_DOCTOR_* _*SAGEER (Complete Hausa novel)

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


Fit...fit...Motoci ne suke faman hucewa A bak'in titi sanadiyar ruwa da ak'eyi. Wata budurwar yarinya ce k'e faman zanbada sauri har takai bakin wane gate, Nan ta tura A hankali saka kafarta da zatayi zuwa cikin gidan sai kuwa ji tayi an dak'a mata tsawa wacce sai da littafin hannun ta suka fad'i....

" Kee yasmin??? Cewar matashin saurayin nan!

" cikin tsoro da kuka tace kayi hakuri yaaa...

" Idiot kawai kalli ki sai kace almajira uban ina kuma kika tsaya...

"Cikin hawayen da batasan dashi ba tace kayi hakuri wallahi lesson na tsaya...ta kalli jikinta da gaba daya ruwa ya jik'ata....

" Wani mugun tsaki yajaaa sannan ya nunata da hannu ..Gashi yanzu na makara sai shigen son makarantar tsiya babu abunda kikasani to bari kiji a sannu sai kin daina makarantar sai dai kidinga wankau...

" fuskar ta cike da damuwa tana shiga tsakar gidan sai tayi karo da dr cikin hanzari tayi baya tana danAllah kayi Hakuri wallhi bansani ba shiyasa...

" Murmushi yayi yace yasmin sarkin tsoro,can kuma yace yaya akai ruwa ya zaneki???

" Shiru tayi hawaye na bin fuskarta babu ta yadda zatace masa su abida ne sukace bazata hau musu mota ba..

" Ki daina kuka kinji yasmin kinga kinfara zama 'yan mata kada ayimiki dariya kije ki canja kaya kinji idan nadawo zanbiyo dak'in mama kinji?

" Har cikin ranta tanajin dadin kalaman dr Amma kuma k'annan sa basa sonta kwata kwata...

" Wayar sa ce ke faman ringing cikin k'idan my love! Cikin nutsuwa ya dauka tare da fad'in Assalamu alaiki!..

" Cikin wata lausassar muryar ta tace bak'asona dr sageer yau 3days baka kirani ba sai dai kullum na kirawo ka? Ta saka kuka..

" Haba Ramlat menene abin kuka to bayan kinfi kowa sanin ina mutukar sonki!..

" Amma kullum kake nunamin aikin ka yafini mahimmanci gaskiya ni gwara ayi auren a huta wannan soyayyar taka kada ta salwanta ni...

" Dariya yayi yace oyaa to kiyi dariya naji!..

" Dariya tasaka sannan tace bari naje hajiya na kirana mayi magana anjima..

" Badamuwa ramlat ki kula da kanki kinji?

" i love u my doctor!!!

" baby same..cikin fara'a ya katse wayar tare da shiga cikin motarsa yana 'yar dariya..


Juya wa yak'eyi akan laushashiyar kujerar sa cikin sanyin office ya K'alli halifa yace kasan me bro??

" inajinka?

" yasmin din mama ina bala'in son yarinyar nan naso aci ta isa aure da kawai sai dai nafara neman auren ta....

" Halifa ne ya ajiye wayar hannun sa yace Doctor sageer kenan ka fiye barkwanci wallahi!!! Hahaha in banda idonka ya rufe ina kai ina yasmin a jss 3 fa take kai kuma kana babban likita mai aji wanda duniya tasan da zaman sa...Kuma yaudarar barister ramlat zakayi ???

" Kai Abokina nagartar mace ake dubawa ba kyau ba, addinin yasmin ko mu da muke manya iya abunda mukeyi kenan,ga nutsuwa kalmar hakuri ta aure bak'inta duk gidan nan private school sukeyi amma baffa dan bashida kudi babu wanda yace bari yasaka yasmin a irin makarantar yaransa sai a gawamnati ya sakata kuma bata taba damuwa ba... maganar ramlat kuwa ka ajiyeta gefe!!!

" Tabbas hakane daman ai ka guji wanda kayiwa alheri...

" Let talk later ina da cs yanzu...

" To Dr see u later...

Yasmin yasmin yasmin bakyajina ne??

" Baffa sallah nakeyi...

" yauwa yarinyar kirki inafatan mahaifiyar ki tagaya miki sak'ona???

" A'a bata gayamin ba..

" To yasmin ke yarinya ce mai tarbiya kinga kuma bani da wata d'iya sama dake yar uwarki tayi nisa tana aure a benin kullum tunani na akan naga kinyi karatu ne...

" Cikin murmushi tace baffa kadaina damuwa dani wallahi banda wata matsala kai dai kacigaba da yimin addua...

" Yasmin inason zan kaiki boarding nasamu kudi Akallah wanda har kigama zan iya biya zuwa litinin sai ki shirya d'an Alhaji sule da yaranshi zaku tafi...

" Toh baffa Allah yakara budi nagode zanyi yadda kace...

" Dak'in mama tashiga ta rungumeta tana kuka dagota tayi tace daina kuka auta babu yadda banyi da mahaifinki ya kyali k'i agida ba,...

" Mama banason nabarki, ke daya duk gidannan basason mu kar susaka miki damuwa...

" Dariya tasaka tace haba auta babu mai samin damuwa kikwantar da hankalin ki kinji...

" Tohm bari naji gurin Anty zulai...

" Tunda tafito maryam ke faman hararar ta har tazo hucewa ...

" Sannu da gida maryam ya makaranta...

" bansaniba 'yar talakawa kudin makaranta ma ubanki yakasa biya miki haka zaku kari ai sai dai talauci ya kashe ku...

" Adaidai lokacin dr sageer yayi parking motarsa maganar data duk'i kunnan sa shine baban ki ma sai mun sa an koreshi a gadi...

" Yasmin ce tace Ai shi arzuki bako ne wanda baizo masa ba shine bai san saba wanda kuwa yazo masa to yasan zai kari, kuma duk iskancin ki kada ki kara saka iyayena tunda naga ke islamiyar taki bata amfana miki da komai ba, banza mara hankali kawai...

" wani dadi yaji ashe yasmin ta iya fada lallai...

" Maryam ce ta wanka mata mari wanda sai da dr yajiyo...

" Sai da ya kifa mata mari har guda 3 sannan yace baki da kunya ke?? to nakara ganin kin zagi yasmin Allah sai nayi miki illah shige kibani guri nonsense kawai...

" Kuka tasaka ta shige tana wallahi sai na gayawa mamee...

" Hannun yasmin dr ya riko yace yi hakuri 'yar kanwata sannan yasa hannun sa ya goge mata hawayen fuskarta sannan yace muji nasiyo miki laptop saboda naga kina kokari a makaranta...

" A'a ni kabarshi nagode sannan ta shige gurinsu...

" yajima yana kallonta sannan ya tafi ....


Kasancewa yau litinin yasmin ta shirya domin tafiya boarding sai kuka takeyi har suka tafi itada baffa mama sai addua takeyi mata...

" yau da daddare dr sageer yace mama ina auta ne??

" Auta tayi makaranta kwana ai..

Boarding??? Why aka kaita haba mama..

" kayi hankali kada baffa yaji...

" Fita yayi cike da damuwa zuciyarsa sai zugi takeyi masa gashi ko zai mutu baffa ba zai kaishi makarantar ba...!!!yanzu yaya zanyi da kaunar yasmin???

ASALIN SU...

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:03PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 

5-10

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

http://deejarhberver.wordpress.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Alhaji Rabiu ba fulatanin mutum da yazo daga garin bande zuwa garin Adbas ya k'anzo garin domin k'awo dabbobi cikin hukuncin Allah tun yana zuwa sau biyu a wata har kasuwancin sa ya habaka ubangidan sa yace zai dinga yimasa zaman kanti anan ne yabar kiwon da yakeyi..

Cikin shekaru shima Allah ya buda masa sai yasamu daukaka takai baya bada kaya sai dila dila, sanadiyar matansa biyu a lokacin hajjo da asabe kowaccen su tanada yara bibbiyu acikin yaran hajjo akwai kawu maikal da suwaiba, ita kuma asabe tanada haruna da isa kowannen su yafi shekara 20 a lokacin mahaifin su rabiu yana bala'in jidasu har takai mutane suna musu kirari da 'ya'yan gata. sanadiyar garin sakoto dayaje daurin aure sai Allah yasa yaga hajiya sadiya har Allah yasa suka dai daita akayi aure yakawota cikin gidansa, Nan ne fa mata biyu suka addabeta har abun yafara isar ta.

Lokacin da ta samu cikin baffa tundaga lokacin Alhaji rabiu yake mata hidima abun yana bawa maikal da haruna haushi har takai suka bayyana bayan lokuta ta haihu bata kuma dade ba Allah yayimata rasuwa tabar baffa a hannun su asabe babu irin azabar da baisha ba mahaifinsu kuma yana sansu bayan wasu shekaru kowannen su akayi masa aure, bayan shekaru sai aka shirya tafiya zuwa wata kasar inda maikal da iyayen nasu gaba daya suka rasu... tunda lokacin haruna da isa suka kwashe gadon suka barwa baffa dan wani part ita kuma suwaiba suka bata dubu 50...

Hajiya suwaiba itace babbar 'ya agidan tayi auren fari sai Allah yayiwa mijin rasuwa daga nan sai tadawo gidansu tare da d'anta sageer yasha fama kalakala amma haruna ya daukeshi lokacin da tayi aure,ta kan cewa baffa kadaina damuwa da lamarin yan'uwan domin su sunyi asara...

Haruna bayan sageer dayake roko akwai yarsa mace abida da maryam sukenan Allah yabashi amma sai mugunta da zalunci atattare dasu ga kuma borin kudi yadda kasan babansu ke bugawa...

Isa kuma yanada yara 3 akwai bilal akwai jafar sai kuma kubra,duk cikin yaransa yana sangarta bilal shine sanadiyar lallacewar shi baya ganin kowa da mutunci sai bin mata da kashe kudi...

Baffa kuwa yanada yara biyu Aisha itace tafarko tun tana karama hajiya suwaiba ta dauketa ta tafi daita benin acan ma ta aurar da'ita, sai yasmin daga nan matarsa bata kara haihuwa ba...

Baffa yasha wahala kala kala arayuwarsa bama lokacin dayace sai yayi karatu dan kudin da yake samu a makaranta da hidimar iyalai yake tafiya, yan uwansa haruna da isa ko kallon arzuki basa yimasa kuma Allah daya bashi yasmin babu ruwanta ba kamar yaransu ba abun yakan basu haushi wataran ko kudin zuwa wajen gadi bashi dashi, watarana suna zaune da mama yake cewa wai ace ni mai kwalin masters amma gadi nakeyi sai yasa kuka...
Yasmin sau ta kalleshi tace baffa Ai lamarin na Allah ne inshaa Allahu wataran sai kazama wani kamar yadda yan uwanka suka zama wasu...

Yakanyi dariya yace Yarinyar kirki Allah yasa, mama tace ameen...

Yasmin yarinya ce fara amma irin siraran nan, ga kuma hanci kina ganinta kinga jik'ar ba fulatani, Babu ruwanta tun tana karama kawayen ke ce mata 'yar aljanna saboda hakurinta, lokacin da take aji biyu a islamiyya kwata kwata bata gane karatu hakan ya kansata kullun cikin kuka har mama ta gane sai tafara tambayar lafiya?? Ta sanar daita halin da take ciku daga nan tace ba kuka zakiyi ba addua zaki dingayi nima zan tayaki inshaa Allahu zaki fara fahimta, "Allah to yasa kamar wasa tana zuwa makaranta tana addua cikin shekaru 2 sai gashi tafara karbar kyauttuka, su abida maryam kuwa da kubra sai ma tsanarta da suka karayi haka ta dinga rayuwa cikin kuncin rayuwa. A kwai lokacin da bata da ikon zaman gate anayi mata karatu sai kiga bilal yazo ya zaneta ita kuma aduniya ta tsani bilal saboda zaluncin sa,Dr sageer kuwa irin hidimar da yakeyi masu takanyi masa Addua sosai duk da karancin shekarunta amma bata sakewa da kowa, tana kallon yaran gidan za'aja su amota amma ita sai dai akafa,tana makatantar gamnati amma su sunayin ta rabin million kullum burin su su zageta dalilin haka mahaifinta yace zai kaita boarding ko tasamu ta huta, Mahaifiyarta taso ya barta ta cigaba Amma ina yaki hakan nasa zuciyarta k'una...

Cigaban labari...

Dr sageer ke faman juyi akan kujerar sa ta office babu abunda ke damunsa irin tafiyar yasmin kai yanzu ba zanga kyakyawar fuskarta ba kullum ga lafazunta mai sanyaya zuciya, har khalifa ya zauna akusa da mashi amma bai kulaba...

" Haba doctor wannan tunani ince dai lafiya???

" Jiyowa yayi yace ina kuwa lafiya? Baffa ya kai yasmin makaranta...

" To a gaskiya dr zangaya maka gaskiya ka ajiye maganar yasmin a agefe kafara zancen bikin ka...

" Hmmm daman ai na lura kafi son ramlat, to bari ingaya maka yasmin tsoka tace babu ta inda zamu rabu ni inaso ka binciko min boarding din da suka tafi...

" ai nasanta ko yabzu sai na rakaka sai dai nisanta...

" yanzu kayi magana mutumi na ina godiya ran sunday maje...

Yasmin dake aji azaune tana karatu kamar daga sama taji anyi mata sallama tana daga kanta taga wata yarinya ce da bata huce suyi shekaru daya ba cikin murmushu ta amsa mata sallamar...

" sunana yusra nima last week nazo skull dinnan kuma naga babu ruwanki ga son karatu ko zamu zama kawaye?

Murmushi tayi tace ni yasmin sunana, ina kuma fata zamuyi kawanci nagari??

" inshaaAllah daga nan suka kullah kawance...

Mumy ce tafito zata tafi office tace dota?

" Tace yes mum har kinshirya?..

" Eh ramlat idan dr yazo kya gaishe shi..

" ohh mum bakyason dr sageer dina wallahi....

" haba my barister ni kuwa nake son sa...

" rungume mumy tayi tace har naji dadi lurv u momma...

Yau sunday kowa acikin makarantar ana kawo musu visiting kowacce tana shigowa da abubuwa amma yasmin tana gefe bata cewa komai, alokacin dr yazo yana zuwa yace yar aljanna kamar daga sama ta ruga ta rungumesa tace yaya??

" Dr sageer ne yaji dadi yadda tayi murna da zuwansa cikin murna yace yakike kanwata?kina dai karatun ko??

" inayi sosai wallhi ga mama da baffa?

" Suna gaida ke! Yasmin yasmin?

'Naam ?? " kinsan ina sonki ko?

