Mutane 3,187,988 ne suka cancanci kada kuri'a a jahar Katsina - REC

<


KATSINA - Hukumar zabe ta kasa, INEC, Kwamishinan zabe a jihar Katsina, Jibril Ibrahim Zarewa, ya ce katin zabe wato PVC guda 3,187,988 aka rarraba a jihar ta Katsina.

Zarewa ya ce, adadin 3,187,988, ne ke daidai da kashi 98 cikin dari, daga cikin masu kada kuri'a 3,230,000 a jihar. Kwamishinan ya kuma ce a kwai katinan zabe guda 63,939 da masu su basu karba ba, sakamakon haka za a kai su Babban Bankin Nijeriya, CBN domin a ajiyesu a can.


 Yace:
 "A Jihar Katsina akwai mutane 3,230,000 wadanda a cikinsu akwai masu rijistar zabe  da yawansu ya kai 3,187,988 wanda ke dai-dai da kashi 98 cikin dari na mutanen Katsina."


Tushen labari:
https://www.vanguardngr.com/2019/02/3187988-sauran-malora-to-vote-in-katsina-rec/

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.