jinsu tayi shuru

In ta 'kaice muku awannan daran SAILUBAH tayi samari kusan shidda masu aji da nera
Kuma sanda suka Nace suka samu numbarta
Dukda ba magana take musu bah. XEE CE take aran bakinta

Gidan Amaryar Saudat yayi kyau Sosai dan Babban gidane. Saidai tana da abokiyar xama Rabi'a.....


Abin takaici😔
Sunfito xasu koma gida. motar Abbas suka shiga inda yajasu sun hau titi yana jansu ahankali dan bayaso yadena kallan masoyiyar tasa SAILUBAH

Basai XEE tahango saurayinta Surajo da wata mace a motarsa ba. Kasan cewar sun kunna wutar motar yarinyar tana duba wani book dake hannunta
Kallo 'daya xaka musu Kasan suna cikin nisha'di.
Gaban XEE ya fa'di hankalinta ya tashi toh dama XEE kishine da ita Sosai akan sahibin nata Surajo
Aiko cikin qara Tace Abbas yabi mata Su
Cikin rashin fahimtarta ko ya bishi
Har suka kai wata unguwa wai ita bacirawa inda sukayi parking a'kofar wani gida
Abbas ma yayi parking kusa dasu
Cikin Xafin nama tayi yunquri fitta daga motar... SAILUBAH tariqe hannunta Tace karkiyi wani abu pls kibarsu mukuma gida

cikin xubar da hawaye Tace naga alamar bakisan kishi bah bakisan miye so ba. Tunda baki ta6a tsaida mutum 'daya ya mantar dake duniyar marasa SOO bah
Wlhi kinji na rantse miki 'daukewar numfashine kawai xai hanani xuwa ga waccan maci amanar

Nan tafuzge hannunta tafuta daga motar
Tana xuwa ta kwankwasa musu gilashin motar
Budurwar tabu'de tana fa'din kai karima kincika naci toh munsiyo miki ice-cream 'din
XEE Tace karimar uwarki........
Aiko da sauri Surajo ya fitoh daga motar cikin tashin hankali danjin XEE Yace meya kawoki nan My XEE
Cikin maseefa Tace sunan nan ya fitta daga bakinka

Munafiki axxalimi makiri dan iska ni xaka yaudara
Kana tare dani. Kuma kowane lokaci fa'damin kake ni ka'daice budurwarka.
Ashe qarya kake.
Ta fashe da kuka tana fa'din na tsaneka
Kasa nabaka yardata gabaki 'daya....
Yau Aurena da kai saura wata biyu amma kake Neman wata......

Kuttumar uba Auran ki dashi wata biyu
Budurwar tatambayi XEE da mamaki

XEE tamata mugun kallo Tace bagaki gashi ba Ki tambaya shi man

Cukume wiyan rigarsa budurwar tayi cikin tashin hankali Tace idan kasaba yaudarar mata ni baka isa ka yaudareni ba
Saura sati biyu Aurena dakai ashe kanacan kana neman wata harda kai sadakinta 'dan rainin hankali ni xaka rainama wayo.....

XEE ta qara tsaida idanta akansa cikin sanyi Tace abinda Tafa'da gaskiya ne

Yayi shuru duk ya burkice
Tayi murmushin takaici Tace kaxo gidanmu ka kar6i sadakin ka na tsaneka.....
Tana fa'din hakan tayi cikin motar Abbas yajasu suka bar gun

Duk lallashin duniyar nan ba wannan SAILUBAH batama XEE akan tayi shuru tayi kuma hakuri ba Amma taqi sauraranta

Haka Abbas ya kaita gidansu Sannan ya juyo da kan motarsa ya dawo da SAILUBAH gida
Akan idan RAMADAN yayi parking

Yace toh Allah ya tashemu lafiya dan nasan baxa ki tsaya saurara taba awannan lokacin sai munyi waya
SAILUBAH tamai murmushin yaqe Tace toh. Dan ba qaramin ciwo kanta yake mata ba

Tana shiga gidan nasu RAMADAN ya bita har 'dakinta
Yace shi kuma wannan Waye
Ta kallesa ka'dan Tace ban sani bah
Yanayin da tayi magana dashi shiya tabbatar mishi ciwan kan nata bai saketa bah
Dan haka ya bu'de dirowar da take saka magun gunanta ya 'dauko mata maganin ciwan kan ya bata da ruwa. Sai taqi kar6a
Sam SAILUBAH batasan magani danjinsu allura
Dake yasan da xaman wannan sai yahau lallashinta akan tasha
Tace nace baxan shabako. ko Ana dolene
cikin fusata Yace Wlhi saikin Sha so kike Ki hanani bacci cikin nutsuwata
Ta kalleshi cikin qarfin hali Tace wai me yasa kagama raina nine RAMADAN
Yace ba rainaki nayiba Auntyna kawai dai Kinsan baxan iya bacci bane kina Cikin ciwan nan dan Allah dan Annabi kisha kitemaken
Sarai tasan inba Sha tayiba baxai barta ba. Kuma da gaske baxai iya yin baccin ba
Dan haka ta kar6a tasha kamar xatayi kuka

Yayi Murmushi dan yasan ba qaramin sa'arta yaciba wajan shan maganin da tayi

Sanda ya barta nakusan minti goma Sannan Yace dan Allah Auntyna Waye Wanda ya saukeki amota

Ta xubamai ido Tace miye damuwarka RAMADAN dan Allah
Baxaka tausayamin cikin wannan halin da nake cikiba saika dameni da surutu

Ya sosa qeya Yace Wlhi nafi kowa damuwa da duk ciwan daxai cafkeki
Amma dan Allah kitemaken kigayamin Waye shi

Tace me sona ne
Yace tab yanxu kina sanshi kuma
Ta kallesa Sosai Tace ai kallo 'daya na mishi naji ina sansa har cikin xuciyata
RAMADAN ya galla mata wata muguwar harara batare daya San yayiba Yace hmm
Lalle bakiyi sa'ar masoyi ba
Tace meyasa
Yace kallo 'daya na mishi nasan bai cika sharu'dan da kikeso agun Wanda kikesan aure ba
Tashi tayi daga gadan nata Tace me ka hango atare dashi wanda bai cika shara'di na ba. Bayan yana da ku'di daga ganin motar daya ke tuqawa. kai ka sani

Yace eh da alama me ku'dinne Amma Wlhi xakisha kunya duk ranar da kika fitoh dashi kika nuna ma jama'a shine mijin da xaki Aure
Ta waro ido. Me kake nufi
Yace yayi muni da yawa ga Wasu haqora da suka mishi cakaro cakaro abakinsa

SAILUBAH tayi shuru tana so ta hango Abbas a idanta Amma takasa dan ita ba kallan tsaf tamasa ba
Kuma dama tacema RAMADAN tana san shine dan ya barta da surutunsa kanta namata ciwo

Ganin da RAMADAN yayi tashiga tunani shiya sashi shafa gefan fuskarta tuni ta farfa'do daga tunanin nata
Yace gaki kyakkyawa abinki Amma xaki Auri me kama da aladu....😆
SAILUBAH ta shagwa6e fuska Tace kai ni har naji na tsane shi
Yayi Murmushi Yace innine ke Wlhi in yaxo gobe baxan futa ba......


By Hajju
[20/03, 17:09] 80k: [9:50AM, 14/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯**Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 31 to 35

XEE tajah numfashi Tace daga nan sai yayi saurin sakeni cikin 'dan nuna tsoro Yace am sorry Aunty XEE nayi abinda bai dace bah dan Allah kayi hakuri
Nayi shuru ina kallansa
Ya marairaice tamkar xaiyi kuka kamar yanda RAMADAN yake miki inya miki lefi. yaci gaba da fa'din. Xan shiga damuwa idan bakiyi magana bah
Nace hmm karka damu Bakomai bakayi abinda bai dace ba. Daka barni ai dana sha qasa Qanina
Yace Yauwa dama naxo induba ko kin fitone. Mutafi in saukeki agida sai kuma naga RAMADAN Yace min kina fitowa yanama Cikin motar ma
Nace toh muje

Kinsan Koda muka shiga motar sai Satar kallansa nake. Yayinda shi kuma ya sake sunata hira da RAMADAN

Ahaka suka saukeni suka kaqara gabah
Ayanxu dai haka Wlhi SAILUBAH damuwata 'daya shine inga KHAMIS ko hankalina xai kwanta

SAILUBAH ta galla mata harara Tace wai ina hankalinki ya tafine.
Ya xaki SO qaramin yaro dan xubar da aji
Yanxu ke kanki bakiji wani iri da kunyar gayamin da kikayi ba
Kalleki mace har mace Amma kirasa wanda xai burkita miki kwanya sai KHAMIS qaramin yaro

Kina wani maganar ya rungumeki ni runguma nawa RAMADAN yayi min akan hakan
Kin san ta6a hannuna agun RAMADAN bakomai bane
Ya riga da ya sabarmin da hakan
Idan kuka nake rungumata yake yana lallashi inyi shuru. Haka idan shi yana cikin damuwa kwantar da kansa yake ya shagwa6e tamkar jariri in lallashi
Agabanki yasha yimin kiss a kumatu a hannu Amma ni meyasa banji san shi ba
Eh idan ya ta6ani inajin xirrrr Amma ban 'dauki hakan a matsayin Komai ba dan dama bansa wani abu araina bah
Kawai kinbi shshashar xuciyarki kinfa'da soyayyar qaramin yaro waima KHAMIS.

Tsaki XEE taja cikin takaicinta Tace hmm to dama ke me xakiji Bayan ba sanin soyayyar ki kayi ba
Sam bakisan miye soyayya bah
Kina maganar na kamu da soyayyar qaramin yaro ai bani na halicci xuciyata bah
Inasan KHAMIS kuma Wlhi in ban Auresa ba baxan ta6a yin Aure ba kinji na rantse

Cikin Baqin ciki hawaye ya xuboma SAILUBAH Tace ai sai kije ki nemama kanki mafuta. Tafa'da da Takaici
XEE takalleta Tace ki fahimce mana. Wlhi SO matsifane so balaqi ne. Shuru SAILUBAH tayi mata
Haka XEE taqarashi kukunta ta hakura tatafi dan SAILUBAH Sosai takasa fahimtarta.


