SANADIN GATA PART 2 (HAUSA NOVEL)

PART 2

Bayan an kammala wasan ne ya koma gida lokacin Patricia ta tafi amma tabar masa wasika cewar zata rinka kawo masa ziyara akai akai domin ta yaba dashi, murmushi yayi tareda dunkule hannunsa, yanmata kuna son junior i don't know why, amma shi kuma junior yanada yarinyar da yake so ya fada a hankali, kwanciya yayi saboda ya gama gajiya take bacci ya dauke shi.

Washe gari sai 11 ya shiga makaranta bayan ya dauki dressing kai idan ka ganshi zaka rantse ba musulmi bane saboda yadda yayi dressing din,bashi da maraba da mawakan kasar turai, su kansu daliban da yawa ba su san musulmi bane domin ko sunansa basu saniba, sudai sunji kawai ana kiransa da junior, to masu karatu ma dai basu san sunan junior na asali ba, yakamata muji waye junior
      ***************
Abdulrahman Kabir Madaki shine cikakken sunan junior, mahaifinsa Alh Kabir madaki shahararren dan siyasa ne domin shine chairman party na kasa a jam'iyar LLP kuma dan kasuwa wanda yayi suna akasashen duniya, matarsa daya hajiya Fati, basu taba haihuwa ba sai akan junior wannan dalilin ne yasa suke sonsa fiyeda kima, tunda junior ya taso baya jin magana bashida girmama na gaba dashi domin bai taso cikin tarbiyar da ta dace ba, ko a makaranta ba a dukansa domin bai san wani abu wai shi discipline ba domin mahaifinsa ya hana adakeshi ko wanne irin laifi yayi, junior ya tashi cikin gata da kulawar iyayensa kuma tun yana dan karami yake abota da mata sam shi bashi da aboki namiji sai bobo, ko lokacin da yana karami idan jawahir tazo gidansu to tare suke kwana mom bata hanawa babu ruwanta da cewar ba gender dinsu daya ba, ga junior da rashin jin tsiya, he's naughty, unruly, rude, and cheeky boy, amma kuma duk da haka he's brilliant, gifted and talent domin baya wuce na first position.
Duk makarantun sa na kudi yake yi tun daga primary sch har zuwa high institution gashi da son kwallo tun yana yaro, ya iya kwallo sosai kusan kowanne lokacin kaje gidansu zaka sameshi yana buga ball, wannan dalilin ne yasa dad dinshi gina masa katafaren filin kwallo inda zai rinka bugawa hankali kwance, asalin mom dinshi shuwa arab ce kuma mahaifinta sarkin borno ne, wannan na nufin junior jikan sarki ne, shi kuma mahaifinsa dan asalin jihar jigawa ne a wata karamar hukuma da ake kira da birnin kudu cikin wani kauye wai shi chiyako.

A lokacin da junior ya dan tasa ya zama saurayi to alokacinne mom dinshi da dad dinshi suka sakar masa ragama dama dad dinshi he's lenient, permissive person, mutum ne da bashida matsawa yaro musamman ma junior domin ko tsawa bai taba yi masa ba balle har ta kaisu ga duka, ko salla junior baya yi  ga kula yanmata kamar me, har gida yanmata ke biyoshi amma babu ruwan iyayenshi basu taba tsawatar masa ba akan haka, lallai wannan shi ake kira da SANADIN GATA, a sanadiyyar gatan da yake samu daga iyayensa yasa yake kallon komai a banza.

3⃣9⃣
  Lokacin da junior ya girma yakai matsayin saurayi har lokacin bai daina kwanciya jikin mom dinshi ba kai har yanzun nan junior yana dora kansa akan cinyar mom, dad kuwa kamar wani abokinshi haka ya zama,sai dai tun lokacin da ya zama saurayi dad ke yawan bashi labarin yan uwansa to amma har yau bai taba ganin dangin dad dinshi ba amma mom dinshi yasan familyn su.

   CIGABAN LABARI 

Kansa tsaye Barack Obama Hall ya nufa inda ake gudanar musu da lecture, wata farar malama ce wadda shekarunta zasu kai 35 kuma da alama sabuwar malama ce, wucewa junior yayi da niyyar zama hee! Tafada get out, you naughty boy, kallonta yayi ya dan harare ta yajuyo zai fita, zo nan ta sake fada, dawowa yayi ya tsaya, meye sunanka, Abdulrahman Kabir, meye registration number ka? 002 yafada yana lasar lebensa na kasa ok fita anjima ka sameni a office dina, fita junior yayi yanufi wurin da dalibai ke hutawa idan sun fito daga lecture, anan ya zauna har Mrs funke tagama lecture dinta tafita yana ganin fitarta yabi bayanta, har office dinta, tana zama ya shiga, kallonsa ta fara kai meye ma sunanka? Junior ya fada yana lumshe mata ido, kai baka da kunya ko? Kallonta yayi ta gefen ido tasha t shirt da jeans mai tsada, sorry ma ya fada agankali, rubutu tafara yi, tunda akayi resuming ba kadawo sch ba sai yanzu why? Bai bata amsa ba, biron aljihunsa ya zaro ya faketa yayi rubutu ajikin wani file dake kan table dinta I LOVE YOU MA, ya rubutu ba tareda ganiba, tana dago kanta tajawo file din nan taga rubutun da Junior yayi daga kai tayi ta kalleshi, shi kuma yana ganin haka ya dauke kansa ya basar, you naughty,kai wayasa kayi min rubutu anan?? Unrespectfull boy,Am sorry ma ya fada yana kallon fuskarta, do i look like your playing pertner? tafi sai anjima tafada lokacin da take ci gaba da rubutun da takeyi ajikin file din.

Tun daga lokacin wannan malamar ta zama budurwar junior amma shidai ba sonta yake ba kawai iskancine irin nasa, amma ita dagaske sonsa take shi kam bata yi masa ba dan ta girme masa nesa ba kusa ba, tun lokacin da yadawo sai ya gadama zai je makaranta idan bai gadama ba kuma sai yayi kwanciyar sa adaki yayi baccin sa da haka har semester tayi nisa alokacin ya shirya yazo ganin gida, ranar da zai dawo mom ji tayi kamar tayi tsuntsunwa taje ta daukoshi, girki kuwa ya sha su kala kala, karfe 3 ya sauka afilin saukar jirage na malam Aminu kano, yana isowa gida mom ta rungumeshi, yasha suit ash colour yayi fresh dashi, har yau gashi nan makale da dankunne da sarka katuwa awuyansa, ga wani sajensa da ya gyara shi yayi kyau, sumarsa kamar yayi mata shamfo dan baki, kansa ya kwantar akan cinyar mom, momyna nayi missing dinki, nima nayi kewarka junior, momy ta fada tana mai shafa sumar kansa, yanzu ka kwanta ka huta kafin na baka abinci kaci, to mom bari naje dakina, dakinsa ya shiga wanda aka sake masa sababbin furniture sai kace wani dakin amarya, kayan jikinsa ya cire ya kwanta, shi dai yana son bacci bashida aiki kusan kullum sai bacci.

