Header Ads

Zabe: An kama samfurin takardun zabe buhu buhu a jahar Jigawa!

<


Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa 'yan sanda sun kama wasu takardun kada kuri'a na gwaji da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa domin yin magudin a babban zaben da za ayi a gone.

Batun dai ya janyo takaddama a tsakanin jam'iyyar PDP da ta APC a jahar jigawa kan abinda ake shirin yi da takardun.

Wakilin BBC na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama buhunhuna makare da takardun kada kuri'a na gwajin, da aka ce za a kai su jihar Jigawa ne da ke makotaka da kano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano muhammad wakili shi ne ya yi karin bayani kan takardun da aka kama.

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce tsakanin jam'iyyar PDP da APC a jihar Jigawa.

Ita dai PDP tana zargin cewa APC ce ta buga takardun a wani mataki na yunkurin magudi.

Shugaban kwamitin matasa na yakin neman zaben dantakarar gwamna na jam'iyyar PDP a Jigawa, Umar Danjani ne ya shaida wa BBC hakan.

"Muna zargin APC ta shirya yin magudi a kananan hukumomi 17, kuma abun da ya ja hankalinmu shi ne ganin cewa buhunhuna 17 ne 'yan sandan suka kuma," in ji shi.

Mutane 3,187,988 ne suka cancanci zabe a jahar Katsina

Sai dai jam'iyyar APC ta musanta zargin cewa matakin wani yunkuri ne na magudin zabe, kamar yadda kakakin jam'iyyar Nasir dahiru Jahun ya shaida wa BBC.

"Mun buga samfuri ne don wayar da kan masu zabe kamar yadda ita ma hukumar zabe karkashin jagorancin shugabanta na kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya tara 'yan jaridu da shugabannin jam'iyyu ya yi musu karin haske kan yadda takardar kada kuri'a za ta kasance da kuma yadda za su wayar da kan mutanensu.

"Don haka wannan zargi ne mara tushe da makama, mu ba yunkurin magudi muka yi ba," kamar yadda ya shaida wa BBC.

To ko wake da alhakin buga wannan takardar wayar da kan masu zabe?

Tambayar kenan da BBC ta yi wa Garba Lawan mai magana da yawun hukumar zabe mai zaman kanta na jahar Kano.

Ya kuma ce: "Hukumar zabe ce ke da alhakin buga takardun da kuma masu sa ido kan zabe da jam'iyyu da al'ummar gari, amma ba ta yarda wani ya buga a karan kansa ba."


Tushen labari:

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.