Koda RAMADAN yaxo gun SAILUBAH bai sameta da warwala ba sai yayi tunanin ko dan rikicinsu na 'daxo ne. Yace waya ta6amin Auntyna. Taqi kulashi
Cikin kalar tausayi Yace Wlhi in bakiyimin magana bah Xanyi kuka
Ta kallesa. Dariya ta kamata. Toh kayi mana.
Yayi Murmushi ai kuma ya wucce tunda kinyi maganar harda dariya pls meyake damunki. Ko wancan mutumin yaxo ne kuma kinji kina sansa haka a munin nasa
Ta 6ata fuska cikin shagwa6a Tace hmm yaxo Amma Nace mishi inada mijin Aurena
Cikin farin ciki Yace Allah Auntyna
Tace Wlhi
Yabata kiss a hannu Yace Yauwa gwara da kikace mai haka
Da xakiban dama da kin samu Wanda ya dace da ra'ayinki.
Tace kamar ya
Yaje feta da kallan nan nasa. Nanko jikinta ya mutu ta rikice mai
Dama haka yakeso danya samu yanda yake so
Hannunsa cikin nata idan shi ma cikin nata Yace so nake duk wani saurayin da kikayi Ki fa'damin dan in tayaki gano Wanda ya dace dake da kuma ra'ayinki
Ya rigada ya gama kashe mata jiki saita 'daga mai kai kawai alamar toh
Yayi Murmushi da ficcewa daga 'dakin dan yasan hirar tasu taqare tunda jikinta ya mutu

Shuru SAILUBAH tayi ta bishi da kallo harya fittan
Kana ta kwanta tana tunaninsa👯👯👯
Sun ha'du Su uku kamar yanda suka saba dan xuwa club. Amma sai FAWAS Yace suje gidansu Aymana budurwarsa
Nan sukaje
tafitoh cikin nutsuwa. Yarinya 'danya shakaf.
[12:36PM, 14/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Kallo 'daya xaku mata kugano nutsuwarta da kyau da Allah yayi mata
Aymana tana MASEEFAR son FAWAS.
Sam duk abinda FAWAS xai mata xata bashi ha'din kai
Duk da wayan 'yan matansa hakan baisa ya rabu da ita ba. dan da gaske ya hango maseefar son shi a kwayar idanta

RAMADAN da KHAMIS bar musu motar sukayi kamar yanda suka saba
FAWAS ya kalleta cikin so da qauna Yace yau kuma hijab aka samun dan karnaga kwalliyar da kyau
Tace aini takace Tafa'da tana mai cire hijab 'din
FAWAS yabita da kallo Sosai
Ya gama gane yarinyar duk abinda yakeso agareta xata mishi dan yarigada ya gama da xuciyarta ya 6ata mata xuciyarta ba wanda yake cikinta saishi. Kuma lokuta da dama yana rungumarta yayi mata kiss ya ta6a duk inda yakeso ajikinta Amma Sam bata hanashi
Shiyasa idan yaso kasancewa jikin mace ko basu RAMADAN xaije gareta yayi tsotse tsotsanshi da ita Su rabu

Ya lumshe ido dan kwalliyarta ta masa kyau Sosai
Direct ya kai bakinsa cikin nata Yafara har gitsata.....
Kamar ance kalli can RAMADAN ya qurama motar tashi ido nan yagano ya matse musu 'ya
Ka 'dan dinguri KHAMIS da yake waya da meenat ganin kamar RAMADAN xai mishi gulma yasashi katse wayan
RAMADAN Yayi Murmushi Yace 'dan iskan ya matse musu 'ya
KHAMIS Yace haba dai anan kalan agansu
RAMADAN ya nuna mishi motar da hannu
Aiko KHAMIS mah ya qura ma motar ido yayi dariya Yace karya zarce fah
RAMADAN Yace hmm ban ta6a ganin doluwar yarinya irin Aymana ba. Yanxu idan ubanta ya fito ya gansu Tace me
KHAMIS Yace tace shine ya fara mata
RAMADAN ya qarayin Murmushi Yace xako tagane kuranta dan nalura babanta irin 'yan qauyan nan ne masu gudun abin kunya
KHAMIS Yace ya kama mu katsesu fah
RAMADAN ya dafashi Yace barsu suji da'dinsu kaga sai mumusu gadi
KHAMIS ya harare shi Yace Kana da iskanci Wlhi
Yace Amma ko nafara iskancin bana kaiwa babban gurin kuma duk da iskancin nawa ai ni nake temakwanku banda haka da yanxu kunma mata 'dari ciki. Pls ka kashesu suji da'dinsu na'dan wani lokaci ne fah.
KHAMIS ya qara qurama motar ido Yace kaga Ya gama kashe mata jiki Kasan Allah saina katsesu.....
RAMADAN ya janyoshi Ganin xai nufesu Yace bara na kirasa
Nan ya kira numbarsa

A wahale FAWAS yasaki Aymana ya duba wayansa ganin RAMADAN yasan yayi hakanne dan katse mishi jin da'dinsa
Ya kalli Aymana da jikinta yagama yin sanyi ya watsa mata wani kallo ta lumshe Yace baby jeki gida sai munyi waya Tace ya kamata katuro iyayanka gidanmu
Ya waro ido tare dayin Murmushi Yace Karki damu ai dole suxo
Nan tafitoh jiki asanyaye
Taga RAMADAN da KHAMIS a 'kofar gidansu KHAMIS sai kallanta yake. Tana ha'da ido da RAMADAN ya gallah mata harara tare da 'dan lasar le6ansa. Suka bar gun
tabisu da kallo

KHAMIS ne me tuqa motar cikin jin da'din tuqin ya kalli FAWAS Yace ka 'dan huta fah yau
Yace danma 'dan iskan nan ya katseni
RAMADAN Yace xanso ganin Amina
Yace ba Asma'u ba
Yace na bata hutu ai
Haka sukayi gidansu Amina tana tare da wani saurayinta kallo 'daya xaka mata Kasan tana hirarne batare da Santa ba
Tana ganin motar masoyin nata RAMADAN tasaki Murmushi
RAMADAN Yace mutafi kawai
FAWAS Yace inka isa in nutse anan 'dan rainin hankali kawai dan kaganta da wani shine..........
Kanya qarasa Amina yaxo jikin motar tasu tabar wancan saurayin nata
Nan tagaisa dasu KHAMIS takalli RAMADAN Tace farin Cikin raina
Ya kalleta da Murmushi Yace na'am tauraruwata
Tace ban xaci ganinka ba
Yace Allah ko. Wancan shine Angwan naki
Da mamaki Tace ban gane ba
Yace ina nufin dai shi xaki Aura. Dan naga ya ha'de
Tace duk duniya ta shai da ba wanda nake so sai kai. Me xaisa kayi min irin wannan wasan Bayan Kasan Kaine mijin Aurena

Ya waro ido Yace wai dama soyayya mukeyi da xaki Sa aranki xan xama miji agareki......
Ba Amina ba hatta KHAMIS da FAWAS sanda suka waro ido😳 cikin tsoran furucinsa
Yaci gaba da cewa Wlhi tallahi ni qawa na 'daukeki ba Masoyiya ba
Atare dukkansu su ukun sukace Kut....
Tace RAMADAN dama haka kake
Ka cuceni ka cuci rayuwata
Ka hanani inso kowa a rayuwata dan mugunta yanxu kace wai qawa ka 'daukeni
Yace gaskiyar xancan kenan. Dama naxo ne in gaisheki inga kyakkyawar fuskarki dan haka naganki Allah Ya tashemu lafiya saimun ha'du gobe....
kai KHAMIS jamu muje
Haka ta raba kanta daga motar KHAMIS yaja motar cikin jin tausayinta


Kai 'dan iskane wanda Yagama raina hankalin mutane
Dama ba San Amina kake ba katsaya raina mata hankali. Cewar FAWAS
KHAMIS Yace bar shege xai ha'du da daidai shi Wlhi kodan cutar da yarinyar nan da yayi
RAMADAN ya ta6a baki Yace mace 'daya nakeso arayuwata itace take da damar mallakata idan taso

KHAMIS ya gallamai harara dayin kwafah
A haka sukaje club kusan Sha 'daya da rabi

Kamar yanda suka Sabah drink ne kala kala sai Wanda kakeso xakasha
Su Sha wannan susha wancan
Su rungumi mata da kissing da tsotse tsotse da dai sauran su.


Sha biyu da rabi daidai SAILUBAH ta kasa bacci haka kawai
Dake tasamu tsarki saitayo Alwala tafara lafula alokacin
Bayan ta idar taga 'daya saura minti uku sai kawai taji tanasan kiran RAMADAN daji Yana gida ne ko yana club


Lokacin duk sunfita daga hayyacinsu. RAMADAN yaga kiran wayan Auntyn nasa. Ya waro ido Cikin 'dan kuxari yaje harabar wajan ya 'dau kiran nata Yace my Aunty
Yanda SAILUBAH takejin ki'da na tashi shi ya tabbatar mata yanacan club 'din. Kamar xata fashemai da kuka Tace Wato kanacan ko
Yace ina 'dakina kallo nakeyi Tace qaryane Wlhi
Yace toh kiyi hakuri yanxu xan dawo Tace karma kadawo ta kashe wayan
Bai sai taji hawaye ya xubu mata bah
Shiko RAMADAN kiranta ya hauyi yana San lallashinta karta tashi da fushi dashi gobe
Cikin fusata ta'dau wayan Tace karka kuskura kada man......
Ya katseta da fa'din Wlhi ganinan dawowa my Aunty ki dena kuka kinji
Tace wayace maka kuka nakeyi
Yace muryar kice ta gaya min hakan.
Tace minti biyar nabaka Naji dawowarka yanxu Wlhi

Yace angama Auntyna Tajah tsaki ta kashe wayan. Tare da miqewa tanajin xafi aranta

Shiko RAMADAN komawa yayi ya janyo Su KHAMIS suka fitta daga gun
RAMADAN natuqin FAWAS na maseefa akan lokacinsu yau bai cika ba ya wani janyosu
Yana jinshi ya masa shuru

Ba qaramin gudu ya dinga shararawa ba. Burinshi kawai Yakai gida nanda minti biyar 'din
Ko takan sauke KHAMIS baiyi ba yaje gidan nasu
Yana tsayawa da motar Yace toh sai da safe Yana fa'din hakan yaje ya kwankwasa 'kofar gidan nasu
nan megadi ya bu'demai ya sallameshi wajan bashi dubu biyunsa yayi part 'dinsa cikin san'da

FAWAS ya kalli KHAMIS Yace kai xan fara saukewa ko insauke Kaina Yace fara dai saukeni...

SAILUBAH najin sawowarsa tayi Murmushi dan ta'dauka xai xarce lokacin data saka mishi
Tatura mishi da 'dan gajeran message cewa _ka tabbatar kaci abinci kafin ka kwanta_
Lokacin yayi wanka kenan yasa kayan bacci xaiyi Sallah yaga sakwan nata. Da Murmushi ya karanta kana ya rubuta mata _xanci insha Allah Auntyna_


Washe gari Bayan sun ha'du da safe Tace dan Allah yaushe xaku dena xuwa club
Yayi mata sanyayyan murmushi me sata in 'dauke idanta akansa ya 'dan susa qeya Yace sai randa mukayi Aure Auntyna
Tace Wato barin ba yanxu ba. Dan nasan xaku 'dau shekara goma Sha biyar nan gaba kafin kuyi Auran dan ayanxu bamai hankalin daxai baku mata
Ya sheqe da wata dariya abinda ya bata mamaki dan tasan Murmushi ne abokin tafiyarsa
Ya kama hannunta tare da kallan kwayar idanta Yace hakane Auntyna
Kin san na rabu da Amina jiya
Tace ayya yarinya me hankali ta tsaya 6atama kanta lokaci akanka. Me ya ha'daku

Ya kwashe Komai ya gaya mata yaqara da cewa Wlhi Auntyna taban tausayi
Tace kwarai Ko nima
Yace yau sha'daya muke da lectures
Tace ni baxanje ba fah
Yayi shuru yana kallanta can ya shafi gefan fuskarta Yace nadena matsa miki akan hakan my Aunty
Tace kadena ta6amin fuska ni sa'arkace wai

Yace abin ya xaman min jiki ne Auntyna ko shima kinajin xirrrr 'din 'din ne
Ta gallamai harara Tace ko 'daya nidai......
Ya katseta da cewa nadena shikenan
Tace inaso kakaini gidansu XEE yau daga can kakaimu gidan Saudat tana ta kirana bansan ko lafiya bah
Yace toh kishirya yanxu na kaiki kafin nagama shirin makaranta nasan kungama sai nakai gidan Aunty Saudat 'din mubarki acan in muntashi daga skull sai mubiyo mu 'daukeki
Tace itama XEE baxa taje ba
Yata6e baki Yace hmm Allah ya ganar daku sanin mahimmancin ilimi
Ta harareshi ya futa daga kitchen 'din
Takira wayan XEE tana CE mata gatanan xuwa.
XEE Tace ki temaken kuxo da KHAMIS dan Allah dan SOYAYYARKI da manxan Allah
Jikin SAILUBAH yayi sanyi Tace toh

