FADAKARWA: Abin Bakin Ciki da Takaici by Comrade Isma'il Auwal (Ismaga)

<

Abin bakin ciki da Takaici

Wallahi wallahi saida na zubar da hawaye da ina kallo da sauraren ziyarar dasu Aminu daurawa suka kai fadar kwankwasiyya. Har yanzu ina kan ra'ayina nacewa ba kuskure bane malamin addini koma wane irin Addini ne ya shiga siyasa, dukda kunce bamu da kishin Addini, ku da kuke da kishin Addinin haka kukeso malamai su koma ? Wannan itace irin siyasar da kukeso malamai su shiga ? Su dinga bibiyar yan siyasa ? Su zama yaransu da 'yan aikensu ?

Duk da Mallam Aminu daurawa da Dan uwansa Dr. Sani Ashir sun bada amsar wasu daga cikin tambayoyin danayi na cewa wai shin shi kwankwason nan bashida Alheri ne da kullum sai dai muji amo da sauti na rashin dai dai dinsa ? Mallaman guda biyu sun gaya mana kokarin da jagoran kwankwasiya yayi wajen kafa hukumar hisba, tallafawa auren zawarawa, gaddamar da shari'ar musulunci dss.

Mallam Aminu Daurawa yayi kokarin nunawa jagoran kwankwasiya kuskuren da yayi a maganganunsa amma sai yayi kwana, munji inda Dr. Sani Ashir yake cewa tsagin Malaman da basa tare Kwankwaso sunayine saboda Bukatun kansu, da ikirarin da yayi na cewa wasusunsu alkawari aka yimasu, kai har nunawa yayi su jahilai ne saboda yace ko littafin akhdari wadansu basu gama fahimta ba.

Haka kukeso Malaman namu su zama yaku wadanda kuke tunanin kunfi kowa kishin Addini, wanda kuke tunanin muda bamu da fahimta irin taku jahilai ne ? Wlh idan wannan shine rashin kishin Addini ku cigaba da yawo da sunayenmu a gari, ku cigaba da kiranmu jahilai hakan bazai taba yima mana ciwo ba.

Amma wallahil azim indai malaman Addini suka cigaba da tafiya a haka lokaci zaizo da Addinin da kuke cewa kuna kishi zai zama bashi da kima ko mutunci a idon kowa. Soyyaya itace idan mutum yayi ba dai dai ba a fada masa gaskiya, ba wadda yace malamai basa kuskure ko akwai ?

Mu ba 'yan jam'iyar siyasa bane, duk wanda yayi zamu fada.

Ismail Auwal
Cikin fushi da bacin rai
Daga kan katanga

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.