Filin Yakin Nigeria : Mutum 6,562 ne suka mutu acikin wata gomashadaya na Wannan Shekarar

<


Daga Clifford Ndujihe


     Yanzu muna cikin sati hudun karshe na shekarar 2018, inda dayawan yan Nigeria suna shirin yin bankwana da shekarar 2018 domin tarbar shekarar 2019.

Shekarar 2018, ta kasance shaekarar kashe kashen rayuka da zubar da jinin al'ummar kasar Nigeria domin kuwa babu wata jaha kwaya daya da wannan iftila'i bai shafaba.Saboda haka Nigeria za'a iya kiranta da kasa da ta kasance a cikin kashe kashen rayuka da fituntinu a shekarar 2018 ta yanda har sama da mutum dubu shida da dari biyar da sintin da biyu suka rasa rayukansu. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa wadannan mutanen da suka rasa rayukansu, sun mutune ta hanyar yankan rago da kungiyar boko haram tayi musu, wasu ta hanyar fadan manoma da maliyaya, da fadan kabilanci, Da yan garkuwa da mutane da kuma aiyukan yan fashi da makami.Yankunan da wannan rikici yaci shafa sune Arewa ta tsakiya, Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, musamman a jahohi irinsu Barno, Zamfara, plateau, Kaduna, Kogi, Benue, Nasarawa, da kuma Taraba wacce anan ne rikicin yafi tsamari.

Wadanda kisan ya hada dasu sun hadar da fararen hula da kuma jami'an tsaro.

A cikin sati goman farko na wannan shekara da muke bankwana da ita, an rawaito cewa mutane sama da 1,351 ne suka rasa rayukansu.

A watan Janairu na wannan shekarar, mutum 676 ne suka mutu, sannan watan faburairu inda mutum 517 suka rasa rayukansu, sannan watan Mach 485, Aprilu 670, Mayu 508, June 639, July 257, Agusta 363, Satumba 926, November 388.


Mayakan kungiyar Boko haram


Wadannan mace mace sun sanya Nageria ta zama daya dagac cikin kasashen da fitinir yan tada kayar baya ta shafa. Sanarwa ta fito daga Global Terrorism Index GTI, cewa Nigeria itace kasa ta hudu a yawan mace macen jama'a sakamakon fitinar yan tada kayar baya. A shekara ta 2016, GTI ta fadi cewar mutum 2,164 ne suka mutu a Nigeria dalilin fitinar yan Ta'adda.


Read more at: https://www.vanguardngr.com/2018/12/nigerias-killing-fields-6562-deaths-in-11-months/

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.