Nan takira RAMADAN Tace dama suje da KHAMIS Yace toh bara ya gayamai yaxo yasa memu
Tace YauwaRiga da siket tasa na atamfa 'dinkin ya amsheta Sosai tayi kyau ba'dan ka'dan ba
RAMADAN ya dinga 'daukarta a hoto
Bayan sun fitoh ne Yace Amma fa kayan nan sun matseki Tace toh yake nan
Yace danine ke da hijab xansa
Tayi dariya Tace tab toh bakai bane ni
KHAMIS Yace Aunty LUUVAH kinyi fah
Ta tallesa sosai eh da gaske KHAMIS na miji ne kuma kyakkyawa amma ita bataga abin so a jikin qaramin yaro ba
Tace Kullun haka kuke cewa KHAMIS
Yayi Murmushi Yace ai hakanne

Haka RAMADAN yaje ya xakulo wata motarsa da yada'de bai hautaba
Suka bar layin nasu
Samarin layin suka dasa gulmar su. Wai RAMADAN yasamu SAILUBAH yanda yakeso

Bayan sunyi parking a Gidansu XEE suka shiga gidan kansu tsaye
A falo sukaga mamah da ita XEE 'din
Nan suka gaida maman tayi kitchen
KHAMIS Yace Aunty XEE
Tace yane Qanina
RAMADAN Yace naga kin fa'da tsakanin jiya da yau lafiya Tace hmm ganinan dai RAMADAN so yanasan haukatar dani
SAILUBAH tagalla mata harara
Yace toh Allah ya kawo Sauqi Amma ciwan so maseefa ne.
Tace AmEEn hakane wlhi
SAILUBAH ta xungureta akan tadena kafe KHAMIS da ido haka
Itama ta harareta abayyane Tace Wlhi baxaki hanani ganin abinda ya hanani bacci ba
SAILUBAH Tace toh tashi muje 'daki
Tace qaramin minti biyu in sami nutsuwa dan Allah
Cikin Baqin ciki SAILUBAH tarabu da ita
Tana kallanta tanata Satar kallan KHAMIS
Shiko basan tanayi ba

Ashe tayi shukar sirri akan idan RAMADAN
Dan haka yace aransa bara ya tabbatar da xarginsa
Yace Aunty XEE xamu tafi
Nan fah tanuna tashin hankalinta akan subari sai anjima
SAILUBAH kamar ta kwasheta da mari haka taji Tace xasu skull muba xuwa xamuyi ba akanme zakice suxauna

Ta harari SAILUBAH idanta akan na KHAMIS ita kanta tsintar kanta tayi da shagwa6e mai fuska Tace dan Allah kubari sai 'dan anjima
Yace Aunty XEE kiyi hakuri Kuba san karatu kuke ba. Muko munaso kibari in aka tashi maxo. Yafa'di hakan cikin kulawa
RAMADAN ya kalli XEE Sannan ya maida kallansa ga KHAMIS ya kalli SAILUBAH sai yayi Murmushi tagallamai harara.
Haka suka tashi suka tafi badan XEE taso ba


RAMADAN na tuqi ya kalli KHAMIS ka'dan Yace ka ankare da Aunty XEE fah

Cikin sauri KHAMIS ya kalli RAMADAN Yace ban gane ba pls ganar dani naji gabana ya fa'di
RAMADAN ya ta6e baki Yace idan budurwa taga 'daya daga cikinmu tana so. kuma 'dayanmu ya gano hakan ai da wannan kalmar muke gayama juna dan ya ankare da ita ko ka manta ne

Sakin wayar hannunshi KHAMIS yayi ya kama kansa da hannu biyu Yace innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un
RAMADAN Yace xaku dace Sosai 😆

KHAMIS yayi shuru.....
Xuciya cike da tunani da tashin hankali Can Yace Aunty XEE wayyo Allah na
ina toh Surajon nata
RAMADAN Yace tsuntsun yatashi daga kansa ya dawo kanka pls kashare kawai kahuta abokina xata kula dakai sosai cikin rayuwar Auranku👌🏻
Shuru KHAMIS yayi duk hankalinsa ya tashi yarasa wane tunani xaiyi
Yana cikin wannan halin yaga kiran meenat a wayarsa data fa'di qasa
RAMADAN Yace saki ranka ka 'dauka pls
KHAMIS ya kallesa Yace kasan me Naji
Yace aa
Yace Wlhi ji nayi inhar na'dau wayannan Aunty na kallona
RAMADAN ya sheqe da dariya Yace naga alamar Aunty XEE 'dinnan ta har gitsa maka kwanya.
Cikin fusata Yace ba itace ta har gitsamin kwanya ba kaine. Daka ankarar dani ita. Ya fa'da dajan tsaki


By Hajju
[20/03, 17:09] 80k: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯**Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 26 to 30.

Taqara shagwa6a fuska Cikin shagwa6a Tace yanxu kenan idan yaxo gobe karna fitta
Yace in nine ke ba
Tace nifah bana san Auran mummuna
Yace na sani ai. mexai hana kice mishi ammiki Miji
Ta qura mishi ido tana san tunanin wani abu. yayi saurin katse mata tunanin da cewa no fah. ki fita idan yaxo Amma kiqare mishi kallo Wlhi xaki yarda da xancena. Yafa'da yana mai miqewa har yakai 'kofa. Tace ina fatan dai kaci abinci. Yace banci bah dan abincin biki ne agidan
Tace ai yayi da'di
Yace tuwan 😳
Da suka sama miyar kabewa kai Gaskiya ba xanci ba Wlhi. Dan natsani kabewar nan
SAILUBAH tayi Murmushi dan tuno qiyayyar dake tsakaninsa da tuwo. Sam ya tsani tuwo musamman asaka kabewa amiyar (kunsan kano da kabewa Allah ya basu hikimar sarrafata😆 )

Tace ka tsaya in dafama ko indomie CE
Ya dawo ya kama hannunta Yace baki da lafiya Auntyna ki barshi. xansa momy ta dafamin. Ina san kihuta banasan Ki wahala kinji
Tace toh 'daukar min alqawarin xakaci
Yayi Murmushi da jefanta da wannan shu'umin kallan nasa
Tuni gabanta ya fa'di tanemi rikicewa
Ganin haka yasashi shafar gefan fuskarta Yace na'dau miki alqawari xanci.
Shuru tayi harya bu'de 'kofar xai fitta cikin wata wahalalliyar murya Tace dan Allah kar kaje club yau

Ya san idan ya qara gigin kallanta tabbas xai hanata bacci yau
Dan haka batare da ya juyo ba Yace toh naji
Alkawari
Nayi
Ya fitta daga 'dakin
SAILUBAH sai taji hankalinta ya kwanta dan tasan tunda Yace baxaije bah toh baxai je 'dinba

Kwantawa tayi tafa'da tubanin XEE
Allah Sarki yanxu haka tanacan dana kukan nata
Tayi Murmushi wai miyema soyayya ne
Sam SAILUBAH batasan soyayya ba
Dan tana fara soyayyar RAMADAN yake katse mata jin da'dinta
Ita dai abinda yake gabanta shine Auran me ku'di
Ahaka bacci 6arawo yayi awan gaba da ita

RAMADAN ko yana kallan Su FAWAS na shirin xuwa club Yace baxai jeba
Sukace me yasa Yace Auntyna ta hanani xuwa yau
Kai Aunty LUUVAH me yasa tayi haka. Cewar KHAMIS
FAWAS Yace share kawai muma mun fasa xuwa.
RAMADAN yayi dariya Yace nasan xa'ayi haka
KHAMIS yajah tsaki Yace naso hutawa Wlhi
Dole haka sai gun 'yan matan nasu sukaje kawai


XEE ko tasa iyayanta tayi agaba tana musu kuka
Da tashin hankali suke tambayart lafiya
Nan tagaya musu Komai taqara da cewa Wlhi BABAH na tsani Surajo. Bana sansa. Kurku ha'da ni Aure dashi dan baxan ta6ayi masa biyayya bah
Kuma ai ana Aure ne dan biyayya Wlhi mamah baba baxan ta6a yimasa biyayya ba nidai bana san shi yanxu

Dake iyayan nan ne masu San 'ya'ya nan suka hau lallashinta da cewa gobe xasu aika masa da sadakinsa basai ma yaxo bah

Nan hankalin XEE ya kwanta
Takira SAILUBAH take gaya mata yanda tayi da iyayan nata
SAILUBAH Tace Wlhi banso rabuwarku bah dakun sa santa kanku dai da yafi
XEE tajah tsaki Tace Wlhi Sam SAILUBAH bakiyi bah
Da Kinsan xafi da ra'da'din da nakeji araina da baki CE haka baWashe gari misalin qarfe biyu ne suke da lectures
Dan haka RAMADAN ya biyoma Auntyn nasa
Ta kallesa da kyau Tace baxan iya xuwa bah
Yace Amma gaki garau mexai hanaki xuwa
Tace ni nasan abinda nake ji
Yace Auntyna akwai ranar da xaki nemi karatun nan ido rufe Ki rasa shi
Me yasa bakya san karatu ne Auntyna. yana da amfani fa. Wannan CE damarki idan kika bari takubce miki ya wucceki kenan har abada
Duk da in san karatu irin na Aunty XEE tafiki
Amma da antashi magana sai kice wai aibake ka'dai bace kike qin karatun

Ta galla mai harara. Cikin raini tace wai in tambayeka man
RAMADAN ya faketa da ido. Taci gaba da fa'din
Ni da kai waye babba
Yace ke
Tace meyasa kake sani agaba da fa'da sai kace Kaine Babban nice qanwar
Yace Auntyna kin kasa ganewa Sam.
Shi karatu idan yaxo gareka kamashi kake da kyau dan kai kake da cin moriyarsa. Ina guje miki ranar da xakiyi Aure kisami Miji me in barin Matarsa fita karatu. Ya hanaki cigaba alokacin dake kike ganin dacewar hakan
Tace na rigada nagama tsarama kaina rayuwar aurena. Insha Allah xata xomin yanda ya dace
Yace koh
Tace kwarai
Yace amma inaji ajikina baxaki samu yanda kikeso ba
Ta galla mai wata muguwar harara tace insha Allah xan samu fiye da yanda nake so mugu kawai
Kaga kaje kawai karka tsaya cikani da surutu 'dan rainin hankali kawai. Ta qarashe da nuna 6acin ranta

Yayi Murmushi Yace toh shikenan Allah yabaki lpy Auntyna saina dawo
Har yakai kofah Tace RAMADAN Yace na'am.
Taqara harararsa Tace kayi kyau Sosai. Tafa'da batare da tasaki fuskarta ba.
Yadawo gareta ya kama hannunta da shafa goshinta. Ba xafi agoshin Yace Allah yabaki lafiya Auntyna kema kinkyau Sosai
Tace kaci abinci ko Ya'daga mata kai alamar eh kana ya mata kiss a hannu ya fitta yana cewa natafi
Tabishi da kallo tana jin da'din qamshinsa.