Kwanansa hudu da dawowa budurwar sa Lana takawo masa ziyara, mom da murna ta karbeta nan junior ya kai mata kayanta cikin dakinsa amma mom babu ruwanta don lokacin da ta shigo ma junior na kwance akan kujera ya tasa kai da cinyar mom daga shi sai dan gajeren wando da riga yar body hug, yana jin sallamar Lana yaje ya rungumota ya shigo da ita cikin dakin, kalubale gareku iyaye wannan Sam ba wayewa bace ya kamata mu farka daga dogon baccin da muke, hannun Lana yaja zuwa cikin bedroom dinsa, Lana you have surprising me, how comes? I never expect you this time, wow! Junior don't talk like this again, ai na fada maka dama i will give you a surprise visit, yanzu kazo muje ka nuna min garinku, tashi Junior yayi yanzu kuwa Lana, yanda yake haka ya dauki key din motarsa ya ja hannun Lana suka fito, mom bari na kaita gari mu dawo, to junior adawo lfy mom ta fada tana murmushi.

Wata dalleliyar mota mai kyau kirar Lexus junior ya dauka suka fita shida Lana, tunda suka fita suke zagaya gari har yamma tayi, bayan ya nunnuna mata wurarene ya kaisu 11 stars hotel anan ya kama musu daki, suna shiga Lana ta kalleshi junior meyasa baka kara dawowa gidanmu ba?? Karki damu Lana yanzu dai ki barni nasha koko tukunna sai muyi magana idan na koshi, mursmushi Lana tayi oh junior case, bakinta yakama da nashi ya fara kokarin nuna mata matsuwarsa, sai dare suka baro hotel din suka koma gidansu junior

4⃣0⃣
  Kwanan Lana hudu agidan su junior, kullum sai sun fita sunje hotel sun shakata da haka har tayi musu sallama ta tafi, kayan goma ta arziki mom ta hada mata yayinda shima dad ya yi mata kyautar kudi mai tarin yawa, haka junior ya gama hutunsa yakoma sai dai har ya koma bai sake haduwa da kuluwa ba amma duk da haka yasha alwashin nemota a duk inda take.
     ****************
   Kuluwa ce zaune ita da ummi sai shirya kayansu suke yi cikin trolley babba wacce, zasuyi tafiya da ita,kallon kuluwa ummi tayi hawwa nikuwa ina saurayin nan naki? Waye saurayina?? Abokin fadanki, sai da gaban kuluwa ya fadi, oh ni tun lokacin nan ban sake ganinsa ba ta fada tana ninke rigar hannunta, tunani ta tsunduma ko yanzu yana ina? Saboda na jima ban ganshi ba amma gayen nan ya hadu matsalarshi daya ya lalace SANADIN GATAN da iyayenshi ke nuna masa amma ni nayi alqawarin zan gyarashi ya dawo cikakken mutum mai cikakkiyar kamala kuma zan aureshi, zan rayu dashi rayuwa mai dadi, duk wadannan zantuttukan da kuluwa take yi acikin ranta take yinsu, da haka suka karasa shirya kayansu suka tarkata suka tafi abuja wurin anty salma kasancewar yanzu sun gama karatu har sun fara neman admission a jami'a, ita ummi tana nema a north west, ita kuma kuluwa tana neman b.u.k, lokacin da suka je abuja ita dai kuluwa hankalinta na kano domin tasan ta bar junior a kano ita kuma shi take nema ruwa a jallo, yanzu ita da ummi basuda wani aiki sai kallo sai kuma yawon ganin wuraren shakatawa.

  Misalin karfe 7 na dare kuluwa tazo ta zauna gaban tv ta kunna, channel din ta canja zuwa wata har zata wuce saboda ganin ball ake yi sai taga wani kamar junior barin tashar tayi tana mamakin to me yakai junior kasar ghana? Saboda taga ball din da ghana da brazil ake bugawa, bayansa aka hasko, JUNIOR tagani arubuce, lah ashe shine, wlhi shine ta fada tana sake kallon tv din, Wasa ake gadan gadan cikin mintuna kadan junior ya zura kwallaye har guda uku acikin raga, da lokacin aka tafi half time wato hutun rabin lokacin. Ku sakarkaru ne kun bar wancan yaron sai kwallo yake zurawa to wlhi idan aka koma ku tabbatar ku karya kafarsa yadda zai fita gaba daya, wannan maganar coach din yan brazil kenan wato mai horar da yan wasa, kadawa aka yi alamar lokacin ya cika, take akoma aka ci gaba da gudanar da wasa, wani dogone ya fara bin junior a baya, duk inda junior yayi yana biye dashi, da zarar an jehowa junior ball zai kwarfe shi ya fadi ya dauke ball din, sunyi haka yafi sau biyu akaro na karshe ne junior ya dau ball din ya nufi raga aguje, binsa wannan dogon yayi yana zuwa ya daki kafarsa da karfe, take junior ya fadi tareda rike kafar tasa, da gudu rafarin yazo ya dagawa dogon jan kati alamar an koreshi daga cikin filin, sukuma likitoci masu kula da yan wasa suka rugo aguje zuwa wurin da junior yake kwance yana rike da kafarsa, kuka kuluwa ta fara, shikenan ya karya shi, wlhi ya karya min shi, Allah ya isanshi, macuci, ya karya masa kafa, ummi ce ta shigo falon ta tsaya tana kallon kuluwa wadda hawaye ya wankewa fuska, daukar junior akayi aka fita dashi ko taka kafar baya iya, waye ya mutu hawwa?? Inji ummi, kallonta kuluwa tayi amma bata furta komai ba ganin haka yasa ummi shigewa cikin daki, kuka kuluwa tafashe dashi saboda ganin an sako wani nadaban wanda zai maye gurbin junior, kuka take sosai kamar wani mijinta, acan gidansu junior ma haka abin yake domin mom ta rasa inda zata tsoma ranta tun lokacin da taga an fita da junior daga cikin filin, hankalinta bai sake tashi ba sai lokacin da taga anyi replacing dinshi da wani, take ta nemi nutsuwarta ta rasa, shikenan sun karya min yaro, daga yau junior yadaina buga kwallo mom ta fada tana kwalla.

Kuka kuluwa taci gaba da rusawa har na tsawon wani lokacin, minti 5 ya rage a tashi daga wasan sai aka fitar da wani, junior ne ya taho yana dan dingisawa take filin ya rude, yes! Kuluwa ta fada tana dariya, junior da karfin hali ahaka ya zira kwallo guda biyu kafin a tashi daga wasan, ana tashi mutane suka taho da gudu suka lullube shi, wani dadine ya ratsa zuciyar ta, um nasan shi har ya manta dani, amma ni ban manta dakai ba junior ta fada lokacin da take kokarin kashe tv din.

   Watansu kuluwa 2 a abuja suka dawo kano saboda sun sami admission a university sai dai kowacce makarantar ta daban, bayan sun dawo ne suka yi registration suka fara halattar makaranta, yanzu kuluwa ta zama yanmata tayi fes da ita kuma tayi kyau ta gyaru sosai, zuwanta b.u.k tayi sababbin friends yan department dinsu da sauran da suke haduwa wurin cin abinci ko wurin salla, medicine shine abinda take karantawa ita kuma ummi tana karantar pol science a north west,amma har yanzu kuluwa bataje kauyen su ba tun lokacin data baroshi rabonta da kauyen su shiyasa wani lokacin take jin kewar mahaifin ta ya kamata.

