Header Ads

Wanne siddabaru yan siyaysa suke yiwa yan Nigeria?

<


Fiye da mutum miliyan 84 suka yi rajistar yin zabe, wadanda ake sa ran za su kada kuri'unsu a zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasa cikin watan Fabrairu, yayin da za a zabi gwamnoni da 'yan majalisar dokoki a daukacin jihohi 36 cikin watan Maris.

Akwai 'yan takarar shugaban kasa saba'in da uku, wadanda suka hada da Shugaba na yanzu Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki da babban mai kalubalantarsa, Atiku Abubakar, na jam'iyyar hamayya ta PDP.

Bisa tsarin zaben, hanya mafi sauki a Najeriya ta samun nasarar cin zabe ita ce samun rinjayen kuri'u.

Sai dai a zaben shugaban kasa, ko da dan takara ya samu adadin kuri'u mafi rinjaye, yana bukatar akalla kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a akalla biyu-bisa-uku na daukacin jihohin kasar.

An fara hada-hadar yakin neman zabe, inda 'yan takara da jam'iyyu ke bullo da dabaru iri-iri kuma su ke amfani da su.

Baya ga manyan tarurrukan jam'iyyun siyasa da manyan allunan tallata manufa da hotunan 'yan takarar jam'iyyu, tare da tallata muradun takara a kafofin yada labarai, 'yan siyasa na amfani da dabaru da dama, a wasu lokuta akan kirkiro sabon salo, bambarakwai ko na barkwanci don jan ra'ayin masu kada kuri'a, wadanda suka hada da:
1. Kyaututtukan jan ra'ayi:

'Yan siyasa da dama a Najeriya kan samar da kyaututtukan jan ra'ayi kamar huluna da riguna da litattafan rubutu da mayafai da tabarau da sauransu.

Irin wadannan kyayyaki sukan kasance dauke da hotunan 'yan takara, da tambarin jam'iyya, tare da wasu rubutattun bayanai.

A kan raba irin wadannan kayayyaki ga 'ya'yan jam'iyya da masu yin zabe a wajen yakin neman zabe, wadanda alal misali idan suka sanya guntuwar riga ko huluna zuwa wuraren da suke aiki ko suka rika kai-kawo (a unguwanni), ta haka ne kai tsaye ko a fakaice za su tallata wadannan 'yan siyasa kafin a gudanar da zabubbuka.

A bangaren masu kada kuri'a kuwa, wasu masu yin zabe sukan cika da farin ciki ko alfaharin mallakar irin wadannan kyaututtukan jan ra'ayi.

    Kun san gwamnonin da suka mulki Kano?
    Da gaske Olivier Giroud zai bar Chelsea?
    Kun san jaruman da ba sa amfani da shafukan sada zumunta?

2. Kabilanci da Addini:

Najeriya ce kasa mafi yawan jama'a a Afirka - kimanin mutum miliyan 200 - da kabilu daban-daban da kuma addinai. Kabilanci da Addini da yanki daukacinsu al'amura ne masu matukar tasiri a siyasar Najeriya.

Don haka, 'yan takarar mukaman siyasa a kodayaushe sukan yi kokarin jan ra'ayin masu yin zabe ta amfani da kafofin da ake da baraka a tsakanin al'uma.

Daya daga cikin wadannan dabarun da suke amfani da su ita ce danganta kawunansu da kabilu daban-daban da kungiyoyin addini a sakonnin yakin neman zabensu, tare da nuna alamu.

Misali, a Kirsimetin da ta wuce, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda yake Musulmi ne, kuma yake neman a sake zabensa karo na biyu, an ga hoton bidiyonsa yana aikewa da sakon wakar fatan alheri ga mabiya addinin Kirista don murnar Kirsimeti.

Al'amari ne da ba a saba gani ba Buhari yana rera waka a bainar jama'a, kuma bai taba fitar da irin wannan waka ta kirismeti ba.

kodayake dai sakon fatan alheri ne na Kirsimeti, wannan bidiyo ya haifar da dimbin ce-ce-ku-ce saboda lokacin da kuma kasancewar abin 'ba-sabon-ba', inda 'yan Najeriya da dama suka yi ta cewa kalaman sun yi kama da na jan ra'ayin siyasa don samun goyon bayan Kiristoci a zabubbuka.

An ga Buhari a bidiyon da mataimakinsa Yemi Osinbanjo da Shugaban Jam'iyya Adams Oshiomole.
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kuma a Disambar da ta gabata a taron yakin neman zabe na dan takarar babban jam'iyyar adawa, Atiku Abubakar, a Jihar Sakkwato, jiha ma dimbin musulmi, wani hamshakin dan majalisar Dattijai da ke goyon bayan Atiku, Dino Melaye - wanda Kirista ne, ya yi yunkurin karanta wasu ayoyi daga Alkur'ani Mai Girma don jan ra'ayin mahalarta taron.