" eh tace.." to kada ki kula kowa kinji da niyar soyayya kinga yanzu karatu kikeyi...

" Tohm bazan kulaba, nagode da zuwanka lokaci yayi..

" sawa yayi aka shigo masa da abubuwa da yakawo masu yawa sannan yace duk nakine..

" Nagode Allah yabiyaka sai anjima..

" har tayi nisa yace yasmin??.

"Naam..

Kikula da kanki kinji?

" Tohm tace sannan aka shigar mata da kayan..

Tundaga nan ya huce gidansu barister ramlat cikin fara'arsa yashiga palour tana zaune tayi bala'in kyau, yanayin saĺlama ta miki...

" to bakin munafuki bakin dan iska yaudarata dakakeyi to Allah ya rufamin asiri murabu tu daga yau...

" haba ramlat me yayi zafi haka??

" dan iska mai bin mata fitar min agida...

" kifa mata mari yayi see this stupid kika kara jifana da zafaffan kalaman ki wallhi sai na hukunta ki, kuma daga yau babu ni abu ke sannan yafita rai abaci......

Cikin kuru ruwan kuka ta nunashi daga nan kuma tafara nashiga uku inason ka sagee....

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_

_Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

*i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com
[2:04PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 10-15

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


Kuk'an da barister ramlat ke famanyi yasa gidan gaba daya ya dauka, adaidai lokacin da momy take kokarin shigowa gidan sautin kukan 'yarta tace yakara firgeta ta cikin sauri da hanzari taisa cikin gidan nan ta tarar da ramlat a shaime tana wasu irin maganganu, dotar??? What wrong with you? Ya'ilahi.....

" Rungume mumy tayi sannan tace baya sona mumy yace mun rabu wallhi zaki'iya rasani akan dr sageer,mumy please kibashi hakuri kuskure nane...

" Ya'ilahi me kikayi masa? Always ina gayamiki kina iya magaba kina barister amma u need to change your words namiji bazai dauka ba....

" Wallahi Rabia ce tace yaudarata yakeyi if yazo naci masa mutunci zai daina kuma zai tsorata....

" are u mad ramlat? Sau nawa ina cewa kirabu da rabia ba mutuniyar kirki bace ba, kuma ke ina ilimin ki? Mtseww ke kika jawowa kanki dan haka sai kiyitayi....

" mumy please karkice haka haba mum please ki bashi hakuri please mum!!

" Har cikin zuciyarta ta tausaya mata especially tafita hayyacin ta hakan yasa tace ke zaki shawo hankalinsa not me tashiga daki...

" cikin wani yanayi da fargaba ta dauki wayarta tafara kiransa ta kirasa yafi sau 10 amma bai dauka ba.....


Yasmin ke faman karatun Al kurani malamin math ya shigo nan yayi musu sannan yabafa class work duk wanda bai iyaba bulala biyar ce, yusra kawar yasmin kwata kwata bata iya ba gashi tarasa yadda zatayi yasmin data lura da hakan sai ta bawa yusra littafinta ta karbe nata tana gama solving a tsoroce ta mika mata nata...

" Duk class din da yafara marking mutum uku ne kawai sukaci nan ya dinga duk'an kamar an aiko shi...

Yusra ce tace godiya nakeyi kawata kin taimaki ne sosai...

" yasmin ce tace bakomai kawata malamin math din nan mugune wallahi taso muje na koyamiki yadda ake solving din..

" Nan suka tafi suna 'yar hirar su can irs teacher yace yasmin?

" jiyowa sukayi suka gaishe shi cikin murmushi yace kina dai lafiya ko?

" cikin rashin fahimta tace eh sai anjima sukayi gaba, yadade yana kallonsu har Allah yasa suka huce wasu senior dinsu wata daga cikin su tace kee yarinyar nan zo?

Tohm gani inji yasmin..

" ga kayana kije ki wanke min kinji...

" Tohm shikenan, zata karba tace au ashe kinada hankali barshi nafison yarinyar da zatace bazatayi ba.....

" Tohm nagode suka karasa hucewa,yusra ce tayi tsaki gaskiya kinada over hakuri yasmin ke komai babu ruwanki ???

Maryam ce ke cikin motar saurayin ta sai rangwada takeyi tana wani narkar da murya abun sai wanda yagani, Adaidai lokacin ne dr sageer ya danno kan motar shirun da yaji anki amatsa daga gurin gate yasa shi sakko wa daga motar cikin bacin rai,maganar da zaiyi yaga maryam zaune saurayin ta yana kokarin taba hannun ta sai dr sageer yayi maza ya bude motar cikin zafin rai ya k'ifa mata mari menene haka dan ubanki...

" Cikin bacin rai tace haba yaya wannan wani irin abu ne??

" uban wanene wannan 'yar iska wannan samarin banzan kike bi??? Dan ubanki shige gida sannan ya juya k'an saurayin ta cikin zafin rai yace idan nakara ganin ka kofar gidannan sai na ballaka wallahi dan iskan banza da wofi....

" simsim ya shige motarsa ya gudu...

" Wallahi mamee watarana sai na karya maryam kina ganin iskancin da tayi amma bazaki hanata ba???

Mamee ce tajiyo tace banson takura banson shishigi kai uban matan dakake hulda dasu waya sani??? To kafita harkar yarana ko sokakeyi su zama kamar yusra babu mai shinshinasu??

" Abida ce tace mtseeww mamee kyale wannan yayan bashida waweyyen kai ahaka dan boko sai kauyen ce???

" Tashi yayi zai daketa ta ruga daki, lallai mamee nagode da kalaman ki kuma kisani uwa na daukeki duk rintse idan naga k'annina sun shiga sun kauce hanya zan musu nasiya in gaya masu gaskiya sannan yafita daga dak'in....

" tsaki tayi tace too muzuba nidakai muga wanda bai fasaba mara kunya ke kuma ki shige dak'i saura naji kinkara futa...

" Tana shiga ta k'ifa k'anta ak'an gado tafara kuka...

" Abida ce tace lafiya maryam ko dai ya dak'i kine??

" wallahi sister ina bala'in son ya sageer wallhi inasonsa narasa yaushe soyayyarsa ta shige ni sannan ta goge hawayenta tace please karki sanar da mamee...

" yusra kenan ke dai mutafi...

Tabbijan lallai kina cikin wahala hahaha wannan k'olon gardin kikeso ga alhajin birni nan!

" banson iskanci abida banson haka ki iya bakin ki nagaya miki...

" Allah ya baki hakuri son koko daukar rai...

Bilal ne ya K'alli mahaifinsa Alhaji isa yace dad wancan baffa ya biyaka kudin ka kuwa??

Ina ai zuciyarsa ta mutu dubu 20 ake basa kudin gadi ina yaga kudin biyan dubu hamsin??

" Yasamu kudi ai tunda yakai 'yarsa boarding yakamata gobe ka kunna mada wuta yabiyaka...

" Angama my son kai dai kanason kaga sun wulakanta kamar yadda mukeso kenan??

" Kwarai kuwa ko kadan banaso sufimu...


Baffa ke lazumi ak'an dadduma,mama ce tafito tace sannu da hutu maigida...

" k'allonta yayi yace yauwa uwargida lafiya dai??

" wallahi kaga nakasa baccin tunanin kada 'yan uwanka su cimaka mutunci akan kudin nan nasu dubu hamsin...

" To yazanyi? Wallahi banida hanyar samu albashina ma dubu ashirin ne kuma kinsan duk naci bashi banga ta 'inda zanbiya ba...

" Ya kamata ka kokarta dan Allah wallahi banason naga suna hayagaga...

" kinfi kowa sanin ni bana maula ballantana nace abani kuma bana rok'o ballanta nakarba,kuma kinsan sun batamin suna babu mai bani bashi,Amma ki kwantar da hankalinki Allah zai bayar da yadda za'ayi...

" To Allah yasa,bari nagyarawa yasmin dak'inta naga gobe zata dawo...

" yauwa goben in Allah ya kaimu kiyimata tuwo danAllah tunda tanason tuwo kuma gobe Aisha ma zatazo sai ayi mata d'an wani abun...

" cikin jindadi tace Allah yakawo mana su lafiya...

Dr sageer ke k'allon 'mbc 2 yana kallon wani vampire hankalin sa rabi akan tunanin ramlat yake tabbas yana son ramlat amma abun yafara bashi tsoro har tafara zargin sa, shiru yayi yana wani tunani har wayar sa tafar ringing cikin murmushi ya dauki wayar ayayin da yaga mahaifiyar sa ce...

" Assalamu alaikum Sageeru???

" Cikin girmamawa yace Allah yakara lafiya hajiyata yakuke ya benin??

" yanzu abunda kakeyi ka kyauta sageeru yanzu bazaka fito da mata kayi aure ba ehhh???

" Haba hajiyata wanene ya tabomin ke, kuma hajiya har nawa nake?? Gaba daya fa kwanan nan nafara aiki???

" kayimin shiru kafin raina yakara baci shekara 30 da daya fa zakayi shine yaro...tun kana karatu nace kayi aure sai kacemin wai ai bakada lokaci sai kagama yanzu ka gama har kazama tsohon ma'aikaci amma katsaya wasa haba sageeru bakaga kanninka na uku yayi aure ba, ko sokakeyi ayimin dariya???

" Haba hajiyata wallahi zanyi ke dai kicigaba da yimin addua nasamu mata tagari?

" Addu'a?? Wallhi babu ranar da zanyi sujjada face na kira sunan ka sageeru ina jimaka tsoron zamanin nan mutum yayi auren ya yacika ballantana ku yaran zamani...

" Hajiyata ki kwantar da hankalin ki wayata tagaba dake inshaa Allahu ak'an aure nace...

" Yauwa ko kaifa Allah yayi maka Albarka yakuma tsaremin ku sharrin mutum da Aljan..

" Ameen hajiyata Allah yakara lafiya agaida su hammad da nazifi inanan tafe inshaa Allahu...

" Yauwa dan kirki zasuji kahuta lafiya kace ina gaida baffa da yasmin..

" Tohm inshaa Allahu..


Yusra ce tace oh tasmin akwana atashi babu wuya kinga saura shekara daya mugama, muna dawowa kuma sai waec da neco ko?

" Shiru tayi tana tunanin baffa tasan bashida kudin biya mata tayi jarabawa hawayenta ta goge tace eh hakane...

" Wallahi yasmin akwai abunda ke damunki sosai ke mutuniyar kirki ce Dan Allah ki taimaka kigayamin bakisani ba ko nakawo miki mafita kinga daga yau bazamu kara haduwa ba sai bayan hutu...

" Cikin murmushi mai kama da damuwa tace yusra bazan dawo makaranta ba...

" saboda me yasmin??

" saboda baffa na baida kudin biyan jarabawa idan yasamu nan gaba sai nazana dan bazan matsa masa ba wallhi....

" haba yar'uwata kada ki damu kamar kin zana jarabawa menene amfanin k'awancen mu idan bazamu taimaki juna ba...

" Allah sarki yusra nagode to Allah yabiyaki ke da iyayenki da irin dawainiyar da kukayi dani,wanda mukazo tare ma basa kulani ballantana kuma ita yayartawa...

" Bakomai ai daman naka yaki ka wane ya soka!..

" Tabbas hakane zomuje muyi alwala sai mu huce masallaci ko?..

" Ehhh..

" Ameen yace..

Barister wai yau lafiya kuwa ba walwala gashi kamar baki da lafiya??

" Wallhi munyi fada da dr na shiyasa nakasa sukuni yak'i daukar wayata yau kusan 5 mouth ko ta kaina bai bi nayi masa text akallah sunyi 50 wallahi "no reply i really love my dr i don't think zan rayu babu shi wallhi I so much lurv him kinsan dai kauna to itace a raina kuma ta dr ce wallahi"..

" Ayyah ni zan kokarta naga na shiryaku inshaa Allahu bani number dinsa na kirasa naji...

" cikin rawar jiki tabata sannan tace amana Amal karki yaudareni kiji tsoron Allah...

" Ramlat kenan nifa saura 1mouth biki na kuma dan Allah zanyi miki wallhi...

" Nagode nagode sosai...


Daidai misalin karfe 3 yasmin ta sauka a mota bismillah tayi sannan ta bude gate din gidan su cikin annashuwa da kuma farin ciki, maganganun da suka dak'i kunnuwanta yasa ranta ya bace cikin sauri tafara tafiya...

" Alhaji isa ne kefaman cewa wallhi yau sai kabani dubu 50 d'ita idan bahaka ba wallahi kotu zata rabamu banza asararre mai jinin tsiya wanda dubu daya take gagarar sa...

" cikin hawaye baffa yace haba dan uwana kayi hakuri dan Allah wallhi ina samu zanbaka...

" bilal ne yace kaji tsohon banza hhahaha...

Yasmin ce ta ajiye akwatin tacikin zafin nama (Daman bahaushe yace mai hakuri bai iya fushi ba) kai bilal iya bakin ka kasan wazaka zaga idan zasuyi kabarsu suyi su biyu...

" Gaba daya suka jiyo suna kallonta takara ktau ga wata kiba datayi ga halittu ko'ina sun ciko abun dai bazaka ce yasmin bace sai ka kara kallonta sosai...

" ke yasmin ni kike gayawa haka...

" nunashi tayi da hannu tace kai bilal idan kanacin kasa to ka kiyayi ta shuri ubana ba sa'anka bani kuma kakara zagensa sai ranka ya baci wallahi...

" Alhaji isa ne yace shigeya 'yar iska yimun shiru dangin talakawa idan kin cika kinason uban naki to sai kibiya masa kudin. ...

" Jakarta ta zuge tabashi dubu hamsin sannan tace tozarci badai akan mu ba kuma ni inada tarbiya bazan ci maka kala ba Amma ina fata Watarana ku gani abunda kukeyi...

" kallonta yayi yace shigeya karuwa inba karuwanci kike ba a'ina kika samu kudin nan...

" tsaki tayi tace nanawa kenan ance da bunsuru dan akuya?

" baffa ne yace shige muje shige muji yasmin...

Bilal kuwa ranshi ya baci shida mahaifinsa suka fita basu so hakan ba...

" mama ce tace daman malam nagaya maka kasamo musu kudinsu gashi kaga yadda takaya...

" yasmin ina kika samu kudin nan har dubu hamsin???

" Nan tabashi labarin yusra da kudin da mahaifinta yabata yace tabawa babanta abiya mata kudin jarabawar ta..

Allah sarki mutanen kirki mungode nan baffa yace banson fitsara yasmin ko gaba kada kikara tanka musu kinji? Duk abunda sukeyi zasu kwashi kashin su a hannun su...

" Tohm baffa bazan karaba inshaa Allahu..

