Header Ads

Caoch din Barcelona ya karyata maganar komawar Neymar Barcelona

<


Ernesto Valverde ya dage cewa Neymar bai kirashi a waya ya rokeshi akan son ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ba.

El Mundo ya ce a wannan makon ne mahaifin Neymar ya roki Barcelona akan su maida dansa - wanda ya koma Paris Saint-Germain a kan fan miliyan 222 a shekarar 2017.

Mahaifin na Neymar dai ya karyata wannan zancen cewa shi bai kira hukumar kwallon kafa ta Barcelona ya roki su maida dan shi kungiyar su ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.