Header Ads

Malcom ba zai bugawa Barcelona wasa ba

<

Dan wasa Malcom zai yi jinyar mako biyu, sakamakon rauni da yayi a kafarsa.
Barcelona ta sanar da cewa Malcom zai yi jinyar kwana 10 zuwa 15, sakamakon rauni da yayi a karawar da kungiyar ta doke Cultural Leonesa a Copa del Rey a ranar Laraba.
Sakamakon haka dan kwallon Brazil din ba zai buga wa Barcelona wasan da za ta yi da Tottenham a gasar Zakaraun Nahiyar Turai ba.
Haka zalikan Malcom ba zai kuma buga wa Barcelona karawar da za ta yi da Espanyol a gasar La Liga a ranar Asabar ba.
Tottenham za ta ziyarci Barcelona a ranar Talata a gasar cin kofin Zakarun Turai da burin yin nasara a Campiyon, domin ta kai zagayen gaba a wasannin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.