Header Ads

Amurka ta kera Irin jirgin Annabi Nuhu'

<


Ma'aikatar kirkire-kirkire ta Amurka, ta kashe tsabar kudi har Dala miliyan 100 wajen gina wani jirgin ruwa kwatankwacin irin na Annabi Nuhu, bisa dogaro da yadda aka siffanta shi a littafin Injila.
Wasu hotuna  sun rinka kai-komo a kafafen yada labarai da na shafukan sada zumunta, a 'yan kwanakin nan dangane da wani jirgin ruwa da aka gina, sun haddasa wata mahawara a tsakanin mutane a arewacin jihar Kentucky ta America, abin da kuma ya yi nuni da irin yadda al'umma ke neman kariya daga wasu bakin al'adu da ba sa so.
Hotunan katafaren jirgin da aka gina domin kwaikwayon Jirgin Annabi Nuhu wanda ya cinye kimanin Dala miliyan 100, kwatankwacin Fam miliyan 77, sun zama abubuwan da za su sanya mutane su yi duba ga irin dimbin basirar da Allah ya huwacewa wani Ba-Amurke masanin hikayoyi, a karni na 19, mai suna Edward Hicks.
Shi dai wannan mutum yana da tunani daban da na mutane kan yadda tarihin Jirgin na Annabi Nuhu ya zama wani abin da zai zaburar da mutane wajen kirkire-kirkire a wannan zamanin.

Jirgin wanda aka yi dai-dai da yadda aka siffanta shi a littafin Injila wanda ya ba da labarin irin yadda Allah ya shaidawa Annabi Nuhu cewa zai saukar da Ruwan Dufana da zai halakar da mutanen wancan zamanin saboda irin laifukan da suke aikatawa.
Yana da girman kimanin kilomita 137, da kuma tsawon kimanin kilomita 23 haka kuma yana da fadin kilomita 14.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.