Bayan sallah magriba yasmin da mama suna bangaran su a soro a zaune dr yana dai dai kofar zai shigo sai yaji yasmin tana fadin..

" Ni nahakura da jarabawar mama zamana zanyi bazan koma ba kudin dasuka bani naje nabiyawa baffa bashi domin kare mutuncin sa...

" karki damu yamin Allah zai hore kinji murmushi tayi tace kems ga chanjin kudin kya siya wani abun...

" yasmin kenan Allah yayimiki Albarka...

Doctor tunda yaji kalaman yasmin hankalinsa ya tashi nan ya sanar da principle din yaturo masa da Account number yatura kudin jarabawar kamar daga sama yaji wayar ramlat cikin yanayi yace hello?

" kuka tasaka masa kayi hakuri dan Allah hubby please nasan nayi maka laifi wallhi u are my life..

" Ya huce ramlat Nima ina sonk'i sannan ya katse wayar...

" Yasmin tana zaune a k'an k'ujera sallama taji sannan ta daga k'anta yaya ina yini???

" ah kanwata k'inzama 'yar dumama ke da boarding ke ramarwa ke kinyi kyau...

" Murmushi tayi tace Allah yaya?

" Wallahi kam nayi missing dinki sosai...

" Shiru tayi sannan tace yaushe ne bikin naku ne da barister?

" Gobe za'akai k'udina nida barister inshaa Allahu...

" kai mashaa Allahu, Allah yasanya alheri zamusha biki ashe?

" inshaa Allah please ki dafamin indomie zandawo anjima kinji??

" Tohm shikenan..

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:06PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 15-20

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yasmin kin dora abincin dai ko?

" Eh mama,har nagama ma dr ne yace na dora masa indomie yanzu zai dawo...

" Ke dai jininku ya hadu da sageeru bakamar su abida ba?

" Suma dan basajin magana ne..

" Lallai yasmin kinsamu bakin magana, Naga kema jiya fad'a kukayi da bilal?

" haba mama yaza'ayi ina gani ana zagin baffa nayi shiru ni wacce irin yarinya ce?

" Ai gwara da kikayi masa magana wallahi bilal bashida kirki babu wanda yake gani da gashi agidan nan...

Kamar daga sama sukaji sallamar Aisha dagudu...

" oyoyo oyoyo yaya Aisha sannu da zuwa cewar yasmin..

" Ai bakida kirki yasmin ace kina kanwata sau biyu kika taba zuwa benin dubi yadda kikayi kyau, kuma wai mama kina ganin ta?

" ke dai shiga muji ki huta ke da kikasha hanya...

Suna shiga palour ta durkusa har kasa tace ina yini mama?? Kuna lafiya??

" wallahi lafiya kalou yasu mujibat da hamid duk suna lafiya dai??

" lafiya kalou wallahi ina baffa?

" baffa yana gurin aiki ai sai yamma ke da ganinsa...

" yasmin ce tace kinsan garin naku ne nisa shiyasa baya burgeni...

" k'injiki ai ke a kaiki mambila naga tsiya..

" ke dai dakikayi auren nisan inshaa Allahu ni bazanyi ba!..

Dr sageer ne yashigo direct kitchen ya huce dan yasan yasmin tagama ta ajiye masa...

" Mama ce tace ke yasmin ba kauri nakeji ba??

" wayyoo indomie din dr cikin sauri ta isa kitchen din ta tarar dashi atsaye yama kasa magana...

" cikin garaje ta riki tukunyar ai kuwa sai tasaki saboda zafi sauri yayi ya riki hannu subhnlhi badai ki kone ba ko??

" Kayi hakuri wallahi ina hira ne shiyasa ta kone...

" Kallonta kawai yakeyi cikin wani irin salo da sai da taji wane yanayin dabata taba jiba acikin jikinta...

" Murmushi yayi yace bakomai bari naje na siyo wani abun...

" sai tace ai mungama abinci kaje daki bari nazubo maka...

" jikin wani salo yace mijinki yahuta yasmin...

" Shiru tayi masa batare da tace masa k'alaba..

Mamee ce tace wai ke maryam menene haka tun safe kike abu daya in anyi magana kiyi shiru meke damunki??

" Gyara zamanta tayi tace cikina ke ciwo..

" bari nakirawo sageeru sai yabaki magani inaji yana cikin gida ai...

" can tace mamee nawa aka kai kudin auren dr?

" dubu dari biyu mana, ansaka wata daya bikin...

" Cikin sanyin murya tace Allah sarki ...

Aisha ce tashigo part din su mamee tare da yasmin dr yana bayansu Assalamu alaikum hajiya mamee menene duniya???

" Tsaki tayi tace kin bayana kenan uwar magana lafiya dai kikazo ince ba auren naki ne ya mutu ba??

" Aisha ce cikin siyasa tace ina auren mu zai mutu naku bai mutu ba kuna soyewarku...

" Ai nayi tunanin auren ne ya mutu ai kizo kukarawa baffan ku wani hawan jinin???

" Ina ai igiyar aure Allah kadai ke rabata mutum komai shidancin sa bai isaba...

" Tsaki takaraja ciki da tsanar Aisha da yasmin can tace sageeru Maryam babu lafiya fa?

" Yasmin ce tace yaya ana magana?

" Allah yabata lafiya anjima tashirya driver sai ya kaita asubuti ai..

" To shikenan ina surukar tamu??

" tananan tana gaidaki...

yasmin ce tace yaya Aisha tashi mu tafi...

" Sum sum sum dake uwar munafukai daga zuwanta zakice tatashi ku tafi to takiya...

" yasmin dai batace kalaba, Aisha tace ohh naga ranar da zaku gani wallahi in banda zumunci mai zai shigo damu??

" Ai kun tsosa agurin uwarku dole kuyi fitsara...

" tashi sukayi suka fita suna fita sukaga Alhaji haruna nan Aisha ta gaidasa..

" dangin tsiya kice kin bayyana bakar kadara haihuwar asara...

" Ko sauraran sa basuyi ba haka suka huce suka huce part dinsu sannan suka fashi da kuka...

" Mama ce tace ke aisha daga zuwanki sai kuka??

" Mama wannan wacce irin rayuwace ta kunci haba mama wannan cin mutuncin ace shi iyayena suke ji...

" Yasmin ce tace ai kadan kikagani yaya wallahi inkinga yadda suka tozarta baffa jiya sai kinyi kuka kuma wai ace bazamuyi magana ba???

" Mama itama taji haushin abun amma sai ta dake tace ai sai hakuri watarana zai zama labari ...

" Aisha ce tace ni ko atatsuniya ban taba ganin irin tsanar nan ba?

Hakuri dai zakuyi Allah yana sane damu...

Mummy ce tace Allah yanunamin ranar auren nan naki barister yau dai ankawo kudi...

" Murmushi tayi tace mumy kinga gidan dayakeyi kuwa anjima zai turomin dan haka kisanar da dady asakamin hadaddun kayan daki please...

" Oh wannan wacce irin Amarya ce lallai zamani...

" mumy kenan Wayar tace tafara ringing cikin sanyin murya ta dauka darling dafatan kana lafiya?

" ke zan tambaya dafatan kina lafiya? Tun dazu tunanin ki kawai nakeyi acikin office , Ramlat ina tsananin sonki DanAllah ki kula dani?

" Har cikin ranta taji tace mijina bakada matsala ba, nima ina kaunarka dr zan iya komai akanka kuma zanyi maka hidima,zuciyata bazan bude wani yashigo ba ko kadan bazan so naga kayi fushi ba...

" Ramlat banason wannan aikin naki please ki rage saboda ina bukatar kulawar ki...

" DanAllah Mubar maganar aikina darling..

" Shiru yayi yace to sai anjima.." cikin juyi ta rungume wayar tare da murmushi, cikin mintuna taja motarta sai office tana iss tace kawata kinsan me??

Sai kinfada ince dai mutumin zai sakar mana kudi??

" ke ba wannan ba kinsan yace wai na jiye aiki!!!

" mtseww bashida hankali ke doluwar inace dazaki ajiye aikin ki ke yana zura kafarsa kema ki zura duniya fa sai da wuta bakiga yadda manyan mata ke shakstawarsu ba???

" Dadina dake kinaso ayi dani wallahi kam daman yaudarar sa zanyi nace zanbari sai nashiga daga ciki nacigaba...

" Yauwa ko kefa, barister lawal yana kiranki kije yana office...

" Tohm ina zuwa kawata bari naje nadawo nadan maganar case dinnan ce.

" Rabia ce tayi dariya mugunta tace ai sai najawo kinsa yasake ki da kanki banza tazata sonta nakeyi? Duk duniya na tsaneta yadda kika samu miji bansamu ba kema bazan barki kiji dadi ba.

" Barister ramlat ce tadawo tace kawata me muke cewa ma?

" Uhm daman zancen kudine million uku yakamata yabaki nagyaran jiki karki yarda ko million daya yabaki mugune fa dr yana samun kudi sosai....

" kinaso kiga nafito kawata kinaso kiga ina harka ban mutafa sannan suka tafa.

Yasmin ce ta dawo daga gidansu fatima tun akan titi wani saurayi ke binta amota har tayi sauri tashiga gida, A dai dai lokacin Alhaji haruna yaganshi sannan ya karaso yace lafiya kuwa??

" har kasa matashin ya durkusa yace ina yini baba? Daman wata yarinya nagani tun dazu shine nazo gurinta yanzu tashiga ciki..

" fara ko baka lukutar ko siririya??

" yadan rissina yace yanzu dai ta shiga.

" To ina zuwa, daman kafin yakarasa yasmin tafito nan tace sannu ina yini? Lafiya dai ko?

" wallahi lafiya kalou daman inason mudan tattauna ne ina yawan ganin ki wallahi kuma naji kinshiga raina inason kitaimaka kibani dama in shiga sahun samarin danAllah?

" Shiru tayi batace komai sai ji sukayi Alhaji haruna yana kai yaro wannan yarinyar dakake gani cikakkiyar karuwace bin maza da mata agurinta yadda kasan dabba, dama daya daga cikin yarana kace kanaso da yafi dan sunfita tarbiya...

" kuka tasaka tace Allah shaida ne kifa mata mari yayi yace zaki yaudari yaron mutane shigiya 'yar iska..

" matashin saurayin ne yace kaji tsoron Allah katuna tsayuwar ka da Allah sannan ya shiga cikin motarsa ya tafi..

" Ke kuma bakiga komai ba sai mun saka miki bakin jinin kare...

" Da kuka tashiga cikin gidan tagayawa mama komai Aisha tace kyalesu yar kanwata Allah shaidar ki ne Ai kuma shi zai cigaba da karemu karki damu da maganarsu.

Baffa ne yayi sallama Aisha tayi masa sannu da zuwa nan suka gaisa yace auta wayatabaki? " Dariyar karya tayi tace babu kowa baba.." To kinji ankafe sunanki amasu zana jarabawa ran monday zaku fara sai ki shirya. " cikin mamaki tace baffa wa yabiyamin? " sageeru ne sai kiyi masa godiya. " inshaa Allahu. " Mama tace aikuwa angode.

" Aisha ce tace kasan ina koyarwa baffa kuma ina daukar kudi masu yawa gakuma business da nakeyi wallahi baffa bana taba komai acikin kudin sai dai ko idan zanyi taimako Allah yabani miji nagare komai shi yakeyi min bana siyar komai kuma nasan gar da adduar da kukeyi min duk da bana kusa daku domin ku iyaye nagari masu koyar da hakuri da yadda da kaddara.. " yasmin ce tace hakane yaya Aisha. " wannan jakar million 4 ce aciki da dubu dari 3 duk kudin aiki na da sana'a tace nakusan shekara 10 danake tarawa wannan gaba daya nabar maka baffa kaja jari domin tarbiyar da kake bani wallahi banda abunda zangode maka duk da bana kusa dakai komai kanwata tasa sai ka turamin duk da munyi nisa kuma mahaifiyata batasaniba, hatta kudin makarantar da kabiyawa yasmin naga kasiyamin atampa duk dan karka fifita wani acikin mu, kaja jari baffa ina fatan wanna kudin yazama dukiyar da Al'umma zasu amfana da'ita ..

" yasmin ce tasaka kuka ta rungume aisha tare da fadin tabbas nayi wani sabon karatun Anan idan kanason d'anka yatashi cikin tafarkin gaskiya to kasanar dashi ilimin addini kakuma zama babban misali nagurin koyar tarbiya,kar kuma kanuna masu bambanci , abunda zamuci miki shine Allah yayimiki Albarka yaya inasonki wallahi...

" Mama ce tasaka kuka tace tabbas mai hakuri shikeda riba, ako da yaushe baffa kana fadan Allah yana sani damu kuma zai dubimu yau gashi ranar tazo ranar da mai hakuri zai ci riba, Allah yayi muku albarka aisha Allah yasaka muku da Alheri halinki nagari yasa 'yar uwarki tagado halinki...

" Baffa ma yayi musu addua tare da godiya sannan yace yadda kikace naja jari zan koma sana'ar mahaifina wato atampofi tunda tun ina karami na iya sana'ar daman ba lallai kayi ilimi kakuma samu sanaar da kake tunani ba wane sain sai kaga alkhairin ka yana inda baka tunani especially idan kana addua ...

" Tabbas hakane..

Yau Aka kai lefen dr sageeru akwati goma sha biyu kaya masu kyau, wani satin za'a fara biki yasmin kuwa ta hada kayanta zata koma boarding tun karfe 8 baffa yasa aka kaita gida ya cika da hidimomi kalakala..

" Da daddare dr sageer yaje gurin ramlat taci kwalliya bakace ita bace ba daman irin siraran matannan ne ga ido amma batada hanci sosai kuma ita chocolate colour ce sai dai iyayi acikin ta kamar me tana zuwa tace ya muradin zuciyata.. " Cikin kayataccen murmushin sa wanda ya bayyana hushiryar sa da hakorin makka yace Amincin Allah ya tabbata agareki ya ruhin zuciyata amaryata kuma muradi
na...

" yauwa mummy tace in gayamaka kayafa sunyi sai sai Allah yabiyaka kuma gobe zasuje jiran kayan dak'i ..

" Dariys yayi yace tohm shikenan na riga nacika saman ku kwacika kasan kitchen dinki katoto kinsanni da son abinci...

" Haha lallai kam..

To ni inada aiki yanzu sai zuw gobe in Allah yakaimu..

" kagaida gida sannan tashiga cikin gida..


Baffa ya bar aikinsa yasamu babban shago ya zuba kaya aciki, da magriba yana dawowa yayi sallah, Dr sageer yana shigowa yace baffa naga yanzu kana yin yamma??