   A bangaren junior kuwa abin nasa babu sauki sai ma sake gaba da yayi, sai dai yanzu haka ya dawo hutu gida daga kasar ghana, misalin karfe 11:30 bobo yazo gidansu, dakyar junior ya tashi ya fito yana sanye da dark brown din wando iya gwiwa yasa yar body hug baka ajiki an rubuta why always me??,kunnensa kamar kullum da dankunne ajiki, wuyansa kuma yasa sarka, ko wayarsa bai dauka ba ya nufi inda bobo yake motarsa ya dauka kirar optima kalarta ruwan toka, tare acikin motarsa suka fita shida bobo, kallon bobo yayi ina son shiga b.u.k domin naga yadda su nasu yanmatan suke, dariya bobo yayi muje nima akwai wanda zanga aciki, suna tafe junior yana bawa bobo labarin budurwarsa malamarsu wadda ta mace akansa, suna shiga suka fara cin karo da dalibai iri iri, a admin block suka yi packing bobo ne ya fita ya nufi wani office shi kuma junior yana cikin motar yana sauraren wakar d'banj, yana jin wakar yana bi, kamar a mafarki ya hango kuluwa su biyu sun fito daga cikin wani office, ta jikin motarsa suka zo zasu wuje burum ya bude kofar motar ya fito yasha gabansu, dukansu sai da suka tsorata saboda yadda yasha gabansun kamar wanda suka yi masa laifi, kallo daya kuluwa tayi masa ta ganeshi amma ita abokiyar tafiyar tata bata san kowaye ba saboda ba saninsa tayi ba.

4⃣1⃣
   Kallon kuluwa yayi ta danyi kiba kuma ta sake zama budurwa cikakkiya, tana sanye da leshi blue da farin hijabi mai hannu, takalminta ma fari ne, so yanzu kin zama budurwa babu maganar saka uniform ko?? Ya fada yana kallonta, kallonsa tayi ta basar malam lfy? Ido ya dan kashe mata tareda duban kawar tata, baiwar Allah dan bamu wuri zamu yi magana, tafiya maimuna s alkali tayi ta barsu a tsaye, baki gane ni ba?? Dan Allah kibani number wayarki zamuyi magana, nifa banida waya kuma dan Allah kar ka sake kulani saboda mutane suna ganina da mutumci yanzu kuma idan suka ganni da mai dankunne a tsaye zasu yi min fassara kuma mutuncina zai ragu a idonsu, ras yaji gabansa ya fadi, anya kuwa wannan yarinyar zata soshi? Ya tambayi kansa, oh dan nasa earring da chain shine mutumcinki zai zube? Basu kadai ba har wannan kayan jikin naka duk Suna iya janyo min zubewar mutunci, ok to yanzu dai ki bari muyi magana, da wa? Dake mana, a'a kabari duk lokacin da kayi shiga irin ta mutanen kirki sai kazo muyi magana, tana gama fadar haka ta wuceshi tayi tafiyar ta,

gosh! Ya fada tareda dunkule hannunsa ya naushi iska, cikin mota ya koma duk jin zaman yake ya isheshi, wato kenan idan nacire chain dinnan da dan kunnen nan zata tsaya ta saurare ni? It seems kamar wannan shigar da nayi ne bata so, zancen zuci yayi tayi har bobo yazo ya sameshi, jikinsa a sanyaye yaja motar suka fita suka nufi gida, yana zuwa gida ya fada akan kujera a falo lokacin mom bata ciki tana side din dad, nan ya zauna har tazo ta sameshi kamar marar lafiya ya zama, junior lafiya? Mom ta tambayeshi cikeda rudu, lafiya lau mom, dad yadawo? Eh ya dawo dazu, mom dan Allah manyan kaya nake so tun daga shaddodi har yadika, to junior nima dama na dade ina son naganka da irin kayan da yayan manya suke sakawa amma tunda yanzu da kanka kana so shikenan bari ina zuwa, daki mom ta shiga ta dauki wayarta takira tailor din dake yi mata dinki yana dauka tace dashi yaje kasuwa ya siyowa junior shaddodi masu tsada da hadaddun yadika adinka masa idan angama an kawo zata biya kudin, murna ta fara yi oh junior an fara girma da hankali da alama yanzu nutsuwa ta soma shigarsa, falo ta koma inda yake.

Tana komawa ta sameshi yana waya da teemah big girl, zama tayi akusa dashi, kansa ya dora akan cinyar mom, mom yanzu idan nasamu mata zaku yimin aure?? Me zai hana junior na, ai zanso naga matarka da yayanka, uhm amma mom nifa ba yaro daya zan haifa ba ni dayawa nake so, shafa kansa mom tayi Allah ya amsa junior dama yanda kake kai daya agidan nan Allah yasa yara dayawa zaka haifa, amin mom, farin cikine ya shiga ransa domin sai yanzu yaji yana son yin aure kuma yaji yana sha'awar ya fara saka manyan kaya.

Kwana biyu junior yana gida babu inda yake zuwa har sai da aka kawo masa kayansa,aranar ya yi wanka ya shirya cikin shadda sky blue mai tsada, baisa dankunne da sarka ba, sai da yasha turare sannan yayiwa mom sallama ya fita kallonsa mom tayi to kodai junior ya fara neman auren ne?? Motarsa ya dauka mai kyau kirar corotoure ya nufi b.u.k ko takan bobo bai bi ba, a admin block yau ma yayi packing yana nan zaune yana tunanin abinyi kamar daga sama sai ya hango su kuluwa su uku wadda suka fito daga wani office,

sai raba ido takai ta inda zata ga junior domin tunda abin ya faru kullum idan tazo sch bata samun nutsuwa duk tunaninta junior fushi yayi, ranar kasa bacci tayi saboda tana gudun kar ya subuce mata, yana ganinsu ya fito daga cikin motar, ganinsa kawai tayi a gabansu amma tuni ta gane shi, kallon juna suka fara daga ita har shi, yayi kyau sosai yayi wani irin kwarjini, Gashi da kalar yan gayu domin kana ganinsa kasan dan gayune, barka da fitowa ya fada cikin muryarsa mai tsananin dadi da zaki, kallon kawayenta tayi kuyi gaba sai na taho ina zuwa, suna wucewa ya kalleta pls mu shiga cikin mota because am not comfortable for this hustle and bustle, wurin naku yayi hayaniya da yawa ni kuma bana sonta, kamar ba zata shiga ba sai kuma dai taga rashin dacewar haka, gidan baya ta shiga shi kuma yana gaba a mazaunin driver,

malama har yau fa ban san sunanki ba, sunana hawwa ta fada a hankali kai kuma ya sunanka? Sunana Abdulrahman, sunanka junior dai tafada tana kallonsa, eh wannan sunan da mom dina take kirana dashi ne.

4⃣2⃣
Kallonsa kuluwa tayi da alama dai yana ji da mom dinnan nashi sannan kuma tana gatale shi abisa dukkanin alamu, maijidda me yasa kika ki saurarata rannan?? Sai da ta danyi Jim sannan tace masa, kaga nan ai wurin mutane ne dayawa kai kuma ranar a yadda ki fito gaskiya bai dace ba amma yau dressing dinka yayi daidai dana mutanen kirki amma idan kaji haushi kayi hakuri, no ba haushi naji ba wlh dadi naji yadda kika fadamin gaskiyarki kuma naji kin burgeni shiyasa nake son ki zama friend dina idan har ba zan takura miki ba, dan murmushi tayi bana yin abota da maza amma kai bazan ki ba, saboda me? Saboda wani dalili, to nagode da wannan alfarmar da kika yimin, kibani phone number dinki, ai na fada maka banida waya, ok idan na siyo miki zaki karba? No ai agida ne har yanzu ba za abarmu mu rike wayar ba, to ba damuwa zan iya zuwa gidanku? A'a ba za abarni na fito ba, to zan rinka zuwa nan din, babu damuwa sai kazo, to yanzu zanje natafi sai na dawo, ok babu damuwa, nagode, fita tayi ta nufi wurin da kawayenta suke shi kuma junior sai da ya dade a zaune kafin ya tafi, tafiya kuluwa kawai take amma tunanin junior ne yake ratsata koda taje wurin kawayenta ma tambayar ta suka fara yi wai ina tasamo wannan mai kyan? Murmushi kawai tayi mijina ne tafada ba tareda ta sani ba, mijinki? Sai asannan tasan maganar ta fito, acikin ranta tace Allah ya amsa domin abokinsa da matar junior ya kirani bazan taba mantawa ba, ummi ma dana bata labarinsa cemin tayi mijina ne, duk acikin zuciyarta take wadannan bayanan.