RAMADAN yana futa bai da'de ba Abbas ya yaxo gidan
Da sauri SAILUBAH takeyin shiri burinta taje taga munin Abbas 'din da RAMADAN yace

Aiko bayan sun gaisa ta qura masa ido........
Eh Gaskiya ne
shi baqine bai cika kyau ba. Kuma da gaske yana da hakwara Amma basu sashi muni bah. Yanda tadinga tunanin xata gansa abin bai kai haka ba. Dan yana kyansa daidai gwargwado
Amma taji aranta Sam bata sanshi dan maganar gaskiya RAMADAN yayi nasarai jefa mata qiyayyarsa


Yace ya kikayi shuru haka kina kallona
Tace hmm ina takaicin abinda xan gaya maka ne
Yace duk abinda xai futo daga bakinki baxai ta6a xama takaici agareni bah
Tace ina da mijin Aure na.......
Da sauri ya kalleta cikin wani hali Yace maganar gaskiya kike gayamin dan.......
Ta katse shi da fa'din. Baxan maka qarya ba
Yayi shuru cikin wani yanayi narashin jin da'di
Can Yace toh Allah ya ha'dani dame kamarki ina barin nan
Tace ina maka fatan samun wacce tafini
Yace Nagode
Haka tana kallo ya juya motarsa yabar harabar gidan nasu

Tana shiga 'dakin Kakah kiran XEE ya shigo wayarta
Tace ya akayine XEE
Daga can XEE Tace hmm Ki saurari xuwana Tace Allah ya kawoki ta ajiye wayan
Kakah Tace yadai jikin naki Tace da sauqi. Tace Toh Madallah
Dama inasan cin tuwan dawa ne miyar ku6ewa. SAILUBAH tafa'di hakan cikin marairai cewa
Kakah Tace toh ai sai ayishi yauKusan qarfe shidda da rabi 6:30pm XEE taxo gidan nasu
Tace qawata ina cikin wani hali
SAILUBAH Tace ai in baki shiga ba a tambayeki dan rabuwarki da Surajo lokaci 'daya ba abubane wanda xai barki haka cikin Sauqi

Tace Kin san Allah na manta da wani Surajo dan nariga da nacireshi kwata kwata daga raina
Ni damuwata itace KHAMIS
Wayyo Allah na SAILUBAH yau yarannan ya rikitani
Ya jefamin sanshi araina lokaci 'daya
ashe dama duk wannan burgenin da Nake cewa yana yimin Ashe na fara sanshi ne dama haka so yake shiga xuciyar mutum farat 'daya
Wayyo ni XEE yaxanyi dasan Wanda na girma qaramin yaro
Saiga hawaye ya xubo mata
Cikin kuka tacigaba da fa'din watoh nafito daga department 'dinmu 'daxo ina tafiya ahankali dan wata gajiyace ta kamani lokaci 'daya
Ban kalli gabana Sosai ba. basai kawai nayi tuntu6e ba. Nayi taga taga xan fa'di.
Sai gashi ya yanko kwana......
Cikin sauri ya kama hannuna da janyoni jikinsa.
SAILUBAH Kaina ya sauka a qijinsa
SAILUBAH na shaqi qamshinsa
SAILUBAH saida xuciyata tabuga hankalina ya tashi dan jin wani fitinannan filing daya kusantoni

Sunkwi da kanta XEE tayi
Tayi shuru agun hawaye yana cigaba da xuba mata
Kana ta'dago ta kalli SAILUBAH da tasaki baki ido hanci tana kallanta

Tace wlhi jinayi dama in dauwama a haka a qirjinsa dan jin yanda qamshinsa yake shiga hancina

Daga nan saime..... SAILUBAH Tafa'da cikin buqata hankali tashe

By Hajju
Afuwa dan Allah MASOYA
[20/03, 17:09] 80k: [3:00PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯**Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 36 to 40

RAMADAN yayi Murmushi Yace ka kwantar da hankalinka pls dan Allah
Yace narasa tunanin da Xanyi RAMADAN Al'amarin ya shigeni Sosai
Kuma bansan ta'ina ni da ita xamu fara ba.
RAMADAN Yace hmm ka fita sanin ta inda xaku fara ai
Tunda bayau nasa ba baku Satan amsa ba ka share kawai abokina. Dan Akwai hanyoyi da dama.......

Ni Wlhi ban ta6a ganin Mara sanin abinda ya dace kamarki ba
Akan wane dalili xakiso qaramin yaro dan xubar da mutunci
Toh ai gashi nan alamu sunnuna RAMADAN ya gano Ki. SAILUBAH tafa'da cikin 6acin rai
Cikin wani yanayi XEE Tace ban damu da RAMADAN ya gano Sirrin xuciyata ba. Ni dai nariga da nayi tunanin xuciyata takamu dasan KHAMIS batun yanxu ba
Gwara ma da RAMADAN 'din ya ganoni nasan ba'abinda xai hanashi temakona
SAILUBAH Tace Amma.......
Cikin fusata XEE ta katseta da fa'din duk abinda xaki fa'da min Wlhi baxai shiga xuciyata ba SAILUBAH.
Dan narigada na gama fa'dawa tarkwan sonsa
Naga alamar bakisan rayuwa ba. Tunda bakisan miye so ba

Tashi SAILUBAH tayi tashiga toilet can tafitoh. Tace yanxu xa muje gidan Saudat 'dinne. ko sai anjima.

XEE ta harareta takawar da fuskarta
Murmushi SAILUBAH tayi kana taje ta dafa kafa'darta. Idan baki xama matar KHAMIS ba ai Al'amuran baxa suyi kyau ba
Kuma yanxu ne naga dace warku ke da shi
Ina san Kibi Komai ahankali dan in kikayi gaggawa abin baxai xo miki da kyau bah
Wlhi na fahimceki duk da gorin da kike yimin akan bansan so ba
Xanyi qoqari insan ya yake

XEE tayi Murmushi cikin jin da'din furucinta Tace nagode ma Allah dayasa kika fahimceni
Wlhi baxan 6oye miki ba. Damuwata ta qasu kashi biyu ne. Da qin fahimtata da kikayi da maseefar son KHAMIS
Naji sanyi araina ta 6angaranki. Yanxu yaxa muyi da KHAMIS

SAILUBAH tajah numfashi Tace inaso kirage xagewa akan san nashi
Tace ni Kaina bansan lokacin da xuciyata ta shagaltu da kallanshi 'daxo ba. Wlhi SAILUBAH bansan ya akayi nakamu da sanshi ba. Ban sani ba. Ina da aji
inada kamun kai.
Ke kin sani Amma lokaci 'daya na burkice. Tafa'da hawaye na xubu mata.

Yanxu ne SAILUBAH taji tausayinta. Tayi shuru tana tunanin ta'ina xasu fara
Can dai Tace bama rasa mafuta XEE kwantar da hankalinki


Can da yanma sukayi gidan Saudat rijiyar xaki inda suka tarad da ita Cikin damuwa
XEE Tace ya naganki cikin damuwa kina amarya
Tace ke dai bari. Ashe Auran mijin da yake da mata maseefa ne
Atare SAILUBAH da XEE sukace lafiya
Tace ba lafiya ba
Kunsan tunda aka kawoni gidannan ban qara ganin idan Mijina ba
SAILUBAH Tace kamarya
Tace Wlhi SAILUBAH Saidai inji muryarshi da shewarshi a 'dakin kishiyar tawa
XEE tawaro ido Tace duk soyayyar daya nuna miki
SAILUBAH Tace tab kuma sai kika xuba musu ido
Tace toh ya xanyi
Tana dai xuwa ta kawomin abinci tajuya tatafi........
Kan SAILUBAH tayi magana sai sukaji muryan Megidan nasu shi dasu RAMADAN
Da 6arin jiki yake CE musu kushiga tana ciki

Su RAMADAN sukayi cikin falan da sallama
Gaban XEE ya fa'di dake idanta na qasa batayi gigin kallan KHAMIS ba

Da murna Saudat Tace qannena
KHAMIS Yace Aunty Saudat ina wuni
Tace lafiya
RAMADAN ma ya gaidata
Yaqara da kallan Auntyn tashi Yace kutashi mutafi ko.
Ta hararesa da cewa toh yanxu mukaxo Yace toh xamu tafi kwa tawo
Tace haba mana 'dan Qanina dan Allah bamu mintina saimu tafi
Shuru ya mata
Saudat Tace kunga yayi shashinta ko
SAILUBAH Tace eh gashi nan kam Ko shigowa nan baiyi ba
Tace Wlhi xuwa anjima xakuji shewarsa shi da ita
SAILUBAH Tace hmm inda nice ke duk ubansu xanci wlhi. Dan saina dafasu ta cikin ruwan sanyi
Shawara 'daya xan baki itace kifuta daga har karsa kwata kwata Sannan ita kuma ki sake da ita dan bakisan abinda tataka ba. Sai kin shigeta xaki gane Komai. Daga wannan lokacin saiki San tawace hanya xaki 6ullo mata
Kina tashi da safe kigama aikinki da wuri sai kije kitchen 'dinta kice kinxo tayata aiki.
Duk yanda tayi dake akan kibari karki bari Ki kwantar dakai kimata ladabi da biyayya tanan xaki kasheta
Ya kasance Ki lixamci 'dakinta da xinmar kinxo tayata hira. Tanan Xaki gane inda tasa gaba
Shi kuma ko yaxo ya sameki a 'dakinta gaisuwace kawai xata shiga tsakaninki dashi kina gaishe shi kibar 'dakin dace musu sai da safe
Shi xai shiga cikin damuwar abinda yakeyi bai dace ba kuma me yake sashi yin hakan
Yayinda ita kuma xataji da'di aranta ta'dauka cewa ashema ke mijin baya gabanki. Kinga daga nan saita qara sakewa dake.
Ke kuma aidama ba xuwan Allah da Annabi kikeba sai kiyi saurin sanin Komai daga nan saiki 6ata mata shiri cikin ruwan sanyi. dan dama kin riga da kinsan Komai saike cafke mijinki tunda kinsan matsalar daga ina take
Amma fah kiriqe Allah a lamuranki bamai miki saishi bamai hanaki saishi
Tace hmm Nagode sosai Xanyi qoqari in gani Allah yasa mudace (AmEEn)

Dako kin temaki kanki dan Wlhi inda nice Sai dai axo rabamu dan ubanki xanci tunda mjin ba naki bane ke ke 'daya. Cewar XEE

KHAMIS ya qura mata ido na'dan daqiqu

RAMADAN ya kalli Saudat Yace Wlhi Aunty kima mijinki ladabi da biyayya karki biyema Auntyna Kinsan ita 6ata abu take Sam bata iya gyarawa ba
XEE ta kallesa Tace ai xata mishi biyayyan
SAILUBAH Tatashi tana cewa saita biyemun. kuma ban iya gyaran ba. Kasanni she'daniyace. Wlhi RAMADAN kafita daga idona in rufe.
Suma tashi sukayi harda XEE
RAMADAN Ya ha'da hannuwansa biyu Yace iyi hakuri toh
Ko kulashi batayi ba tafita daga falan.
Har waje Saudat tarakosu
RAMADAN Yace Aunty XEE da mota biyu muka xo kinga.....
Xaki shiga tawace in kaiki gida ko KHAMIS ya kaiki.
Da sauri KHAMIS Yace kaji ka da wani kwa'du.
Aunty LUUVAH xaka 'dauka tunda layinku 'daya ko nace gidanku 'daya
ko ba haka ba Aunty XEE ni saina kaiki gidan. Ya fa'da da kallanta cikin murmusawa

SAILUBAH tayi Murmushi tana fa'din aranta Lalle yarannan sun raina musu hankali. Yanxu haka sungama shirya abinsu xasu kawo musu wani alaye.