" Eh da yake yanzu nakoma shago nazuba kaya.. " shago baffa? Ina kasamu kudi?? " Wanda ya yarda da Allah ai shi zaisha kallo, ga dubu dari tukwuicin bikin ka Allah yasaka albarka a auren ku kuma kaji tsoron Allah kariketa dakyau..

" To baffa nagode Allah yakara budi sannan yatafi, " mama tace gaskiya nayi dacen miji wallhi mai boye sirrin gidan sa akwai da babu..

" Murmushi yayi baice mata komai ba...

Yau jumma'a yau aka fara biki sunyi kamu da dinner sai dauren aure abun ba a magana sai wanda yaje biki dai yayi kyau sosai kuma manyan mutane sun halacci bikin su abida da maryam da bilal basu haukace ba sai da sukaga gida kowa baisan yana ginin ba kallon kolo sukeyiwa dr sageer nan suka dawo gida suma zagin. " mumy da dady sunyiwa ramlat fada abisa gaskiya da amana sannan aka tafi da ita hajiya suwaiba itama tayi mata sannan akayi gidanta..

Lokacin da aka kaita bayan kowa ya watse tayi kwanciyar ta sai bacci lokacin da dr sageer ya shigo yaganta ta kifa cikinta sai bacci takeyi yana kokarin tashinta sai kuwa tace please darling bacci sai da safe shima haka yayi shafa'i da wutir sannan ya kwanta da asuba kuwa bayan yafita tayi sallah rabia ta kirawota tace kada fa kisake kice zaki zauna kiyi tawowarki office kinga munada case mai zafi..." eh daman zanzo sannan ta kashe wayar...

" Hajiya suwaiba tare da aisha suka koma benin , yasmin kuwa batasan abunda ake ba tana can tanata karatun ta..

Su abida kuwa yanzu aka kara samun kofar yawo, mamee tace kowannen su yaje ya dangwalo mata babban arzuki dan bazata aurawa talaka ba..

Ina zakije ramlat??

" wacce irin tambaya ce dr inada aiki mai mahimmanci a office i neef to live kafin na makara..

" Ai ban baki izini ba ko ni na dauke hotu a office.." sai ka koma kaga matarka tafita itama..

" Ramlat ban baki izini ba nagaya miki...

" hmm kaga sai nadawo...

" zama yayi kan kujera tare da takumi...


_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

*WANNAN SHAFIN SADAUKAR WANE GAREKU FACEBOOK READER'S ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI SAK'ON NINKU SUNA ISA TA, INA KUMA GODIYA SOSAI...*

   GOD BLESS YOU OLL....

Ya zo a hadisin Mu'ãz d'an Jabal (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:
(( Ka ji tsõron Allah a duk inda kake, sannan ka bibiyar da kyakkyãwan aiki a kan mummuna; sai ta shãfe/guge ta -ita mummunar-, kuma ka yi mu'ãlama da mutãne da kyãwawan d'abi'u )).
Imãm At-tirmizy, kuma yace: "Hadisin Hasan ne".

Wato ana son bãwa ya yawaita kyãwawan ayyukan alheri, musamman ma ace ya yi wani aikin kuskure ko sã'bo, to, sai yayi sauri ya tuba kuma ya yi kyakyyãwan aiki.

Sai jin tsõron Allah a duk inda mutum yake, kuma inda tsõron Allah yake, shi ne zuciya; sai dai ayyukan fili suna nuna abin da mutum ya qudurce a zuciyar, dã wani zai ce shi yanã tsõron Allah, sai kuma aka ganshi yanã abin da ya sã'bãwa taqawar; to, qarya ya fad'a kenan !

Abin da ke sanya bãwa yin taqawa kuwa shi ne tsananin kulãwa da zuciya da hanã ta bin son zuciyar, sa'an nan a tilastã mata wajen tsantsar biyayya ga Allah da kuma Manzon tsira (SAW).

Ana son bãwa yayi kyakkyãwar mu'amala da 'yan uwansa 'yan Adam kai har ma dabbobi, shi Allah (SWT) yanã duba aiki mai kyau ne wanda zuciya ta tausaya yayin gudãnar da aikin, sannan duk wanda aka kyautatãwa su ne suke yiwa mutum adda'a musamman bayan komawa gidan gaskiya.


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:09PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 20-25

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


Dr sageer da yakusan rabin awa azaune ya rasa me yakeyi masa dadi,tabbas wahalar da yasha acikin rayuwarsa bazata faduba shi a tunaninsa yasamu mata tagari wannan zaiji dadi da'ita Amma ina brstr ramlat ta yaudari shi da k'alaman ta Yana, cikin sanyi jiki yace ya Allah kaganar da Matata tabbas inason ramlat....

" sallama tayi acikin office din tace kawata kinga nafito ko?

" rabia ce tace yaya kukayi da mutumin naki??

" Wallahi baiji dadi ba harda cewa bai bani izini ba...

" Dallah kyaleshi ke kike tashi ai yanzu lokaci ne da account dinki zai kara nauyi fa?

" kamar yaya??

" Rabia ce tace ke komai bakya kawo wuta ina nufin lokacin da zaki tatse kudi agurinsa yazo ke hatta dariyar ke kice sai ya siya if not ki kuntata masa...

" haba kawata mijin nawa?? " lahh kinjiki sai kace ba barister ba ai tahaka ake kwace miji ai abinci ma kice baki 'iya ba..

" Hahaha rabia kina bala'in sona fa ina godiya kudin adinga yimiki transfer kema koba haka ba??

" yauwa bestie kokefa bari mu tattauna akan wane case...

Mamee ce ta kalli abida da maryam tace shigen raina mutune da kukeyi kukalli dai gidan da dr sageer yagina yadda kikasan 'dan shugaban kasa...

" maryam ce tace wallahi mamee har Allah yaisa sai danayi azuciyata da ban aureshi ba ashe yanada kudi sosai da sosai...

" Alhaji haruna ne yace ai sageeru babu maijin cikinsa ba'asan me yake samu ba shiyasa Amma nasan ta yadda za'ayi zan rance kudin nasa sannan mucinye mu hanasa...

" abida ce tace yauwa Alhaji gwara haka dan mu gaskiya bama jindadin da yakeji kwatakwata naga mama ma sai sababbin kaya take sawa inaji shi yabata...

" Aikuwa zaizo yasameni inji mamee..


Mama ke zaune ak'an tabarma ta kalli baffa tace ya cinikin naka kuwa???

" Murmushi yayi yace Alhamdulillahi wallahi muna samun riba sossi da sosai mun hadu da wasu 'yan chana mun basu kaya munsamu riba mai tsoka sai dai Allah yasa musu akbarka...

" Alhamdulilahu har naji dadi muna nan dai muna addua sai kaima kadage saboda makiya yanzu kuma zasuyi maka chaaa akai!

" Ni bazan iya kare kaina ba Amma Allah yafiso ai duk abunda sukaga dama suyi nidai dogarona Allah kuma shi zai tsaremu mu dai kada Allah ya kawo ranar da zamu cuce wani...." Ameen yaa Allah baffa..

" jiya naji makarantar su yasmin tace agaida ki sosai kuma takusa gama jarabawar saura guda biyu2...

" To Allah yabada saa.. " Ameen


Yusra ce tace lallai yasmin soyayyar ku da uncle nafee'u karfi takeyi fa dubi yadda kika damu ak'ansa....

Murmushi yasmin tayi tace duk da malamin irs dinmu ne wallahi addinin sa yana burgeni kinga tun lokacin da yace yana sona shikenan naji ya kwanta mini...

" yasmin kenan ina guje miki fadawa tarkon da bazaki iya fita ba kicere soyayyar nan yanzu...

" Tohm kawata zanceri inshaa Allahu bari naje na tambayi shi littafan mu koya gama dubawa kinga gobe exam din muke dashi ..

" Yauwa tohm shikenan...

" sallamar dayayi ita ta doki kunnan sa cikin murmushi yace yasmin?

" Naam daman nazo naga ki kagama marking din books din ne?

" Daman inason muyi magana dake ina fatan bazaki daukeni mai son zuciya ba??

" kada idonta tayi cikin rashin fahimta tace kamar yaya uncle?

" kindai san inasonki kuma ni ba dawasa nakeyi ba tabbas ina kaunarki inason kisani acikin zuciyar ki bangare mafi daraja please!!!..

" Murmushi tayi tace Allah ya zabamana abunda yafi alheri...

" Ameen tauraruwar taurari...

" Murmushi tayi tare da jin wani zafin soyayya acikin zuciyarta tace ban san so ba Amma ina daf da kamuwa dashi sannan ta shiga class.

Dai dai shigowar ta cikin gate sai wayar ta tafara ringing bata dauka ba sai da takarasa cikin gidan nan ta tarar da dr sageer yana kallon film zama tayi kusa dashi tace darling am back ...

" Kallonta yayi cike da kauna yace sannun ki yaya aikin??

" wallahi lafiya am hungry akwai abunda zan danci???

" Ga tea nan da burger sai kici...

" Dauka tayi sai data gama ci sannan taje tayi wanka nan tasaka kayan bacci tayi sallah yana zaune k'an gado sannan taci darling yanaji kayi shiru???

" Murmushi yayi yace nayi tunanin ke macece tagari da kowanne namiji yake bukatar yasamu? Duk kyan mace in bata bin umarnin mijin ba mace bace ba kinyi kirari cewa kina sona amma kuma bakyason abunda nakeso anya kuwa ke na kaunata??

" Rungume sa tayi tace please darling dina kayi hakuri inagama case dinnan zan ajiye aikin domin ina mutukar son naga nasamu damar taimakon sa please ina gamawa shikenan zan ajiye...

" Shiru yayi mata can yace mata babu komai Allah yataimaka....

" yadda yayi magana yasa ta tabbatar yana sonta sosai da sosai cikin shaukin soyayya ta rungume sa nan tafara gigitasa daga nan kuma suka fada wata sabuwar duniyar...

Kai baffa kai baffa uban wani ne yabaki kudi ne naga har kasiya mota...

" baffa ko kallan sa baiyi ba sannan yaja mota yafita..

" Kai isa kanacan wannan makiyin namu sai kudi yakeyi musan abunyi???

" bilal ne yace motar da yake hawa mu kanmu bamu da'ita bakuga yadda mutane suke bashi girma ba...

" alhaji haruna ne yace zanyi bincike akan lamarin..

Yana fita yaga abida tafito tana kuka tace baffa ina kwana?

" lafiya lou ya karatun?

" ban biya kudin makaranta ba gashi saura 1days kuma last semester ce...

" Baffa ne yace nawa ne kudin makarantar??

" dubu 50 ne kuma Alhaji ya hanani!!

" To munafika ke wannan mutumin kike sanarwa me zai baki kudin sata kokuma kudin yankan kai??

" baffa ne yabata kudin yace gashinan Allah yataimaka abida...

" Kuka tasaka tace tabbas nagani wallahi mutumin kirki daban yake tabbas kai mutum kirkine baffa har ka'iya biyamin kudin makaranta Amma lokacin da baka dashi babu wanda ya taimakawa yarinyar ka???

" ba dan kowa nayi ba nayi dan Alkah ne sannan yashiga cikin gida yana zaune suna tattaunawa sukaji sallamar yasmin tare da akwatinta...

" baffa kuna lafita??

" mama ce tace sannu da hanya yasmin Allah yasa kici jarabawar sai kuma jami'a...

" baffa ne yace jami'ar lafiya sai dai aure miji yana fitowa zatayi aurenta...

" ita dai dariya tayi tace Allah ubangiji yayimana zabi nagari..

" Ameen auta..

Shekaru sai wakana sukeyi yasmin kullum cikin kuka domin baffa har yagaji tafara makaranta tunda babu maganar miji da sunzo sai aji shiru ga abida tayi aurenta sai maryam kadai ga barazar da kullum khalil yake mata na yana sonta yauma kamar kullum uncle nafeeu yazo tashirya kenan sai ta zauna k'an kujera...

" mama ce tace wai yasmin ba baki kikayi ba??

" kuka tasaka tace mama kullum ace saurayi in yazo bazai dawo ba mama basa sona ace yayan mahaifinka su dinga korar maka samari gashi har ina kokarin gama jami'a kullum zagin da akemin naki aure sai mai kudi...

" Nima mahaifiyar ki sai danayi tunanin haka yasmin sai daga baya nagani akwai wani abun akasa yasmin karki damu jinkirin ki inshaa Allahu zai zama Alkhairi ki tashi kije bansanki da wulakanci ba kinji?

" Tohm tace sannan tafita tanayin sallama yace yasmin lafiya bakida wayane???

" eh wallahi banda ita baffa ne bai siyamin ba shiyasa...

" A daidai lokacin dr sageer yayi parking yana fitowa yatsaya amsa waya...

" yasmin daman nazo nasanar dake sai nadawo daga sudan za'a kawo kudin mu inason naje nakara karatu...

" kallonsa kawai takeyi hawaye na bin fuskarta tabbas tasan zatayi rashin masoyi nai kaunarta mai sonta shikenan tasan kuma balallai ta auru ba tunda shi kadaine yane idan alhaji haruna ko isa sunyi mata sharri sai yace bakomai yana son abarsa...

" Yasmin menene na kuka kinsan dai ina sonki kuma 5month kawai zanyi nadawo kima kafin lokacin kin karasa makarantar ki dan haka kada ki damu ina tare dake kinji?

" idonta daya riga yayi jajir tace to Allah yabaka saa tayi shigewar ta tana karasa gate Alhaji isa yace k'arya mai bakin jini yauma yazo ya gudu kenan ke da aure sai dai kiga anayi , aguje ta takarasa gida tana shiga ta kifa kai sai kuka...

" wai ciwo kikeso kisawa kanki ne so kike nima nakamu da ciwon?? Yasmin ina hakurin naki...

" kuka takara fashewa dashi sannan tace mama kinji me baban bilal yace min wai bazantaba auruwa ba kullum sai ya zageni kullum kuma samarina basa zama, yanzuma uncle yatafi bansaniba ko shima guduwa zaiyi sannan takara saka kuka tace mama shi kadai nakeso inason uncle nafee'u tayaya zuciyata zata rabu dashi...

" Dr sageer ne yayu sallama ya shigo amma basuji ba sai tsorata da yayi da irin kukan da yasmin takeyi...

" mama ce tace to kibar kukan...

" kukan takara fashewa dashi tare da fadin kibarni nayi ko naji dadi inason uncle nafee'u yaya zanyi yanzu mama??

" mama ce kwallah suka cikomata idonta tare da barin gurin ta shiga daki...

" Dr sageer ne ya tuna da irin rayuwar da yayi abaya sannan yazo yazauna akusa da yasmin hannunta ya riki yace haba kanwata me isa kike damun kanki haka???