Abangaren junior kuwa wurin bobo ya nufa bayan yabar wurin kuluwa, labarin kuluwa ya fara bawa bobo, bobo in banda dariya babu abinda yake yi.

Tun daga wannan ranar junior ya ke zuwa wurin kuluwa a makarantar su yanzu sunyi mutukar sabo da junansu kuma sun shaku kowa yana tsananin son dan uwansa amma har yau babu wanda ya furta, ita kuluwa tana ganin a matsayinta na mace ai bai kamata tace tana sonsa ba, shi kuma junior yana ganin shi duk wadda yayi mata itace take cewa tana sonsa amma shi baya furtawa mace kalmar so sai dai idan bada gaske yake ba sai ya fada amma shi baya cewa mace yana sonta,yau ma tsaye suke ajikin motarsa yana sanye cikin farin boyel yasha kyau har ya gaji duk wanda zai wuce sai ya kallesu amma mafi akasari junior suke kallo ba kuluwan ba domin junior ya hadu iya haduwa komai nasa ya tsaru, kallon hannunsa kuluwa tayi, junior ya kamata ka yanke farcenka fa kaga yadda yayi zako zako, oh yah zan je na yanke sai nakoma gida mom dina zata yanke min, yanken farcen ma mom ce take yi maka?

Eh nifa komai mom dina ce ke yimin, ke barima kiji ni ko abinci mom dina ce ke bani wlh,babu abinda nake yi, yanken farce, abinci da sauran wadannan small small things din duk mom ce ke yimin, to kuma idan ka koma ghana waye ke yi maka?? Farce Patricia ce ke yanke min, take kuluwa ta hade rai ta bata fuska, wacece haka? Junior wai meyasa kai baka jin tsoron mace ta tabaka? Babu kyau fa wlh akwai wani hadisi dana taba karantawa da mutum ya taba matar da ba tasa ba... To ke wai wa ya ce miki tabata nayi? To in ba tabata kayiba me kayi? Allah ya baki hakuri, yabaka hakuri dai, amma dan Allah kasamu islamiyya ka rinka zuwa kana jin hadisai da fassarar littafi mai tsarki, nagode da wannan shawara, zan barki haka zanje gida kin san jibi zanje ghana, gabanta taji ya fadi saboda sai duk taji hankalinta ya tashi da zai tafi, ina sonka junior ta fada aranta, meyasa zaka barni? Takara fada acikin ranta, sai nazo sallama gobe, ok babu damuwa, sallama suka yi yatafi.

Tunda yaje gida ya zauna yayi tagumi domin ya rasa yadda zaiyi da son kuluwa dake azalzalarsa gashi shikuma yarasa dalilin da yasa yake nauyin bakin sanar mata da sirrin ranshi, washe gari haka ya shirya yana cikeda damuwa ya nufi b.u.k amma kananan kaya yasa yayi kyau sosai amma sumar sa tana nan tuli guda yakasa askewa domin yana son sumar nan bayajin zai iya asketa, inda suka saba zama yauma anan suka zauna kowannensu zuciyar sa cikeda kuncin rabuwa da junansu da za suyi, kamar marassa lafiya suka dan taba hira,

kallonta junior yayi kinga gobe zan koma ghana, eh nasani Allah yakaika lafiya sannan kuma akoda yaushe ka rinka tuna hakkin Allah akanka, ka tsare hakkokin Allah da suke kanka, insha Allah ya fada yana kallonta da idanuwansa wadanda suka danyi ja, ita kanta kuluwa ji take kamar ta fashe da kuka, sanin idan yaci gaba da ganin kuluwa zai iya yin kuka agabanta yasa shi yi mata sallama ya tafi.

4⃣3⃣
Hawaye ne suka sauko akan kumatunta duk yadda taso dannewa hakan abin yaci tura dole sai da junior yaga kukanta, meye abin kuka ya fada cikin dauriya da yake shi namiji ne shiyasa shi bai yi kukan ba amma yana yin nazuci, i don't know why am cry, tafada tana share hawayenta, karki damu jidda zan dawo nanda 3 months ya fada yana dan murmushin dauriya, motar yaja yatafi, yana tafiya kuluwa ta dauki shirginta ta nufi gida tana shiga dakinsu ta fara kuka dama lokacin ummi bata nan hakan yabata damar yin kuka son ranta, gashi duk irin son da takewa junior takasa sanar da ko ummi saboda tsabar zurfin ciki, shi ma junior yana zuwa gida ya shige dakinsa ya zauna wani irin kunci yake jin ya lullubeshi amma bai san abinyi ba, yana nan zaune har mom tashigo ta sameshi, zama tayi kusa dashi taja shi jikinta ta rungume shi, hawaye ya fara yi, dasauri mom ta kalleshi junior meya saka kuka? Mom ina jin haushin rabuwa daku ne, ayya junior kar ka damu kaji haka mom tayita lallabashi kamar wani jinjiri.

Washe gari junior yabar Nigeria ya sauka a ghana ranar kuluwa ko makaranta bata shiga ba saboda tasan idan tashiga damuwace zata addabeta domin zata rinka ganin kamar zata ga junior yazo wurinta alhalin shi kuma baya nan, sai yanzu tayi da tasanin rashin karbar phone number dinshi, dan da ta karba da ko aron  waya sai tayi ta kirashi.

Shima junior tunda ya sauka a ghana yake tunanin kuluwa, wai meyasa ban sanar da ita son da nake mata ba? Kar fa kafin nakoma ta hadu da wani ya sace min zuciyarta, Kalmar da yayita furtawa kenan, wayarsa ya dauka ya kira bobo ya fara bashi amanar jiddansa har da cewa bobo kullum yaje b.u.k yaga halin da jidda take ciki, amsa masa bobo yayi sannan sukayi sallama.

Tun bayan tafiyar junior kuluwa ta shiga damuwa gashi tun lokacin da yatafi bata sake jin muryar sa ba, amma abokinsa bobo kullum yana zuwa wurinta suna gaisawa kullum idan yazo sai tayi niyyar tace masa ya kira mata junior su gaisa sai ta kasa fada da haka har suka fara exam, lokacin kanta ya dauki zafi sosai. Junior kuwa lokacin da ya koma ghana ya fara kokarin canja dabi'unsa sai dai amma yakasa musamman da Patricia ta sakoshi a gaba da ziyarar dole, dolensa yake making love da ita ba don yaso ba.

Bayan su kuluwa sun kammala exams ne anty salma ta shirya musu tafiya kauye ita da ummi musamman ma da taga kuluwa tayi yar rama to sai tayi tunanin ko damuwar gidace ta sata shiga damuwar dan haka lokacin da suka gama exams sai tace su shirya su tafi kauye suje can suyi hutunsu acan.

4⃣4⃣
Shiri sukayi sosai na tafiya domin kuluwa tunda ta baro kauyen nan bata taba zuwa ba sai wannan lokacin, duk abinda suka san zasu bukata sun dauka, aranar asabar da yamma suka sauka a kauyen chiyako wanda a yan shekarun da kuluwa tayi ba tajeba taga an samu ci gaba sosai, anyi titi ankai wutar lantarki ga gine gine da aka yiyyi, ga burtsatsen diban ruwa sun wadata da rijiyoyo.