Tace hakan shine daidai. Tafa'da da shigewa motar RAMADAN

Ahankali XEE tashiga motar KHAMIS

RAMADAN ya 'daga mishi gira. KHAMIS yayi Murmushi ya shige shima natare da Auntys 'din nasu sun ganosu bah

Sanda suka fita daga layin RAMADAN ya tada tasu motar.
[3:01PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Suna tafiyar cikin nutsuwa RAMADAN ya kalli SAILUBAH ka'dan Yace Auntyna ki dinga gyara abu pls kidena 6atawa
Tayaya xa'ayi Ki gaya mata tashare mijinta.
SAILUBAH Tayi mai banxa
Shi kuma yanace sai tayi magana ya qara kallanta
Haba mana dan Allah Auntyna ki dinga gyara ki dena 6atawa ki dena xiga mutum yanxu kin xigata akan ta yaudari 'Yar uwarta inkece aka xoma ta wannan hanyar......
Da fusata ta katseshi da cewa. Waiwa ya gayama ni xugata nayi shawara na bata wacce ta dace da ita. Tafa'da da 6acin rai
Shuru yayi mata dama so yake tayi magana kuma tayi
Har suka qaraso gida bai qara magana ba
Yana parking tafuta daga motar da xafin rai. Yabita da kallo yayi Murmushi
itako tana xuwa 'daki tasaka key dan tasan ba barinta xaiyi ba


KHAMIS da XEE ko shuru kakeji acikin motar bamai magana acikinsu
Saima XEE ce da lokaci lokaci takan kalli KHAMIS 'din dan xuciyar tata hanata daurema kallansa

Da yayi parking a 'kofar gidansu ya kalleta cikin wani yanayi ya sanyaya murya Yace my Aunty mun'iso
Duk da XEE tasan sun iso hakan bai hanata kallansa cikin sauri ba. Dan muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata maganar ta shigeta ba'dan ka'dan ba. Ya lura da hakan sarai. saiya futa daga motar yaxo ya bu'de mata motar kamar yanda masoyi yake yima masoyiyarsa
Tafi toh xata 'dau jakarta sai kawai yayi saurin 'dauka yana cewa da alamun gajiya atare dake my Aunty xanso in kai miki har gida idan kin amince min. Yafa'da da jifanta da wani kallo mesaka Sarki yayima Bawansa ladabi.
Da sauri Tace na amince. Ya qura mata ido
Tace lafiya kike kallona haka
Yayi Murmushi yace Wlhi wani tunani na shiga. Tunda nake dake Aunty XEE ban ta6a jin da'din muryarki irin tayau bah.......
Da'di kamar ya kashe XEE Tace sai yau ka ta6aji
Ya waro ido Yace kinga xan 'daure Kaina. Ai Kullun muryarki acikin da'din sauraro take
Tace toh Nagode
Ta shige gaba yana binta abaya yana qare mata kallo har suka iso falan gidan Yace mamah bata nan ne. Tace gashi dai daga dukkan alamu
Ta ibo drink taxuba mai a cup itama tasaka ma kanta kana Tace xanso kasha Qanina
Ya kar6a da Murmushi Yace banso shaba dan banajin shan Komai saboda damuwa Amma tunda kinaso nasha ba'abin da xai hanani Sha
Sanda ya Sha ka'dan Tace meya sakaka cikin damuwa Yace Wlhi Aunty wata nake So❤ saidai ta girmeni ban san ya xanyi bah
Da sauri ta furzar da drink 'din da yake bakinta ha'de da sakin cup 'din ya fa'di qasa......
jikake tass ya fashe
Tayi saurin xamowa daga kan kujerar da take cikin tashin hankali Tace wa kakeso kuma
Da sauri ya matso kusa da ita da ciro hankicif 'dinsa cikin nuna tsoro ya kama hannunta taji wani shock shima yaji Amma ya share ya fara goge mata hannun nata da gefan bakinta Yana cewa am sorry Aunty XEE na tada miki da hankali ko. Karki damu nasan baxata soni bah. Sai dai Wlhi baxan ta6a Auran wata mace ba in ba ita ba. Ya qarashe maganar da sake mata hannun nata
Aiko saiga hawaye ya xubo mata cikin kuka Tatashi xata bar falan.
Yace baxan ta6a yafema kaina ba idan har kika tafi cikin kukan nan kika barni batare da kin gayamin dalilinki nayin shiba
Juyowa tayi ahankali Tace KHAMIS nakamu tasan wani yaro wanda na girme masa gashi kaima kakamu dasan wacce ka girma. Ganin da nayi matsalarmu 'dayace shi yasani rikicewa har nayi wannan kukan
KHAMIS yajah numfashi ha'de da lumshe idansa yanajin kukanta har cikin ransa kana ya bu'de idan
Yace ki dena bana so bana san jin kukanki yana damun xuciyata pls kitsai dashi karci sakani cikin wani dan Allah
Ahankali XEE ta qaraso gabansa Tace shin abinda kafa'da haka yake
Yace akan me xan miki qarya. Yafa'da yana mai goge mata hawayan

Kawai ki share my Aunty xan kiraki anjima kiban shawa'a akan ya xan 6ulloma da ita budurwar tawa. Sannan kema kinemi shawarata akan wanda kikeso. Tunsa kinga mu SAMAREEN BANAH ne xan iya baki shawara yanda xakiyi dashi kema Kinga kyabani shawarar yanda xanyi da ita
Shuru tayi masa
Shiko har yakai 'Kofa ya juyo ya dawo dan yana so ya hanata bacci
Ya shafi gefan fuskarta Yace kimin alqawarin xaki cire damuwa aranki my Aunty
Tace idan na iya cire ko wacce damuwa araina ai baxan iya cire damuwar SO ba
Ya lakuce mata hanci Yace insha Allah xaki kasance da wanda kikeso dan shima yana MASEEFAR SONKI
Tace ya akayi kasan hakan bayan.....
Ya katseta da cewa saboda ko makawone yaji wuccewarki kawai yanasan Allah yayi halittar kyakkyawar mace anan
Tayi Murmushi Tace yanxu kai ka tabbatar da hakan
Yace Wlhi ayanxu bawanda ya kaini tabbatar da hakan koda ko Ya Surajo ne
Ta 'daure fuska xatayi magana Yace bye bye sai munyi waya Ya fitta
Tabishi da kallo


Sallar magriba SAILUBAH tayi tafa'da tunanin wani Alhaji Aliyu da ya kirata 'daxo wai abikin Saudat ya ganta dan Allah dan annabi tabashi dama yaxo gareta. Yanda yake rokwanta ne yasata bashi ixinin yaxo
Tana tunaninsa ne zaizo bayan Isha'i ne ko xaixo gobe bata sani ba

To ganin yanxu mah taji wayanta na ringing sai tayi tunanin shine
Ashe bashi bane wanine kuma wai Alhaji Aminu
Duk dai abikin Saudat ne suka ganta. Yana gaya mata dan Allah taso shi Yana Santa yana garin Abuja da xama. Baida mata. Kuma da maganar Aure xaixo gareta dan Allah tabashi dama yaxo gareta
Dan yanxu haka yana Cikin garin kano dan gobe yake san komawa Abuja

Toh fah😳 kunsan SAILUBAH da Alhazawan garin abuja ba qaramin so take musu ba dan ku'dinsu nan take taji ya wanta mata arai dan muryarshi nada da'di
Amma danta gwada shi sai Tace hmm banajin yau xaka ganni dan nagaji da yawo sai gobe
Kamar xai mata kuka yake mata magiyar tayi hakuri ya ganta dan Allah Tace toh kaxo Amma kasani minti biyar kacal xan baka
Yace angama ranki ya da'de

Bayan tayi sallar isha'i. Kyalliya tayi Sosai RAMADAN Yace Auntyna wannan kwalliya haka. Sam ta manta sunyi fa'da 'daxo taje takama hannunsa ta sakarmai kiss a kumatu Tace yau burina ya fara cika nayi saurayi 'dan abuja anjima xaixo
Da tsoro RAMADAN ya waro ido cikin wani yanayi Yace pls Auntyna Karki soshi dan Allah
Ta galla mai harara tare da sake hannunsa tana ta6e baki Tace Wlhi saina so shi
Kuma na ranshe da Allah kakorar min shi saina maka dukan tsiya
Yayi Murmushi Yace wasa nake miki baxan koreshi ba

Sam SAILUBAH bata yarda da murmushin da yayi ba. Dan tasan halinsa sarai fa'danta da cika bakinta baya hanashi korar mata su. Dan haka sai Tace suje 'dakin shi xata gaya mishi wani Abu
Haka ko sukayi gidansu dayin part 'dinshi
Suna shiga 'dakin tacire key 'din 'dakin nashi tafita da gudu ta kulle shi ta baya tana ai nasan maganinka
Ta window ta leqo tasheqe mishi da dariya Tace in yaxo ya tafi xan dawo in bu'deka. tana fa'din hakan tabar gun

Shuru RAMADAN yayi yana tunani
Gaskiya ta shamma ceshi dan yasa aransa ko ganinsa baxatayi ba xai koreshi Ashe ta ankare dashi
Yayi kwafah da fa'din ni da ke har abada muna tare da juna Auntyna


SAILUBAH na shiga gidansu saiga Alhaji Aminun yaxo
Sanda tashafe minti goma Sha biyar Sannan taje gareshi
Yace ina wini tauraruwa me haskake taurari
Tace lafiya da fatan kaxo lafiya Yace lpy lau
Tace toh Madallah
Nan ya qara fa'da mata shi ko Waye
Wai yana Saida 'dan kunne da tsarqa na xinare ne a Abuja iyayansa 'yan nan kanone sana'ar tasa ce takaisa Abuja

Sosai mutumin ya tafi da imanin SAILUBAH dan ganinshi da tayi kyak kyawa ga xaxxafar motar da yaxo da ita
Ta'dan dai bashi dama haka
Yace Yaji da'di xai turo iyayansa suxo dan bai ta6a SOYAYYA ba bayasan yaudarar mata
Kuma komai xa'ayi shi da sauri
Tace toh itadai saita xanta da mahaifinta tabashi labarin yanda sukayi Yace duk da haka xai turo iyayansa gobe

Daxai tafi saiya bu'de mata wani qaramin akwati Yace ta ibi iya adadin ku'din da takeso
Nan cikin SAILUBAH ya mun'da dan ganin yawan ku'din kuma duk 'yan dubu dabu ne a ciki
cikin wani yanayi Tace ka barshi Nagode
Yace aa fah ina San Ki 'dauka ko ku'din xai sami farin jini aguna kisa mai albarka dan Allah
Tace aa dai ka barshi
'Daukar wata leda yayi yasaka mata bandir 'din ku'dinnan guda goma😳 miliyon 'daya kenan a ha'duwar farko.
Ya saka mata akan cinyarta Yace nasanki da temako duk xaki iya bayar da wa'yan nan Amma dan Allah ko naira biyar CE kici aciki
hakan xaisa inji da'di. Ga wannan cikakken bayanai ne akaina kiba Abbanki nasan mah xaisan mahaifina
Shuru SAILUBAH tayi tafuta daga motan da ku'din a hannunta.
Tana kallansa yafita da motar tashi yana 'daga mata hannu
Bayan 6ace warsa tayi cikin gidansu da gudu tayi 'dakinta ta xaxxage ku'din a gado. tana murna sai watsa ku'din take sama tana ta dariya
Can ta tuna da RAMADAN. Aiko da gudu ta'dau kin 'dakin nasa tafitoh xuwa Gidansu ko gyale babu ajikinta sai 'dan kwalinta data rufe kanta dashi xuwa kafa'darta