" bakinta ta cije tace dr so shakuwa su ba'a boyesu ina mutukar sonsa kamar yadda yake sona shi ya koyamin sonsa in yatafi yabarni yaya zanyi ina zan saka kaina???

" Yasmin kenan bakisan akwai wanda yakeson ki ba fiye da kanki fiye da masoyanki??

" shine uncle nafee'u yaya har yanzu bakasan zafin soyayya ba tunda kana tare da wacce kakeso dan haka ka kyaleni kada...sannan tasaka kuka mai cike da tausayi ta shiga dak'inta...

" yanayin da yashiga yasa shi barin gidab gabadaya yana isa yaga ramlat bata dawo ba tana dawowa ya kifa mata mari ke wai bazakiji maganata ba to menene amfaninki ban isa na baki umarni ba kullum kina titi tunda nayi auren nan gaba daya na rame wai ahaka ina da mace meke damunki wai aikin ince sai da izinin miji???

" in kagaji ka sakeni kokuma ka auro mai yimaka bauta dan ni bazanyi ba...

" eh aure babu fashi wannan watan zan kainm kudi zan kawo wacce zan koya mata soyayyata...

" tsaki tasaka sannan tace kakaro uku idan ka'isa...

Tana shiga daki mumy ta kirata tace mumy kuna lpya??

" lou tambayarki zanyi daman mijinki yayarda kidinga aikine kullum kina tafe? Banson hauka ramlat ina gayamiki gidan ki shine rufun asirinki kuma kawaye ba nakibani ba in bahaka ba sai sun kashe miki aure...

" mumy yafa yarda har kaini yakanyi..

" to Allah yarufa asiri...

'" Nan takirawo rabia cikin rawar murya tace ke wai aure zai kara dr fa???

" haba? To kidaina gyara gidan kidaina girki kidaina komai kizama kazama hakan zai taimaka miki sosai yace yafasa??

" Tohm kawata angama!!!


Yasmin ke kusa da mama tana karatu sai wayar mama tayi ringing tana dauka tayi salama yusra ce ta dauka tace kawata kina lafiya???

" yasmin tace kwana biyu shiru baki da kirki!

" kinsan ina benin sai next 4month zan dawo dama kiranki nayi ingaya miki wata magana Amma inaso ki fahimce ni kikuma yarda cewa matar mutum kabarinsa kuma mijin wata baya aurar matar wani, soyayyar da kukayi abaya ki dauka kaddara ce kuma kidaina damun kanki akan abu domin Almah kadaine keyi...

" Nifa bansan inda kika dosa ba?

" uncle nafee'u yayi aure suntafi tare da matar sudan tun 4days back!..

" Tohm nagode Allah yasaka min yaudarata da yayi...

" kitsaya ki saurare ni yasmin sannan ta katse wayar kan kafadar mama ta kwanta tana kuka nan tasanar da'ita...

" mama tace bakomai Allah yabaki wanda yafisa...

"Tun daga ranar ta rage magana tama daina kula kowa sai gaisuwa yau baffa yana kan kujera mama tace kaga yasmin zata kashe kanta fa kullum kuka!

" Dak'in ta yashiga da kansa yace auta??

" Naam baffa..

Ki shirya zamuje benin gobe kuma kada nakara ganin ki kina wani tunanin kinji..

" tohm baffa inshaa Allahu fuskarta ta kumbura saboda kuka...

Dr sageer yana zaune a office yace kai khalifa karin aure dole fa...

" please kabar zancen nan menene aibun ramlat???

" fitsara karya kazanta ....dan haka soon zankara aure...

" Toh Allah yabada tagari...

"Daga nan ya dauki motarsa direct sai gida bayan yagaisa dasu ummi sai yayi hanyar su yasmin yana shiga tazo fita zata karasa kenan ya riko hannun ta tajiyo tace lafiya???

" Yasmin zaki aure ne danAllah ki taimakawa zuciyar data dadi tana begenki tana kaunarki...

Kada kasoma kada kafara uncle yana cikin zuciyata bam tunanin akwai mai ciremin sonsa kagane...

" yasmin pleass kitsaya taja hannunta sannan tafice...


_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*
*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:11PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 25-30

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dr sageer da yafi minti talatin atsaye bak'omai yake tunani ba face in Allah ya rubuta yasmin ba martar sa bace ba dole ne ya hakura, cikin yanayi yaja numfashin sa sannan yace ya Allah ka dubi ne, motar sa yakarasa ya bude bai isa ko'ina ba sai asubuti nan ya duba wasu marasa lafiya sannan ya huce office yana zama yana kokarin cike wasi files sai wayars tafara ringing dauk'a yayi yace hello ramlat ina lafiya??

" eh lafiya! Please ka tawo mana da abinci a resturant cuz bazan dawo da wuri ba!...

" wai ke ramlat zamanki nakeyi kokuma zamana kikeyi?? Tunda kikazo gida 3times kika dafa abinci kullum ina hanyar gidan ABinci yanzu abunda kikeyi adalci ne??

" Kaga dr gwara kadaina bata bakin ka cuz ba fahimtar maganganun ka zanyi ba danhaka sai kadaina yimun ihu aka idan kaga dama sai kasiyo wa kanka ni zanci anan...

" Dr sageer ne yace yayi kyau ramlat zaki gani k'urunki..

" wane tsaki taja mtseww na dade banganiba...

Juyawa yakeyi akan kujerar sa cike da tunanin mafita can nurse kwankwasa kofar..

" sir akwai marasa lafiyar da zakagani fa sunata jiranka..

" okay zasu iya shigowa wata matashiyar ce ta shigo tace ina yini dr?

" Lafiya file name?

" fatima idres.." meke damunki??

" wallahi dr inada matsala bakina sai ya dinga wari kuma gabana shima wani wari dr mijina bakaga yadda yake wulakanta ne ba doctor please ka taimaka min..

" okay zanyi miki abunda zan iya amma nafarko kinayin brush??

" eh doctor wane sa'in inayi amma ba sosaiba..

" to kice ke kazantar ki kikeyi kinsan kuwa babu abunda namiji ya tsana irin kazanta kidinga kokarin wanke bakinki ko sau biyu ne kuma kisiya mouth frshner kina kuskurewa kuma kada kici abinci kikwanta batare da kin kuskure bakinki ba inatunanin inkika bi hanyar nan bakin zai daina wari inshaa Allahu...

" Tohm likita zansiya brush ina fita inshaaAllahu sai dai kuma warin da gabana yakeyi likita...

" kafin nan amsamin tambayoyin nan idan kina shaving din gashin gabanki??

" Wallahi likita banayi tunda nayi kafin haihuwata naga kuraji sunfito min sai kawai nadaina...

" Ai ko amusulci babu kyau barin gashi yahuce 40days kuma babban abunda ke kawo warin gaba harda rashin aske duk wata kazanta ta dank'are agurin kuma dazarar kinsa pant zakiga yayi datti dan..kuma zancen kuraje dakikeyi halittane wane idan ya aske bayayi wani kuma yanayi dan haka yanzu sai ki aske sai kishafa mai agurin kuma kina askewa akai akai...

" tohm likita inshaa Allahu...

" idan kikayi fitsari bayan kinyi tsarki kidinga barin ruwan yana kafewa saboda wannan danshin da ragowar ruwan da zai jika miki pant dinki shima yana saka wari sosai kuma zaiyi miki illah..yana da kyau kidinga canja wando sau biyu kuma kidaina zama akasa kokuma guri mai danshi kidinga wanke gabanki da ruwa sosai kina canja sabon wando akai akai..kuma kidinga wanka janaba da wuri dan rashin wank'an da wuri kan iya saka warin gaba shima kodan ka kasance cikin tsarki da rahamar Allah kayi wankan da wuri..kuma ki daina yawo babu takalmi kina saka safa inda hali kuma kidinga yawan shan kayan marmari wayo fruit zasu taimaka miki inshaa Allahu in dai kika lura da wannan to zaki daina wari...

" To likita hammata fa?

" ita kuma menene matsalarki??

" wallahi babu wuya nayi wanka ko 1daya banayi sai wari har banaso nashiga cikin mutane kuma koyaya nasaka kaya wari mai idan nasaka turaren warinsa daban warin hammatar daban warin sure daban...

"eh gaskiya abunda ke kawo warin hammata shine rashin askewa dazarar gashi yafito mutum sai ya aske zaiga baya irin warin nan amma idan gashi yayi yawa kowanne irin sure zaki saka bazai dauka ba, Amma idan kinayin wanka kisa soso kidirje hammatar sai ki aske kikara wankewa inkika fito ki shafa turaren hammatar ki ko baki shafa ba indai bakya barin gashi yayi yawa to zakiga bakya warin nan dan haka sai kikula da aske da kuma shafa turaren hammata da dirje hammatar idan anje wanka kuma ku masu miji kudinga daurewa kuna wanka sau biyu...

" likita me zance maka da wannan sharawa naje asubuti da yawa babu wanda yagayamin gaskiyar daka fadamin nagode nagode kuma inshaa Allah zanyi yadda kace daman sonjiki ne irin nawa Amma yanzu naga son jiki baidace ga mace ba...

" juya kujerar sa yayi sannan ya danna bell dinsa next person ya shigo...

Yasmin ke zaune k'an sallaya tagama sallar walhar ta sai jin wayatayi cikin rashin kulawa ta dauka tace yaya aisha kuna lafiya??.

" bansaniba wai meke damunki kowa yazo kice bakya sonki abunda makiya sukeso kenan wayagamiki asiri akai miki ke ma harda halinki idan anyi miki asirin kema sai kina kokartawa ai amma kowa yazo sai kice bakyaso ba dole suji dadi ba sudinga tunani mugun tuggun da suka hada yayi ba..

" Haba yaya aisha ke fahimce ne mana wallahi...

" dakata yasmin dazu mama takirani kin dage ke sai nafee'u mutum makaryace mara sonki wanda yayi miki karya yace karatu zaitafi bayan aure zaiyi kina tunanin miji to wallahi kiyi tunani kuma kikula kada mama ciwon ta yatashi akankk kowa ai mijinsa yake aure inma abun duniya kike hanga sai ki daina shi arzuki na Allah ne kiyi fata kisamu mai addini mai kuma rufin asiri ba mai kudi ba...

" Cikin kuka tace nagode sannan ta katse wayar cikin kuka mai ban tausayi tace yaAllah in zunubi nakeyi dan yarasulillahi ka yafemin kayimin afuwa ya Allah kazabamin abunda yake alkhairi agareni...

" mama ce ta liko au kukan kikeyi uwar kuka kidaije kisawa kanki ciwo...

" sauri tayi ta goge fuskar tace aa mama..

" To ki bari kije ki doramana abinci Allah yana sane dake!..

" tashi tayi ta sun kuyar dakanta..

" Mama da hawaye ya wanke mata fuska ta goge tace Allah yayi miki albarka yasmin..

K'wance take kan gado tana faman danna waya cikin zafin nama ya k'wace wayar ramlat wai ni banida lokacin ki ne??

Haba ya zaka kwacen waya wai sokake na goyaka?? Kokuma sokakeyi na daukeka naga kwance nake akusa dakai..

" Amma kinsan ina bukatar hankalij ki ko ina bukatar ki yanzu...

" Tsaki tayi tace to gani ai kabani please nakarasa chat dina...

" Shiru yayi mata sannan yace kiyi ahankali ramlat banjin dadi sosai fa, rungumeshi tayi sannan ta sumbace shi cike da son mijinta tace sannu husby Allah yasawake yakara sauki...

" Rungumeta yayi cikin yanayin soyayya yafara kissing dinta cikin soyayya tafara mayar masa da martani daga nan suka wada wata sabuwar duniyar...

Da asuba dakyar yasamu yaje masallaci saboda zazzabin da yarufeshi bayan karfe 6 ramlat tatashi tana kokarin hada tea sai kuwa cewa tayi jikin nakane??

" Daga mata kai yayi tace bari ta kira dr yace aa basai ta kiraba nan ta shiga kitchen takirawo rabia tace kwalliya yaufa bazan zoba jikin dr yayi tsanani...

" ke brstr bakida hankalin namiji zaki tsaya kina kulawa dashi ki wacce irin shasha sha ce??

" Kina nufin natsallake shi nafito?..

" kwarai ma kuwa ai namiji ba dangoyo bani inda kece bakida lafiya fitarsa zaiyi kifito muje gurin bikinnan kinji?

" hahha angama aminiya yanzu zan shirya sai natawo...

" tea din data dora takashe sannan ta shiga wanka tana shirayawa dr yace ina zakije?

" Office mana akwai abu mai mahimmanci da zanyi but kafin 3 ma zandawo sannan tadauki jakarta cikin zafin ciwo ya lalubo wayar mama bugu daya ta dauka tace lafiya sageeru???

" Mama danAllah ki dafamin abinci akawomin kinji...

" Tohm shikenan ta kashe wayar ta kalli yasmin tace dora couscous da miyar hanta sai ki hada salad da lemon kankana...

" cikin biyayya tace baffa me kace nahada maka ma??

" auta kiyi duka iri daya sai azubamin...

" baffa ne yace lafiya naga wayar sageeru??

" to dai lafiya ba lafiya ba tabbas yaronnan yanada wata matsalar wallhi dan bakaji muryarsa ba,abinci yace adafa musu...

" To in zanfita sai yasmin tabini sai takaimasa, yanzu bari naje nayi wanka dan hajiya suwaiba tana hanya amma gidan dr zata sauka...

" Tohm shikenan

Alhaji isa ne yace kai bilal ina kudin daka dauka?? Banson iskanci fa yanzu alhaji mudi ya dauke motata abashin da yake bini.

" Bilsl ne yace haba baba ai kudinnan munriga mun kashe tuntuni...

" mamee ce tace oho muku dai nidai abani kudin ankon dana fada...

" Abida datazo tace gaskiya baba da kaida Alhaji kubawa baffa hakuri ko kwasamu wani rangwamen...

" Alhaji ne yace zakici ubanki mahaukaciya sai mun wuhulakanta shi kuma kitsaya kigani...

" Shi dai alhaki kwikwiyoni duk abunda kayi babu makawa sai anyi maka kuma wallahi babu ta inda azzalumi zaiyi gaba gashinan nayi auren amma kullum ina gida abunda kuka shuka sai bibiyarmu yakeyi...

" Mamee ce ta rufeta da duk'a tana zazzagenta har tashiga dak'i..


Dr sageer daya jingina ajikin gado sallamar hajiyarsa yaji cikin rashin karfi yataso da daddafawa yakarasa..

" Sageeru lafiya dai subhnlhi ina ramlatun??

" Dakyar yazauna akan kujera sannan yajingina yace sannu da zuwa hajiya..

" Ai kai zanyiwa sannu sageeru yaushe jikin yayi haka???