Har kofar gidansu driver dinsu ya kaisu babu abinda ya canja na gidan tunda ga ginin har cikin gidan, da sallama suka shiga, iyatu ana zaune ana iza wuta ta dan tsufa gefenta kuma mahaifin kuluwa ne, zumbur iyatu ta tashi, kuluwa sannu da zuwa kulu, fara'a mahaifinta ya fara sannu da zuwa hawwa, yanzu kuke tafe, jakarsu iyatu ta kinkima takai daki ita dai kuluwa duk abin ya daure mata kai ganin yadda iyatu ta sauya.

Tabarma iyatu ta shimfida musu suka zazzauna aka fara gaggaisawa ido iyatu ta zubawa kuluwa ganin yadda ta goge tayi kyau tayi kal kal da ita gashi ta zama katuwa sosai, tacika ta zama cikakkiyar budurwa, mahaifinta kuwa bakinsa yaki rufuwa dan farin ciki domin yaji dadin ganin kuluwa yadda ta sauya tayi kalau da ita, da alama burinsa zai cika. Sannu kulu ina maman naku? Iyatu ta tambaya duk ta zama abun tausayi dama haka rayuwa take, abunda ya baka tsoro watarana shi zai baka tausayi.

Daren ranar har 12 suka kai suna shan hira gaba dayansu sai wurin 1sannan suka shiga daki ananma kuluwa da ummi wani babin hirar suka bude har 2 tayi sannan suka kwanta akan gadon karfen iyatu. Washe gari da safe suka shirya suka nufi gidan Mairo kawar kuluwa, suna tafe suna kallon canje canjen da aka samu agarin, gidan mairo suka shiga tana zaune da yaranta guda 2 duk maza, sallamar su kuluwa ta sata juyowa tana ganin kuluwa ta tashi da gudu ta rungumo ta, nan suka zauna aka fara hirar yaushe gamo. Kuluwa baki tambayi shamsu ba? Hmm yana ina to? Yayi aure ai bada jimawa ba, ayya Allah ya basu zaman lafiya, amin kuluwa saura naki bikin.

Kallon Mairo kuluwa tayi yanzu Mairo har kinyi yara biyu? Har natuno lokacin danazo kina amarya kike bani labarin daren farkonki, dariya Mairo tayi ehh ai gashi yawuce saura naki, dan nasan kema zaki dandana, dariya kuluwa tayi aranta tace har na hangoni nida junior acikin wannan yanayin ranar nasan zansha lasa kuma shima zai sha lasa ko ta ina.

4⃣5⃣  
Shiru tayi taci gaba da sassaka abun aranta domin ita duk lokacin da take hangota da wani namiji to junior ne, dariya ummi tayi wannan uwar tsoron ai mijinta ya banu dan wlhi ranar sai ta kashe masa dodon kunne, dariya kuluwa tayi wlh indai gayen da nake sone sai dai ma na kara masa karfin gwiwa amma idan ba shi bane sai ahankali, ai kuwa zakisha wuya dan da wahala inji Mairo, to ai Mairo tun zuwan da nayi kika bani labari tun daga lokacin naji tsoron maza ya shigeni, ke fa na dare dayane, Mairo tafada tana dariya, duk da haka dai, haka suka sha hirarsu sannan suka yiwa Mairo sallama.

Suna zuwa gida suka san anyi baki saboda ga wata jibgegiyar jeep nan akofar gidan, haka suka shiga suna cikeda mamakin ko waye yazo? Suna shiga gidan suka tarar da baki mace da namiji ga body guard dinsu a tsaye, cikin girmamawa suka duka suka gaishesu, kuluwa ga dan uwana Alh Kabir Wanda yake birni, wannan kuluwa ce ga ummi kuma yar gidan Salma, ah sune wadannan? Eh sune ai awurin salman ma suke acan birni, masha Allah kyakkyawar matar tafada,ya karatu lfy lau su kuluwa suka amsa tareda tashi suka shige daki, kallon burgewa matar tabisu dashi, suna shiga daki ummi tace kuluwa wannan shine dan uwansu anty? Eh dama kin san su ukune, kinga ikon Allah yau gashi yazo dan uwan nasu.

Kallon mahaifin kuluwa dan uwan nasa yayi,ahamadu nidai ina tunanin yarinyar nan hawwa ahadata da yaron wajena kaga shikenan zumunci ya kara kulluwa, murmushi Baban kuluwa yayi to ai yarka ce dama Kaine zaka aurar da ita tunda kayi mata miji shikenan, ko yanzu kace ayi sai a daura, a'a ahmadu abari sai sati na sama zanzo adaura auren, murmushi matar tayi wannan abu yayi daidai Allah ya sanya albarkarsa aciki amin dai iyatu ta fada dan yanzu ta saduda, sai yamma dan uwan Baban kuluwa ya tafi shida matarsa.

Su dai su kuluwa basu san abinda ake yi ba kullum sai dai suyi wanka su nufi gidan Mairo can zasu jima suna hirar aure, ai aure akwai dadi Allah ya Baku mazaje nagari dan ku debi romon dake cikin aure, baki kuluwa ta tabe amin dai dan ni wlh ina tsoron maza namiji dayane bana jin tsoronsa, shima zaki ji tsoronsa sai ranar, ni kin ganni har yau ban daina tsoron abban kalifa ba saboda bai bani dadi ba wuya yabani ranar, dariya kuluwa tayi wai ni nashiga uku, dan nasan ranar dogon suma zanyi dariya su ummi da Mairo suka fara yi mata.

Sai da suka gama shan hirarsu suka taho gida suna zuwa suka tarar da baban kuluwa a tsakar gida zaune, kiransu yayi yafara sanar musu da batun auren kuluwa wanda za a daura gobe, jikin kuluwa ne yafara rawa amma bata musa ba saboda tasan mahaifin ta bazai yi mata zabin banza ba amma tasan da ciwon son junior zata bar duniya.

Mazewa kuluwa tayi ko kwalla bata yi ba, amma ranar bacci baiga idonta,washe gari dan uwan mahaifinta yazo da jama'arsa aka daura auren kuluwa da angonta Abdulrahman, bayan an daura aure ne su anty salma suka zo suka dauke ta ita da ummi sai birni ita dai kuluwa ganin abun take kamar a mafarki, wai yau ita aka daurawa aure babu ko shiri, yadda taci burin aurenta amma sai gashi yayi mata zuwan bazata, wani gawurtarccen gida aka kaita a unguwar jan bulo da zummar washe gari za a kaita gidanta.
      *************
A bangaren junior kuwa yana can ghana yana fama da ciwon son kuluwa, ana cikin haka dad dinsa yayi masa waya yace yana son ganinsa nan da sati biyu, cikin rudewa yace dad lafiya kuwa? Saboda duk a tunaninsa wani abun ne ya faru a gidan

Lafiya lau junior kasan dai nadade ina nuna maka gata ko? To SANADIN GATAN da nake yi makane yasa na daura maka aure da yar dan uwana hawwa'u, ajiyar zuciya junior ya saki to dad babu komai Allah ya kaimu zanzo amma duk da haka dad zan sake aure nan da shekaru 2 lokacin budurwar da nake so ta kammala sch, to junior Allah yayi maka albarka, amin dad agaida mom kafin nazo, kashe wayar junior yayi ya lumshe idonsa ya fara hango suffar jiddansa, bakace ba can ba amma yafita haske bata da tsayi sosai sai dai tsayinta daidai misali yake gata da dan jiki madaidaici sai dai yanzu tazama yar lukuta, tanada abubuwan da yake so ajikin mace, fuskarta zagayayyiya ce mai dauke da dan tsukakken baki da hanci dogo da fararen idanuwa, duk da yasan yafita kyau to amma ta burgeshi.