Da sauri take bu'de 'dakin tana bu'dewa takama hannun RAMADAN tana jansa har cikin gidan
Sanda sukaxo 'dakinta taja musu burki Tace kalli gadona
RAMADAN ya xaro ido cikin tsoro Yace Auntyna wannan ku'dinfah
Tayi dariya ta 'dane gadan ta watsa ku'din sama Tace aikin Alhaji Aminu ne
Sai kuma tasauko ta ta tsaya agabansa
Kaga burina xai cika xan xama matar Babban mutum. xan mallaki ku'da'de masu yawa. xanje gidan marayu inbata tallafi. xanje asibitoci nakai xiyara.........
Ya isa da Allah Ki mayar masa da ku'dinsa
Cak ko ta tsaya da maganar tata
Tace kut......
Na lura ba qaramin Baqin ciki kake yimin bah. Wlhi inxaka mutu baxan mayar da wannan ku'din bah


By hajju
[20/03, 17:09] 80k: [4:47PM, 19/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR*👯*Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 41 to 45

Ban da haka me xaisa na mayar masa da ku'dinsa
Tambayarka nake kaban amsa.
RAMADAN yaja numfashi Yace saboda ba sanshi kike ba ku'dinsa kike so
Yanxu ya dace Ki yaudare shi
Tace eh ai rayuwace
Qila indan na Auresa naji ina sansa
Yayi Murmushi Yace toh Allah ya tabbatar da alkairi
Tace AmEEn Amma kadena min baqin ciki Sannan inaso gobe kaxo ka rakani gidan marayu da wajan almajirai
Kamar ya tsinka mata mari haka yaji Yace gaskiya baxan 'dauke ki da wannan qaxan taccan ku'din ba, ma'ana baxanje ba

Tace toh shi kenan karka kar kaje. Ainima nakusa yin mota xanje ko ina da kaina basai nane mi ka kaini ba jeka nagode.......
Da mugun kallo yabita kana Yajuya ya futa xuciyarsa nayi masa xafi

SAILUBAH ta bishi da kallan harara. Kana ta ha'de ku'da'danta tanemi guri ta adana Sannan tanemi kiran XEE.

RAMADAN juyi ya dinga yi akan makeken gadansa duk ya rasa nutsuwarsa
Can yatashi yana safah da marwah yana tunanin ta inda xai biyoma Auntyn tasa
Yasan tashiga da yawa. Da gaske wannan karan saiya bita ahankali
Yana cikin tunaninne FAWAS ya shigo 'dakin nasa shi da KHAMIS
FAWAS Yace lafiya naganka Cikin damuwa
Yace Auntyna ce ta jefani cikin damuwar kun santa da ku'di
yanxu tayi wani tsinanne wai daga Abuja.
Ni damuwata yanxu na sanshi.
FAWAS Yace tokai mexai dameka
Yace kun kasa ganewa har yanxu
KHAMIS yayi Murmushi Yace hmm Aunty LUUVAH kenan
Ni dai tana burgeni Sosai. Tana burin ta mallaki ku'di masu yawan gaske. Kuma ta temakama marasa shi
Wannan burin nata yaba tsumani ba'dan ka'dan ba
FAWAS Yace toh wai me xai dameka akan hakan Bayan kafi kowa sanin wannan burinta ne
RAMADAN Yace dole Komai ya dameni akanta.
xaku gane ne nan gaba. Ya dafe kansa na mintunoni
Can ya saki murmushin mugunta dan tuno da wani abu wanda in yayi mata xai bala'in 6ata mata rai har Tace ta hakura da Alhaji Aminun

ya kalli KHAMIS ya 'dora da fa'din ya Aunty XEE...
KHAMIS yayi dariya Yace tana nan qalau na burkitata kamar yanda tayi nasarar burkitanin daga ankarewa da ita.
Wlhi RAMADAN banajin ko wacce mace arai ayanxu kamar Aunty XEEE
Ya abin xai kasance idan kunya ta hanata furtamin Kalmar SO

Ha'da ido FAWAS da RAMADAN sukayi atare kuma suka saki Murmushi

Shege yaga cikakkiyar mace
Ai dole kaso ta. Dan ta ha'du tako ta'ina
Kagaya mata pls karki dinga hargitsata. dan nasan ka'dan da aikinka ka tarwatsa mata kwanya....... Cewar FAWAS

KHAMIS yayi dariya Yace aina rigada na tarwatsa mata kwanyar dan Wlhi yau nayi alqawarin saina hanata bacci
Yanxu haka nasan tana cikin damuwa dan na jefata cikinta

RAMADAN Yace ya isa haka dan Allah
Pls karka wahalar da ita da yawa
Dan bana san tashiga damuwar da har tasata jefamin Auntyna aciki.

KHAMIS ya tashi yana dariya Yace Aunty LUUVAH ka sani kawai. Itace damuwarka karka damu baxan bari she'daniyar xuciyata ta wahalar da Masoyiyata ba. Bare ta shafama Auntynmu

FAWAS Yace lokaci yayi ya kamata muje ko
KHAMIS Yace ina😳
Ai yau ba xuwa xance bare club dan wannan daran na Aunty XEE ne xanje gida ina buqatar kwantawa in tsara mata kalamai. Na barku lafiya (ya fita) cikin nisha'di
FAWAS Yace naso naga Aymana Wlhi
RAMADAN yayi Murmushi Yace kanajin wani filing kenan dan baka xuwan axxiqi
Yace hmm watoh RAMADAN ina San Aymana Amma banajin xan Aureta Gaskiya. Kuma abin mamaki ta tsaya min arai kamar maiya
RAMADAN yayi Murmushi Yace har yanxu dai kana tana tare da wannan burin naka
Yace sosai ma kuwa
Damuwata 'daya a ina xan sami 'Yar Qauyan
Yace hmm yanxu dai muje in rakaka gun Aymanan Amma dan Allah karka matse musu 'ya dan abinda kayi shi xa'ama 'ya'yanka
Yace kada'de kana fa'da mana wannan Kalmar inda karatune nasan ni xanxo na 'daya pls muje dan Allah karkace komai
RAMADAN ya ta6e baki Yace toh Allah ya ganar daku......Qawata nashigo babbar harka fah😀
Gaskiya arxiqi da'dine dashi. Na samu wani Alhajin Abujah Wanda ya rikitani yan xunnan da tsabar ku'di har nera million 'daya.........

XEEE wacce take kwance tana jinyar xuciyarta da tatafi da tunanin KHAMIS Wanda ya hanata nutsuwa Sam.....
Aiko tanajin furucin SAILUBAH tadiro daga gado Tace what one million naira 😳
SAILUBAH tayi Murmushi Tace kema abin yabaki mamaki ko. Karya tsoratar dake dan yanxu aka fara wasan
Inaso gobe kixo gida ki gani ganin idanki
idan kuma kintashi xuwa kixo da Wannan qaramar jakar taki dan ki sami rabanki
XEEE Tace abin mamaki dama nasan burinki xai cika. Xaki ganni qarfe tara gobe yanxu ma dan dare yayine
SAILUBAH ta kwashe da dariya Tace shegiya XEEE taji maganar nera aiko goban xaki wanke idanki dasu
Tace na sani aminiyata idan ina tare dake ban wanke idona da naira ba ai babu ranar daxan wanke idan dasu
SAILUBAH tajah numfashi Tace ya kikayi da qaramin yaran naki
Tace hmm ina sane ai naqi kiranki dan ya burkitani
SAILUBAH Wlhi Wlhi Wlhi ina MASEEFAR SON KHAMIS Ya Xanyi

Nan takwashe Komai tagaya ma SAILUBAH.

SAILUBAH tayi mata dariyar rainin hankali Tace karkiyi yunqurin ki ransa. ki bari har sai shi yane meki akan ki bashi shawarar imba haka bah Wlhi ina tabbatar miki saiya baki wahala yadinga garaki
Tace Kinga ko kiran shi ya shigo a qaramar wayata kamar yasan hirarshi muke
SAILUBAH Tace yauwa. Na sanki da rikicewa kinutsu karya rainaki da yawa pls
Tace hmm SAILUBAH kenan bakiji yanda jikina yake rawa ba.
SAILUBAH tajah tsaki Tace Gaskiya kinada matsala XEEE da Takaici
XEEE tayi dariya Tace hmm Allah ya jarrabeki dasan qaramin yaro kiji fiye da yanda nakeji..........
Cikin maseefa Tace ba AmEEn ba 'yar is.......
XEEE ta katseta da cewa saida safe ta tsinke hirar tasu
SAILUBAH Tace tajah tsaki Tace Allah ya rabani da soyayyar qaramin yaro........


XEEE ko bajewa tayi agado tatattara nutsuwarta cikin bugun xuciya ta'dauki wayan KHAMIS Wanda saura ka'dan tayanke a karo na biyu

Tace hello
Yace inata kira Aunty. Allah yasa jin da'dine da lafiya da kwanciyar hankali ya hanaki 'dauka
Tayi murmushi Tace toh bansan me xance maka ba KHAMIS Amma ina cikin lafiya da kwanciyar hankali musamman mah yanxu
Yace toh madallah dama nakiraki ne akan.........
Sai kuma yayi shuru
Cikin sanyi XEEE Tace akan nabaka shawara kan budurwarka ko
Tace eh Aunty Allah yasa baxan takura miki ba. Wlhi xuciyata CE take san xuwa gareta yanxu gashi kuma idan naje bansan me zance mata ba
Shuru XEEE tayi kishi nacin xuciyarta.

Dama ace ina tare dake tana shafi gefan fuskarki na dawo dake daga tunanin da kika fa'da
KHAMIS ya fa'da Cikin sanyin murya....
[7:24PM, 19/11/2016] Rahamat Nalele 👯: XEE tajah numfashi Tace hmm ba tunani na fa'da ba kawai......
Yayi saurin katseta da cewa kar kiyi min musu Aunty inaso kawai naji me yajefaki cikin tunani
Taja numfashi Tace tunani nakeyi yanxu idan Nace kar kaje gunta baxa kabi umarnina ba kuma ni haka kawai Naji bana san kaje gunta wlhi kaje sai nayi kuka. shiyasa kaga nayi shuru
Kuma baxan iya gaya maka dalilin hakan bah

KHAMIS ya lumshe ido tare da gyara kwanciya kallo 'daya xaka mishi Kasan yana cikin wani hali na tafiya a cikin SO da qauna
Yace yanso ki gyara kwanciyarki
Tace nagyara
Yace haba Aunty. Me xaisa baxan bi umarnin ki bah.
Ki shareta kawai Wlhi ba xanje gareta ba na hakura. Dan da kiyi kuka gwara in hakura da ita gabaki 'daya dan nasan kukanki xaifi damun xuciyata fiye da soyayyar da nake mata

XEEE taqara qan qame wayan akunnan ta cikin muryar sanyi Tace ina sanka Qanina da xaka ha'kura da ita gabaki 'daya da sai nafi kowa jin da'di.

Yayi Murmushi yana raina wayo irin nata. Ga wata xaxxafar soyayyarta da take cafkar xuciyarsa
Yace LA
Idan hakan xai saki jin da'di Wlhi xan iya hakura da ita har abada Amma sai dai in xaki.....
Sai ya kasa qara sawa
Cikin murna Tace Amma sai dai me
Yace ina jin tsoran qara sawa ne Aunty.
Tace kafa'da man. Karka damu. Tafa'da da San jin furucin nashi
Yace ki bani minti biyu kacal Xanyi addu'a kafin in fa'da miki. Xakiji shigowar sako yanxu
Tace toh ina jira dan Allah karka wucce 2 minutes 'din
Yace angama Aunty....

Shuru XEEE tayi tana addu'ar Allah yasa ta mallaki KHAMIS a matsayin mijinta ita ka'dai. Dan yayi mata tako ta'ina. Sai juyi take

KHAMIS ko dariya yayi Yace yes my Luv Allah yasa Ki xama mata agareni
Sannan yayi rubutu kamar haka......