Dangane da kabilanci da al'ada kuwa, 'yan siyasa sukan sanya tufafin gargajiyar kabilun al'ummomi daban-daban, musamman lokacin da suka je wajen al'ummomin yakin neman zabe

Ba abin mamaki ba ne a ga dan takarar shugaban kasa Bahaushe-Bafulatani daga Arewacin Najeriya sanye da tufafin gargajiyar kabilun Igbo ko Yarbawan da suke a yankin Kudanci, kamar yadda shi ma Bayarbe ko dan kabilar Igbo za a ga ya sanya tufafin Bahaushe ko na Bafulatani a lokacin yakin neman zabe.

Sukan yi hotunan takarar yakin neman zabensu sanye da tufafin kabilu daban-daban. 'Yan siyasa da dama sukan yi amfani da irin wannan dabarar yakin neman zaben don su kulla alaka da mabiya addinai da kabilu daban-daban da suka bambanta da nasu.
3. Halartar tarurrukan al'umma:

Ana yawan sukar 'yan siyasar Najeriya kan nesanta kansu da talakawansu, wasu ma har shafe watanni ko shekaru suke yi ba tare da sun ziyarci al'ummarsu ba. To amma ba sa yin sakaci wajen kai ziyara da zarar an shiga hada-hadar yakin neman zabe.

Lamari ne da aka saba da shi a ga 'yan siyasa suna halartar tarukan al'umma ba kakkautawa - ko da ba a gayyace su ba lokacin da zabe ya karato.

Cikin sauki za a gan su suna mu'amala da talakawa a wajen bukukuwan aure da tarukan addini da sauransu. A lokuta da dama, sukan bayar da gudunmuwa, har ma su bayyana ra'ayinsu na siyasa.

Wannan wata dabara ce ta tallata kansu ga masu yin zabe. 'Yan siyasar Najeriya da dama sukan yi amfani da damar da aka samu sanadiyyar bunkasar kafafen sadarwa na shafukan intanet, wajen aikewa da sakonnin taya murna ko na jaje ga daidaikun mutane ko al'ummomi. Sai dai da zarar an kammala zabubbuka sai a ji shiru.
4. Zayyanar kawata ababen hawa:

Wata dabarar 'yan siyasar Najeriya ta jan ra'ayin masu zabe, ita ce yin zayyanar kawata ababen hawa da hotuna da tambarin jam'iyyarsu.

Wadannan ababen hawa akan bai wa magoya baya su yi ta hawa suna kewaya gari da zuwa tarukan yakin neman zabe. Wadannan zane-zanen fenti bambarakwai a ababen hawa sukan dauki hankalin mutane, tare da tuna wa masu kada kuri'a cewa wane ko su wane na takara.

Mafiya yawan lokuta akan daura wa irin wadannan ababen hawa amsa-kuwwa su yi ta sakin rugugin sautin wakokin yakin neman zabe da ke yabo ko yaba kimar 'yan takara da jam'iyyarsu.

5. Tasirin harkar nishadantarwa:
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar tare da Sani Danja

Harkar fina-finai da kade-kade da raye-raye ta Najeriya na dada bunkasa, ta yadda taurari a cikin harkar ke da matukar tasiri a tsakanin masu sha'awar wasanninsu.

Tun daga kan harkar fina-finai ta Nollywood da ta kafu a Kudancin Najeriya zuwa Kannywood - ta fina-finan Hausa da ta kafu a Arewacin kasar - taurarin fina-finai da dama sun zama jigajigan jan zugar yakin neman zabe kafin a gudanar da zabukan shekarar 2019, kuma sun alakanta kansu da 'yan siyasa.

Su ma mawaka ba a bar su a baya ba, inda ake damawa da su a hada-hadar yakin neman zaben. Misali shahararrun 'yan wasan fim din Hausa irin su Sani Danja da Maryam Booth sun fito karara sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Yayin da su kuma taurari kamar Ali Nuhu da Adam Zango da mawaki Dauda Kahutu, wanda ya shahara da lakabin Rarara ke goyon bayan a sake zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wani mawakin Davido tuni ya mara wa jam'iyyar adawa ta PDP baya.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shahararren mawaki Davido lokacin da yake wasa a wurin taron kamfe

'Yan siyasa kan saka irin wadannan shahararrun 'yan wasa a rukunin masu fafutikar yakin neman zabensu don jan ra'ayin masu zabe, musamman masoya 'yan wasan.