4⃣6⃣
Shirin tafiya gida ya fara, dakyar ya lallaba Patricia ta yarda ta kyaleshi sukayi bankwana.

A bangaren su kuluwa kuwa kayayyaki sosai mahaifiyar mijinta ta siya mata tun anan tasan dan nasu dan gatane kuma suna ji dashi,  ga manyan mata da mom din angon ta gaggayoto aka zo aka gudanar da wani hadadden lunching wanda aranar aka shirya kuluwa cikin leshi pink mai tsadar gaske, ba karamin kyau kuluwa ba, kwansu 3 agidan aka rakata gidanta wanda yake girke a unguwar shagari quarters, uwar mijinta da kanta takaita gidan wanda aka gyarashi yasha kayan alatun more rayuwa, dan zamanta agidan su mijin nata taga abubuwan ban mamaki kala kala domin uwar mijin nata itace ta zage ta gyarata tsaf tayi mata gyara na musamman ta tsumu gaskiya wannan matar tana ji da dan nata. Tunda aka kaita ummi tatafi tabarta amma har lokacin kuluwa ko hawaye batayi ba sai dai tasan tana son junior kuma gashi ta rasashi, washe gari sai ga anty salma da ummi sun dawo, kayane cikin viva na mata anty salma ta kawo mata tareda yi mata bayninsu dalla dalla, wlh idan baki sha ba nadawo sai naci mutuncinki, to anty tafada tana kallon kayan, bayan su anty salma sun tafi ne tafita gidan nata ta fara zazzagawa, gidane katon gaske wanda ya amsa sunansa gida, ga ma'aikata masu tarin yawa komai yi mata za ayi.

Ranar litinin da daddare junior ya sauka akasar Nigeria, gidansu yaje nan mom ta rungumeshi da murna tareda yi masa albishir na auren da sukayi masa, wanka yayi yaci abinci ya shirya ya nufi gidan nasa lokacin karfe 10 na dare, lokacin da ya shiga gidan jin jikinsa yayi yai sanyi ahaka ya karasa amma bai shiga sashen amarya ba sashensa ya wuce ya kwanta saboda agajiye yake sosai.

   Kamar kowanne dare yauma kuluwa tayi shirinta na bacci jin alamun shigowar mota gidan yasata kudundunewa tareda kankame jikinta wuri daya tana addu'ar Allah yasa ba angon bane yadawo, tunanin junior ta fara Allah sarki junior narasaka har abada duk irin son da nake yi maka ashe bazan sameka ba, idonta ta rufe ta fara hango rabuwar su, junior akwai kyau saboda duk budurwar da ta ganshi sai ta fada mata tace mata wannan saurayin naki kyakkyawa ne,shiyasa wani lokacin take kishin zuwansa b.u.k dinma.

4⃣7⃣
  Hawayene suka fara sauka akan kumatunta, juyawa tayi ta rungume filo, duk rayuwarta ta tsarata ne kan zata yita da junior kuma taga alamun nasara domin yana jin maganar ta kuma yana daukar shawarar da duk ta bashi, gashi kanta tsaye take fada masa maganar da ranta ke so wacce ya kamata ace yayi fushi amma sai kaga bai yi fushin ba da alama dai ba mai saurin fushi bane kuma bashida zazzafar zuciya.

  Tunanin wani lokaci da yaje b.u.k tafara, suna tsaye suna yar hirarsu ta duniya dan ba za ace ta soyayya ba domin duk cikinsu har yau babu wanda ya taba tona asirin zuciyar sa, wayarsa ce tayi yar kara ya daga, hello teemah, kin samu sakona? Yayi miki kuwa? Ya suka zama? Sun kara girma? No dan Allah kiyi using da wannan abun ke naki sun cika kanana da yawa, kallonsa kawai kuluwa ta tsaya yi ya wani saka hularsa agefe shi yadda ake saka hular ma ba haka yake saka tashi ba amma yadda yasaka tasan sai ta bada wani style na musamman kuma tayi masa kyau sosai, kashe wayar yayi yana dariya, amma ita kuluwa ta cika fam tayi dam sai tattare girar sama da ta kasa take yi tasha dogon hijabi har kasa babu abinda ake gani ajikinta daga fuskarta shikenan dan ko hannunta ba a gani,

shi kansa Junior duk da bai taba ganin surar jikinta ba amma yasan ta mallaki komai na ya mace gata yar lukuta kamar ummi A'isha, harararsa tayi meye haka? Wlh kaji kunyar duniya data lahira, me nayi?? Kawai dan kinji ina yin waya sai kice haka? Oho maka amma wlh ka rage sabon Allah domin kaima zaka haifa shiyasa nake tausayawa matarka domin bata yi sa'ar miji ba, nikuma kinga nayi sa'ar mata saboda matata wlh mahaddaciya ce mai son addini, she's pious lady, baki kuluwa ta tabe, Allah wadaran naka ya lalace tana gama fadin haka ta juya tayi tafiyar ta,

murmushi junior yayi yakoma cikin motarsa ya zauna, a tunanin kuluwa daga ranar ba zai sake dawowa ba amma sai gashi ya dawo, maimakon ita tabashi hakuri shine ya fara bata hakuri akan abunda ya faru jiya, kuma tun daga lokacin da ta hanashi saka sarka da dan kunne ba sake ganinsa dasu ba, suma ce dai yakasa askewa

4⃣8⃣
   Tun daga lokacin ya daina yawo da boxer da yar t shirt sai dai agida, amma komawar sa ghana bai daina yawo da sarka da dan kunne ba, tunanin junior tayi ta tayi barkatai har bacci ya dauke ta.

A dakin junior kuwa kwance yake cikin bargo gashi ana dan yin sanyi a garin,tunanin jiddan sa ya fara, bashida niyyar yin jayayya da auren da su dad dinsa suka yi masa domin yasan dan suna sonsa ne asalima SANADIN GATAN da suke yi masa ne yasasu aura masa matar da suka aura masa ahalin yanzu, sai dai fatansa Allah yasa jidda ta yarda tazo a second wife dan yaga kamar tana da kishi, kudundunewa yayi sosai kamar wani karamin yaro saboda shi ko agida alokacin sanyi mom ta rinka kai komo kenan akansa saboda tasan akwai shi da jin sanyi shiyasa a dakinsa na gida harda heater sannan blanket dinsa ma mai heater ne yanda idan yaji babu sauki zai jona shi ajikin socket yasha duminsa, amma gashi anan babu ko daya.