_xan ha'kura da ita gabaki 'daya idan har xaki mayemin gwurbinta. Xanso Ki xama mata agareni Ki haifamin yara kyawawa kamarki_

Saiya tura mata

XEEE najin shigowar sakwan tayi saurin dubawa....
Wani qara tasake cikin farin ciki ta kwashe da dariya......
Mamah tashigo hankalinta tashe Tace meya faru ne Zainab

XEEE Ta rungume maman tana Tace yau Xanyi kwanan farin mamah nasamu wanda yafimin Surajo
Din gure mata kai mamah tayi tajah tsaki Tace Nina 'dauka wani abunne Wlhi
Da dariya XEEE Tace aa ba Komai koma gun BABAH kawai
Fitta mamah tayi tana fa'din Allah ya shirya
XEEE ta koma gado tana da'da karanta sakwan nasa.
Kafin ta kashe wayan nata gabaki 'daya


Qarfe 11:30pm na dare SAILUBAH ta kwanta danyin bacci. Sai kuma tatuna bata tambayi Qanin nata ko yaci abinci ba
Nan tafara Ne mansa a waya. Sai kuma tatuna sunyi fa'da tajah tsaki da dai kiran nasa dan tasaba da hakan in bata kirasa ba hankalinta baxai kwanta bah
Lokacin sun dawo kenan daga wajan 'yan matansu FAWAS yayi gida shi kuma ya kwanta kenan yaga kiranta
Yayi Murmushi dan yasan abinda xata tambayesa
Sai yaqi 'daukar wayan yana ji har takira sau uku
Daga qarshema ya kashe wayan gabaki 'daya yabi lafiyar gado

SAILUBAH tayi kwafah Tace Wlhi in dai akan Alhaji Aminu ne sai dai kata fishinka tajah tsaki takwanta

Can takasa bacci sai juyi takeyi
Ta da'de da sanin idan RAMADAN yayi fushi da ita qaurace mata yakeyi na Wasu kwana Wanda hakan ba qaramin axaba bane agareta
Dan har ciwo takeyi na rashinsa

Salloli tadinga yi tunda baccin yaqi 'daukarta kamar yanda shima ya kwana Yana lafular


Washe gari Suna breakfast da Abbanta take bashi labarin Alhaji Aminu da kuma bashi qarin bayanai akansa kamar yanda yabata jiya
Da murna Abban nata ya kar6i takaddun gannun nata yana dubawa
Can ya kalleta Yace ai wannan yaran Malam Saluhu ne
Kiga ikwan Allah ban sanshi da wannan 'dan ba
Kuma yaushe yayi ku'di haka
Hmm Allah me iko
SAILUBAH Tace Abba Waye mahaifin nasa
Yace baxaki sanshi ba
Amma acan baya da nake da ku'di yayi aiki a qarqashina mutumin kirkine
Tace ayya.
Yace Naji da'di Sosai da kika bi umarnina kika kawo min Wanda kikeso. Karki damu xan nemi mahaifin nasa muxanta Tace toh
Abban nata na barin gidan tatashi dan xuwa lalla6o qanin nata
Sai matar Abban nata Tace xan samu dubu 'daya dan Allah agunki fita nake san nayi Amma ba ishash shan ku'di a hannuna
SAILUBAH Tace eh xaki samu na manta in gaya miki jiya nasamu ku'di ahannun shi Alhaji Aminun da yawa xan baki dubu 'dari biyu Amma Karki gayama Abba
Da wata irin murna ta rungumi SAILUBAH Tace Allah ya miki albarka kinji ai Wlhi ba Wanda xaiji
SAILUBAH Tace toh Allah yasa
Nan taje ta ibo mata mata tabata
Kana taje gun Kakah Tace Kakah na kawo miki Wasu ku'dine da wani Alhaji Aminu yabani
Tace aa ki barsu suyi miki amfani kinga ni ba abinda xasuyi min tunda na tsufah
SAILUBAH ta dafata Tace Karki damu dubu ashirin yaban shine nace bara na baki dan ba'abinda Xanyi dasu yanxu kuma kinga inna ba Abba baxai kar6aba xaice in mayar masa da ku'dinsa kuma kinga bakyau maida hannun kyauta baya shiyasa nakesan kikar6a dan Allah
Kakah ta waro ido Tace har dubu ashirin gaskiya ku'din yay yawa Karki sake kar6ar ku'dinsa haka
Tace toh. Da miqa mataXEE na tashi da safe ko breakfast batayi tabu'de wayanta tana san qara karanta sakwan masoyin nata......
Sai kuma ga kiransa ya shigo mata...
Ita kanta batasan ya akayi tayi saurin 'dauka ba da cewa hello.....

Kin hanani bacci jiya Aunty gashi yanxu yana damuna dan ma yau bani da lectures da abin ya ha'du min biyu. dan Wlhi baxan iya xuwa ba. Xuciyar tacika da tunaninki da fargaba. KHAMIS Yafa'da kamar xaisa ma XEEE kuka.....

Tace toh minene
Yace ina sanki ina qaunarki xaki Aureni
Tayi Murmushi Tace har na haifa maka yara masu kama dani kyawawa
Ina sanka KHAMIS
Yajah numfashi cikin farin ciki Yace na samu nutsuwa Aunty xan 'danyi bacci kafin naxo ganinki
Tace ina fatan xakayi mafarkina
Yace kwakwalwar tawa babu komai acikinta sai tunaninki. Mafarkin ki shi yadace da ita
Cikin murna Tace me xan ce ne dan Allah

Yayi Murmushi Yace da'dine yayi miki yawa my Luv. kawai ki kwanta kema xanxo miki cikin baccinki na tayaki hira. Kuma xanso Ki canja min Suna daga Qanina xuwa.........
Tayi saurin katse shi da cewa xuwa my sweetheart....
Yace yayi Sosai saikin ganni mun ha'du
(Toh ha'duwar XEEE da FAWAS kenan. Rahamat na gaisheku👯)Shuru SAILUBAH tayi cikin mamakin ganin kofar RAMADAN akulle da'alamar xai hukuntata ne kamar yanda yasa ban
Tayi kwafa xuciyarta nayi mata xafi tana kuma tsoranma kanta ciwo kamar yanda lamarin ya saba xuwan mata.
Da kuka tayi part 'din momynsa tana tambayarta ina jaye.....
Momy Tayi Murmushi Tace lefin me kikamai haka.
Tace Wlhi Momy bawani abun xafi bane Amma yake san hukuntani kamar yanda ya saba. danya samin ciwo😰
Khairat tayi dariya Tace Aunty LUUVAH wai yaushe xaku dena yin fa'dane ke da Ya RAMADAN ya dena miki haka yana saki kuka
Ta harareta tare da kallan Momy Tace dan Allah Momy ina yake.....


By Hajju
[20/03, 17:09] 80k: [1:12PM, 21/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR*👯*Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

Part 46 to 50

Momy ta qarayin Murmushi Tace ban san inda yaje ba SAILUBAH. Amma ya shigo 'daxo Cikin jin yunwa harna lalla6a shi yaci abinci daqar...

Goge hawayanta SAILUBAH tayi Tace toh bara naje waje ko Allah xaisa na gansa
Murmushi Momy tayi Tace toh Allah yasa ki ganshin
Khairat Tace nima futa xanyi Aunty mufuta tare

Sun fitoh harabar gidan ne SAILUBAH ta kalli Khairat Tace me Ya hanaki xuwa skull yau
Tace kai Aunty LUUVAH. Ya RAMADAN yana neman har gitsaki amma ai yau ba ranar skull bace
SAILUBAH tadafe kanta Tace na manta Wlhi

Haka suka dinga zagaye layin ba RAMADAN ba alamarsa.
Da takaici SAILUBAH tadawo gida
Tasan baxai ta6a yarda Su ha'du ba

Batafi minti biyu ba XEE ta shigo 'dakin nata
Aiko suka rungumi juna suka tafa. Kana suka xube agado
XEEE Tace yana ganki haka. SAILUBAH tajah numfashi kamar xatasa kuka Tace Wlhi duk na rasa nutsuwata XEE. RAMADAN yana gwarani san ransa imba bin umarninsa nayi ba baxai birni cikin nutsuwata bah.
XEE tayi dariya Tace nasan tatsuniyar gixo bata wucce ta ko'di. Basai kince Komai ba. Nasan yana san ne kirabu da wannan Alhajin da yashiga xuciyarki farat 'daya
Tace Wlhi XEE hakkane. Ya xanyi da RAMADAN kwata kwata baya san ya ganni da wani 'da namiji sai yayi duk yanda zaiyi ya rabani dashi
Gashi idan Nace bai'isa ba ya qaurace min ya samin ciwan rashin ganinsa
Gaskiya XEE sabo da mutum matsala ne. Ba kiji yanda hankalina yatashi 'daxu bah. Kwata kwata nane meshi na rasa alayin nan kaf
Ban ta6a ganin 'dan iska irin RAMADAN ba.
XEE tayi dariya Tace kice wannan karan mah saiya kwantar dake ciwo. Hmmm rikicinku yana tsamani
Ba wanda ya isa ya miki abinda RAMADAN yake miki
Shine yake miki duk iskancin da yaso kuma Ki rabu dashi
Shine Wanda idan yace miki Auntyna bar abu kaxa iyi abu kaxa kike yi kuma Ki bari
Gaskiya yana burgeni Sosai Amma daga dukkan alamu baxai samu kanki akan wannan Alhajin ba

SAILUBAH tata6e baki Tatashi ta 'daukoma XEE ku'da 'dan nan ta dire a gabanta

Tace ayanda na rikice 'daxo. Kuma jiya na kasa yin bacci wanda har yanxu hankalina atashe yake. Na kasa samun nutsuwa. Wlhi xan iya hakuri da Alhaji Aminu saboda RAMADAN
Da na'dauka xan iya jurewa Ashe abin ba haka yake ba
RAMADAN ya shiga raina Sosai. Ayanxu nagane farin cikinsa shine nawa XEEE....

XEEE wacce tawaro dan ganin tulin ku'din da yake gabanta sam dena jin kalaman SAILUBAH tayi dan tarikice da ganin ku'din Tace tab Amma wannan mutumin yaxo da xafinsa. Kataqi 😳

SAILUBAH tajah numfashi Tace nayi kyauta da dubu 'dari biyu da ishirin
Yanxu ki ibi yanda yamiki. Sai muje gidan marayu in basu yanda natsara sai muje wajan almajirai daga nan sai muje supermarket da biotic muyi siyayya ko
XEE ta washare baki Tace yayi yayi yayi SAILUBAH Gaskiya kin ha'du
Nan suka dinga tattaunawa har suka bar gidan

Kamar yanda SAILUBAH Tace haka ko sukayi
Sunje gidan marayu sun cike takaddu sun bada nasu tallafin inda SAILUBAH tasha kyakkyawar addu'a sukayi wajan almajirai nan ma sunsha saka albarka
Daga nan sukayi supermarket da biotic sukayi siyayyarsu suka dawo gida agajiya
XEEE Tace Kinga bara nayi gida dan yau ina da babban ba'ko KHAMIS
SAILUBAH tayi dariya Tace toh. Saiki shirya kalaman da xasu burkita shi
Tace hmm wannan shegen yaran aiya fini kalamai........