" dazu ne.." toh ina ramlatun??

" Ta tafi gurin aiki..

" yanzu dan rashin imani da tausayi ahaka tafita tabarka subhanallahi anya kayi sa'ar mata kuwa??

" Sallamar yasmin sukaji tasaka doguwar riga blue da farin mayafinta sai k'wandu na a hannun ta ahhh hajiyarmu yaushe kika karaso??

" Ja'ira bayan kinki zuwa garin namu?

" hajiya kenan bazaki gani ba garin nan fa banason sa kwata kwata yanzu dai yagida ya hanya??

" Lpyalou ....ina samarin naki??

" Murmushin karya tayi tace samari sunanan sannan ta kalli dr cikin dakewa tace ina kwana ya sageer...

" dakyar yace lafiya sannan yayi shiru abunka da mai haske duk fuskarsa tayi ja gakuma idonsa dayayi jajir sai dan karamin nishi dayakeyi...

" hajiya ta kalla tace bashida lafiya ne??

" Yanzu nazo naganshi ahaka tunda kinzo taimaka wa yayan naki kibashi abinci wannan wawiyar matar tasa tafita...

" Dan shiru tayi sai jitayi yace DanAllah..

" Ni bari nashiga gidan hajiya hansatu mugaisa...

" yasmin ce ta zuba masa abincin sannan ta ajiye masa akusa dashi amma sam yakasa motsawa sai dakyar yadau cokalin yana dauka ya wadi saboda rawar da hannun yakeyi...

" Yasmin dake satar kallonsa ta tausaya masa sosai aranta tace wannan wacce irin matace mijinta na wannan halin zatafita?

" zai dakko cokalin yasmin ta tashi ta dau abinci cikin sunkuyar da kai ta bashi sai da yagama ci tabashi lemon riki hannunta yayi da hannunsa dake dauke da zafi yace yasmin DanAllah kisoni danAllah..

" Shiru tayi tana tausaya masa tace yaya so fa kace?? Kaima yaudarata zakayi kenan?

" yasmin ke dai ki aminci min kigani inhar da yaudara nazo...

" hmm tatashi zata tafi sannan tace kanemi wata ba dai niba kagani..

" haka tatafi tabarshi yana wani irin tare mai gigicewa...

" mumy din ramlat ce tana sallama taganshi acikin jini caba caba aguje takarasa tana innalillahi wainna illahirrajiun dr sageer??*Assalamu Alaikum*

_Tabbas kun cancanci yabo da kuma godiya masoyana nagode da irin kaunar da kukeyiwa wannan littafin ina kuma fatan kuna amfana da abunda ke cikinsa? Kuma ina neman afuwarku abisa jimawa danayi banyi rubutuba wani uzuri ne ya rikine...lurv u oll_


_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

_Mumini na qwarai shi ne wanda yake yarda/amincewa da duk abin da Allah SWT ya tsãra kuma ya zartar, abin da yafi alheri shi ne duk abin da Allah SWT ya zã'barwa bãwansa mumini; bã abin da shi muminin ya yake so ba ko ya zã'barwa kansa.._


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:12PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 30-35

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


Yanayin da momy ta tarar dashi ko motsi bayayi nan takira mai gadi ya taimaka mata suka nufi asubuti directly emergency sukayi nan akayi dak'in dashi sannan babban amininsa wato dr khalifa yashiga domin ya dubasa...

Mumy dake faman sintiri da salati abunda yafi tsaya mata ina ramlat tashiga?? Aikin tatafi mijinta na wannan halin?? Cikin kankanin lokaci takira dady nan yakaraso yanata salati da fadin sai ya sabawa ramlat...

" mumy ce ta kalli Dady idonta cike da hawaye tace to yanzu yaya zamu sanar da mahaifansa??

" Tun ahanya nakirawo baffa dan shine mai sauki kuma sai yafi fahimtar abun cikin sauki....

Baffa dake faman sauri mama tace ina zakaji ne??

Au namanta bangaya miki ba sageeru ne babu lafiya rai ahannun Allah suna can asubuti...

" Innalilahi kuma yasmin tacemin jikin da dan sauki kaga yanzu yayi tsanani to innakarasa aiki matawo ko??

" tohm bari nasanar da alhaji haruna da isa ko??

" Toh a sanar dasu kuwa kasan dai halinsu dama dai ka kyalesu ko??

" Ai shi zama da mutum sai kayi hakuri ballantana hakkin maqotak'a...

Yana fitowa daga part dinsa yatarar dasu harda su maryam bilal da mamee zasu fita babu wanda ya k'alli shi sannan ya dubesu yace sageeru babu lafiya ankwantar dashi asubuti...

" Alhaji haruna ne yace wannan matsalarka ce, Alhaji isa kuma yace ai da mutuwa yayi kaga sai muci gado ko??

" mamee data tamutse fuska tace ku dayake wahaltawa ai sai kuje kuyi jinyarsa sannan suka fita...

" Dai dai lokacin da zai shiga mota hajiya suwaiba tashigo nan yace mata tatawo suje asubuti, Akan hanyarsu tatafiya tace kaddai ciwon sageeru ne ya tashi???

" Eh hajiya shine abundai sai addua... " D'ana bai samu macen kwarai ba ina tabbatar ita zata karasa shi...

" Baffa ne yace hajiya kamar yaya?? " Nan ta kwashi labarin duk abunda ramlat take masa ayadda aka bata labari...

" kidaina kuka Allah yana sani dashi kuma za'a daidaita su inshaa Allahu...

" kallon baffa datayi tace babu yarinyar dakake ganin za'a hadasu??

" Shiru yayi yace kina nufin yakara aure wai?? Haba hajiya abu abun asannu tukunna...

Suna karasawa asubutin sukayi gurinsu nam suka gaisa dasu mumy sannan likita yafito yace ina mahaifansa??

" Gamu cewar baffa daga nan suka bisa office shi da hajiya kallonsu yayi yace kunsan yanada ciwon zuciya ko??

" Kwarai kuwa cewar hajiya... " To yanzu dai jikin nasa Alhamdulilahi zai farka nan da 10hours inshaa Allah amma inasu ku lura kukuma kula sosai akwai matsala atare dashi...

" Kamar ta tunani saka abu arai da damuwa gakuma yunwa har ulcer takamashi yana da kyau alura da lafiyarsa..

" Inshaa Allahu za'ayi...

Brstr ramlat da ita da rabi suke hira nan ramlat tace kawata cikine fa dani???

" Wani bakin ciki ne ya tokari mata wuya wato har ramlat tasamu jindadi da mijinta tabbas tasan abunda zatayi...

" Dake fa nake magana brstr rabia??

" Nan da nan kwallar bakin ciki ta cika idonta nan ta goge hawayen ta tace ina tausaya miki ramlat ace ashekarunki kin haihu? Mijinki zai gujeki daga nan yafarayi miki wulakanci daga karshe kuma sai kishiya...

" Ramlat ce tace anya kuwa kinsan yadda dr yakeson haihuwa kuwa?

" Tohm shikenan zakiga yanason haihu akan idonki zai wulakanta ki kuma babu yadda zakiyi kuma acikin manyan mata ma kallon raini zasu dinga yimiki kina babbar hajiya araina ki...

" wallahi hakane yanzu yaza'ayi to??

" ki tashi muje azubar shine kawai mafita...

" To wanne asubutin zamuje??

" Babban asubuti zamuje akwai kawata acikin asubutin ai... " awanne bangare take?? " tana bangaren emergency...

" Okay tashi muje sannan suka huce zuwa asubutin ...

Yasmin dake k'an gado tana tunanin irin kalaman dr sageer tabbas namijin mazaje ne mijin da kowacce mace ke fatan ta samu wani murmushi tayi sannan tace ya Allah karabani da auren da ba soyayya...

" yasmin zanje asubuti kafin nadawo ki dora abinci...

" Mama wane babu lafiya?? " Sageeru mana ...

" Shiru tayi sannan tace tohm Allah yabashi lafiya sannan taje tayi alwala nan tayi sallah tare da addua Allah yabashi lafiya..

Su ramlat suna sauka tace rabia mijina fa babu lafiya muyi sauri ji nakeyi kamar wani abu zaifaru...

Ke kinfiya matsala wallahi aikin banza zo muje suna shiga sai kuwa sukayi karo da dady nan yakifa mata mari sau biyu da sauri baffa yace haba alhaji menene haka???

Dan ubanki mijinki bai baki daman fitaba kike fita ?? Sai yanzu kikaga damar zuwa??

Gabanta ne yayi mummunan faduwa sannan tace wallahi ...

" mumy ce tace kada kice komai munafuka...

Rabia ce ta salallaba tayi sauri tafita bata tsaya ko'ina ba si motarta cike da dariya hahaha har iyayenki sai nasaka sun tsinemiki hahaha taja motarta tatafi....

Ramlat ce ke kuka tana fadin nashiga uku ina mijina yake??

Mumy ce ta dakatar da ita mijinki din uban wa mara tarbiya??

" hajiya ce tace haba mumy ai bahaka ake ba har yanzu fa yarinya ce ramlat kiyi mata ahankali kikasani ko wane case din takeyi mai mahimmanci...

" mumy ce tace wane irin case ne daya huce cutar mijinta eh??

Haka sukayi jugum jugum mumy tace ramlat bazata zauna dashi ba mama ce zata zauna ....

" Har karfe tara shiru har ya huce 20hours har yanzu bai farka ba...

" hajiyar sageeru ce tayi cikin dakin nasa ta zauna akusa dashi inbanda kuka da addua babu abunda takeyi...

Yasmin dake zaune a palour tarasa menene yake mata dadi, tun dazu sai tunanin dr sageer takeyi cikin yanayin kunci tace why my heart nan hankalinta yakara tashi taga har goma basu dawo ba abinci ta zuba sannan ta nufi hanyar fita tare da rufe kofar su tana kokarin fita bilal yace uwar gantali inakuma za'aje??

" Gidan uban da ka aikine sannan ta bude kofa tafita nan tasamu mota tahuce asubutin...

Lokacin data isa gaba dayansu sunyi jugum jugum tana karasawa dakin taga hajiya tanata kuka... cikin tashin hankali tace hajiya lafiya shiru tayi mata sai alamar kuka...

" a tunanin ta mutuwa yayi cikin tashin hankali ta matsa kusa da gadonsa tana kuka hannunsa ta ruki tace ya sageer please karka mutu danAllah karka barmu tana wani kuka mai cike da tashin hankali...

" A hankali ya bude idonsa kalmar da tazo bakinsa shine yasmin...yasmin..yasmin....zaki aure ne???

" batasan lokacin data miki sannan tayi waje ba tana kuka nan dukk'an su suka tashi sukayi hanyar ciki ba kowa yana kallonsa yana Alhamdulilhi ramlat ce ta matsa gurinsa tana kuka...

" likitane yashigo sannan yakara yimasa allura..

" Alokacin hajiya suwaiba ta miki tabi yasmin...

Assalamu alaikum!!!

*Please and please kuyimin afuwa da yawan shuruna da kukeji,Allah yasaka muku da Alheri ina ganin sakon ninku....Nana diso love u so much....*


_I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's_

*How was the page???*

_Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS

Wato haqiqar haquri shi ne bãwa ya gudãnar da rãyuwarsa a lõkacin musiba/balã'i kamar yadda yake gudãnar da rãyuwar lõkacin zaman lãfiya !

Dõmin Allah SWT bã ya qar'bar wani abun daga wajen bãwa; fãce sai dan ya bãwan yayi haquri, haqurin kuma ya sanya Allah SWT ya so bãwan kamar yadda Allah SWT ya fad'a cewa:
(( Kuma Allah Yana son mãsu haquri )).

Bisa ga haka idan Allah SWT Yana son bãwa sai ya zã'bar masa abin da yafi alheri gare shi da ma duk abin da zai zama maslaha a gare shi, don haka sai bãwa ya yarda da hakan.


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:13PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 35-40

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yasmin dake faman kokarin samun mota sai ga hajiya suwaiba nan ta karaso cikin karamci da dadtaku irin na manyan mutane tace yasmin har kin fito??

" Eh hajiya naga dare yanayi kuma zan shiga makaranta da safe kinga na kwanta da wuri ko??

" Eh nima din tare zamu tafi sai kitsaya su baffan su fito ko?

"Au ai nayi tunanin ke zaki zauna dashi tare da ramlat?

" aa mamanki zata zauna dashi ramlat gida zata koma...

Suna tsaye sai ga baffa sunfito bayan sunyi sallama suka shiga mota sannan suka tafi suna isa suka bude gidan bilal ne yazo hucewa yace yasmin dama magana zamuyi?

" tsaki tayi tashige gida can sai yayi ihu yace daman rufamiki asiri zanyi tunda babu mijin aure sai kizo a taimake ki in aure ki shine zakiyi min iskanci to indai muna gidannan maga masu kwasar ki....

" Hajiya suwaiba ce ta rufe kofar tare da fadin ohhh su dai sun tsotso tsiya marasa kunya da tarbiya Haka zaku kare dai....

" brstr ramlat tunda tabar asubutin ta tafi gida sai take ganin kamar mumy zasu kashe mata aure can sai ta kirawo rabia awaya cikin yanayin bacci tace lafiya??

" ke ina lafiya ana cikin wannan hali miji ba lafiya iyaye sunyi fushi dani sosai fa...

" To aikece doluwa aikin banza sai me in anyi fushi dake wayasani ma ko matar da zai aura ce tayi masa wani asirin? Kinga ki watsar dasu kitawo aiki gobe in bahaka ba ina tabbatar miki sai sun haifa miki ciwon zuciya waye kula da namiji yanzu? Sai sokuwar mace?

" Haba rabia mijina shine rayuwata fa banda kamarsa shida iyayena kina nufin na bujere musu?

" kaji banza tsaya su hada miki damuwa kema ace ciwon hauka ya kamaki kifito mu shakata yarinya....

" kumafa hakane kawata shawarar ki ta karbu kinga kinfine iya case fa??

" hahaha..sannan rabia ta kashe wayar cike da dariya acikin fuskarta can tayi wani tafe tare da fadin ai wallahi sai na kashe miki aure sai kingane kawance ba da kowa akeyi ba...


Cikin ikon Allah jikin dr sageer yayi dadi dan har sallar asuba yayi suna 'yar hira da mama yace mama aure nakeson karawa Amma kuma ina tsoron matan...

" Murmushi tayi tace sageeru kenan yaushe kasamu lafiyar ma? Kabar zancen nan sai an kwana biyu..

" Tohm na amince amma ke nakeso kisamo min yarinya mai tarbiya mai ilimin addini DanAllah kinji??

" To Ni yaya zanyi sageeru dama hajiya kagayawa tafini hulda da mutane ai...