Baccine yayi awon gaba dashi sai dai sanyi yakasa barinsa ya sake har gari ya waye bai yi wani baccin kirki ba, sai 11 yatashi alokacin yayi wanka yayi sallar safe ya fito zuwa falo, yana tafiya da cumb a hannunsa yana taje sumar kansa,

ita kuwa kuluwa tun asuba ta tashi tayi salla ta koma ta kwanta domin babu abinda take yi komai akwai masu yi mata hatta girki kuku ne ke yi mata shi, sai 9 ta tashi tayi wanka tasa atamfarta rigada skirt tasa hijab ta fito zuwa kitchen daidai lokacin junior ya fito,yana ta fito da bakinsa kamar yadda al'adar sa take saboda bashida abunyi kullum daga waka sai fito, buruntun da yaji anayi acikin kitchen ne yasa shi shiga kitchen din, bayanta ya hango tana hada tea hello! Ya fada ahankali, juyowa tayi caraf suka hada ido, me yakawo ka gidana da sassafe? Tafada tana kallonsa, shigowa cikin kitchen din yayi daga shi sai boxer baki da shirt fara, ke zan cewa me ya kawoki gidana da sassafe ko kin san matar tawa ne? Oh kenan kaine angon? Kenan kece amaryar? That's great, juyawa kuluwa tayi cikeda farin ciki amma duk farin cikin da take ciki junior ya fita domin shi ji yayi tamkar ya zuba ruwa akasa yasha dan murna, haba shiyasa ko sau daya bai ji ya tsani auren ba ashe jiddanshi ce matar, ajikin bango ya jingina bayan ya harde hannuwan shi a kirjinsa kai Allah shine abun godiya ya fada acikin zuciyarshi, juyowa kuluwa tayi da cup guda biyu rike a hannunta, muje falo ta fada lokacin data wuce gaba, bin bayanta yayi har cikin falo,ga tea ta mika masa, kai ya girgiza ni bazan sha tea ba, to me zaka sha?? Ni koko zan sha ya fada yana lasar lebenshi kamar wani maye,kaji ai, ni yanzu ina zan samo wani koko, ka karbi tea din kasha, kwanciya yayi akan kujerar nafada miki ni koko zan sha, tom kayi hakuri na sa kuku ya dafa maka wani abun, ke nifa agida komai mom ce ke bani har abinci, da safe ni bana shan tea,to me kake ci? Dankali da miya zaki min kuma ki bani koko, nifa na fada maka banida koko ko gasara bani da ita, acikin ransa yayi magana ke kuwa kike da ita kuma nasan kokonki ba irin na sauran bane saboda ke naki fresh one ne, tashi yayi ya kalleta ina zuwa zanje gidan mom yanzu, gidan mom da safen nan junior? Eh ai dole naje saboda akwai kayan kwallona da kayan motsa jikina acan, to kuma ahaka zaka fita?? Dakinsa ya koma ya sako dogon jeans yazo ya wuceta a falo ya tafi gidan mom.

4⃣9⃣
  Yana fita ta rakashi da murmushi oh junior manya wai junior da mata, kuma matar ma ni, tab! Zansha aiki da shagwabar junior ga tsirfa iri iri, ga shi shagwababbe komai mom komai mom yanzu kuwa tunda babu mom ai nice zan karbi aikin mom dolena, tashi tayi tashiga dakinta sai yanzu ta ciro kayan da anty salma ta kawo mata ganin junior ne mijin ya sata fara amfani da kayan, tana sha aranta tana cewa wannan shagwababben ma me zai iya, ai inajin ko irin kukan nan da ake cewa anayi a first night ni bazan yi ba saboda junior ai yarone karami ko isa auren ma bai yi ba amma SANADIN GATA yasa aka yi masa yanzu, kayan ta duddura acikinta sannan ta tashi ta shiga kitchen, hmm nidai ummi A'isha ban raina junior ba ehe.

Gidan mom junior ya shiga cikeda farin ciki yana zuwa ya tarar da ita zaune akan dining taci kwalliya sosai tana yin breakfast, good morning mom ya fada yana murmushi, morning my boy, karasawa inda mom take yayi yai mata kiss a kumatu, mom bari naje filin kwallona nadawo, ho junior ba za dai ka hakura da kwallo ba ko? Murmushi yayi mom ko nadawo nan gidan ne naga dad baya nan mun barki ke daya, a'a junior ni ai haka yafi min dadi ganin kaima da gidanka sai dai kazo min yawo, ya amaryar taka? Lfy lau mom,fita yayi zuwa filin kwallonsa ya fara wasannin motsa jiki.

A bangaren kuluwa kuwa yau jinta take wasai wasai, kitchen ta shiga ta soyawa junior dankali da kwai kuma tayi masa miyar tunanin inda za asamu koko tafara gashi rana tayi anya za asamu koko kuwa? Daya daga cikin ma'aikatan gidan ta aika ko  za asamu, cikin sa'a aka samo agurin wata inyamura, fari tas dashi gashi yayi kauri, yawwa nasan junior yau zai yi murna ganin na samo masa koko, wanka taje ta dauka tafito ta shirya cikin leshi mai kyau tana zama junior ya shigo, sannu da zuwa, dadi yaji wai yanzu shi ake yiwa sannu da zuwa, wai shine da mata kuma nan da kankanin lokacin zai zama baba, yawwa sannunki, sai dai ba kayi sallama ba, oh sorry mantawa nayi, komawa yayi da baya ya sake shigowa Assalamu alaikum, wa alaikumus salam warahamatullah ta fada tana murmushi, ga breakfast din naka, to bari nayi wanka, dakinsa ya wuce yayi wanka ya fito sanye da gajeren wando da yar shirt, kan kujera ya zauna ya jawo abincin ya fara lakuta ita dai kuluwa tana zaune tana kallon ikon Allah,gashi ganinsa da gajeren wando sai duk taji kunya ta kamashi domin ko cinyarsa wandon bai rufe ba,

ga fa kokon nan nasa an siyo maka, kallonta yayi sai kuma ya fara dariya, abin yabata mamaki ganin junior yana ta dariya, wai kokon aka siyo min? Eh tabashi amsa, a ina aka siyo? Acan unguwar ne,to ki dauke kayanki dan ba sha zanyi ba, kaifa kace kana son shan koko, eh ni nace amma ba wannan ba, daukar flask din kokon tayi tafita zuwa kitchen bin bayanta yayi da kallo yana murmushi, lallai jiddana baki fahimci kokon da nake nufi ba amma hakan ya burgeni da alama nine zan sanar dake kokon yadda yake, abincin ya rufe ya dau wayarsa ya fara chaten da bobo da teemah anan yake sanar mata yayi aure, yana nan zaune har 1 tayi ita kuma kuluwa tana cikin kitchen tana yi masa girkin rana, lokacin data gama ta fito yana kwance yana bacci gashi anata kiran sallar azahar, kusa dashi taje ta fara tashinsa, junior, junior, junior, ko motsi bai yi ba, hannunta yana rawa tafara dan dukan kafadar sa junior ka tashi, uhm yayi juyo sannan ya tashi, bakayi salati ba junior, salatin yayi yana murmushi, katashi kaje masallaci karka makara, tashi yayi ya nufi dakinsa yaje yayi alwala ya fito tana tsaye afalon sai nadawo, to kayi addu'ar tafiya masallaci fa kasan akwai zikirin da akeyi lokacin da ake tafiya masallaci sannan idan za ashiga masallacin ma akwai addu'ar da ake yi, kuma da kafar dama ake shiga, meye dama left? No right ta fada tana murmushi ok tnx nagane, fita yayi akaro na farko don zuwa masallaci saboda shi sallar ma ba yinta yake ba balle har yasan wasu dokokin zuwa masallaci, lallai duk jahilcin miji indai matarsa mai ilimi ce to ya tsira saboda ko babu komai yaransa zasu tashi cikin tarbiya shiyasa fiyayyen halitta yayi umarni da a auri mai addinin domin tafi lasting kar aduba kyal kyalin fuska.

Bayan ya dawo daga sallar ne kuluwa ta gabatar masa da abincin rana, nifa kinga bana son tafarnuwa kuma bana son gishiri da yawa sannan bana son yaji, indai akwai daya daga cikin wadannan a abinci to bana iya ci, kallonsa kuluwa ta fara yi, junior ba dai iyayi ba, komai nasa a kididdige yake, to yanzu dai kaci kaji, bani aron wayarka zan kira anty salma, a ina anty salman take? A sharada to bari nagama sai muje gidan nata kodai kinfi son kuyi wayar? A'a muje din idan ka gama ta fada cikeda murna.