Bayan tafiyar XEEE Alhaji Aminu ya dawo ma SAILUBAH
Ta kallesa Tace Ashe Abbana yasan mahaifinka
Yace aidama na gaya miki
Ni dai yanxu fatana Allah ya temaken kixama mata agareni cikin wata 'daya
SAILUBAH tawaro ido Tace wata 'daya fah kace
Yace yes. Yayi ka'dan ne
Tace kwarai mah kuwa
Ya xa'ayi a wata 'daya in soka. Inji ka kwanta min arai. Yaushe na sanka Da har xan san ko kai waya cikin lokaci qanqani haka
Kuma mah ina da buruka araina wanda nakeso saina cikasu kafin nayi aure.
Kawai ka share batun na'dan wani lokaci kafin nan na sanka ka sanni

Ya kalleta da kyau. Kallo 'daya yayi mata ya gane yarinyar xatayi gaskiya. Xata fa'deta komai 'dacinta yayi Murmushi Yace xaki soni Amma agidana
Ban ta6a soyayya ba sai akanki
A tunanina SAILUBAH tsayawa soyayya atiti rashin wayewa ne. Akan me xan xauna in 6ata mana lokaci gurin so bayan Auranki xanyi
Me xai hana muyi duk abinda xamuyi agidanmu
Sam baxan ta6a tsayawa yaudararki ba.
Kiyar dani baxan ta6a yarda in 6ata miki lokaci abanxa ba.
Ina sanki. Xakiji da'din Aurena. Kuma xaki soni fiye da yanda xaki so kanki
Ina rokwanki da Allah ki yarje min in mallakeki nan mah da sati biyu
SAILUBAH ta kallesa Tace ragewa mah kayi.
Yace aike 'dince akwai burkita mutum
Wlhi tunda na ganki nadena samun bacci Cikin kwanciyar hankali. Duk juyi idan nayi tunaninki ne yake damuna.

Juya ido tayi Tace hmm Gaskiya sai nayi tunani dan bana san aikin gaggawa
Yace OK. 'daxoma mahaifina yake cemin xaixo ga Abbanki
Tace ba lefi Allah ya tabbatar da alkairi
Yace Ameen


Shuru SAILUBAH tayi a 'daki tana tsaqa da warwarwa
Shin ta AmEEn CE ne ko tabari na'dan wani lokaciXEEE na xaune kan kujera tana danna wayarta addu'a take Allah ya kawo mata sahibin nata yanxun kamar yanda Yace mata....
Mama Tace naga kinyi wanka kinci ado kuma kin xauna badai fita xaki da'dayi ayammar nan ba dai ko
Tace ba inda xani mamah kawai.....
Bata qarasa bah saiga KHAMIS yashigo harabar gidan nasu da motar shi
Daga window XEEE ta han goshi.
Mama Tace ga mutuminki KHAMIS
Tayi Murmushi cikin basarwa Tace bansan da xuwanshi bah dana fita shikenan yayi rashin sa'a
Mamah Tace aikowa dai......
Daidai nan ya shigo falan ya durqusa ya gaida mamah Tace lafiya lau yaran kirki ina ka baro RAMADAN da FAWAS yaran kirki
Yace Suna bayan layin nan wajan wani abokinmu nima inasan kar6ar wani abu ne gun Aunty XEEE. Tace ayya Allah yayi muku albarka. Yace AmEEn. Tatashi tabar falan
KHAMIS yabi XEEE da kallo ka'dan Yace my Luv Kinsan baxan iya sakewa anan ba ko.
Pls temakeni muje mota kona samu na gaisheki cikin nutsuwata
Cikin sanyi Tace idan naqi fah
Yace sai in saka miki kuka
Tace toh 'danyi ka'dan inji ya kukanka yake
Tashi yayi yana murmushi Yace ba ruwana. Ina san kiyi bacci yau cikin kunciyar hankali idan kuma nayi miki baxa kiyi shi cikin kwanciyar hankalin ba. ina jiranki amota
Har ya kai 'kofah ya juyo.
Idan kintashi fitowa kifito min da dariyar ki me sani qara sanki. Yana fa'din haka yaficce daga falan
XEEE tabishi da kallan so

Lalle 'da namiji bashi da kunya. Kuduba yanda KHAMIS ya rufe ido yayi fatali da matsayin da yake bata ada na yayarsa yanxu ya juya shi ya koma na Masoyiya.
Tayi Murmushi Tace Allah na roqeka idan da aikairi soyayyata da wannan bawan naka ina rokwanka kasa ya xama miji agareni ya soni fiye da San da nake masa
Idan ko ba alkairi acikin tafiyar Allah ka munsanya min da Wanda xai xama alkairi agareni.

Ahaka tafitoh dama ya bu'de mata qofar sai kawai tashiga tarufe
Yace ina wini my Luv
lafiya lau
da fatan kinkai yammaci lafiya
lafiya qalau
Yace toh Madallah
Suka 'danyi shuru ka'dan can Tace ya kake jina aranka ne KHAMIS
Yace kamar yanda masoya sukeji aransu idan suka fa'da soyayya.
sai ya kama hannunta cikin yanayin damuwa Yace na sanki ina qaunarki my Luv dan Allah ki riqeni amana.
Tace Kaine xaka riqeni amana
Bana san kishiya KHAMIS bana san in ganka da kowace mace ka temaken mu gina wata rayuwa dagani sai kai
Yayi Murmushi Yace na miki alqawarin inhar kika iya dani ba wata mace da xata mallakeni saike 'daya.
Tace Wlhi xan iya da kai Sosai masoyina
Yace toh Allah yasa

Can Tace wai ina RAMADAN ya shiga ne yau. Yace yata dama Aunty LUUVAH hankali ko
Tace sosai ma
Yace yana nan yana jinyar kansa. Ki share kawai. Dan kin san bayau suka saba ba.
Tace Hakka ne Amma fah kasan bana san damuwar SAILUBAH
Yace kar wani abu ya dameki. Kibari xan lalla6a yaje gareta
Tace dako ka kyauta.......


Qarfe Tara na dare SAILUBAH na tare da Abbanta itada Kakah yana gaya musu mahaifin Aminun nata ne yaxo 'daxu shida qannansa kuma sun xanta yasamu gamshash shan bayanai
Gashi yanxun sun bada kudin sadaki da nagani inaso da dai sauransu. Yaja nufashi ka'dan kana yaci gaba da fa'din
Saiki shirya na basu KE nan da wata biyu xa'a 'daura muku Aure...........
[3:40PM, 21/11/2016] Rahamat Nalele 👯: SAILUBAH ta waro ido da dafe qirji Tace kabasu ni
Yace eh dan sun nunamin yaran yana sanki Sosai kuma yana so ayi komai da wuri danshi ba maxaunaci bane

SAILUBAH Tace jiya fah na fara ganinsa Abba akanme xan Auresa da wuri haka dan Allah

Abba yajah numfashi Yace ko yau kuka gamu da juna tunda kika nunamin kina sanshi kuma nayi bankice akansa nagane yaran kirkine dole Ki Auresa yanda na tsara
Tace haba Abba......
Yayi saurin katseta da fa'din kar kice min Komai. Dan baxan canja maganata ba.

Da kuka SAILUBAH tabar falan
Kakah taja numfashi Tace nidai abi yarinyar nan ahankali banaso a matsa mata
Shuru Abba yayi mata dan yana kulata xatace abarta har susan juna....


SAILUBAH na kwance tana kuka dan Allah ya sani batasan ayi mata Aure yanxu
Can tafara kiran RAMADAN tana addu'ar Allah yasa ya kunna wayan nasa
Aiko bai kunna ba. Dan haka tayi firo da wayan takaicinta ya xaman mata biyu
Can Tatashi daniyar taqara xuwa gun Qanin nata......

Lokacin ko RAMADAN yana 'dakinsa shida FAWAS Suna gulmar wata yarinya da RAMADAN 'din ya burkitata yau
Fa'dama Fawas yake
Kasan kuna barin gurina 'daxu
Kawai saina fitoh dan shiga Jifatu.....
Basai kawai naci karo da ita ba.
Nace am sorry dan Allah bansan kin tawo bah
Ta kasa min magana
Niko na kwashe mata kayan nata na miqa mata ina qara bata hakuri
Kasan meys faru
FAWAS Yace aa
Yace dana kalli fuskarta sanda gabana ya fa'di
Bayanta Wasu manyane masu tsaranta
Kallo 'daya xaka musu Kasan ba imali atare dasu
'Daya daga cikinsu Yace kai Kasan wannan wacece da kayi kuskuran cin karo da ita.
Ayanda na lura suna da xafi
Sa6anin ita da takemin wani kallo me nuna alamun in ankare da ita
Ganin hakan yasa nayi Murmushi Nace Allah yajah da xamaninki gimbiya tauraruwa kuskure nayi hakan baxata qara faruwa bah
Tace ayya karka damu me sunanka
Nace RAMADAN
Tace suna me da'di. Xansu kaban number naka dan ka iya kalamai idan naji sha'awar hakan xan kiraka
Nace ba damuwa
'Daya daga cikinsu ya kar6i kayan ni kuma na kar6i number nata nakirata
Tayi Murmushi Tace saika jini
Nayi yaqe nace toh...
Muka rabu a haka
FAWAS Yace kyakkyawa CE ita 'din
RAMADAN yayi dariya Yace ina fa wani kyau mummuna da ita
Dana kalleta fah saida gabana yafa'di
FAWAS yayi dariya Yace saika shirya gaya mata kalamai idan ta kira ka
Kan yayi magana SAILUBAH tashigo 'dakin ahankali
Ta kallesa da muguwar harara.
Ya kafeta da ido Yace me yasa Ki kuka Auntyna
Cikin jin haushinsa Tace ban sani ba
Ina kashiga yau
Ya ta6e baki. Wani gu naje
Shine ban kai ka gaya min ba
Yace kinyi min lefi Auntyna ya xanyi in gaya miki.......
FAWAS Yace Barka da dare Aunty LUUVAH
Ta kallesa Sam batasan dashi bah Tace barka FAWAS ya Momynka Yace tana lafiya. Ya fa'di hakan dasan ficcewa. yana me cewa kasameni a mota
RAMADAN Yace toh Amma fah sai naji da Auntyna
Yace nasan ai wannan dole ne
SAILUBAH Tace me yasa kake san jefani cikin damuwa ne RAMADAN

Kallanta yayi da qarasowa kusa da ita ya kama hanunta Yace ko wani ne yayi yun qurin saki cikin damuwa saina 'dauki mummunan mataki akansa bare ni da Kaina
Ina San farin cikin ki Auntyna ki yarda dani.
Rai nane bai kwanta da wannan mumumin naki ba
Tace gashi har Abba ya basu ni wai nan da wata biyu biki da fashewa da kuka......

Arikice RAMADAN yasaki hannunta cikin tsoro Yace bar fa'da min dan Allah Auntyna pls
Tace na rantse da Allah mana
Kuma gaskiya ni bana san Aure yanxu
Durqu sawa yayi a gabanta Yace innalillahi-wa'inna'ilaihir-raji'un
Haba Auntyna me yasa xaki min haka
Xan iya rasa rayuwata akan hakan. ki temaken dan Allah. Yafa'da kamar xai fashe mata da kuka hankalinsa tashe
Cikin alamun damuwa ta durkusa. A gabansa cikin sanyi Tace me xaisa ka rasa rayuwarka
Ya kalleta idan shi jajur Yace nima ban sani ba....
Ta kama fuskarshi cikin tashin hankali Tace ka gayamin dan Allah pls fa'damin.....


By Hajju
[20/03, 17:09] 80k: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR*👯

*Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

*Bismillahir-rahmanurrahim*

*Part 51 to 55*

Tace hmm ina San ganinka yanxu.
Yace muna qauyan takai fah😳
Tace ko qauyan inane ina

Post a Comment

Previous Post Next Post