Header Ads

Ba zanyiwa Atiku Kanfen ba - Obasanjo

<


Tsoahon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya roki yan Nigeria akan suyi amfani da hankali da tunanin su a lokacin babban zaben 2019, domin kuwa shi bazai yiwa wani dan takara kanfen ba.

Obasanjo ya fadi mwannan magana ne a jihar Osun a taron 27th annual Owu National Convention. Yace dole ne yan Nigeria su zafi shugaba wanda ya cancanci ya jagoranci al'umma kuma ya kaisu zuwa wani mataki na ci gaba.

Ya kara da cewar adalin sugaba ne kadai zai iya kawo wa kasa ci gaba, saboda lallai akwai bukatar yan Nigeria suyi aiki da hankalinsu a yayin zaben shekara 2019.

Obasanjo ya fada yayin da yaka magana da yaren Yarabanci yace "Wannan ba taron siyasa bane, amma zamu iya yin maganar siyasar atakaice. A shekarar data gabata, munyi wannan taro a jahar Ibadan. Gashi kuma wannan shekarar muna yinshi a jahar Osun. Shekara mai zuwa kuma zamu iya muyi a jahar Kwara saboda muna da mutanen Osun a jahar Kwara. "

"Babban zabe yana nan yana karatowa, Ku bude idanuwan ku kuyi zabe da hankali. Ku zabi jamaiyar da baza ta sakaku a cikin matsin rayuwa ba."

A cikin sharhin da Olowu na yankin Kuta, wanda shine Chairman na Supreme Council of Owu Obas, Oba Hammed Oyelude, yayi kira ga mutanen garin Owu da su shiga harkar siyasa domin su bada tasu gudun mawar a wajen ciyar da kasa baga.

Haka kuma yayi kira ga mutanen garin Owu da su marawa yan takarkarun da suka kasance yan asalin garin Owu baya a kakar zabe ta 2019.


No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.