" Ai duk maccen dake jure akwai da babu itace mace..

" sageeru kenan yanzu sai zuwa kwana biyu sai a sallameka kenan??

" Ai na warke anjima karfe 4 akwai wacce zanyiwa cs...

" Haba sageeru yaushe ka warke din ka hadata da wani likitan sai ya yimata....

" Mama banga amfanin aikina ba idan bana taimakon talakawa domin wannan matar danake gayamiki satinta daya a asubuti batasan wake kanta ba sai shekaran ko abincin da zataci batada shi ko kudin ganin likita tana cikin halin taimako sosai...

" Tohm shikenan sageeru Allah yakara budi da takawa da imani ...

" Ameen mama....


Yasmin ce ke zaune tanacin abinci sai kuwa hajiya cewa tayi kinga har an sallamesu har ya huce asubutin sa...

" kai amma anya ya warke kuwa??

" ina wata warkewa? Kawai dai kinsan mutum ne mai taimako...

" Allah sarki Allah to yakara lafiya..

" Ameen ... Nikuwa yasmin har yanzu babu tsayayye??

" Murmushi tayi zuciyarta cike da kunci tace Allah bai tsayar ba,Amma munata addu'a..

"Hajiya tace ai dama abun na Allah ...Allah yabada nagari ..ameen tace sannan tatashi tayi cikin dakinta da wayarta ke faman ringing...

" Hello yasmin ykke yusra ce .....

" Banza sai yau kikaga damar kulani to kinkyauta.....

" wayata aka sacemin shiyasa ankawo kudina ansa wata 5 fa..

Haba danAllah congrat Allah yasa damu za'ayi...

" Ameen yasmin DanAllah ki amince da dr sageer ba lallai sai mara mata ba kowa fa da zabinsa da Allah yayi masa ke dai kiyita Addua Allah ya tabbatar muku da Alherinsa...

" bazaki gani ba yusra bafa wani sona yakeyi ba kawai yaudarata yakeyi...

" kada ki yanke wannan hukuncin kibashi dama yasmin...kuma kisani wayake auren soyayya yanzu? Malama anayin aureni dan kauna in akwai kauna ai babu wulakanci da tozarci kuma dan a rufawa juna asiri ne, dukiya ba itace aure mai wadatar zuci mai tsoron Allah wanda zai kula dake wannan shine mai sonki...

" Yasmin ce tace tabbas hakane dan bazan manta maganan malamin mu ba da yace idan kuntashi adduar miji kuce in talakane Allah yabaku mai addini mai kuma sanaa in kuma mai kudine Allah yabaku mai addini mai kuma aiki dashi...

Hakane kawata nagode sai kinjini, sannan suka kashe wayar...

Dr sageer dake zaune akan kujerar sa yana cin abinci wayarsa ce tafara ringing salama yayi sannan yace wake magana...

" yasmin cikin rashin kulawa tace nice dama mama tace mekakeso adafa maka??

" cikin murmushi kamar tana kallon sa yace duk abunda kika dafa ai zanci...

" yajin naka?

" Naji sauki ai.." Allah yakara lafiya..

" Ameen nagode my queen Allah ya mallaka min ke a matsayin matata yadda nake sonki Allah kadai zai shaida...

" Batare da tace komai ba ta kashe wayar cike da murmushi tana fadin kai kasani...

Hajiya suwaiba ce tashiga cikin part din su mamee ko sallama batayi ba tace tabbas kun nunamin ku makiya nane kunsaka hassada da bakin ciki acikin ranku tayaya zakuyi gaba to sageeru dai bai mutu ba, haruna kuma sharrin ka kai da isa akanku sai kare marasa mutunci kawai...

" Dukkan su babu wanda yayi magana dan suna shayenta sosai da sosai...


Abida dake faman kuka tana kaci amanata garba baka kula dani baka sona har yaushe mukai auren zakaci kishiya hatta kusa dabi baka zuwa ...

" Garba ne yace ai ko jaki yanason kulawa da hutu ballantana ne mutum, menene bana yimiki acikin gidan nan menene bana baki tundaga kan ruwa har reza? Bakya tsafta kwata kwata dubi dakinki sai kace na mahaukaciya naga har tsintsiya sai na siyo?? Bakya kitso akan kari bakya dan kunshin nan da mata sukeyi ke harma irin style dinkinnan bakyayi wanda zan kalleki naji sha'awar ki komai ina baki har kudi kaya abinci komai akwai ayimin naji dadi ne baza'ayi ba ba? Dan haka aure babu fashi, karatun Alkur'ani tunda muke agidannan banga kinayi ba to uban me kikeso nayi miki??

" Kuka tasaka tace inshaa Allahu zangyara har sallah ma zantsayar inshaa Allahu kayi hakuri sannan ta durkasa...

" bakomai abida ni ina kaunarki shiyasa natsaya ina gayamiki gaskiya...

" zangyara inshaa Allahu mijina...


Ramlat ce ta fito daga wanka tana amsa waya nan dr sageer ya shigo jakarsa kawai ya ajiye sannan ya rungumeta my brstr kullum kyau kiketa karati sannan ya sumbaci bakinta...

" shiru tayi sannan tace wane irin so kakeyimin dr?

" kara rungumeta yayi sannan yace wanda bazai fadu ba...

" Nan tafara sakashi fita hayyacin sa tabbas mijinta daya tamkar dubu ne samun mai hakuri irinsa sai an tona...

" Nan suka shiga wata duniyar cike da soyayya da farantawa juna...

Da safe baffa ya shirya zai tafi kasuwa sai yasmin tace baffa kudin wayar anjima zanje nasiyo...

" Auta kenan gwara da kika tunamin sai kisiya biyu ke da maryam ko??

" Hajiya suwaiba ce tace wannan marasa mutuncin kaima dai narasa irin ka dakake jin tausayin su Alhalin su basuji naka ba...

" baffa ne yace haba babbar yaya ai komai rubewar hannu baka yanke ka yarba...

" Sallamar dr sageer ce ta katsesu nan suka gaggaisa sannan ya zauna yasmin dake barandar tsakar gida tana gyara wasu abubuwan ta ...

" mama ina yasmin ta shiga ne ko tana makaranta?..." aa tana can baranda kaje ku gaisa mana...

" Ita dai hajiya suwaiba takasa cewa komai sai adduar Allah yasa ta amince...

Amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar sarakai hasken zuciyata...

" Dagowa tayi ta kalleshi nan idonsa yakara rikita ta ta, can tace katashi lafiya...

" lafiya kalou ina mamakin kin yarda dakikayi da maganata yasmin kuma ke kanki kinsan bazan yaudareki ba...

" Shiru tayi sannan tace idan ma ka yaudare ni ai kaikaga zaka iya domin shi alhaki kwuikuyo ne ai...

" yasmin kalli cikin idona magiya nake ki kauna ce ne danAllah!!! Banda ke bazan yabi kowacce 'ya ba kinsani.. tabbas tun kina karama nasa kaki acikin zuciyata.. kinsan zafin soyayya tunda kinyi kuma kinsan wahalar ta..yasmin dita mai kyan hali ga kuma kyan halitta kwayar idonk'i yana riketar dani har na k'asa dauk'e idanuwa na akanta......

Shiru tayi sannan tace danAllah doctor ka rufamin Asiri ka hakura da soyayyar mu...please sannan ta goge hawayenta...

" Tabbas yasmin idan kika yimin haka baki kyauta ba kuma zaki sakani halin da yafi nada...DanAllah ki taimaka min sannan ya zauna ...yau zakiji labari na

Sunana sageer...


Assalamu alaikum

Naga Sak'onin ku nagode Allah yasakada alheri...kuyi hakuri da shiru na da kukeji..lurv u oll

_I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's_

*How was the page???*

_Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:51PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 40-45

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Sunana sageer an haifeni a garin band'uwa wato wannan garin da muk'e cik'i, mahaifiyata itace maccen ta fark'o da mahaifina ya aura wato Dr yahaya babban likitane kuma kwararren mai hada magunguna ne da duniya tasan dashi, Allah yayi masa rasuwa bayan an haifeni da kwana arba'in tun daga wannan lokacin mahaifiyata tafara samun matsala wato agurin kannin sa da yayyensa Alokacin ita bata biye musu don ta mutuwar mahaifina takeyi abinci ma bataci saboda bak'in ciki bayan mahaifina yayi kwana arba'in da mutuwa sai kuwa 'yan uwansa sukace ai araba gadonsa saboda a sauke masa nauyi...

A wannan lok'acin mahaifiya ta tayi kuka sosai Amma abun bai tayar mata da hankali ma sai da dan uwansa Naziru yazo yace ana binsa bashin miliyan 100 abun ya jijjiga kowa saboda kowa yayi masa shaidar mutumin kirki ne tunda yake ko aron kudi bai tabayi ba nan Alhaji munzali wato yayan mahaifina yace to ai bai rubuta shaida ba bai kuma sanar ba, gaba dayansu suka gigice sukayo kansa har sai da suka kwashe kudin nan daga karshe sukace mahaifiyata sai tabar gidan takoma gidan iyayen ta, cikin halin maraici da bakin ciki ta koma gidan su, da yake Allah baya zalunci bayan shekara 1 Alhaji tanimu babban dan kasuwar nan yazo yace zai aureta da farko bata amince ba sai da yanuna yana mutukar sona kuma yayi mata alkawari duk abunda zai faranta mun rai shi zaiyi yakuma tabbatar da shi amatsayin d'a ya daukeni...

" yasmim da kuka ya cik'a mata ido sai cewa tayi kuma ya cika Al'kawari??

Hmmm ai dan adam sai Allah a wannan lokacin muna rayuwa acikin gidan har nakai shekara biyar Amma kwatakwata ko makaranta bai sakani ba yaransa suna makaranta mai tsada wacce a kowanne term akan biya musu dubu dari biyu kuma alokacin kudi yana kudi, kanina abdul lokacin yayi shekara biyu ya kaisa makaranta amma ni har nayi bakwai bai kaini ba watarana na shiga makota sai waya yarinya tacemin banza jahili wanda babansa bai sakashi amakaranta ba alokacin kuka nasaka ina shiga na tarar da Alhaji tanimu nace masa baba kasani makaranta tare da abdul da sauran yayena sai kuwa kifamin mari yayi yace "ubanka ne zai saka amakaranta ba niba banza agoli tafi kabani guri...

" Yasmin ce tace Allah sarki rayuwa kai alokacin kayi tunanin baban ka ne kenan??

" Eh sai alokacin na tabbatar da ba babana baniba lokacin da nace hajiya ina babana???

" sai tace min sageeru me yafaru?

" Sai nace mata ai bana zuwa makaranta kuma ba'a sona agidannan Alokacin tace karka damu sageeru anjima zan kaika makaranta kuma kaima ina sonka kaji...

" Nace mata me isa baba bazai kaini ba?? " Sai tace aini kaga nafiso nakaika da kaina saboda ina sonka sosai...

" To a ranar ta k'aini mak'arantar Allo ta k'uma sak'ani a government school kullum karfe 4 na dare zata tashine ta k'aini makaranta sai karfi bakwai zan dawo na shirya na tafi boko karfe 3 idan nadawo nakoma makarantar Allo daga nan k'uma sai karfe 6 tukunna zandawo, A lok'acin Bana gane karatu saboda duk 'yan ajin sun huceni kuma nayi girma ban shiga makaranta da wuri ba haka hajiya tadinga koyamin karatu, ina gani zaa kaisu makaranta amota kayan dazu saka nadabban ne haka nadinga hakuri da rayuwar gidan...

" In takaita miki ahaka nayi haddar kur'ani nakuma yi kandi naso nacigaba Amma sai ya kasance malamai suna jana muna zuwa da'awa da kuma wa'azi alokacin Allah yasa sunana ya daukaka sosai Alhaji tanimu sai ya dinga kokarin ya koreni agidan Amma mahaifiyata sai ce masa tayi yana korata zata bar masa gidan...

" To ya rayuwarka ta cigaba??

" A lokacin kanina abdul da usman da sumayya da sauran yaransa Alhaji tanimu ya biyamusu su tafi karatu kasar America kai A lokacin nashiga tashin hankali domin ina bala'in son yin karatu wallhi ko kudin zuwa sudan banida dashi sai dubu ashirin din da nakanyi faskari nasamu na nemi taimakon mutane da yawa Amma bansamu ba har kanina suka tafi lokacin Alhaji tanimu ya dinga wulakantani sosai ke wani abun ma bazai fadu ba kwatakwata, Mahaifiya ta babu yadda batayi ba Alhaji tanimu ya biyamin Amma yace Allah yakiyaye kishiyoyin ta suka dinga yimata dariya da har ciwo yakusan kamata haka nazo na rarrasheta nace mata Na hakura da karatun....

Watarana muna zaune awaje sai abokina khalifa yace min anata siyarda takardar karatu Akasar waje akan dubu biyar gomnati zata biya tun daga lokacin Na dinga bin gida gida ina tambayar ko da wanda yasani haka na hakura nadawo ingayamaki ina zaune khalifa yakawo min takardar nacike sannan na huce zuwa gida ina bawa hajiya labari tasaka dariya tace wai kai karyar gwamnati zakabi dama kadaina wahalar da kanka, nace hajiya kenan kada ki damu inshaa Allahu zan samu haka kuwa akayi nakai takarduna ingaya miki abun mamaki sai Suka aikamu london mu kusan 8 duk basu ci jarabawa ba sai mu uku haka muka tafi kasar london hajiya tabani dubu hamsin na canja...

" iko sai Allah haka kukayi karatun?? dama ai ance wani hanin ga Allah baiwa ne...

" Yasmin Anan nazama cikakken likita bandawo kasar nan ba sai danayi phd ke ingayamiki har nafara aiki acan cutar da hajiya tadinga yi lallai akan abdul da aka kama a kasar america yasani dawowa mukayi cuku cuku aka sakeshi daga lokacin ne Alhaji tanimu ya kasance kamar mahaukaci saboda duk yaransa babu wanda yayi karatu dai mutum 3 acikin su 8 sai ma karar da dukiyar sa dayayi har banki sai da suka bisa bashi ke gidansa ma sai dasuka daga Alokacin mutane suka dinga yimasa dariya mahaifiyata kuma hankalinta yatashi saboda batasan inda zataje ba idan aka siyar da gidan....

" Yasmin ce tace iko sai Allah! To yaya akayi da gidan?

" zuwa nayi nasamu hajiya nace mata zansiyar masa gidan saboda rikeni dayayi nazauna agidan sa, tayi bala'in jindadi haka ya dinga bani hakuri kanina kuma duk nayi musu aure suma suka zauna agidan Amma abun mamaki kowacce sana'a basa iyawa saboda tsabagen sangarta da sukayi...