6-'Yan koren shafukan sada zumunta:

Babu tababa shafukan sada zumunta na intanet kafofi ne masu karfin gaske da 'yan siyasa ke amfani da su a irin wannan lokaci.

'Yan siyasa kan dauki matasa 'yan korensu don su yi masu yakin neman zabe a shafukan sada zumunta na intanet wato kamar su Facebook, Twitter, WhatsApp, Youtube da makamantansu, ta hanyar yada sakonnin da ke dauke da manufofin 'yan siyasar.

7. Raba kudi:

Siyasar kudi na daya daga jiga-jigan al'adun da ke da tasiri a siyasar Najeriya.

Akan ga wasu 'yan siyasa ko 'yan korensu a garuruwa da kauyuka suna watsa kudi inda su kuma talakawa kan yi ribibi ko wasoso.

A wasu lokutan a kan hango 'yan siyasar sun daga wa mutane hannu daga cikin motocinsu ta saman rufi ko ta taga, suna watsa kudi, yayin da masu yin zabe ke jinjina musu, tare da turereniyar karbar kudi.

Sukan kuma dan dumbuzo kudi su raba wa masu kada kuri'u a mazabunsu, musamman a karshen yakin neman zabe wato lokacin da ake gab da zuwa rumfuna don kada kuri'a- kai har ma ana zargin cewa ana yin rabon kudin a lokacin zabe.

Wani abin lura shi ne, rahotanni sun nuna cewa, wasu masu yin zaben da ke fama da talauci in an yin rabon kudin ba sa samun abin da ya kai Naira 700 don jan ra'ayinsu su zabi dan takara. Wasu kuma na sayar da kuri'unsu kan kudin da bai taka kara ya karya ba.

Wata dabarar da ta yi kama da rabon kudi, ita ce ta rabon kayan abinci. 'Yan siyasa na raba kayan abinci kamar ledar taliya ko mudun shinkafa ko gishiri da makamantansu ga masu kada kuri'a. Irin wannan dabara ta zama ruwan-dare.

Har ta kai ga su kansu wasu 'yan siyasar sun fara sukar wannan al'ada.
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamar tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben shekarar 2015, kwanakin baya a wajen kaddamar da littafinsa mai suna "My Transition Hours" ma'ana ''Karshen Mulkina'' Mista Jonathan ya ce,

"Sayen kuri'u na kasancewa abin kunya ga Najeriya. Mun san cewa akwai dabarar na ta bai wa masu zabe abin hasafi, al'amarin da mafiya yawan kasashe ke kokarin shawo kansa.

"A dukkan kasashen da na je aikin sa'ido a zabubbuka, bai wa masu zabe abin hasafi kawai, babban laifi ne.

"Amma a nan Najeriya, muna daukar bayar da abin hasafi a matsayin wani bangare na tsarin zabenmu. Abin da nake nufi da bai wa masu kada kuri'a abin hasafi shi ne a lokacin zabe mukan debo shinkafa da gishiri da hoton dan takara da tambarin jam'iyya mu raba wa mutane.

"Wannan ba daidai ba ne bisa mizanin inganci na kasashen duniya. Ban san haka ba, har sai da na shiga aikin sa'ido a zabubbuka".

Kodayake, masu lura da lamura na bayyana cewa siyasar kudi ta ragu kafin gabanin zabukan 2019, in an kwatanta da zabukan da suka gabata, to amma har yanzu matsalar ba ta kau ba.

8. Alkawuran mukamai:

'Yan siyasar Najeriya kan yi dabarar alkawuran bayar da mukamai wadanda ba su da tabbas inda masu takarar mukaman siyasa kamar na shugaban kasa da gwamnonin jihohi kan yi alkawura bai wa wasu mutane ko wasu yankuna mukamai.

Wato za su bayar da mukaman siyasa ga 'yan wata kabila ko wani yanki matukar aka goya musu baya suka samu kuri'un da suka kai su ga lashe zabe.

Irin wadannan alkawura marasa tabbas ba su tsaya kan nadin mukamai ba, har ma a wasu lokutan wasu 'yan siyasar kan kara da alkawarin mika mulki kacaukam ga wata kabila ko wani yanki a karshen wa'adin mulkinsu.

Ana yin irin wadannan alkawura marasa tabbas ne don juya akalar kuri'un wata al'umma ga 'yan takarar ko kuma jam'iyyarsu.

Yanzu dai abin da babu tabbas shi ne ko irin wadannan dabaru bambarakwai da 'yan siyasar Najeriya ke amfani da su wajen jawo hankalin masu kada kuri'a za su yi tasiri a zabukan bana - kamar yadda suka yi a zabukan shekarun baya- ko kuwa ba za su yi ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.