5⃣0⃣
Cikeda murna ta shige dakinta tafara shiryawa ta sake kwalliya ta fesa turare ta fito, lokacin ya gama cakular abincin sa, tashi yayi suka fita, acikin motarsa Lexus suka fita suka nufi sharada, itace ta rinka nuna masa hanyar har suka shiga kwanar gidan, kin tuna nan wurin lokacin da na watsa miki kwata, dariya kuluwa tayi tayaya zan manta wannan wurin, murmushi yayi aransa yace ina sonki Jidda sosai amma kin kasa ganewa, gidan suka karasa suka shiga ummi na zaune a falo tana karatu, ganinsu yasata tashi ta rungume kuluwa hawwa har kin fara fita, daidai lokacin anty salma ta fito a'a yau amare ne agidan, ita dai ummi kuluwa taja zuwa dakinsu na da, suka bar anty da junior a falo, suna shiga ummi tace hawwa wannan fine guy dinne mijin dama? Eh shine fighting partner dinnan nawa fa? Tafawa suka yi da ummi, to ya ake ciki? Komai ya faru ko?? Dariya kuluwa tayi babu abinda ya faru ummi saboda kin ga bai ma wani jima da dawowa ba fa, kuma still he's young, kut ai young din sunfi bada wahala banza, tab duk ranar da wannan gayen ya kamaki ina tausaya miki dan bazai kyaleki ba sai ya fasaki wlhi, hararar ummi kuluwa tayi dalla malama bari yimin fatan tsiya, ni yanzu ma kayan nan nake son akaro min dan wlhi wadancan sunyi min kadan, haba? Ummi ta tambayeta, Allah kuwa kifadawa anty akaro min wasu, anya kuwa hawwa junior bai fasaki ba? Ke sai kiyi kuma inma abinda yafi fasani yayi ai matarsa ce, eh ni dama bance ba tasa bace,amma junior yafi karfinki, wlhi kinji na rantse miki wancan gayen sai ya saki kuka duk ranar da kuka hadu, kin manta ihu zai sani ba kuka ba, eh ihunma ai zakiyi, hmm hawwa matan aure naga alamar junior bai baki feeling ba har yanzu, anty salma ce ta shigo hawwa to ki fito ku tafi ni ko gaisawa ba muyi ba sai da dan nawa muka gaisa, fitowa sukayi kuluwa tana cewa anty yi hakuri wannan ummin ce duk ta hanani sukuni, yawwa anty wai akara mata wadannan kayan, to kya kai mata shidai Junior yana jinsu amma bai gane wadanne kayan bane.

Har bakin kofa inda motarsu take su anty salma suka rakosu daga nan jan bulo ya kaisu gidan mom dinsa, suna zuwa taga yaje ya rungume mom hadida kwanciya ajikinta, murnar ganin kuluwa mom ta fara, hawwa sannu da zuwa nan da nan aka cikasu da kayan cima iri iri, lallaba junior mom ta fara ta bashi fruits ya dan ci dakyar ita dai kuluwa duk abin ya zame mata Sabo lalle junior dan gatan mom ne, tashi yayi yashige dakinsa ya kwanta, ita kuma kuluwa da mom suna yar hira lokaci lokaci.

Sai bayan sallar isha sannan suka koma gidansu, lokacin da suka shiga kowa dakinsa ya wuce, wanka kuluwa tayi tasaka rigar bacci ta dora rigar sanyi asama saboda sanyin da akeyi ta kwanta bayan jikinta ya karbi turarruka masu kamshi. Shima junior kwanciyar yayi sai dai sanyi ya hanashi sakat shi kwata kwata basa shiri da sanyi, kaje gurin matarka kasha dumi kawai zuciyarsa ta bashi shawara, tashi yayi yafita a hankali ya tasamma dakin kuluwa wadda ita tuni lokacin ta dan fara bacci, a nutse ya bude kofar ya shiga tana tukunkune da alama itama sanyin yana shigarta kuma ya ratsata, bargon ya yaye ya hau kan gadon daukartar yayi cancak ya dorata a samansa yaja bargon ya rufesu tun shigowarsa kuluwa ta farka amma sai taki bude idonta, wata irin runguma yayi mata wadda ta kusa sakata shidewa domin gaba daya kankameta yayi jin dumin baya shigarsa yadda yake so yasashi cire rigar sanyin da tasaka yabarta daga ita sai yar sleeping dress wadda da ita gara babu amma da yake duhu ne baya ganin jikin nata, lamo kuluwa tayi ajikinsa tana shakar daddadan kamshin turarensa na special man, shi duk a tunaninsa bacci take, bakinsa yasa yayi kissing din gashinta, goshinta, da kumatunta, sai jujjuyata yake akansa kamshin turarensa da nata turaren sun hadu sun bada wani kamshi na musamman, hannunsa yasa ya zagaye kugunta yana sake motsata ajikinsa yadda zai kejin dukiyar fulaninta akan kirjinsa, hannuwanta ta dora akan kirjinsa ta sake cusa kanta cikin kirjinsa sosai tana shakar kamshinsa ji take kamar ta kama bakinsa ta tsota amma kuma tana jin kunya, kamar yasan abinda take so, ji tayi ya dago kanta ya hada bakinsa da nata ya fara tsotsarsa a hankali kamar ta tayashi amma sai ta fasa sai shi kadai ke kidanshi yake rawarshi, alhalin itama tana so, sai dai abinda ya tayar mata da hankali shine tana off, tun jiya tafara fashin salla kar kuma ko junior ya shirya yin harka a wannan daren bayan ita kuma akwai matsala, wani irin numfashi taji yana fitarwa wanda ke sauka akan hancinta, murginata yayi ta koma kasa ya haye samanta, abin mamaki sai bataji nauyinsa ba ko kadan, bakinshi ya sake mannewa da nata tareda zame rigar baccinta ya rungume ta sosai, ahaka bacci ya daukeshi yana kankame da ita bakinshi cikin nata domin anashi tunanin har yanzu ita bacci take bata san abinda ake yi ba, ita kam kuluwa tafishi morewa saboda wani ni'imtaccen dumi taji yana ratsata, duk wannan sanyin da ake zurawa ta nemeshi ta rasa sai dumi mai dadi da yake shigarta dumin jikin junior ga bakinsa kuma hade da nata, saboda jin yanayin da bata saba shiga ba yasata kasa yin bacci sai junior ne keta sharar baccinsa, can cikin baccinsa yakai hannu ya dafe na fulaninta guda daya, wani zimmm taji kamar an saka mata wayar nepa dan shock din da taji, baccinsa yayi mai ni'ima har asuba tayi,karar agogon da kuluwa ta saita ne ya tasheshi, bakinsa ya cire daga cikin nata ya dauke hannunsa daga kan na shanunta sannan ya kai bakinsa kai ya goga harshensa ya tashi ya mayar mata rigar tata ya zira mata ta sanyi ya lullubeta ya fita, duk kuluwa najin sa, wani lafiyayyen sanyi taji ya fara kunno kai cikin dakin kun san sanyin asuba yanda yake, bargon ta nunka gida biyu ta rufa amma duk da haka a banza jikin junior yafi komai bata dumi, shima junior duk da sanyin da yake ji haka ya daure yayi alwala da ruwan zafi yafito acikin sanyin ya nufi masallaci. 


Post a Comment

Previous Post Next Post