" a lokacin ne nagina asubuti mai zaman kansa wanda yanzu ake alfahari dashi, ke saida Allah ya daukakani Amma duk sanadiyar wa??

" Hakuri da kayi da kuma yarda da Allah da kuma biyayya da kayiwa mahaifiyarka...

" A dalilin kawo mara lafiya da barister ramlat tayi anan muka hadu takan kirani mugaisa je har muka saba zancen soyayya yashiga yanzu aduniya banda buri sama danaga na haihu kuma nakuma mallake ki...

K'allon sa tayi cike da sonsa can sai tace tabbas namijin mazajeni dr sageer ga kyau gashi dogo irin masu dan kibar nan badai fari bani Amma colour dinsa nada matukar kyau ga hanci ga kuma red lips dinsa ga zaje afuskar sa ga kwarjini huramin iska yayi sannan na motsa idona...

" lafiya gimbiyata??

" Murmushi tayi tace bakomai bari naje na shirya zanje skull yanzu...

" Okay tohm jeki shirya sai na kaiki kinji...

" No nagode katafi aikinka Nan tashiga palour mama tace hira kuka sha ne???

" Hajiya ce tace ai naga jinin su yazo daya ne..

" karatu ya koyamin cewar yasmin..... " Dr sageer ne yace a'a ke kika koyamin sannan yasa dariya yace to sai anjiman ku ...

" To agaida su ramlat...

Bayan d'an lokacin yasmin tafito sanyi da afterdress sannan tace mama natafito skull sai nadawo...

" Toh Allah yakiyaye...

Tana fita ta tarar dashi amma bata kulashi ba tana kokarin fita gate sai yajawo ta yasmin please ki taimaka yau kadai please sweetheart....

" maryam dake tsaye takaici duk yacikata ...

" kokarin bude kofa zatayi sannan sai yace please and please
...

" jiyowa tayi batare da ta ce komai ba sannan tashiga ta zauna agaba suna cikin tafiya ya rigo hannunta yasmin DanAllah kin Amince da soyayyata???

_I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's_

*How was the page???*

_Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[2:51PM, 4/9/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 45-50

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dago k'anta tayi sannan ta k'alli yadda ya rike hannun ta, cikin kuzari ta zare hannun ta sannan tace lok'aci fa yana kurewa?

" batare da yace mata komai ba ya cigaba da driving sai da yaje daidai kofar jami'ar sannan yatsaya...

" jiyowa tayi tace nagode... " har tayi gaba sannan yace yasmin?

" Cikin nutsuwa ta karaso har inda yake sannan tace Naam!

" cikin daure fuska kada taki gayamasa yace karfe nawa zaki tashi???

" sai lokacin da malamar tazo nayi mata submitting ai...

" Okay to kikula da kanki bye bye..." wata harara tayi sannan tace tuntuni bai taba cewa in kula da kaina ba sai yanzu...Wallahi mamee dr son yasmin yakeyi Allah bazan yarda ba sau dai ni ya aure ne...

" ke ki kwantar da hankalin ki indai nice bai isa ya aure yasmin ba tabbijan ki kwantar da hankalin ki nasan me zanyi...

" Maryam ce tace yauwa mamee ta ai yasmin da mai gadi ta dace wallahi...

" Alhaji haruna ne yace ai sageeru sai nasa yan fashi sun nakasa shi ina tambayar sa bashin kudi sai cewa yayi kowa zai bashi kudi amma banda ne ai wannan raini ne zaici ubansa....

" lallai wuyansa yayi kauri Daman ai shi dan Adam butulu ne...


Barister ramlat dake zaune a office dinta duk cikin yanayin damuwa, irin rashin kulawa da dr yake mata har yafara taba mata zuciya tana cikin tunani sai ga rabia ta shigo....

" ke dai sai kinsawa kanki hawan jini baki da tunani sai na namiji to sai kiyi tayi su hada miki hawan jini ai ki rabu dashi nahada ki da sugar dady wanda sukafi miji ki komai....

" me kike Nufi rabia?

Dallah ina nufin maza mana ki rabu da dr nahada ki da wasu ku shakata akwai wani sabon Alhaji da aka hadani dashi sai na barmiki shi...

" Allah yakiyaye wallahi ai ni bana zina ingayamiki ko shekara nawa dr zaiyi baya kulani bazan bi maza ba...

" kinga kar kigayamin babu dadi kikasan irin shi matan dayake kula? Ya dirka miki cikk yabarki da sha'awar sa kuma yayi ficewar sa dan love dinnan bai nunamiki shine zaki dinga fiffiga akansa??

" aa rabia komai fa lefe nane abubuwa nawa nakeyi baya kulanani yayi hakuri dani sai yanzu zanje haushi, ciki kuma kinsan babu maganin da ban shaba yake barewa ke duk ba wannan ke damuna ba aure da zai kara...

" ke kikasani malama ainaga nakya daukar shawarata sai kiyi abund kikaga shine daidai...

Mtsww ke fa rabia matsalata dake fushi dallah kigayamin zan dauka...

" kinsan namiji ba'ayi masa sanyi in kin koma ki yimasa rashin mutunci kikuma yimasa kashidi ke in san samune ki gudu gida zakiga ya janyi ko kefa yanzu kikayi magana me kyau ni bari natafi sai gobe...

Okay bye bye...tana fita rabia tasa dariya tare da fadin ai sai na kashe miki aure bake kawa ba...

Karfe 5 yasmin ta dawo daga skull abinci tace sannan tazauna bakomai take ba sai tunanin dr sageer tabas tabbas tana tsoron shiga tarkon soyayya Amma kuma gwara tayi aurenta itama ta huta cikin wannan tunanin hajiya tashigo tace yasmin?..

" Naam hajiya .... " wai meke tsakanin ki da dr ne? Naga duk ya mutu akanki ko soyayya kukeyi...

" Murmushi tayi tace lahhh hajiya bakomai fa kawai jinin mu yazo daya ne... " Da bakyason sa bazakiyi wannan murmushin ba bazakuma kiyi magana a hankali ba abunda nakeso kigani shi miji nagare shine wanda zai soka koda mutane na zagin ka kuma kigane cewa ita soyayya masu hankali akan saba kuma a daidai ta, kuma ki daina tunanin sai wanda ranki yakeso aa kiyi adduar nagari mai addini wanda zai tararrayi ki, tabbas nasan sageeru yana sonki Amma kuma ya kamata ki amince bawai ina goyan bayansa bani aa kinsan yana da matsalar zuciya kuma zanso ki kasance akusa dashi...

" Ita dai yasmin batace komai ba har hajiya tafita palour...

" wayar ta ta kunna hotonan sa ta shiga dannawa kallonsa takeyi cike da kauna..

Mama ce tace daman hajiya inaso muyi magana kafin ki tafi?

" Akan me fa?

" A kan sageeru ne dayace a nemar masa mata ni kinga ba harka nake da mutane ba kamar ki ko ke zaki duba masa dannaga yana bukatar karin aure...

" To ke banda abunki ga yasmin nan me zai hana ahadasu...

" Nasan halin yasmin hajiya ba lallai ta soshi ba kuma kinga shima dr sageer din ba lallai yasota taba kina ganin yadda ake sokarta cewa taki auruwa nafeson daidai da'ita ya aure ta....

" Mama kenan ne zanyiwa baffan magana inyaso sai abasu lokaci zakiga in suna son junan su...

" Mama ce tatashi tashiga daki nan takira aisha tagayamata...Aisha ce tace ai mama kece baki saniba yasmin ta dade azuciyar dr ai ke dai kawai kiyimata addua Allah yasa alkhairi ne ...." inshaa Allah sannan ta goge hawayen ta dama zanga auren yasmin Allah nagode maka...


Alhaji haruna ne yafito yaga baffa ya chanja mota tsayawa yayi yana kallon ta can yace kace kafara sayar da kawonan mutane kazama dan fashi ko dan mafiya in ba mafiya ba uban wa zai baka kudinnan dakake samu...

" Baffa babu abunda yace sannan ya huce bangarensa....

" Nan hankalin su isa haruna har su khalil ma duk yatashi sai jafa'i suke jawo mada... matar isa inna itace tayi magana tace ai bakuga komai ba tunda zalunci kuka saka agaba...

A lokacin dr sageer ya shigo kallon motar yayi tayi bala'in kyau sannan yace musu sannunku ya shiga part din baffa bayan sun gaisa da baffa sannan ya shiga cikin palour hajiya da mama suna zaune suna hira yayi musu sannun su sannan yace mama ina yasmin?

" hajiya ce tace me zakayi mata da tsohon daren nan?

" hajiya sak'ona zan karba

" Tana daki bari na kirawo ta tana fitowa yarasa me zaici mata sai kallon ta yake sai kuma yace turamin suratul bakara please...

" hajiya tace ina na wayarka? " hajiya nayi deleting dazu bansaniba....

" Yasmin tace bari na dakko maka memory din sai kayi copying...

" sauri nakeyi please ki mikomin mota..

Tana fita ta tarar dasu carko carko suna ta gulma karasawa tayi tace ya dr gashi karba yayi yace wallahi nakasa sukuni kwatakwata so nakeyi kawai naganki shiyasa na biyo domin naganki zani gayamiki son da nake miki cikin raina zankula dake please ki kula dani...

" Shiru tayi tana kallonsa domin kalar tasa kaunar tana burgeta...

" Darajarki a zuciyata tana karuwa, Wahalar sonki nashata sam bana damuwa, wallahi banki ace yau zaa daura auren mu ....

" Murmushi tayintace kayi ahankali karsu mamee suji please...

" To yaushe zaki bani amsata??

" zanbaka ga wannan sannan ta juya tana zuwa gurin su mamee maryam tace iyayan asiri za'a asurce shine, khalil ne yace ai dr bazai aureta ba komai nacinta a daije akare da masu faskare....

" Yasmin ce tace Allah ko ke ai zai soki sai kije ki aure shi tunda ansaba bin dutse...can tace ko bahaka ba Alhaji....

" Nace ubanki ne yake bin kan dutsen banza masu yankan kai....

" ubana yafi karfin ku wallahi nangani nan bari nagaba yayi gaba sannan nan tashige....

" Hajiya tace ke dawa yasmin nida wayannan 'yan rainin hankalin...

" Mama tace banson tsokana salan suzo su zazzageki...

Dr yana shiga brstr ramlat tace munafiki tsinanne mai bin mata kagama kazantar taka shine kashigo???

" Cikin zafin rai yakifa mata mari mara mutunci naga take taken ki wallahi sai kingane kuranki mara mutunci duk hakurin danakeyi dake??

" hakurin me to wallahi sai dai kazaba ko kafasa kara aure kokuma nabar gidan ....

" Waya hanaki bari tafi yanzu ma sai kindawo kuma aure nan da 2month sannan yashiga daki kuka takara saka gashi tajawo sunyi fada gashi tana bukatar mijinta dakin ta shiga ta kwanta akan gado kusan awanta 2 tanata juye ahaka har dr ya fahimce ta nan yafara sarrafata har hankalin ta yatashi daga nan tafara kissing dinsa cikin kidemewa har sai da suka shiga wata sabuwar duniya....

Da asuba rabia ta kirata tace lallai kibar gidan kitafi gida yazaba ko ke ko aure...aikuwa ta biyewa rabia da safe tatafi....

" ya shirya zai tafi aiki ya kirata ta gaggaya masa magana cikin zafin rai dakyar yake tukin har ya'isa kofar gidan ya kira yasmin yace please tafito zata ga black mota...

" Mayafin ta ta yafa sannan tafito ta bude motar tashiga cikin damuwa da idanun sa sukayi jajir yace zaki aure ne yasmin please kada namutu...

" Yasmin ce tace so ai baya kisa...

" Amma kema kwanakin baya aikin san zafin soyayya da masoyin ki ya gujeki ko??

" Shiru tayi tana kallonsa...

Dani dake akwai alak'ar mu ta 'yan uwa, zuciya tawa ke ta kama, komai wahala dake zani kasance, Alkawari ki rik'e komai wuya kar mu rabu kinji... rashin yarda dani zaisa nafada halaka ki taimakawa ruhina kisoni danAllah ni ke nake so yasmin...

" Cikin hawaye tace kai daya na yarda muyi soyayya acikin ruhina, banyi zaton zan kamu da soyayya a nan kusa ba, Na baka dama kasan kaunar ka, tabbas nagani bani da tamka kaine kadai zabina, kai kagwadamini son da kakemin dan na shaqu da da kai, sannan ta rike hannun sa tace na baka amanar kai na...


Assalamu alaikum

Kuyi hakuri masoyan wannan littafin tabbas ina cikin busy ne shiyasa banayin post akai akai Kuyi min afuwa masoyana ina tare daku....

Ko yakuke ganin wannan soyayya???

Yasmin da dr sageer sun dace??

Barister ramlat wane hali zata shiga in taji labarin yasmin zai aura???

Wacce irin k'awace rabi'a??

Ko yaya auren su dr zai kasance???

*WANNAN SHAFIN SADAUKAR WACE GAREKI MATAR KIRKI MATAR K'WARAI UWA GA 'YAN BIYU WATO ANTY MAI JIDDA ALLAH YASAKA MIKI DA ALKHAIRI YAKARA SOYAYYA DA MAIGIDA*


_I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's_

*How was the page???*

_Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS


*Wadãtar zuci {Qanã'a}*

Duk wanda ya wadãtu da abin da Allah SWT ya bã shi; to, zai sãmu nutsuwar zuciya da kuma dãcewa a rãyuwar duniya da qiyãma.

Allah SWT yana fad'a cikin suratun Nahl ãya ta (97) cewa:
(( Wanda ya aikata aiki na qwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mumini, to, haqiqa, Muna rãyar da shi, rãyuwa mai dãd'i. Kuma haqiqa, Muna sãkã musu lãdarsu da mafi kyawun abin da suka kasance sunã aikatãwa )).

Manyan Malaman Tafsirin Alqur'ãni da yawa sunce game da wannan ãyar shi ne:
( Rãyuwa mai dãd'i a duniya shi ne wadãtar zuci ).

Sannan kuma duk mai wadãtar zuci yã rabauta bisa ga abin da Allah SWT ya bã shi, kuma ya kasance arziqinsa dai-dai buqãtunsa, wato ya kasance tsakãnin yalwar kud'i da kuma talauci.

Don kasantuwar komai tsakã-tsaki shi yafi; Nawa nawa ne mai kud'in da kud'insa ya shagaltar da shi ga barin sanin Ubangijinsa ! Kuma nawa nawa ne talaka wanda talaucinsa da neman abincinsa ya shagaltar da sh
Arewablog.com.ng

Post a Comment

Previous Post Next Post